← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 154

Sashe 44

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aurensa aka daura da SANAAH dinka ayau mun shiga uku wace sabuwar masifar ce wannan?
Wlh tarko aka nada maka wanda zai kasheka da gaggawa....hada kayanka ka tafi tin a.........

Kallanta yakeyi da duka idanuwansa batareda ya motsaba sbd bai yadda ko kusa da wannan zancen ba da har abada bazai taba yiyuwaba wai Godfather dinsa da aure a irin tsarin rayuwarsa da babu gurin shigar kowane irin mutum ma sbd ahalinsa basason yawa su kansu bare qarin aure.

Tayaya ma?mutanen da basa wani son wani ma yazo cikinsu ya zauna yayi rayuwa bayan iya su to ta ina zai iya kallan wata macen bare qarin aure,

Hakama tayaya SANAAH datake saar yarsa aure zai yiyu a tsakaninsu....

Dauke kansa yayi daga kallan hajiyar yana miqewa tsaye zai fice sbd gabaki daya ta rasa kanta tinda abin ya faru a kwanakin kullum cikin tinani da zullumi kala kala take.

Riqosa tayi da karfin gaske tana kallansa tace

"Bakaji abinda na fada bane?
Kanajin Auren da aka daura?
Wlh ba aure ne ba kai akaiwa tarko wannan auren,
Baka jina ne???

Wani mummunan daci da baqin cikin kalmar auren datake furtawa ya hadiye sbd da ace wani ne yake maimaita kalman an daurawa SANAAH aure da zai iya hallakasa da hannuwansa amma hajiyarsa dan haka ya sake hadiye wani dacin mai karfi ya kalleta da idanuwansa da suka sauya yace

"Hajiya babu auren da zaa daurawa Godfather da kowa a duniya bama wai SANAAH ba,
Babu aure a yanzu kuma babu shi har abada dan haka ki dena wannan tinanin yayi nauyin dama yake kaman haramun"

Kallansa takeyi da tsananin takaici itama da baqin cikin data rasa abin fada amma itama tanason tabbatarwa dan haka ta wucesa ta fita tana dan gyaran mayafin tsadaddiyar abayar dake jikinta ta nufi bangarensu SANAAH sbd tasan bazata iya zuwa bangaren Dad ba kai tsaye ko hauka ce ta haifeta.

Tana isa bangaren ga mamakinta Umma na bangaren tana taya mommy murna wadda take amsawa cikeda farin ciki da sakewa da walwala tana godiya hankali kwance.

Ganin yanayinsu ya saka hajiyar itama tattaro karfin hali da danne tashin hankalinta da baqin cikinsu da takaicinsu ta dan saki fuska cikin karfin hali tana gaisawa da Mommyn kafin ta bude baki tace

"Sai mukaji abinda yake faruwa,
An daura auren ne ko zaa daura ne?
Allah ya nuna mana"

Umma data gama karantar halin datake ciki murmushi mai sanyi da nutsuwa ta sake kafin hankali kwance tace

"An daura tin dazu bayan jumaa sedai fatar Allah ya nuna mana tarewa lafiya idan lokaci yayi"

Miqewa tayi tanawa mommy sai anjima ta fice.

Hajiya datai mutuwar zaune tana kasa yadda har lokacin sake bude baki tayi ta tambayi mommy itama mommyn ta tabbatar mata da an daura.

Bata san lokacin data miqe ba ta fice batareda cewa komaiba mommy ta bita da kallan mamaki da fatar Allah yasa kada ta sake zuwar mata.

Tana baro can bangaren tsabar rikicewa da rudun tashin hankali kai tsaye bangaren Dad ta nufa tana zuwa yana palonsa na kurya zaune cikin hutawa yana waya da wanda aka daurawa auren yau dan sanar dashi sai gata.

Kokarin tinkaro inda yake takeyi ya daga mata hannu ya dakatar da ita cikin wani irin umarni da kaifin daya saka kafafunta tsayawa cak ba shiri ta bude bakinta dayake rawa tace

"Alh Auren FLEET RAHEEM da SANAAH aka daura ayau????

Maganar a kunnen wanda ake waya dashi ta sauka kai tsaye cikin wani irin direct da slow yaji saukanta a cikin kunnuwansa da suke karban kowane zance da nutsuwa da kamewa yana zaune a palonsa dayake saman cikin gidansa matarsa tana zaune gefensa hannunsa na sarqe cikin nata tana jiran ya gama yaci fruits din data hado masa masu tsafta da sanyi.

Dago fararen idanuwansa masu tsananin kwarjini yayi daga qasa a lokacin daya ji zancen ya ratso wayar batareda ya motsaba.

