← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 154

Sashe 69

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kanta jin takeyi yau Hakeem zai sake tabbatarda taurin ranta da kafiyarta akan duk abinda ta sakawa kahon zuqa dan haka jiran takeyi ko wace mayyar ce aka maqalawa Raheem yau saita barsa itada uwarta.

Shiru sukai tsawon mintina kowa da abinda yake gudana a cikin zuciya da kirjinsa da kansa hakama bata kuka kallansa ba sai shi dinne yake kallanta akai akai yana sake karanto tsananin kafiya da taurin ranta.

FLEET ne ya fara isowa ya shigo palon da nutsuwansa dake cikeda kamewa da mutunta kai ya kalli iyayen nasa da kowannensu ya dago ya kallesa harya isa ya zauna ya sake gaidasu a tsanake yana jin yanayin dayake dauke da wata tension a palon dayake gudana ko yake shirin gudana.

Yana zaunawa ba jimawa saiga Maamah itama iso ta zauna suka gaisa sosai da Dad din itama take taji tension din dayake gurin a jikinta dan haka tabisu suka shiru ana jiran abinda zai biyo bayan shirun.

SANAAH da Mommy ne suka iso kofar palon cikin nutsuwa da rashin sukunin zuciya sbd ganin imran a kofar shigowa babbar palon farko ta bangaren ya tabbatar musu da Fleet yana bangaren dan haka mommy ta shiga rashin sukini ita kuma SANAAH rasa kuzarinta tayi tana jin kaman zazzabi zai qara kamata dan haka tayi sanyi a gefen Mommyn har suka iso babu wanda yace komai a tsakaninsu.

Mommy ce tayi sallama tafara sako kai a tsanake bayan ta bude kofar palon kenan kallanta a dan kasa batareda ta kalli dawa dawa ke palonba bayan Fleet da suka tabbatarda yana palon shikam sbd bayan ganin imran a waje qamshinsa ya tabbatarda hakan.

SANAAH ma sako kafafunta tayi tayi tana takowa ahankali kanta a qasa batareda ta iya dagowaba sbd wanda tasan yana gurin kuma tinda ta sako kafa tayi sallama da sautin muryanta daya ratsa kunnuwansu ahankali taji saukan idanuwansa akanta dan haka ta sake riqe kanta da jikinta dake mutuwa ta qaraso ciki ta isa har inda ta saba zama gefen kafafun Dad a qasa ta zauna ahankali tareda dagowa da kanta ta fara gaida Dad ya amsa yana kallanta itace Mommy datake gaidasa itama ya amsa yana sauke numfashi mai sanyi kafin ya maida kallansa akan su Dr Mum da suka qi ko kallan inda su SANAAH din suke hadda Maamah wadda kallanta da hankalinta yake kan Dr Mum dan hanata fidda zafinta a gaban wainda bai kamata ba.

SANAAH da kanta yake qasa har lokacin bata dagoba ya kalla da Mommyn ma da itama bata dagoba ya bude baki yace

"Zainab ga iyayen RAHEEM nan daga Morocco ku gaidasu"

Mommy na jin hakan ta dago da san sauri da girmamawa ta kallesu batareda tsammanin ganin su Maamah ba dan yanda Dad ya fadesu kaman babu kowace alaqa a tsakaninsu bayan wadda aka kai yanxu.

Kasa motsi mommy tayi cikin wani irin mugun shock da mamakin daya saka bakinta rawar furta

"Maamahhhh" da wata yankewa kalamai tana dora hanunta akan na SANAAH ahankali batareda tasan tayi hakan ba sbd ganin wainda bata taba tsamanninba..

Maamah a rikice ta juyo ta kalli Mommyn idanuwanta na budewa dakyau ta ambaci "Zainab" da dan karfi tana maida kallanta da sauri a bayan mommyn ta kalli SANAAH wadda ta dago ahankali lokacin tana kallan inda aka ambaci Maamah itama cikin faduwan gaba da shock mai tsanani.

Suna hada ido da Maamah din take idanuwanta suka ciko da wasu zafafan hawaye ta bude baki cikin wani irin son fashewa da Kukan daya saka Fleet dagowa ya kalleta a tsanake batareda ya motsaba ba tinda suka shigo tace

"Maamah"

Tana fadan hakan ta taso da sauri tayo kan Maamahn wadda itama da sauri ta ware mata hannu ta rungumeta tana cewa

"SANAAH" da muryanta dake rawa.

Dr Mum datake jin kanta na neman kuncewa da sauri ta kalli Maamah tana kokarin riqe rikicewanta da tashin hankalinta tace

"Baby SANAAH din Nasir???

Gyada mata kai Maamah tayi tana cewa

"Baby SANAAH ce kuwa da Zainab gasunan a gabanmu"

Kallan Dad Dr mum tayi tana son riqe abinda yake taso mata shima ita yake kalla ta dawo da kallanta akan SANAAH wadda ayau take fara ganinta a fili ido da ido tinda Nasir yake sonta ta kafeta da ido tana ganin wata irin kamar Nasir mai karfin gaske na bayyana akan fuskan SANAAH din wadda take hana hawayenta fitowa tana kallan Maamah da tsananin kewa da mamaki.

Rikicewa Dr Mum take neman yi ta maida kallanta akan RAHEEM dake zaune har lokacin baice komaiba kaman baya gurin taga hankalinsa a kwance da wata irin nutsuwansa yana zaune yana jinsu.

