← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 154

Sashe 104

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan yayi mata dadi taji sosai ta ringa masa godiya taje tayi sallama dasu Fammah din wadda ta yadda ita zata tafi din itama SANAAH bakwana sukai ta tafiyarta.

Fleet kuwa koda abbu ya kirasa a wayar ya sanar dashi hukuncin daya yanke baice komaiba siyan tickets din akai hadda tinda daman itama SANAAH visa dinta hadda ta zuwa America dince akai mata komai tintini.

Sbd da fammah zataje ya saka hankalin SANAAH dan kwanciya bata sake sakasa a ido ba sai yamma lis da suka fito suka shiga mota dan tafiya airport batareda Ms Meenah din tasan hadda shi zasai tafiyar ba.

Haka suka isa airport hannunta a cikin na fammah kaman yanda suka saba aka gama komai jirginsu ya daga daga Morocco din Ms Meenah data kalli time ta tabbata zuwa yanzu jirginsu ya daga dan gaka ta sauke ajiyan zuciyar batada sauran nauyi kuma ba yanzu zata komaba gaskia.
#MAMUH
09033181070
[09/06, 9:55 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

100
Tinda fammah ta kasance kaman a tsakiyarsu ya saka bata sake iya kallansa ba duk tsawon tafiyar kuwa duk da tana jin bacin ransa da fushinsa dayake a bayyane dan kuwa Mum ba qaramin kaisa qololuwan bacin rai tayi ba amma kuma ya danne hakan sbd kada su biyun su shiga rashin walwalan ganin fushin nasa a bayyane.

Itadai tana maqale da Fammah wadda fammah din ke jin kaman itace uwar Amanar SANAAH din a yanxu dan kuwa wani tattali da taka tsantsan taji tana nunawa akanta dan hakanne ma batajin idanma sun rafi America zata ringa yawo da ita koina sbd SANAAH batason yawo hakama itama yawon dazata ringa yi ba zama na hada kan wasu takardunta datake buqatan karba ne na tafi dasu.

Shi kansa sbd sanin irin girman kauna da kulawan dake tsakaninsu ya saka bai kuma nuna kulawa da tattalin nata ba sbd kaman yanda zai bata haka Fammah zata batasu dan haka a yanxu su biyun shine mafiya rayukan dazai bawa tattalin a tare.

Cikin wata irin jin dadi da nutsuwa suke a jirgin sbd inda suke hakama SANAAH a miqe take ta dan kwanta da jikin fammah kafafunta a rufe da wata tattausan showel da aka kawo mata na rufa.

Tafiya mai tsayi sukai kafin suka isa,
Jirginsu na sauka tini motocin navy suka iso daukansu a airport da asalin karfin tsaron da SANAAH bata taba gani ba kowannensu yana sare masa cikin girmamawa mai karfi da tsari.

Shiga motocin sukai take aka bar airport dasu zuwa gidansa da tinin akasan da isowansu sbd Imran daya sanar da babban mai kulawa da komai na gidan da masu aiki da sukaje hutu mai tsayi sbd babu kowa dan haka tin suna airport acan Morocco ya kira ya sanar aka kira duka masi aiki suka dawo kan aikinsu tinin suka gyara koina da kunna abubuwan wuta dasu ac da fridge fridge da komai hatta ruwa da drinks saida aka saka a kowane fridge dake palonsa da komai.

Dan haka suna isowa gida kai tsaye bedroom mai zaman kansa Dad din yace akaiwa SANAAH kayanta wanda yake gefen na Fammah wadda bata damuba sbd tasan hakan dole daman zaayi dan nunawa Masu aiki da ita kanta SANAAH din taji nan kaman gidane duk da sunsan daman daki daya zasu koma su hade.

