← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 154

Sashe 148

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fammah da itama kallan SANAAH din takeyi da dukkanin mutuwan jikin rashin ganin Al'amin a kan idanuwanta tsawon kwanaki sbd boyon da sukewa juna yana nesanta kansa da ita sai Dad dinta yaxo ta gansa yaje gurinsa sun hadu shima basu hadu face to face ba bai bari sun kasance tare a gaban na fleet ba sosai ya tafi wanda hakan ya sake sakawa Fleet ganin qimarsa sbd yanda yake kaucewa kowace hanyar da shedan zai iya tasiri akan zuciyarsa da amanar datake kansa na yarsu da suka basa.

Ganin SANAAH a gabanta da asalin kamanninsa akan fuskan SANAAH ya sakata zaunawa tana kallanta da rasa tinaninta da zuciyarta da walwalanta data jima da rasawa akan soyayyar da ita tata wahala ce mai karfi suke sha kawai.

Dauke idanuwanta tayi akan SANAAH tana dan sauke ajiyan zuciya da bude baki daga inda take zaunen tace

"Are you missing him this much ne da zaki mun kuka anan??

Tashi zaune SANAAH tayi ahankali tana kallan fammah da idanuwanta da suka sake marairaicewa tana neman sauko da hawayenta sai kawai ta matso kadan ahankali ta sauko gadon tana zaunawa gefen fammah da shigewa jikinta tana fara mata hawaye da kasa cewa komai sbd harga Allah tayi tsananin kewanta itama datake son fada mata abubuwa da dama amma sbd akan mahaifiyarta ne sai bazata iya fada ba dan wata kusar tafi wata hakama tasan dole har abada bazasu taba komawa yanda suke asalin asali ba sbd uwa ta daban ce.

Rungumeta famman tayi tana dan shafa bayanta da cewa

"It's ok,its ok,Dad ne???

SANAAH batasan lokacinda murmushi ya kufce mata ba ta gyada kai tana sake shigewa jikin fammah din da itama cikin karfin hali tai murmushin tana jin dadin yanda abubuwan suka koma daidai sbd tana waya da mahaifiyarta amma bata fada mata komaiba kaman yanda bata nuna mata komaiba kuma tajita a cikin wani irin sanyi da rashin son hayaniya ko kadan kaman ba itaba hakama Dad din baice mata komaiba shima da alama duka hankalinsu ya kwanta hakama babu labarin kowace tashin hankali da aka kuma yi dan haka takejin nutsuwa da kwanciyan hankali soyayyar Al'amin ce kadai take neman kasheta a cikin sanyi.

Shiru sikai na dan lokaci kafin suka saki juna suna kallan juna da murmushi da farin cikin ganin juna suna fara magana...

SANAAH miqewa tayi tafara shiga bathroom bata wani jimaba ta fito tayi sallah tana idarwa suka fito sbd yunwar SANAAH.

Dining a cike sika samesa Al'amin ya aiko da komai an jere a dinin da fresh fruits dan haka suna sallan magrib gabaki dayansu da Dad da Mum sukai dinner cikin kulawa da kauna.

Suna gamawa daki suka shige suna shigewa Fleet na shigowa gidan sanye da fararen Diors Da suka maidasa kaman sabon matashin da rayuwarsa take cikin shekarun rashin hayaniya da hutu.

Fammah Dr mum taje ta kirawa ta fito Su Dad sukai magana da ita sosai suka kuma tabbatarda raayinta akan aure ta kasa fada musu komai saidai mahaifiyarta datake nuna musu ayi magana da ita wadda jinta kawai Dad yayi yana yanke shawarar ma kawai bazaa jira komaiba zaa daura aurenta da Al'amin din a nan italy idan yaso tana qarasa gama program dinta nan da sati biyar ta koma gida ayi biki acan ta tare kawai.

Dad dinta bai musawa hakan ba dan haka kai tsaye kuwa Dad yanke daura auren Friday nan da 4days kenan.

