← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 154

Sashe 65

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ya bata lafiya,zuwa gobe Dr zataxo ta dubasu su duka"

Yana fadan hakan Mum ta washe baki tana maida kallanta akan SANAAH da fammah tana cewa

"Allah ya bawa yan matana lafiya"

"Amin" SANAAH ta bude baki ta furta a hankali ita kuma fammah dad din ta kalla tace

"Thank you Dad"

Kallanta yayi da miqa hannunsa daya ya shafi gefen fuskanta yace

"Just get well soonest Mamanah"

Murmushi tayi daya fidda tsananin kamarta da mahaifin nata tana kallan dawo da kallanta akan SANAAH wadda ta dago ta kalleta Murmushinta na qaruwa take SANAAH ta dauke kallanta daga kanta tana cigaba da dan cin abincin sama sama kafin tasha ruwa tace she's full ta miqe tabar dining din.

Da daddare bata iya zuwa gurin Dad ba sedai ta kirasa a waya lokacin ma yana tareda Dad din ta gaidasa ta sanar basa batajin dadi amma da sauki sukai sallama da kulawa.

Dad na gama wayar ya dago ya kalli Fleet wadda bazaka taba sanin akan dad ko aa tinaninsa da hankalinsa yake sbd yanda yake karanta sako a wayarsa a natse da kamewa da wata irin girma da kwarjini.

Numfashi Dad din ya sauke a karo na uku bayan wainda yayi kafin kiran SANAAH ya shigo masa na zancen da RAHEEM yaxo masa dashi.

Bude baki yayi a tsanake sbd dagaske kenan Dr fammah zata iya zuwa Nigeria bayan shekarun baqin ciki da girmama tsanar dataiwa qasar da wainda suke cikinta.

"Babu kowane dalilin zuwanta kaman yanda na santa da dagewa da rashin hakura ga dik abinda ta kudurta bayan akan maganar aurenka da SANAAH ne,
Zata taho ne bazata tafi ba saita tabbatarda babu auren,
Bazata taba hutawaba da zubar da makaman yaqinta ba sai ta raba auren dani mahaifinka na daura maka sbd a koyaushe duk baqin cikin da zata sakamun shine yake sassauta nata baqin cikin na shekaru shiyasa ban taba damuwaba ko jin dacin yanda ta nema maka auren farin sbd na bata daman yin duk abinda zai sassauta baqin cikinta,

A yanxu kuwa tana damara ne da yaqin da batasan kanta zata yaqa da kanta ba sbd matar da zata dauro damarar yaqin fixgewa daga rayuwar 'danta dayake raye itace matar 'danta da baya raye.

Dagowa FLEET ADMIRAL RAHEEM JEERAH yayi da wani irin nutsuwa da slow ya sauke idanuwansa da suka saka Dad din da kansa daukewa ganinsu ya saukewa Dad din batareda yace komaiba.
#MAMUH
09033181070
[12/05, 10:12 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

61
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Numfashin manya Dad jeerah ya sake saukewa kafin ya yanke nasa hukuncin dayake tareda umarni yace

"Bazaa nema mata masauki a koina ba matiqar a qasar nan kuma nan garin zata sauka,
A cikin matana ne akwai wadda babu aure a tsakanina da ita amma sbd mutuncina da nata mutuncin dana zuriata ban bari tabar JEERAHsV ba tana ciki a zaune karkashin kulawata da ikona,
Hakanne itama a gareta matiqar ina raye da kuma iko bazata taba iya zama ba a inda ba cikin JEERAHsV ba sbd anan ne mutuncinta yake da girmanta da kuma ikonta yake,

Koda babu aure a tsakaninmu ta sani mu ahalin juna ne da duk abinda yake tsakaninmu bazamu taba goge hakan ba dan haka duk gyaran da zaayi mata kasa ayi mata anan cikin JEERAHsV
Akwai bangaren dayake tsakiyar na Zainab da Hajiya khadija a sauya mata tsarinsa zuwa tsarin da zai mata dadin zama a gyara mata ta zauna zan zauna na jira abinda duk ya kawota taxo dashi"

Fleet da baisan mexai iya cewaba sbd hayaniyar iyayensa zata sake tashi kenan duk da sun manyanta amma haka lamarin nasu yake motsawa dan haka baya wani shiga sbd rayuwarsa daban take da tasu,

A tasa rayuwar babu hayaniya da tashin hankali sai miskilanci da tafiyar da komai a tsarinsa na baturen ruwa da bai hada komai da peace dinsa ba,
Sabanin su dasuka kasa hakura da juna indai akan duk abinda zai taso ne kowa zai iya kokarinsa gurin nunawa dan uwansa ikonsa akan dansu da sam basu wani damu da farin cikinsa ba ko amincinsa shiyasa a bangaren ahalinsa a gurin 'yarsa kawai yake samun cikakkiyar sukuni da kaunar da batada kowace irin sirki ko manufa dan ko matarsa tanada manufofinta akan soyayyar datake masa dan kuwa matsayin datake dashi na matar Fleet admiral RAHEEM JEERAH of the Us navy bata hada matsayin da komaiba tana tsananin alfahari da bugun gaba da hakan tareda dagawa da jin bazata taba iya rasa matsayinba ko yadda wata ta amsa irin sunan da sunan RAHEEM JEERAH.

