← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 154

Sashe 54

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yeah insha Allah zamuci gaba da kokarin gyarawan"

"Maamanka ta sanar dani kwanakin baya cewan an baka wata matar acan Nigeria harma an daura aure ko?
Allah ya sanya alkhairi ya bada albarka mara yankewa a rayuwanku ya hada kanku ku dika ya qarawa familynka yawa da farin ciki"

Dago fararen idanuwansa yayi ya kalli Abbun adduoinsa na sauka a kunnuwansa yana jinsu kaman wani lamari mai nauyi sbd shine na farko dayayi maganar auren da zuciyar datake a tsarkake daga kowace irin tinani da manufa,

Ko mahaifinsa bai masa irin wannan adduoin ba akan auren sedai juyasa dayake da manufofi da dama.

A tsanake ya furtawa Abbu "Amin" a taqaice sbd baisan me zai fada ba hakama bayajin akwai wanda zai iya tsayawa yiwa bayanin komai akan auren yanzu sbd baida kowace maganan komai akan matsayi da auren dayake dashi yanzu,
Bazai kuma bawa kowa daman shiga maganarba harsai lokacinda zuciyarsa ta tsayar da bayani daya akan auren da matsayinsa a gurinsa shi dayake riqe da auren.

Bai fadawa Abbu wacece Aka daura auren da itaba sbd duka bai shirya kowace hayaniyar raayin kowa akai ba zai bawa komai lokaci tukuna dan haka suka fara firarsu har saida sukai sallah suka gama tukuna ya isa cikin gida gurin iyayensa mata wainda sunji isowansa tasa.

A babban palon ciki ya tadda Maamah tana zaune tana duba wayarta da alama waya ta gama yana ganinta yaji nutsuwansa ta sake qaruwa sbd bai taba hada kaunarta da girmanta da wasu abubuwanba da dama,

Ba itace ta haifesaba amma itace uwar data shayar dashi ta basa kaunarta da rayuwarta dan haka kowa ya sheda ya sani kaunarta da matsayinta a gurinsa daban ne.

Takowa yayi ya qaraso cikin gabaki daya wanda qamshinsa daya fara kauwa qamshin palon yana maye gurbi ya sakata dagowa tana kallansa a tsanake da wata irin kauna mai tsananin karfi da kulawa tareda kewa fuskanta na cikewa da farin ciki da murmushi da walwala ta bude baki tana ambatar sunansa da cewa

"ABDULRAHEEM"

Shi kansa murmushinsa mai kyau ne ya gauraye kyakkyawar fuskansa datake dauke da haiba ya qaraso har gabanta ya zauna a natse tareda bude baki yace

"Ya Maamah"

"Ya hanya?
Kun iso lafiya ko?
Yasu Hajiya meenah?
Yaya fammah?
Kana lafiya??

Duka tambayoyinta cikeda kulawa da sakewa da farin ciki ta jero masa su tana ajiye wayarta gefe.

Da kwanciyan hankali da farin cikin kasancewa da ita ya fara bata amsar kowace tambayarta a natse da turanci kafin ya dora da cewa

"Fammah kuma tana Nigeria ba yanxu xata koma ba sai daga baya insha Allah"

Kallansa Maamah tayi da mamaki tace

"Nigeria kuma?
Zata iya zama ne acan din batareda ta saba da kowaba?

Dr Mum ce ta fito daga bedroom dinta sanye da wata maroon luxury Abayar da kana kallo kasan sai masu arziki ne ke iya sakata a qasar ma dan kuwa babu kowace hayaniya a jikinta zallan black sequence ne a jikinta da suka qarawa rigar nutsuwa ta zaunu a jikinta da fatarta datake fara qal har tana daukan ido ta manyanta amma kuma tanada sauran kyanta sosai da sosai sbd bazaka ma ce itace ta haifi Fleet ba duk da shima kusan kyan jikinta ne ya dauko sam babu kowace manyanci tattare da jikinsa da fatarsa.

Fuskanta a daure take babu kowace sakewa ko wasa a cikinta wanda wannan halin nata shine halinta da bai taba sauyawa tin kuruciyarta wato rashin yadda da kowace raini ko laifi,bata iya boye bacin ranta ko kadan idan aka tabata ko yi mata laifin daya tabata sosai dan hakane tin ranar da sakon aurensa ya isa kunnuwanta take cikin bacin rai da fushi sosai kawai ta danne ne sbd babu wanda zata saukewa a kusa amma ranta yayi mummunan baci da daukan zafin da ace har Raheem zai qara aure kokuma mahaifinsa zai qara masa wata matar tsawon shekaru amma bai sanar mata ba kila ma harya karba auren yana rayuwa da wata macen batareda sanin su ahalinsa ba,

Kenan itama matarsa datake amana a gurinta tin kafin rasuwar mahaifiyarta ta damqa mata ita amana kuma ta amsa amma gashinan zaa maimaita mata abinda ita akai mata a lokacin nata auren wato auren cin amana dan haka bazata taba yadda ba ko hakan na nufin ta fuskanci Hakeem ne tinda tayi imanin da gangan yayi amma kafin Hakeem Fleet ne zai fara fuskantar bacin ranta.

Tana shigowa palon ya dago kansa a natse ya kalleta ya dauke kansa a tsanake yana kamewa sbd da dukkanin girmansa sbd daman a cikin iyayensa babu wanda yakeda kyakkyawar sakewa dashi ko walwala sosai koyaushe girmamawan ce kawai sai umarni.

