← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 154

Sashe 15

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan gyara khalil yayi musu a gidan suka cigaba da zama kuma ita fatima bazata iya zuwa jeerahs ta sanar dasu ba dan itama batason kowace hulda dasu tinda babu fammah a cikinsu.

Irin zaman da sukeyi ya saka khalil fara tinanin aure dan kawo mace a gidan ya zama ba daga shi sai fatima ne a gidan ba duk da ga Nasir ya zama saurayi sosai aikin security yakeyi a wani babban hotel kafin ya fara karatun dazai cigaba da yi idan admission ya samu kenan.

ZAINAB itace kyakkyawar buzuwar amaryar da khalil ya auro ya kawota gidan suna zaman lafiya da kauna me tsanani tsakaninta da fatima wadda ta zama tamkar uwa a garesu tinda girman ya riga ya hau kanta,

Girmama Maamah fatima sosai zainab keyi kamar uwar data haifeta hakama itace uwar sirrinta,
Bayan Maamah fatima Nasir shine mutum nabiyu dayake tsananin shiri da Zainab din wadda yake cewa momy duk da kananun shekarunta dan iyakacinta tsararsa.

Shiru sukeyi wanda dole tasan rabin jikinsa dan uwansa da babu ranar da baya ambatarsa dan kuwa wani gurbi ne me girma rashin Raheem yabarsa dashi dayakejin kozai mutu gurin aikin wahala zaiyisa ya tara kudin zuwa ga RAHEEM HAKEEM JEERAH.

Shakuwar Momy zainab da Nasir ta saka damuwa da kuncinsu ragewa sosai suka maida hankali a gurin nema da gwagwarmaya da hakura da komai.

Ita kanta momy zainab da ita ake hada kudin Nasir daya sakawa ransa saiyayi aikin soja sbd Dan uwansada sukai alkawarin yin aiki daya a rayuwarsu tin yara.

*******Shekaru sun sake ja sun tafi ayau an wayi gari ADMIRAL HAKEEM JEERAH shine babba mai jagorantar familyn jeerahs kuma wanda ya sake auren wata macen bayan Fadeele ya dawo Nigeria bayan yakai matsayin karshe yayi retire,

Matarsa ta farkon bata taba haihuwaba sai ta biyun ce ta haifar masa wani 'da namijin mai suna ABDULSAMAD JEERAH wanda ya taso a cikin gata da daular arziki da dukkanin jin dadin duniya sbd mahaifinsa yana tareda su a yanzu a Nigeria yana juya manyan qasar yanda yakeso akan tsarinsa sbd kowa dakeson kasancewa tareda ahalin jeerah.
#MAMUH

GANIN IDO
1K
VIP 5K
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070
[09/05, 4:16 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

15
*_HARGITSI_*
By
*_TALATU ZAKI_*
+201031621512
*Duk maaboci kuma masoyin karatun littafin Hausa to karya wuce labarin nan bai karantasa ba sbd duk wani tsari da labari yake buqata to akwaisa tattare a cikin labarin HARGITSI Na TALATU ZAKI*🔥
https://chat.whatsapp.com/ERrtA3G4obwBQzBTiJUad3?mode=gi_t

*********
A shekarar da Nasir ya samu admission daqyar bayan khalil yayita shiga guraren namen alfarma ya samar masa da komai a wannan lokacin ne Raheem yayi fitowan hutun farko daga karatunsa kuma sam Dad dinsa bai bari ya baro America ba acan yayi hutun sbd bayason ya tafi Morocco dan haka yanaji yana gani duk tsananin son dayake yazo yaga dan uwansa bai samu dama ba dan abinda dad din bai saniba shi Nigeria yaso zuwa hutun amma sbd wata irin tsanani da rashin wasa ko sakewan dake tsakaninsu sai baima bada damar hakan ba.

De fammah batama san anyi hutun ba sbd Raheem din da sukai waya bai sanar mata ba dan kada taji ba dadi ko ranta ya baci dan haka har sukai hutun suka gama suka sake komawa ciki bata saniba.