Dad kuwa bude baki yayi cikin kaifi daya da zafi mai tsananin dayake tattare da sautinsa da hukuncinsa yace

"Kije ki shirya komai naki gobe zaa bude miki bangaren dayake kusa dana su SANAAH zaki koma can"

Sarewa kafafun hajiyar sukai ta kifa qasa da karfi jikinta na rawa ta dago kai ta kallesa da sauri idanuwanta na yin ja a take ta bude baki zatai magana ya dakatar da ita yana cewa ta fice kuma dan ta yana wayuwar garin gobe a qasar Nigeria bama a cikin gidan ba bazata sake jinsa ko ganinsa ba sai takusa manta kamanninsa.

Zarewa taji tana neman yi dan haka a rikice ta juya tabar bangaren zuciyarta ne neman dakatawa daga bugawa ta nufi bangaren Samad din bataji bata ganin komai daman tafiyarsa a goben ne amma yace ya fasa.

Ko data shiga bangarensa yana palo yana waya ganinta ya sakasa kashe wayar yana kallanta.

A haukace da tashin hankali ta kama hannunsa ta turasa hanyar bedroom dinsa tana cewa

"Ka hada komai naka ka shirya a cikin daren nan zaka wuce airport kafin asuba lokacin tashin jirgin da zaka bi,
Wlh tallahi Dad dinka ya daurawa SANAAH aure da Godfather dinka kuma daga yanzu zuwa gobe ya baka kabar qasar,
Ka taimakeni Samad ka tattara ka tafi dan Allah ka taimakeni ka tafi kada ka bari yayi maka hukuncin da bazamu iya dashiba."

Mutuwan tsaye Samad din yayi yana jin jiri na dibansa idanuwansa na wani irin duhu da dauke gani kafin ta sake wata magana ya yanke jiki ya fadi a gurin.

Ihu ta kwalla tana kamosa da kiran sunansa da karfi jikinta na rawa tashin hankalinta na daduwa.

*****Acan palon Dad kuwa bayan ficewanta shiru Yayi na seconds kafin ya bude bakinsa cikin girman matsayin dayake dashi akan Raheem din da ikonsa akansa na mahaifin daya haifesa da nutsuwa da kamewan datake cike da isar da umarnin daya riga ya zartar ba neman shawara ba ko tausasa ya ce

"Kaman yanda ka riga kaji zancen daya fito daga bakin hajiya khadija a yanzu shine sakon dazan isar maka daman na ayau na Daura maka aure wata 'yata datake da matsayi me girma a cikin ahalina,
Inason ka fara sanin darajar datake dashi mai girma a gurina ne ya saka na baka aurenta,
Ban nema shawaranka ba akan hakanne ba sbd ita din bana buqatan shawara da kowa akan duk lamarin daya shafeta dan haka ayau ni mahaifinka ina sanar dakai na sake daura maka aure da wata matar bayan wadda kake da ita ina kuma fatan zaka girmama wannan hukuncin dayake hade da umarnin nawa"
#MAMUH
09033181070
[04/05, 2:25 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

43
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
Wani irin shiru ne mai tattare da nutsuwa da kamewan manyan mutane biyu ya ratsa yanayi da wayar wadda sukeyi batareda kowannensu ya bayarda wani motsi ko hayaniya ba wayar....

FLEET ADMIRAL RAHEEM HAKEEM JEERAH shiru ne ya ratsa bangarensa wanda baiyi kowane irin motsiba ko bada reaction bare bayyanarda kowane irin yanayin dazai bayyanarda halinda zuciya da kunnuwansa suka shiga bayan jin kakkausan umarnin da bai taba tsammanin ji ba ko a lokacin dayake da samartakan kara aure ba sai yanzu da baisan ma yanda zai iya kallan kowace mace da sunan mace da namiji zai buqaci kulawa ba bare aure,
Bai taba saka ran aure ba koda yayi aurensa na farko ba,
Bai taba tsammanin bawa mace wani space na rayuwarsa da zuciyarsaba saida yayi aurensa wanda haryanzu yake struggling na yanda zai bata cikakkiyar iko da zuciyarsa,
Haryanzu zuciyarsa da rayuwarsa suna kokari ne sosai gurin bawa mace daya dake rayuwarsa dukkanin dama da haqqinta da farin cikinta daya rataya a wuyansa ba,
A duniyarsa da rayuwarsa mata uku ne zuciyarsa da rayuwarsa basa iya yaqi da yanda zai basu duka sonsa da kaunarsa ba sune iyayensa biyu mata sai 'yarsa amma ko matarsa duk yanda yake sonta da bata kaunarsa duka hakanan yake jin kaman yana tilasta kansa ne sbd kada ya tauyeta da bata duka sonsa,

To a yanzu da Mahaifinsa yazo da umarnin daya riga ya yankesa a garesa baida kowane space a zuciyarsa da familynsa da gidansa da zai iya bawa kowace mace da sunan baqunta ma bare zaman rayuwa,
Chapter 44 · 0% Book details