Fleet na barin gidan Dad ya fara wayoyinsa yana sanar wainda ya kamata su sani musamman Mommy da kansa ya kirata suka jima suna magana itama kai tsaye tayi naam da duk abinda Dad zai yanke akan yayanta tinda shine uba a garesu.

Su Maamah kuwa farin ciki suka shiga mai tsananin gaske suna jin matsuwan ma ta gamo ta dawo ayi biki.

Dr tayi farin ciki sosai da hakan sosai dan haka koda ta sanar da SANAAH take taji duka damuwanta ta tafi farin cikin ganin mutane biyu datake kauna sosai zasu kasance daya.

Washe gari Al'amin a tsanake yazo gidan sanye da Fararen kaftan masu kyau da suka fito dashi wani mutum din daban.

Tareda su yayi breakfast amma banda Fammah da bata fito ba sam dan anan ta kwana tama dawo nan sai ranar da suka tafi kila.
#MAMUH
09033181070
[26/06, 4:09 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

147
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*
07042293387/09118783317
Ina masoya kamshi da gyaran jiki na asalin matan da suka amsa sunansu mata?
Kinaso/kunaso ku kasance a cikin kamshin da duk inda aka jisa a tattare dake ko gidanki sai ankasa hakuri an tambayeki?
Shuwa Incense And more itace karshen inda zaki samu asalin kamshi da abubuwan gyaran jiki da mayukan gyara gashi masu inganci da kyau wanda mukeda guarantee dinsa,
Kowace irin turaren wuta na asali na gasken a gurinta ne zaku samu wanda qamshinsa kam har nesa da maqota hakama babu kalan dilka ta gyaran fata data fuska da babu a gurinta,
Kada kubi labari kawai ku siya ku gwada..SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387.

***********
Bayan gama breakfast dinsu Dad zaunawa yayi da Al'amin ya sanar masa da komai da suka yanke take Al'amin din ya dago cikin wani irin slow da nutsuwa ya kalli Dad din wani nauyin dayake danne da kirjinsa tsawon lokacinda zuciyarsa take tsananin azabtuwa da son Fammah jeerah yaji yana motsawa da wata irin sabon nauyin yana qara toshe kirjinsa dayake jin rayuwansa bazata taba moruwaba ayanxu idan ba famman ya samu ya mallaka ba a matsayin wadda zai qarasa rayuwa har mutuwa da ita.

A irin kallan da yayiwa Dad da kasa cewa komai Dad din ya hangi wata azababbiyar soyayyar fammah dake cikin jininsa wadda yake riqewa da dannewa da duk wata karfi da jarumtarsa.

Godia kawai ya iya yi a cikeda nustuwa da cikar burin daya kasa yadda da zai cika din.

Wata maganar Dad ya janyo masa wadda sam ya kasa cirewa da dauke tinaninsa akan maganar anbasa auren fammah jeerah zata mallakinsa.

Ganin hankalinsa ya kasa dawowa daidai sam kwata kwata ya sanya Dad din sakin murmushi yana dawowa akan maganar auren wanda zaa daura a kwanaki kadan Al'amin ya zuba masa idanuwansa yana bin kowace kalma da lafiyayyan nutsuwa da bita daga karshe wani murmushin da baisan yama sakeba ya saki yana sake godiyar data saka Dad shiru yana kallansa da murmushi akan fuskansa yana cewa

"Kodai zamu bar daurin auren nan ne sai ta gama an koma Nigeria gabaki daya?"

Kallansa Al'amin yayi yana dariya mara sauti da girgiza kai yana cewa

"No no ai baka magana Biyu"

Dariya Dad yayi yana cigaba da maganar datake saka bakin Al'amin din buduwa yana magana kaman ba shi dinba da babu hayaniya rayuwansa sam.

Sun jima a tare kafin Al'amin ya fice duniyarsa na buduwa zuwa wata sabon babin dabai taba tsammaniba a lokacin.

