← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 154

Sashe 13

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Hakeem wata macen zaka kuma aura bayan ni??
Hakeem sbd rayuwata ta lalace ne bazan iya sake haihuwaba zaka sake aure?
Hakeem bazaka iya hakurin na samu lafiyar dana rasa ba?
Hakeem menene saurin da kukeyi?
Hakeem menene amfanin rayuwata a cikin familynka????

Dakatar da ita yayi da cewa

'Karki saka a ranki cewan sbd kin rasa lafiyarki ko haihuwa ya saka zaayi wannan auren Fammah sbd kinsan kece soulmate dina,bazan taba son kowace mace ba a duniya bayan ke,
Kece ni fammah,wannan auren aurene kawai na umarnin da bazan iya kaucewaba....

Fammah bata girgiza ko jin kalamansa ko dayaba a jiki da zuciyarta saima wani dacinsu dataji yana ratsata dan haka kai tsaye ta sake kallansa da jajayen idanuwanta tace

'Ka fada musu bazaka iyaba,
Bazaka iya hada matarka da kowa,
Bazaka iya auren kowace macen ba,
Bakada raayin kara auren kowace mace har karshen rayuwarka,
Bazaka iya cika wannan umarninba ka fada musu sbd idan ka fada babu wanda zai maka dole tinda kai ba yaro bane shekarunka sunkai har sun wuce...

Da mamaki ya kalleta yanda take maganar kai tsaye cikin kaifin harshen daya hango matakin datake tsaye akai kenan.

'Iyayena ne ake magana anan kina tina hakan ko??

Wani numfashi me zafi ta fidda tana sake riqe nutsuwanta sbd kwakwalwanta dake neman bugawa da abinda take ji tace

'Hakeem jeerah ni fammah wallahi tallahi matikar zakai wannan auren nabarka na bar aurenka har abada bana fatar sake ci gaba da zaman aure da kai da familynka......

Da tsananin mamaki ya kalleta yana shiga shock da bugawan zuciya ya kafe idawanta dake bushe da kallo sunyi jajir shima nasa jan sukai ya bude baki yace

'Fammah,kinsan me kike fada kuwa?
Kin rasa hankalinki ne ko me?
Akan wani auren kike cewa kin gama naki auren?
Idan nayi auren zai raba mu ne kokuwa zai rage soyayyar dake tsakaninmu??

Lumshe idanuwanta tayi ahankali kalamansa na ratsata sbd auren dai yi zaiyi bazai fasa ba ko maganar dakatawa ta samu lafiya ba da futa quncin rashin mahaifiyarta data rasa ba.

Miqewa takeson yi a hankali tabar masa gurin amma ta kasa tashi hannuwanta na wata irin rawa ta boyesu a cikin jikinta tana jin zuciyarta kaman zata fashe.

Duk maganganun dayake yi cikin tashin hankali baiga alaman tana jinsa ba sbd idanuwanta da alamar sun bushe batareda yasan zuciyarta wani irin kuna da kuka takeyi ba me tsananin abinda yake shirin yi mata ba na zabar auren wata ba a cikin wannan halin datake ciki datake tsananin buqatarsa fiyeda koyaushe ba na rayuwar aurensu.

Miqewa yayi ya fice daga dakin ko gani sosai bayayi ya nufi gurin Abbu muryansa harta fara shaqewa ya zauna gabansa ido jajir yafara jero masa abinda yake faruwa wanda ya saka Abbun zuba masa ido bako kyaftawa sbd baimasan da maganar aurenba dan fammah bata fada musu ba.
#MAMUH
#JEERAHS
#DR MUM FAMMAH
#BROTHERS
#RAHEEM HAKEEM JEERAH
#MUHAMMAD NASIR IBRAHIM

GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171
AccessBank maryam sani gummi
[09/05, 4:16 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