Maida kallanta ta sake kan Dad wanda ya sake dagowa ya kalletan kallan da babu kowace tashin hankali ko damuwa a cikinsa ta kasa bude bakinta da yayi wani irin nauyin da duk duniya bai taba mataba hannuwanta suka fara wata irin rawa da jin kirjinta yana toshewa da azababben nauyi da tashin hankalin da batai tsammanin zata shiga ba idonta kyar akan Dad din dayake jifanta da wani kallo tace

"Me su BABY SANAAH sukeyi a nan?

"ITACE MATAR DA 'DANKU YAKE AURE,
ITACE MATAR DA KUKA KWASO JIKI DAGA WATA QASAR KUKAZO KASHE AURENTA,
ITACE MATAR DA A YANXU 'DANKU ZAI RUBUTA TAKARDAR SAKINTA YA BANI,
KUMA ITACE WADDA A YANXU ANA BANI TAKARDAR SAKINTA ZAN DAURA MATA AURE A GOBE DA WANI SBD BABU IDDARSA DA AURENSA AKANTA"

Kalamansa tareda dagowan duk wanda yake palon suka sauka idanuwansu kaf suka sauka akansa cikeda tashin hankalin daya danne ya share wanda suke ciki banda SANAAH wadda ta sauke kanta da rufe idanuwanta ahankali tana zamewa zaune.

FLEET kuwa irin kallan daya dago ya saukewa Dad din ya saka Dad din juyowa da kallansa akansa yana janyo wata takarda daga cikin file din dayake gefensa wanda na wani aikin ne ya ajiye akan table din tsakiyarsu dake palon ya sake bude baki yace

"Ga iyayenka nan hakan shine ya tadosu daga wata qasar suka xo batareda tsoron fushin Allah ba dan haka a yanxu a sauwakewa 'yata a bani ita nine na daura kuma yau nace a kunce"

Babu wanda ya iya motsawa tsit gurin yayi zuciyoyinsu na buga wani irin tsalle da tashin hankalin da basajin sun taba shigarsa bayan na rashi.

Dr Mum dataji kaman paralyse na neman kamata dan yanda bakinta yake neman juyewa da kasa furta komai kafe Dad tayi da idanuwanta da sukai jajir lokaci daya tayi tana jin babu mugun mutum daya iya kasheka daga zaune irin HAKEEM JEERAH...

Maamah jin tayi ayau Dad ya gama sakasu a inda zasu iya zarewa da iya kalamansa dan haka jajir idanuwanta sukai ta sunkuyar da kanta.

Mommy kuwa a yanzu batada kowace zabi ko ikon daya wuce wanda Dad yake dashi akan SANAAH dan haka tayi qasa dakai jikinta na tsananin sanyi kirjinta na harbawa da jiran inda hukuncinsa zai tsaya.

SANAAH kasa bude idanuwanta tayi daga rifesun datai tana kama jikinta guri daya kirjinta na nauyi mai tsanani.

Jin tsit ko numfashin kowa baya fita palon kaman babu kowa ya saka Dad kallansu daya bayan daya ya tsayar da idanuwansa akan Fleet dabai motsaba har lokacin ya dago suka kalla juna da Dad din kallan isa da ikon da kowannensu yake jin yana riqe dashi a hannunsa shi na iko da isar yana matsayin ubanta shikuwa Fleet isa da ikon shine wanda igiyoyin rayuwa da mutuwan auren suke cikin hannuwansa.

Magana Dad zaiyi Dr Mum datake neman bugawa ta wani mugun abunda takeji na masifa da barazanar samun matsala a gangar jiki da ruhi da wata sautin dayake kaman harshenta zai karye tace

"Me kake nufi da AYI SAKI??
WANE AUREN ZAA SAKI?

girgiza kai Dad yayi yana mayarda bayansa ya ginjinar a kujera yace

"Ai nasan bazakuyi amai yanzu a gabana ba kuma ku lashesa ba girmanki bane Dr"

Takardar daya aje ta kalla tana jin kaman zata hadiye zuciya ta mutu ta dauki takardar tayi wurgi da ita tareda dagowa ta kallesa zatai magana ya katseta da daure fuska sosai yace

"ABDULRAHEEM inason a aynzu ka sake auren dana daura maka banason kowane zance"
#MAMUH
09033181070
[14/05, 9:32 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

65
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
EID MUBARAK PROMO PACKAGE
Gara basa gara basa da 7500 dinki
duk wadda ta bari promo nan ya wuceta tayi hasara ba karamaba don wannan ya wuce duk tunanin ku kayan dake ciki ko 50k ka siyesu bakayi hasaraba bare 7500 hmm inba gurin Zuzeam ba wazai muku wannan gatan
1. Tabajen kankana
2. ⁠Gumbar aya da ridi
3. ⁠Tsimin mallaka mai maganin infection
4. ⁠Garin dadi har madiga
5. ⁠Hadin dafa kaza ko Ciccibi ko nama, Kinga yanzun sallah za ai nama ya wadaci kowa hajiya kina iya dafa nama tsoka 7 da maganin ki zai miki mallaka naban mammaki zai ciko miki da gaba zai kara miki dadi da dandano.

Sannan mutun ashirin na farko nada kyautar Turaren tsugunno na mallaka gagara badau 5k

Ina amaren bayan sallah wannan hadin ya dace daku ko mai jego wadda take shirin haihuwa ma Tana iya siya ta aje ko shekara yanayi bai komi
Ina Uwar gida maiji da kayanta wannan hadin nakine
08144015291 For more information say hi,
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
DAHUWAR KAZA
Kin taba cin DAHUWAR KAZA 5in1 wato Ni’ima,Matsi,Chikowa,MAllaka da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya.
INA MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku 08144015291 Zuzeam ventures.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set
08144015291
Chapter 69 · 0% Book details