Baro gurin Dad din yayi yana zuwa bedroom dinsa wanka yayi ya fito daure da towel a qugunsa da tabawa daya zaa masa ya warware ya fadi sbd yanda yake daurasa shiyasa kusan matarsa ta riga ta gama mutuwa da shaawansa data zamar mata jarabawa sbd akwai abubuwan dake tattare dashi da matiqar ta gansu bata iya riqe shaawanta akansa dan hakanne ne kusan yawan muaamalansu neman datake masa yafi wanda yake mata dan ko cikin kwayar idanuwansa ya sauke mata take tsigar jikinta take tashi taji tana tsananin buqatan jinta a jikinsa musamman idan ya fito wanka kallo daya takewa murdadden jikinsa da koina kusan jijiyoyin karfi ne a bayyane nan ma bata iya hana kanta tsananin kwadaituwa da mijinta.

Shiryawa yayi cikin kayan bacci dogon wando kawai da wani mayen qamshinsa dayake tashi a jikinsa ya kwanta.

Yana kwantawa Ms Meenah ta shigo dakin sanye da kayan bacci itama masu tsayi har qasa da ciki data sama silk blue kala.

Isowa tayi ta zauna dayan gefen gadon sbd ta riga daman ta gamo komai na shirim baccinta ta haye gadon gabaki daya tana qarasa rage hasken dakin ta matsa cikin jikinsa ta shige masa ahankali.

Washe gari SANAAH da lafiyarta ta tashi dan haka tana yin wanka kafin kowa ya tashi tabar bangaren tayi gurin mommy.

Tana zuwa dakin Mommyn ta shige ta kwanta tana gaida mommyn dake zaune tana waya da Al'amin.

Tana gama wayar da kulawa ta kalleta tana mata ya jiki idanuwanta akanta.

"Naji sauki" ta furta tana janyo mata wani zancen suka fara kafin suka koma maganar yaya Al'amin dayake ta samun cigaba acan ahankali ahankali arziki da damammakin cigaban rayuwa suna samuwa.

Anan ta wuni harma dasu Mum din dukansu anata fira da abubuwansu hankali kwance.

Acan bangaren Fleet kuwa Imran ya sanarwa Dr Mum zata taho a cikin JEERAHsV zata zauna kuma.

Imran dayake shima Dr Mum din ta kirasa ta sanar masa yayi musu shirin tahowa Nigeria din dan haka take ya shiga aikin duka biyu na nema musu komai na tahowa da kuma na aikin bangaren da zaayi wanda kusan zubar dashi akai zaa mata sabon ginin da zaiyi daidai da duk abinda takeso.

Sauran mutanen villah din sunga anata sabon aiki a bangaren wanda yakeda girma shima kuma aikin imran ne a tsaye a akai da qwararrin maaikan daya dauko amma babu wanda yasan aikin na menene dan haka Mum ta fara murnan ko ita akewa bangaren dan tanason ace tanada nata bangaren wanda take ciki sedai ta ringa zuwa bangaren mijinta kwana sbd tana matsayin matar Fleet RAHEEM JEERAH guda da zai iya siye Villa din da yan canjin da ba komai bane a gurinsa ba amma ace batada bangarenta mai zaman kansa dan haka koma ba ita akewa ba to ana gamawa itama zata buqaci gaskia a ware mata nata bangaren su baro na Raheem ya zama tirakarsa ce shi kadai.

Hajiyar Samad dataga ana bangaren abinda yazo ranta shine SANAAH zata tare kenan maganar auren bayyana zatai dan haka ta ringa jin wani irin dadi da farin cikin jiran ganin tashin hankalin da zaayi sbd babu abinda take jira yanzu kaman Ms Meenah ta gane auren ta tsani SANAAH da uwarta wanda ita hakan ne zai bata daman shiri da Meenah din sbd tana neman wanda zasu hada kai su hana SANAAH da uwarta da sukai sanadin mutuwan auren zaman lafiya da kwanciyan hankali.

SANAAH da mommy kuwa tashin hankali da tsoro suka shiga mai girma na ganin aikin da akeyi din wanda zai iya yiyuwa tarewanta zaai magana dan haka suka shiga tinani mai zurfa da yar shakka.

Rage zama sosai bangaren SANAAH tayi sbd zuciyarta da a yanxu batada sukuni sam a bangaren zaman dole takeyi musamman indai zaa hau dining ta ringa jin rashin nutsuwa kenan duk da babu wanda ya taba gane abinda take ciki dan kuwa ko a dining a tsanake take komai.
Chapter 65 · 0% Book details