← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 154

Sashe 72

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna gama aikin ta wuce bedroom dinta tayo wanka ta sauya kayanta anan ta saka riga da skirt na soft cotton lace pink da touch of ash kadan mai tsadan data sakasa kwantawa sosai da rashin nauyi ko kadan.

Tana fitowa palon zaunawa taso yi taci abinci Mommy tace ta dauki abincin suje itada safiya sukai wa su Dr Mum.

Batai musu ba sbd daman dole zataje ta gaidasu dan haka wayarta ta dauka a natse ta dauki dayan basket din suka fito.

Koda suka isa bangaren ba kowa a palo sai qamshi da sanyi ne kawai yake tashi.

Hanyar dining suka nufa suka ajiye kayan safiya na cewa

"Bara na shiga kitchen na sanarwa su nafisa"

Fidda kayan daga basket SANAAH tafara kokarin yi saiga Maamah ta fito palon tana waya cikin farin ciki sosai da Al'amin data karbi numbernsa ta kirasa suna waya cikeda farin cikin jin juna tana jin kaman ta janyosa gabanta ta rungume ta saka masa albarka.

SANAAH ajiye abinda takeyi tayi ta iso gurin Maamah din wadda tana ganinta ta sake washe baki tana kamata a natse suka zauna tana cigaba da waya.

Ganin wayar ba gamawa zasuyi yanxu ba ya sakata kallan SANAAH tace

"Kije dakin Dr Mum dinku ki gaidata"

Miqewa tayi ta nufi bedroom din ta dan buga kadan kafin ta bude a natse ta shiga da sallama a tsanake.

Ba kowa a dakin da alama tana bathroom dan haka zaunawa tayi a sofa a natse tana shaqar kamshin dakin mai dadi da sanya nutsuwa na Dr Mum.

Tana zaune tana jiranta aka buga kofar a natse tareda budewa.

Juyawa tayi ta kalli kofar daidai sako kansa ciki shima yana kallan ciki take idanuwansu suka shiga cikin na juna ta dauke nata da sauri tana dan juyowa.

Takowa yayi a tsanake da kwarjininsa ya qaraso ciki tareda sake kallanta kafin ya zauna a gefenta kan sofan datake zaune sbd guda daya ce mai fadi a dakin.
#MAMUH
09033181070
[14/05, 1:43 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

67
*ZUZEAM VENTURES*
08144015291
EID MUBARAK PROMO PACKAGE
Gara basa gara basa da 7500 dinki
duk wadda ta bari promo nan ya wuceta tayi hasara ba karamaba don wannan ya wuce duk tunanin ku kayan dake ciki ko 50k ka siyesu bakayi hasaraba bare 7500 hmm inba gurin Zuzeam ba wazai muku wannan gatan
1. Tabajen kankana
2. ⁠Gumbar aya da ridi
3. ⁠Tsimin mallaka mai maganin infection
4. ⁠Garin dadi har madiga
5. ⁠Hadin dafa kaza ko Ciccibi ko nama, Kinga yanzun sallah za ai nama ya wadaci kowa hajiya kina iya dafa nama tsoka 7 da maganin ki zai miki mallaka naban mammaki zai ciko miki da gaba zai kara miki dadi da dandano.

Sannan mutun ashirin na farko nada kyautar Turaren tsugunno na mallaka gagara badau 5k

Ina amaren bayan sallah wannan hadin ya dace daku ko mai jego wadda take shirin haihuwa ma Tana iya siya ta aje ko shekara yanayi bai komi
Ina Uwar gida maiji da kayanta wannan hadin nakine
08144015291 For more information say hi,
Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam ventures tashirya tsaff dominku muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu
DAHUWAR KAZA
Kin taba cin DAHUWAR KAZA 5in1 wato Ni’ima,Matsi,Chikowa,MAllaka da Karin soyayya Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt Akwai kyauta mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya.
INA MASU JEGO DA AMARE
Karku bari wannan dama ta wuceku 08144015291 Zuzeam ventures.
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar gıda set
Mai jego set
08144015291

*********
Motsawa tayi ahankali tareda dan dagowa batareda ta iya juyowa ta kallesa ba ta bude baki tace

"Ina kwana"

Fararen idanuwansa ya juyo ya kalleta dasu kafin ya bude baki kai tsaye ya amsa gaisuwan tata da sautin muryansa daya ratsi kunnuwanta da wata irin nutsuwan data sakata dan sake motsawa tana jin son tashi tabar dakin.

