← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 154

Sashe 17

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba mutum ne shi mai boye boye ba ko shakka dan kuwa duk ladabinsa ga iyayensa shi mutum ne da babu tsoro a tarihin rayuwarsa babu shakka babu abinda baya iya fada a gaban kowa koda kuwa iyayen nasa ne sun tabbatarda sun shedar da baya shakka idan har ya fada abu to babu shakka zaiyi idan kuwa ya furta ba damar hakan to kuwa kaf duniya babu wanda zai sauya masa raayi dan hakan ne su kansu suke tsananin gudun ranar dazai musu aa dan kuwa aa dince.

Da kansa ya sanar da mahaifinsa Aure zaiyi ya samu matar dayake raayin aure a Morocco.

Tinda Dad din yaji hakan yasan burin dr fammah ne zai cika mata dan kuwa daman yasan bazata taba barin danta yayi aure anan ba hakama shi tinda danta ne tanada iko da umarni akansa bazata taba barin ya qara aure ba har abada bare tinda kabilarta ce matar kenan wani auren ya haramta ga Raheem....

Tsananin daci da baqin ciki harma da bacin rai me tsananin gaske ne ya sake rufe zuciyarsa a karo na biyu tin bayan rabuwarsu amma idan har yaqi aminta da auren da Raheem zai samu matsala dan haka ya amincewa auren amma bazai taba barin ta samu nasarar sakawa danta kabilancinsu ba dan kuwa Raheem jinin jeerah ne kuma a yanxu ba yaro bane da zai zauna akan raayin wani cikakken dan raayin kansa ne da shi kansa yana shakkar irin kaifin da zaiyi da riqon raayi da akida dan haka a yanzu shi kam ya aje makaman zafinsa akansa.
#MAMUH

GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070
[09/05, 4:16 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

17
Maganar auren CAPTAIN RAHEEM HAKEEM JEERAH ta bayyana ga family da duniya dan haka aka hau murna familynsa kuwa babu wanda yayi farin ciki ko murnan hakan sbd inda matar ta fito dan haka kusan duka wainda suka mugun saka rai akansa da mutuwa akansa na familyn suka cire rai dan kuwa sunsan kabilar da aka auro da kuma sanin shi din bama me yiyuwa bane yin mata biyu a rayuwarsa sbd miskilancin rayuwarsa yayi bacin da ko mutane baya buqata sosai dan haka babu yanda zai iya mace biyu tinda ta farkon ba sunsan aikin mahaifiyarsa ne bawai yanada raayin auren ba.

A nasa bangaren yayi iya kokarinsa ya budewa Meenah wahab zuciyarsa ko zata iya shigewa duka dan kuwa baima san ta inda zai fara ba kawai dai yasan baisan ya ake so ba idan ta shiga kila zata koyar dashi harma ta samu mallakar zuciyarsa dan matiqar zata iya hakan shi baida matsala tinda itace zata mace daya a rayuwarsa har abada baya buqatan wata.

Aurensa ya saka shirin tafiyarsu Nasir sake kankama dan har service dinsa ya gama ya hada komai na takardunsa,

Shi kwata kwata baa Nigeria zai zauna da matarsa ba sbd nasa raayin kenan sbd ya shirya bawa matar da zai aura dukkanin kulawa da kaunarsa sbd ta rabu da iyayenta da rayuwarta ta zabesa dan haka she deserves dukkanin kauna da kulawa daga garesa shi kadai batareda kowa ya bata kowace irin damuwaba.

Zainab nada ciki tsoho aketa shirin tafiyar tana jin tsananin kewa da kadaicin rabuwa dasu amma kuma tana musu farin cikin tafiyar dan haka ta fidda kudadenta tana musu abubuwa da dama da zasu tafi dasu hakama ta saka hannuwanta da kanta tayiwa dr mum lafiyayyar gyada da cashewnuts da akace tanaso a lokacinda tayi zama Nigeria tace a kai mata tsaraba.