Abu daya daya sake qamar da zuciyar Raheem ga aikinsa da karatunsa shine ya tabbatarda matiqar bai zama abinda mahaifinsa yakeson ya zama ba bazai taba samun rayuwar yanci da mahaifiyarsa da Dan uwansa ba da maamah dan haka baida kowace irin sakewa ko walwala a rayuwarsa a cikin makarantar dako ina bayan tsayar da kansa cak akan abinda yakaisa wanda hakan ya saka ya zama wanda kusan kowa ya sani dan bayan sunan mahaifinsa da matsayinsa daya taka a aikin haryakai matsayin Admiral to shi kansa Raheem kamewansa da rashin fuskansa ko kadan da wani irin karfin halinsa ya saka ya banbanta da abokan karatunsa da yawansu duka suna cikin kulawa da tattalin iyaye biyu tareda kawo ziyara da duk abinda dai ya danganci nuna tsananin so da kewa ga yayansu,
Shi a cikin iyayensa tinda ya taho babu wanda ya taba zuwa bare sakasa a ido sbd kowannensu yana jin bazai taba zuwa ba matiqar zaiga dan uwansa dan kuwa duk inda zasu iya haduwa sun yankesa a rayuwarsu,
Kowannensu a cikin zafi da tsananin baqin cikin juna suke har yanxu bayan duka wannan shekarun,
A familynsa da iyayensa shine wanda ake ikirarin ana yiwa son da baa taba yiwa kowa ba amma kuma sam baida farin ciki da walwala a rayuwarsa dan kuwa ya zama shine yake karban dukkanin hukuncin rabuwar iyayensa tin yana zanin goyonsa haryanzu,
Sun sakasa a tsakiya yana karban baqin cikin da kowannensu yake jefawa juna ta zuci,

Duka wannan ya sake sakawa zuciyarsa bata san komaiba bayan kadaici da rashin sakewa da rashin son rayuwa da kowa bayan kansa shi kadai tinda ya rabu da dan uwansa da shine kadai yake sakewa da walwala a gabansa dan haka ya dage dan kuwa daga ranar daya samu yancin fitowa cikakken navy soldier babu abinda zai sake rabasa da nasir wanda daga garesa kadai yake samun nutsuwa da kwanciyan hankali zai dawo dashi rayuwarsa.

Dad Hakeem jeerah kuwa duk wata kulawa da sakewa ya soketa ne tsakaninsa da Raheem sbd yanason ya zamo namijin da baisan shagala ba ko soyayyarda zata lalata rayuwarsa tin daga kuruciya har tsufa kaman yanda tasa rayuwar ta riga tamutu har abada bazai taba farin cikin daya saniba a baya wanda ya saka zuciyarsa a duhu take babu komai daya sani yanzu bayan doka da order da tsananin zafin doka da wani irin kaifi akan duk sharadi ko umarnin dazai bada wanda a yanxu ahaka duniya tasansa, tsayayyen mutum kaifi daya da babu abinda ya hada da sunansa da mutuncin sunan familynsa da karfin ikon mai nauyi.

Akan Raheem yafi tsaurara Umarninsa da ikonsa wanda hakan keta sake tsayar da Raheem din ga zamowa wani irin miskilin namijin da babu komai a rayuwarsa da zuciyarsa bayan zafi da qwazon aiki dayake ta budesa yana zama wani kakkarfan namijin da lafiyarsa take da karfin gaske dan kuwa bazaka hadasa da Nasir da ko shi idan ya gansa sai yayi mamakin ganin yanda jikinsa yake murdewa sbd azababbun exercises da geamin da bama haka yake ganin sojojin nan ba daya saba ganin gashi shi a tsaye yake baida wani jikin karfi tinda baima taba exercise ba duk da baida rama ko kadan amma kuma baida jiki bare irin wannan na masu geamin.