Sake bude baki yayi ya jefa mata tambaya a wata irin gajarcewa da tsantsan ilimi da turai data ratsesa yace

"Dr Mum??

Kai tsaye cikin kunnuwanta maganar ta shiga zuwa cikin kanta da kirjinta sbd muryansa wani strong aura ne da ita da babu wanda zai jita a tsanakenta da kamewanta ba baijita a tsokar jikinsa ba dan haka ahankali ta dan qanqame hannunta daya ta dago idanuwanta tareda kasa hana kanta juyowa a hankali ta kallesa da idanuwanta da babu abinda ya raba kamarsu sak da sak da Nasir.

Jin saukan idanuwanta akansa ya sanyashi sake juyowa ya kalleta da idanuwansa dake fizgar duk ajin mace akansa..

Kasa motsawa tayi hakama kasa fidda numfashi tayi idanuwanta na kokarin daukewa daga kallansa yace

"Menene say dinki akan abinda yake faruwa??
Idan kinada kowane raayi akan hakan zaki iya sanar dani"

Kaman daga sama taji zancen dan haka ta sake kallansa gabanta na dan faduwa sbd a yanxu batada say ko wani raayi akan komai sai yanda akai da ita.

"Karki komai just fadi abinda kikeso akan auren"

Dagowa ta sake yi wannan karan bata iya kallansaba sbd idanuwanta dasuka narke kaman zasu tara hawaye ta bude baki zatai magana kenan Dr Mum ta fito daga bathroom din a shiryenta tsaf da doguwan riga baqa daman tayi wankanta alwala ta koma tayo dan bata son zama ba alwala a jikinta.

Da wata irin sakewa da kauna mai tsananin karfin gaske ta kalli SANAAH tareda bude hannuwanta tana cewa

"Y'allah habebty"

Tasowa SANAAH tayi ahankali ba rashin wayewa ta shiga jikin Dr Mum din tana cewa

"Ina kwana Mum"

Amsawa da farin ciki dr mum din tayi kaman ba itace mai fada da bacin rai ba jiyan itama ta tashi ranta fes batada sauran kowace damuwa bayan ganin SANAAH ta samu right dinta a hannu.

Shi kansa RAHEEM din albarkacin ganin SANAAH ya samu da sakewa da kulawa ta gaisa dashi tana tambayar Meenah da Fammah.

Amsawa yayi da tsanaki kafin ya kalleta lokacin datake zama tareda SANAAH a gefenta tana riqe da hannunta yace

"Maganar gurin zamanki danai miki alkwari ya kammala zaku iya shiryawa zuwa anjima kadan a kaiku"

Kallansa ta juyo tayi babu alamar nauyin komai ko tina komai hankali kwance tace

"Wane gidan kenan??

Kallanta ya dago yayi yana karantar yanayinta na dagaske take tambayar yace

"Gidan da zaki bar nan ki koma"

"Kabarshi kawai na hakura zan zauna anan din"

Kallanta ya kuma dagowa yayi ta kame fuska .

Baice komaiba jin abinda ta fada kawai yayi mata sallama ya fice yabar dakin.

Yana fita ta sake fuska tana kallan SANAAH da kulawa tafara kokarin mata tambayoyi akan karatunta da zaman Gidan.