Maamah kallan Dr Mum din tayi tana fatan kada ta bawa Fleet kowace irin damuwa tinda dai anriga anyi ko yayane hakuri zaayi indai ba shine da kansa yayi raayin rabuwa da aurenba ya sawwake,
Ita Hajiya Meenah ma take tausayi sbd itace ta gama yadda da har abada babu kowace macen da zata shigo gidanta kuma suma duk sun saka ran hakan amma sai ga wannan tashin hankalin kwatsam ya sauko wanda ya dawo musu da ciwon abinda akaiwa Fammah din a baya.

Zaunawa tayi tana kallansa ta bude baki da mamakinta dayake hade da dacin zuciya tace

"Fammah naji kaman ana cewa tana ina???

Maamah ce ta bata amsa da cewa

"Tana Nigeria,nima mamaki nakeyi ta yanda zata iya zama a cikinsu"

Cikin tsanaki da kwanciyan hankali da kamewa yace

"Barka da fitowa Dr Mum,
Mun sameku lafiya?
Allah ya qara lafiya da nisan kwana"

Bata iya amsa gaisuwansaba duka idanuwanta na kansa tace

"Me famman ta tsaya yi a Nigeria?
Akwai dalilin daya sakata tafiya ne?

Kasancewansa ya saba kuma tasa rayuwar daban take yanada nasa akidar da tsarin maana nasa principles din da baitaba sauyasu akan kowaba harda iyayensa dan haka dan kai tsaye ne babu boyo a lamarinsa kai tsaye yake sbd iko da powern data shigesa hakama baya bayani wa kowa idan ba shine yayi raayi ko ga daman hakan ba shiyasa kaf duniya duk wanda ya tambeyasa har iyayensa suka bai bada amsa ba ya yanke zancen to hakura kakeyi ka tsaya iya nan.
Dan hakanne yake kowace maganarsa da rayuwarsa a tsanake da kwanciyan hankalin da babu hayaniya a ciki sbd rayuwar hayaniyarsa da karajinsa suna a fagen aikinsa ne.
#MAMUH
09033181070
[08/05, 1:12 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

52
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya🔥🔥🔥
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa Duka akan 7k ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa, Mutun goman farko da goman 2 Zuwa goban 3 da suka siya promo dimmu na 7k na
1. Sashen kaza
2. Ciccibi
3. Gumba madara da chocolate
4. Gari 7in1
5. Tsimi mallaka 5. Tsimin matar minister
6. Women coffee 3in1 sunada kyauta abubuwa kamar haka:Matsin ba a Fira da wando 1k,Matsin maganin infection 1k,Dripping pills 1k,Turaren mallaka 2k
Total total gift 5k
Kiyi kokari ki kasance aciki Garabasa kan garabasa Da 7k dinki ki mallaki kayan da ko 16k Bata bakisu zakisha dadinki oga ya more har kyauta saikin samu insha Allah 08144015291 Maman yasmeen takuce For more information say hi
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
*DAHUWAR KAZA*
Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato Ni’ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya
MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku
Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 2000 kacal.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set.

*******
A natse da bata girmanta ya bude baki yace

"Daga Nigeria din nake shine ta buqaci abarta can tukuna tana son sake sabawa da mutanen can"

Shiru daga Maamah har Dr Mum sukai sbd mamakin daya sake shigarsu mai girma Dr Mum tace

"Kana Nigeria kenan duk satikan nan?"

"Naam" ya bata amsa a taqaice wadda ta sake sakata shiga mutuwan jiki da tsoro mai tsanani sbd barin fammah ma acan yana nufin komawansa Nigeria guarantee ce.

Rasa cewa komai tayi sbd abinda take hangowa daga kamalansa ma na baya buqatan kowace hayaniya akan komai daya shafi Nigeria.

Wani nauyi ne ya sake danne kirjinta tanajin kila harta mutu Hakeem bazai taba barin ta warke daga abinda yayi mata ba tin tana matashiyarta haryanzu.

Numfashi mai zafi ta fidda wanda yake tattare da damuwa da nauyin zuciya tace

"Nasan kasan zuwa yanzu duk munsan da maganar auren da kake dashi na biyu,
Tambayata ta farko anan itace matarka tasan da hakan?
Idan bata saniba inason kafin ta sani kasan matakin da zaka dauka akan auren kafin kowace damuwa ko fitinar ta taso"

Maamah kallan Dr Mum din tayi tana buqatan sassauci a zancen nata kafin ta maida kallanta kan Fleet wanda babu kowace yanayi a tattare dashi dazai bayyanarda halinda ya shiga najin maganarta mai kama da umarnin sawwake auren.

Dago idanuwansa masu haske yayi bayan dan seconds daya bata na sauke kalamanta ya bude baki yace

"Dr Meenah batasan da maganar auren ba sbd banbawa auren kowace irin mahimmanci ba da time shiyasa ba buqatan ta sani sbd kwanciyan hankalinmu duka amma a yanzu zata iya sani sbd Auren bame warware bane a yanxu"

Da wata irin shock mai karfin gaske daya dakesu su biyun suka kallesa Maamah na cewa

"Daman Saki a auren da bai wani jimaba babu amfani gwara a nutsu a duba"

Dr Mum kuwa jin tayi bakinta ya kasa furta komai sbd kai tsaye yanke kowace magana ce Raheem yayi akan auren.
Chapter 54 · 0% Book details