Tinda a tsananin gajiye suke bedroom din da aka bata ta shiga sbd su samu wanka da shiryawa lokaci daya Tinda idan suka shiga dakin fammah dole wani ya jira wani a gurin wanka da suke tsananin buqata dan rage gajiya musamman da ba wani baccin suka samu ba hardar fammah da tin daren shekaran jiya bata rintsa ba suka wayi gari da neman SANAAH dan haka kanta har wani sarawa yakeyi.

Tsakiyar sare ne suka sauka sosai dan haka wankan sukai tareda Shirin bacci kawai sai sallah da kowannensu yayi basa tareda wata yunwa sbd sunci small chops a jirgi kusan so biyu ko uku ma dan haka SANAAH dai ita cikin tsakiyar lafiyayyan gadon dakin ta shige tareda rufe jikinta take bacci mai nauyin gaske ya dauketa tana sauke numfashi mai sanyi ahankali.

Fammah ma baccin ne ya dauketa da batajin zata tashi a kusa kusa dan kuwa tana cikin buguwan rashinsa.

Tsit gidan yayi babu kowace motsi gashi daman dare ne,
Shi kansa tinda suka iso din yana isa bedroom dinsa zare kayan jikinsa yayi yana fadawa bathroom ya sakarwa kansa ruwan dumi suna saike jikinsa yayi wanka ya fito daure da blue towel a qugunsa ya tsaya a gaban mirror rin dake tsaye mai girma a cikin closet dinsa ya shirya cikin tights tom ford short daya lafe jikinsa ya saka jallabiya fara qal ya fito daga closet din yana fidda kamshi mai sanyi yayi sallah yana gamawa ya kalli time akwai sauran kusan 2hrs kafin sallan asuba dan haka zare jallabiyar yayi ya jefar yana hayewa lafiyayyan kingsize bed dinsa tareda rife idanuwansa ya sauke numfashi mai sanyi da nutsuwa.

Koda gari ya waye sosai babu motsi ko alaman fitowan kowa daga cikinsu sbd sunyi sallar asuba ma dukansu sun sake komawa dan haka masu aiki ne kawai ke aikinsu cikin nutsuwa da rashin hayaniya da kuma sanin aikinsu.

Baa shirya dining ba sai after 10 lokacin akasan zasu iya fitowa cin abincin kowace time dan haka ana gama shirya dining da kawo komai gidan ya sake yin tsit.

Fammah ce ta fara fitowa a shirye cikin free riga da wando na zaman gida da qaramar hula akanta da bata rufe gashinta bama sam tana dan kamshinta mai sanyi.

Dakin SANAAH din ta nufa ta tadda ta tashi amma tana kwance har lokacin idanuwanta a rufe tana jin bude dakin tasan fammah ce ta bude idanuwanta tana saukesu akan fuskanta batareda ta motsaba fammah dake isowa gurinta ta bude baki tana cewa

"Hey good morning"

Wani kyakkyawan murmushi mai tsananin kyau a fuskanta SANAAH ta sauke tana bude baki tace

"Hey I missed you"

Yar dariya fammah ta sake tana qarasowa taja dan dogon hancinta tana cewa

'Bangama fushi dake bafa dan kima sani"

Murmushi SANAAH din ta sake sakewa tana tashi zaune ta riqe hannunta tana cewa

"Haba nace kiyi hkr my rabin rai"

Dariya famman ke sake sakewa tana yaye mata rufar tace

"Breakfast"

Ziro kafafu SANAAH tayi tana miqewa tsaye ahankali ta nufi bathroom ta shige tana jin hankalinta a kwance sbd anan tana tare ne da fammah da iya Dad dinta babu tarin mutanen da bata saniba a zagaye tako ina kaman acan Morocco dan haka sai takejin kaman nan din zatafi dan samun nutsuwan sakewa fiyeda can duk da anan dinma tanajinta a baquwa ne.