13
*_HARGITSI_*
By
*_TALATU ZAKI_*
+201031621512
*Duk maaboci kuma masoyin karatun littafin Hausa to karya wuce labarin nan bai karantasa ba sbd duk wani tsari da labari yake buqata to akwaisa tattare a cikin labarin HARGITSI Na TALATU ZAKI*🔥
https://chat.whatsapp.com/ERrtA3G4obwBQzBTiJUad3?mode=gi_t

*********
Abbu har a cikin zuciyarsa wani irin zazzafan kishin yarsa da bacin rai ne ya rufesaai tsananin daya kasa dauke idanuwansa daga hakeem dayake kallansa yana fada sbd zai qara aure fammah na cewa zata rabu dashi.

Numfashi me sanyi da mutuwar jiki Abbu ya sake yana jin nauyin kirjinsa na qaruwa ciwonsa na son tasowa amma cikin karfin hali ya bude baki yana kallan hakeem din yace

'To kai Hakeem da gaske auren zaka kara a yanxu da iyalinka batada lafiya sosai ko tafiya fa kanaga bata iyayi sai an riqeta,
Batada cikakkiyar lafiyar komai da komai harma da kwakwalwa dan kuwa ayanzu datake cikin ciwon da fiyeda shekaru biyu tana jinya a kwance komai sai anmata ga mahaifiyarta ta rasa ga danta kun rabata dashi kuma zaka iya aure ka tafi gurin wata kai ka huta
Kasan da baqin cikin duka wannan lamarin da wanda zasu kara mata zai zama ajalinta??

Shi auren bazaa iya hakura dashi ba zuwa gaba ba kodan darajar dan dayake tsakaninku???

Shiru Hakeem yayi sbd yasan ba abune mai yiyuwaba tinda ko yanzu tafiyar nan zuwa Morocco da sukai ta saka aka qarawa auren sati uku yanzu sunyi biyu saura kwanaki kenan daurin auren dan kuwa su acan anacan an fara shagalin bikin tini amarya na cikin lalle an saka.

Rasa abin fada yayi sbd shima duk yanda suke tinanin a fasa auren yanayi yana kuma fada amma bazai taba iya bude baki ya cewa iyayensa aa ba sbd ita fammah ma ana auren daga india idan ya baro Nigeria so yayi ya dauketa su tafi America tare amma gashi lamarin na neman rikice masa.

Bude baki yayi ya bawa Abbun hakuri da tabbatar masa auren bazai saka fammah ta kasa samun kulawansa da kaunarsa ba har abada.

Ganin duk yanda ya fito fili ya roki alfarmar a daga auren daga hakeem bazai yiyuba sbd abinda ya nuna masa bazai taba iya bijirewa iyayensa ba akan komai dan haka Abbu daya rasa abin yi magana yayi da fammah wadda ta gama yanke hakeem daga zuciyarta har abada matiqar zaiyi auren nan da ko rasuwar mahaifiyarta bazai saka a daga mata kafa ba idan bazaa duba yanayinta ba da depression ma tini yake kokarin illata kwakwalwanta.

Abbu kai tsaye ya zabi bin bayan yarsa sbd tako ina yasan anci Amanarta an cutatar da ita an kashe rayuwarta an gama illatata tako ina dan haka babu amfanin zama a cikin mutanen dasukeda tsananin qabilancin da kansu kawai suka sani gwara ta dawo hannunsa kawai ya nema mata lafiyarta data rasa.

Tsayuwa akan raayin fammah da abbu yayi ya saka zancen zama babba har saida su Alh babba suka shigo akaita fama har lamarin ya fara zama babbar matsala me girma,

Sudai jeerahs basu taba hada sunansu da mutuncinsu da komaiba har abada dan haka maganar janye auren Hakeem sam bata taso ba suna dai bada hakurin ayi hkr fammah ta dawo ga mijinta tayi hakuri zasu kula da ita sosai zasu nema mata lafiya kuka bazasu bari hakeem ko kishiyarta su shiga haqqinta ba amma dai ba maganar fasa auren da anacan an fara biki.