Anan taji inda SANAAH din take zaune tayi shiru tana juya lamarin a ranta wanda kusan su dukan zasusha wuyar hakan dan gwara Meenah batasan da kishiya take zaune ba ita kuwa data san meenah matar mijinta ce zatafi shan wuyan abubuwan da idonta zai gani ba daman nuna damuwa hakama bazata taba samun daman kebewa da mijinbama.

Fitowa sukai tare tana sake magana da SANAAH din wadda take cikeda jin nauyinta.

Har lokacin Maamah waya takeyi dan haka kai tsaye dining suka nufa inda abincin da suka kawo.

Maamah na gamawa acan ta samesu dan haka acan suka gaisa suna zaunawa su duka hadda SANAAH din da Dr Mum tace ta zauna taci a cikinsu.

Suna cin abincin suna magana da SANAAH din da nuna kulawa wata kauna mai karfin gaske har suka gama.

Suna baro dining din Ms Meenah na shigowa gaida su itama tana ganin SANAAH ta fara nuna kulawa da mata fadan ta dena fita batareda ta tsaya taci breakfast dinta ba.

Da mamaki dr mum ta kalli Meenah din kafin ta amsa gaisuwan datake mata da kulawa alaman ta sauko daga bacin ranta dan haka farin ciki ya cike meenah ta zauna tana gaida Maamah da fara zuba tana nuna ita yanxu ta zama yar gari da nuna iko iko akan SANAAH a matsayin uwa.

Maamah tausayinta taji ya ciketa sosai dan haka ta ringa nuna mata kulawa da kauna sbd a yanzu kam sedai kowa yayi hakuri Dr Mum bazata iya hada kaunar SANAAH da kowaba duk da bazata taba qin Meenah ba sbd itama tatace.

Ita kanta Dr Mum din tausayin Meenah taji tana ji sosai sedai ba yanda zasu iya wata kusan tafi wata hakama soyayya da tsantsar kaunar datake wa Nasir kai tsaye daga jiya xuwa yau ta koma akan SANAAH.

Anan bangaren suka wuni gabaki dayansu sunata walwalwansu hadda mommy nan ta taho suka wuni suna shaaninsu.

Sai dare kowannensu ya watse kai tsaye Dr Mum tace abar SANAAH anan tayi zamanta tukuna.

SANAAH da daman hanya take nema take ta amince da lallaba fammah da dadin baki da shagwaba har famman ta amimce tana tsokanarta da cewa indai dr mum ce kwana biyu zata sha fadanta da saikayi kwana biyu kana zazzabi.

Wani nutsuwa da farin ciki SANAAH taji na baro bangaren dan haka ta sakewanta anan gurin su Dr Mum.

Washe gari itace ta rigasu fitowa ta isa kitchen ta saka hannu a shirin breakfast dinsu tana gama jerawa suna fitowa kusan a tare.

Sunci sun gama kenan saiga Ms Meenah tazo.

Tana gaidasu ta zauna ta kalli Maamah tace

"Maamah dan Allah kiwa fleet magana ko zai amince a bani bangare na daban sbd ko SANAAH ta kasa sakewa sosai a bangaren sbd muna guri daya da Dad din nasu inason inda zamu sake sosai"

Dr Mum dake duba sako a waya dakatawa tayi ta juyo tana kallan Meenah din cikeda mamaki dan kuwa ita kadaice haka a cikin mata tana ganin.

Maamah ma kallanta tayi dakyau kafin tace

"Kina tareda mijinki zaki nema raba guri Meenah?
Kinfi son ki ringa yawon zuwa kullum gurinsa kenan?

Gyada kai tayi tana dan nuna kwantar da kai tace

"Maamah sbd yaran kinga sun zama yan mata muna guri daya dasu gwara a bamu gurimu din zaifimin na ringa zuwan"

Kara bata shawaran tabar maganar maamah tayi tana lurar da ita illar hakan sbd zai iya zamana sun iya fara samun rashin kusanci anan din,
Chapter 72 · 0% Book details