Wanka tayo na dan tsawon lokaci kafin ta fito ta tadda fammah bata dakin dan haka zaunawa tayi ta shirya a natse ta saka straight gown mai laushin data dan lafe ta kwanta a jikinta sai hulan da itama ta saka din tana gamawa Fammah na sake leqowa kiranta dan haka miqewa tayi suka fito a tare tana gefen fammah din tana saurarenta daga bayanin datake mata Dad bai fitoba sui breakfast dinsu kawai sbd wata irin azababbiyar yunwa takeji.

Suna isa Dining room din wanda tsarinsa yake na musamman shima da wani irin tsari na asalin turawa masu daula da iko kaman yanda koina gidan tsarinsa na musamman ne datake tabbatarda dole rayuwansu ta banbantaa koina sukaje.

Zaunawa SANAAH tayi fammah na kokarin zaunawa qamshinsa ya ratso gurin wanda ya sakata fasa zaunawa tana juyawa ta kalli kofar gabaki daya wanda yayi daidai da sako kansa cikin gurin kyakkyawar fuskansa mai cikeda kwarjini na fidda wata freshness idanuwansa suna sauka akanta kallo daya yayi mata mai nutsuwa ya maida kallansa akan fammah wadda ta iso gurinsa tana gaidasa tareda dan rungumesa ya dan buga bayanta tareda amsa gaisuwan suna isowa suka zauna yana dago idanuwansa daidai da bude bakinta cikin nutsuwa tace

"Ina kwana" tana dago idanuwanta da sukai sanyi a take da zuwansa ta sauke akansa ta kallesa kadan.

Amsawa yayi yana dan dauke idanuwansa akanta yana kallan abincin da fammah ke serving nasa a natse.

Abincin kowannensu yafara ci kafin fammah ta bude baki tace

"Dad zuwa gobe insha Allah zan fara zuwa karban papers dina dan banma shigar da request din karban nasu ba so tomorrow insha Allah zanyi hakan"

Dan gyada kai yayi yana bude baki yace

"Thats good,zan saka akira a sanar dasu hakan kafin kije sbd kada su bata time"

"Ok Dad thank you amma kaman basai anyi magana ba zan iya bin process din insha Allah"

Sake gyada kai yai a natse yana cewa

"As you wish Doc"

Murmushi tayi cikin jin dadi tana sake masa godia da dauko masa wani zancen dayake na process din dazata bi yana gamsuwa da dora mata wasu bayanan suna firarsu ta uban dayake tsananin kauna da son 'yarsa har suka gama suka tattaro suka baro dining din batareda ta iya sake kallansa ba dan silalewa ma tayi ta koma dakin Fammah ta zauna tana dauko ipad dinta ta shiga kalle kallenta a media.

Fammah kuwa tana can tareda Dad din har lokacin sallah yayi ta shigo tayi sallah bayan ma har SANAAH din tayi tata tana zaune tana cigaba da kallanta a ipad.

Suna gamawa fira da kallace kallacen sukaci gaba suna dariyarsu da tsokanar SANAAH da famman keyi..

Da daddare Fammah tayi ordern sabuwar wayoyi guda biyu masu kyau da tsada aka kawo securities ne suka amsar mata aka kawo mata su ciki.

Maid ce ta kawo mata har bedroom dinta ta karba tana budewa tareda nuna SANAAH tana cewa nasu ne sbd kwana dayan datai ba wayar kaman zata zare takejinta.

Kallan wayoyin SANAAH tayi tana jin shaawa da kewan waya itama amma kuma tinawa da hukuncin dayake kanta ya sakata jin jikinta yayi sanyi gashi bazata iya fadawa Fammah bataso ba sbd kada kokarinta ya tashi abanza dan haka godia tayi ta amsa wayar ta ajiye kawai bama tareda ko kunnawa tayiba.

Tin safe bata sake ganinsa ba sbd yana office dinsa dake cikin gidan sbd tarin ayyukan dake gabansu suna jiransa.
Chapter 104 · 0% Book details