Ana saura sati biyu tafiyarsu a lokacin ne CAPTAIN RAHEEM jeerah ya sauka Nigeria dan daga nan zasu wuce Morocco,

A daren ranar daya sauka din Nasir a jeerahs ya kwana cikin tsakiyar dare guraren karfe biyu da mintina kiran wayar baba khalil ya shigo wayarsa.

Da mamaki da tinani ya dauko wayar cikin bacci daga gefen gadonsa kan bedside drawer yaga baba khalil ne me kiran.

Tashi zaune yayi a natse yana daukan kiran cikin shakka ya ambaci sunan baban.

Baba khalil dake tsaye akan Zainab dake gap da rasa rayuwarta maamah na riqe da ita ajiyan zuciya ya sauke tareda fadawa Nasir din yazo da sauri akai zainab asibiti jikinta yayi nauyin da ankasa karban haihuwan a gida dole asibiti zasu.

Baccin dake tattare da Nasir sakinsa yayi gabaki daya ya ziro kafafunsa qasa ya miqe ya tsaye yana sauya kayan jikinsa cikin sauri ya zari mukullin motarsa ya fice batareda yaje dakin Raheem ba ya sanar dashi.

Kai tsaye gida ya nufa yana isowa suka dauki zainab din zuwa asibiti hankali tashe sbd yanayin jikinta.

Private asibiti me kyau da Nasir ya dauki nauyin tana zuwa awo suka nufa,

Suna zuwa aka amsheta akai ciki da ita sukuma suka tsaya jiran abinda zaa fito ace musu cikin damuwa da tinani kala kala.

Takardun biya wasu abubuwa aka miqo musu bayan mintina da shiga da ita dan haka Nasir ne ya karba ya wuce pharmacy dinsu.

Yar dadewanta tana naqudar datazo mata gadan gadan ya saka lamarin yake neman lalacewa dan haka aka fara dubarun yanda zata haihu da kanta amma abin ya gagara ga bp dinta yana hawa dan haka aka ringa kokarin controlling dinsa.

Cikin tashin hankali da damuwan mummunan halin da mommy zainab ke ciki akai asuba dole aka yanke shiga tiyatar gaggawa da ita.

Kudin komai da komai Nasir ya biya suka wuce lap bada jini da aka nema roba biyu dan haka shi da baba khalil dinne zasu bada daddaya.

Suna shiga lap Raheem ya kirasa dan bai gansa ba a gurin sallan asuba.

Sanar dashi komai yayi kafin suka kashe wayar.

Geamin kadai yayi wanda ya saba kaman cikon rayuwarsa ne datake farawa kowace safiya baya taba missing bai tsaya breakfast ba ya fito sanyeda sweatset riga da wando black na original balenciaga da suka nutsu a jikinsa ya sako hular sanyi black ta bvlgari data boye gashinsa dayake kwance da tsayi sai facemask daya rufe fsukansa da ita itama black sbd bayason yawan kallo kuma duk inda ya shiga a Nigeria idan yaxo kallansa akeyi dan haka bai cika rabo da mask ba, sai sneakers a kafafunsa na Original.

Ko daya iso Asibiti an gama diban jininsu Nasir din suna lab baa basu daman fitowaba kuma da gaggawa ake buqatan shiga da Mommy zainab din dan haka kai tsaye Shi Baba khalil ya cewa yaje kawai ya saka hannu a takardar aikin

Boyayyan numfashi me dumi da nutsuwa ya sake kafin yayi signing a takardun da aka gabatar masa na shiga tiyatar.

Maamah ce a tsaye dashi aka shige tiyatar da ita dan tini likitan da zaiyi tiyatar ya iso asibitin.

Cikin ikon Allah da yardarsa akai aikin cikin nasara ciro mata Baby girl dinda babu abinda ta baro na mahaifinta sai hasken uwarta wadda ana fitowa da ita daga ciki cikin showel dinta fari tas mai laushin gaske Raheem jeerah Nurse ta miqawa babyn cikeda girmamawa da kulawa sbd ganin shine ya saka hannu a takardar shiga da uwar.