*****Zainab ta haihu tin kafin samun admission din Nasir harta gamo zaman wanka ta dawo ansamu Al'amin wanda tini ya fara wayo ya saba da Nasir sosai dan idan zai fita baya barin ya gansa maqale masa yake,

Maamah fatima ta samu nutsuwa da rufin asiri sosai ba laifi sbd Baba Khalil ke ciyar da gidan gabaki daya hakama Nasir ranakun da bayada lectures aikinsa yake zuwa yana kuma samu ba laifi dan haka shima yana daukan nauyin gidan.

Dr fammah data kasa samun nutsuwan rashin fatima na shekaru tafara shirin yanda zata iya zuwa Nigeria data dauki alkwarin har abada ta yafe zuwanta duk yanda zasuyi a nemo musu fatima sunyi gashi sun saida gidansu sun sauya anguwan tin bayan gobarar da sukai.

Ga Raheem da shima tasan yasan yana fitowa hutu idan har ya isa Nigeria bazai taba barowa batareda ya nemesu ba dan haka ta sake jiran ya samu hutun wanda kusan fiyeda shekara nawa kenan babu wani hutu kilama bazai fitoba saiya zama cikakken soja dan haka duk ta shiga damuwa da tsananin matsuwan son dauko fatima musamman sbd Nasir datake son yayi karatu anan duk da tasan yanxu kam yana gap da kammala jamia idan ma bai gamaba.

******shekarar da Nasir ke kokarin gama university a shekarar Senior Seaman Raheem jeerah ya sauka a Nigeria tareda Mahaifinsa daya kwana biyu acan suka dawo tare.

Bangaren Mahaifiyarsa da aka sauya kowane tsari da zuba sabuwar dukiya da luxuries din da akasan su ya saba dasu da duk abinda zai buqata aka zuba tareda mai aikinsa Namiji aka ware masa.

Kaf familyn babu wanda baiyi murna da farin cikin zuwansa ba dan sun dauka ma shikenan ya zama na mahaifiyarsa.

Matan mahaifinsa da babu wani sani ko sanayya ko kadan a tsakaninsu suma sun dan nuna murnar ganinsa duk da suna jin wani irin mamaki da dacin yanda kowa familyn ke tsananin kaunarsa fiyeda sauran yaya hakama shi kansa mahaifinsa da baa gane inda ya dosa sunsan yafi kowa da komai tsananin sonsa bai kuma hadasa da komaiba a duniyar nan.

Mummy khadee mahaifiyar Samad kishinsa taji tana yiwa kanta da 'danta sosai har cikin qasan zuciyarta dan bata wani damu da kishin Ummah Fadila ba sbd fahimtar babu wata soyayya a tsakaninta da maigidan nasu ba gwara ita ko dan 'danta data haifa masa ta samu matsayin daya fi na umman dan haka kusan tafi fadilan iyayi da zuba iko a gidam Sir hakeem jeerah.

Raheem baida sanayya da kowa dan haka koda ya isa gurin kakanninsa da safe ya gaidasu sukai kokarin gabatar masa da familynsa ya gaisa da kowa batareda ya kallesu da kyauba ya tantance su,

Koda Rana ta qarasa yi tini aka kawo masa mota sabuwa dal da kakansa Alh farouk ya siya masa sai wadda dad dinsa shima yasa aka kawo masa tareda driver dan bazai iya yawo da kansa ba sbd baisan koina ba.

Kai tsaye gidan Maamah da bazai taba mantawaba koya manta da koina yasa driver yakaisa da yamma lis sbd sai a time din ya samu kansa yana tareda kakansa.

Bayan sun isa suka tadda gidan an maidasu shaguna da gurin abinci dan haka maqota driver ya shiga yayo musu tambaya sai gashi kuwa akai musu kwatancen inda su Babak khalil din suka koma.

Koda suka isa gidan Baba Khalil na waje kofar gida yana magana da wasu maqotansa akan harkar masallacinsu na anguwa.

Kai tsaye baba khalil din bai gane Raheem ba sbd girmansa da sauyawansa gabaki daya dan kuwa babu alamar dayake nuna ya hada jini da yan Nigeria dan ya koma mahaifiyarsa sak ga wani irin kamewa da kwarjini da tsananin kamun kai a tattare dashi.
Chapter 15 · 0% Book details