Wannan maganar tasu ta sake ciresu daga zuciyar fammah sbd ji da tabbatarda ana can ana bikin ma kenan,
Babu sauran mutunci ko raayin cigaba da zama da hakeem da jeerahs a rayuwarta dan haka a gavan su Alh babba ta dago idanuwanta ta yanke dukkanin wata kauna a tsakaninsu ta maimaita ta gama zama da hakeem da familynsa bata buqatan sake rayuwa a cikinsu har abada.

Mamakinta sosai su Daddyn sukai hakama hakeem mamakinta kashesa yayi yanda iyayensa suka basu hakuri suka rokesu akan komawarta amma ita zuciyarta ta gama bushewan da taurin kai dana zuciya hakama Abbunta ya tsaya cak akan raayin yarsa dan baiga alaman zata samu kwanciyan hankali a tattare dasu ba.

Duk yanda hankalin hakeem ya tashi ya shiga mummunan tsoro da tashin hankali sbd yana tsananin son fammah kaman rayuwarsa bayajin ma zai taba iya rayuwar jin dadi idan bada itaba amma kasa barin girmansa da zafinsa yayi ya zube dan kuwa bayajin shima zai bari ta shimfida masa sharadi ya hau sbd shine yake aurenta ba itace take aurensa ba,

Idan har ta zabi ta rabu dashi sbd auren daya fada mata baso yake ba to shikenan zai bata abinda take son dan kuwa a matsayinsa na cikakken namijin dayake shugaba a dagar yaqi mace bazata juya sa ba ga iyayensa sun roketa da kansu amma ko gezau.

Dagowa yayi ya kafeta da ido daidai nan Ammin cairo ta shigo palon itada SHAKUR babban danta wanda yake balaraben asali ta uwa data uba kaman Fammah din.

Gefen Fammah ya zauna cikeda kulawa ya kalleta yana mata larabci da turanci akan duka abinda yake faruwan sbd lawyer ne babba kuma shine zai zama cikakken lawyer dinta a komai daga yanzu.

Dagowa fammah din tayi da idanuwanta da sukai jajir ta kalli Shakur din tai masa kalma daya tak da labari ya dan gyada kai natse suna maida kallansu kan Alh babba dake magana alama ransa ya fara baci da hukuncin da abbu ya tsaya akai.

Hakeem kuwa da idanuwansa sukai mummunan jajir hatta jijiyoyin kansa sun fito yanayinsa yayi munin gani idanuwansa ya tsayar akan Shakur dake kusa da fammah wadda ta riga ta kafe babu abinda duk duniya yanzu dazai sauya raayinta dan kuwa koda son captain hakeem jeerah zai kasheta ta zabi hakan tafison ta mutu amma ta gama dashi har gaban abada.

Jeerahs basu taba sheda karfi da taurin zuciyar larabawa ba sai a yanxu dan kuwa wata irin zafi da bushewan da suka gani a tattare dasu ya saka lamarin komawa bacin rai da zafin kishin daya rufe idon hakeem sukai fada mara dadin daya sakasa ajiye mata takardar rabuwa da ita kaman yanda ta buqata.

Tsananin zafin juna da wata irin tsanar juna da jin har abada sun gama da juna suka rabu akai wanda iyayensu suma suka rabu akai tareda fizgewa da cire juna a zuciya da rayuwa kwata kwata.

Sun barin qasar suna dawowa da kwana shida aka dauka aurensa da sabuwar matarsa Fadeela.

Aurensa da fadeelan ya karbesa ne a yanzu da hannu bibbiyu sbd zafi da radadin fammah dan haka yake kokarin yin rayuwarsa hankali kwance,

A bangare daya kuma ga fatima da tashin hankalin duniya tana cikinsa na wannan rabuwar data gama sanin ba abu bace me gyaruwa sbd sanin halin Fammah da kakkaifan raayin da babu wanda ya isa ya sauya mata shi.
Chapter 13 · 0% Book details