Cak Raheem ya tsayar da idanuwansa akan babyn wadda take motsawa ahankali fara tas da ita idanuwanta a rufe yaji zuciyarsa tayi wani irin dum sbd bai taba daukan baby ba a rayuwarsa sau din shi baima taba kasancewa a zahiri da baby ba sbd bayama tareda dangi bare ayi haihuwan da zaije yaga baby,abokan aikinsa biyu suka haihu amma baiga babys din a zahiri ba a waya kawai ya iya ganinsu yayi musu barka dan haka sai yaji kaman bazai iya daukan babyn ba sai da Nasir ya matso gurinsa ya kallesa kafin ya kalli babyn Baba khalil ya bude baki yace

'Captain ka karbeta ai kune iyayenta'

Amsarta yayi a natse tareda sake sauke numfashi mara sauti yanajin wani irin nauyi a hannuwansa da kirjinsa ya kafeta da fararen idanuwansa ya bude bakinsa ahankali ya furta 'Masha Allah' tareda adduoi masu kyau da tsari tukuna ya kalli fuskanta a karo na uku yana ganin kamannin Nasir dinsa akan jaririyar fuskarta.

Nasir da zuciyarsa ta tsaya cak akan tsananin kaunar babyn miqa masa ita Raheem yayi ya karbeta da Bismillahi yana jinta har qasan zuciyarta fiyeda yanda yake kaunar Al'amin yayanta.

Addua yayi mata aka bawa mahaifinta ita yayi mata addua da kiran sallah kafin ya miqawa Nasir ita ya Ambaceta da suna SANAAH KHALIL MUHAMMAD.

a cikin kunnuwanta ya fara kiranta da sunan kafin ya ambata a bayyane take Baba Khalil ya maimaita sunan yana mata adduar girma da gamawa da duniya lafiya cikin aminci da tsaron ubangiji.

Maamah tayi farin cikin haihuwan zainab suna nan dan haka itace tayi jinyarta har akai sati daya aka sallamesu suka dawo gida taci gaba da kulawa da ita kafin tafiyarsu.

Baa bari sati biyu ba akai sunanta sbd idan akai sati biyu kaman yanda wasu keyi idan tiyata ce to su basa nan,

Captain Raheem jeerah ne ya aikowa da baba khalil Manyan shanu guda biyu da raguna biyu na sunan Baby SANAH sbd Nasir daya kwallafa mata rai da wata irin kauna.

Shi kansa Nasir hana baban siyan komai yayi shine ya siya mata duk wani abin buqata da kayan sakawa itada mommyn wadda tace ta cika masa alkawarinsa na cewa itace zata haifa masa mata.

A duk lokacinda suke wannan maganar tasu ta wasa dariyarsu kawai baba khalil keyi sbd yasan wasar ce tinda yaushe Kamar Nasir zai tsaya jiran girman yar Zainab harya aureta tinda a lokacin ai yayi manyancin da bama zai iya aurentaba.

Baby SANAH nada sati biyu cif a duniya Nasir da maamah suka bar Nigeria suka tafi cikeda tsananin kaunarta da kewanta bama kamar Nasir daya tabbatarwa iyayenta shine zai dauki nauyin komai nata komai zaa siyawa baby SANAH a sanar masa bai yadda suyi lalurarta ba ya dauke musu.

*****A ranar da suka isa Morocco a washe garin ranar ne daurin auren CAPTAIN RAHEEM HAKEEM JEERAH da matarsa Meenah wahab wadda tini suka fara hidimar bikim kafin isowan ango da danginsa da suka taho kusan kaf dangin Jeerah sun samu tahowa bikin.

An Daura auren daya samu halarta mutanen da bama ayi tinanin halartarsu ba kuma a cikin kwanciyan hankali da aminci.
Chapter 17 · 0% Book details