Kasa iya kiran Fammah yayi sbd baisan tayaya zasu iya magana da juna ba kaman yanda sukai kwanaki batareda ji ko ganin juna ba.

SANAAH ce ta kirasa sukai magana tana tayasa murna fammah na zaune tana duba abu a waya tana jinta tana kuma jinsa shima baisan me zai fadaba sai kame kame yake nasa farin cikin bame iya rawan kai bane jinsa yake har jijiyoyinsa dabai san yaya zai iya fidda abinda yake jin dinba sedai a cikin tsakiyar idanuwansa da zaa iya karanto zazzafan yanayin dayake cikinsu da babu me iya kallan cikinsi idanba fammah dinba kila itama hakan ba qaramar karya garkuwan jikinta zaiyiba idanma ta iya kallan cikinsu kenan.

Shi kansa sanin fammah na tareda SANAAH din a lokacin ya sanyasa kasa kowace irin doguwan magana hakama itama datake jinsu shirun tayi tana sauraron kalamansa da basuda kowace hayaniya.

Da daddare dukansu haka suka gama surutunsu sukai bacci SANAAH na lafewa damuwanta kowane dare na tasowa na rashinsa dake cinta a ciki kaman zai kasheta.

Washe gari fita sukai tareda Dr Mum wadda zuwa wani tsadadden luxury spa da kusan acan suka wuni gabaki daya ana gyara sai dare suka dawo abinci kadai SANAAH taci ta kwanta sbd dan zazzabi da damuwanta datake tasowa ta rashin Fleet wanda shi kasa hakurinsa ya gama qarewa tako wane bangaren babu sauran kowace nutsuwa a tareda shi dan hakanne ma bai sake zuwa gidanba har aka biya sadakin Fammah din wanda Al'amin dinne ya biya da kansa da dollar kuma sun karba.

Washe gari haka suka sake fita basu wuni ba basu zauna ba sai dare dan haka ranar da akai kwana ba uku basu fitaba koina sbd SANAAH da sam ta kasa jin dadi duk da tayita daurewa sbd kada ta hana komai na hidimar.

Har ayau da ake gobe daurin auren Fammah da Al'amin din basu hadu ba bare yin magana sbd a nasa bangaren ya kasa iya zuwa ganinta sbd nasa son mai zafine da yake rasa kansa gabaki daya idan yana ganinta dan hakanne ya saka yake nesanta da ita tin farko sosai,

Ko a yanzu dazai mallaketa jin yakeyi bazai iya kasancewa a guri daya da itaba har sai anyi bikin da ake buqata an basa ita gidansa.

Wunin ranar gidan da wani irin farin ciki sosai harda Sammy ma tana gidan da wasu abokan karatun famman data hadu dasu anan suka wuni sai dare suka watse.

Washe gari da wani irin mutuwan jiki rashin sanin tinanin yi fammah ta tashi sbd Mum dinta batai maganar aurenba kuma ita ta kasa sanin yanda zata fada mata karshe dai Dad ne ya kirata ya zaunar da ita ya sanar da ita ya kwantar mata da hankali da sanar da ita sai bayan daurin auren kafin ayi biki ta tare zaa kaita gaban mahaifiyarta a fahimtar da ita komai.

Sosai ya kwantar mata da hankali harta samu nustuwa ta fito ta dawo daki tana jin zuciyarta na bugawa da sabon bugu mai sanyi da nauyi na rayuwar da zata hau kanta ayau da zata xama matar wani itama.

SANAAH cikin kulawa da kauna da jin ranar itama har cikin kirjinta zaunawa tayi gefen famman tana dan kwantawa jikinta tace

"Zakiyi rayuwan farin ciki mai dorewa da Yaya Al'amin insha Allah sbd yana miki son dabai san iyakansaba son da baisan yaya zuciyarsa zata iya daukaba"
Chapter 148 · 0% Book details