← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 154

Sashe 12

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kati da duk abubuwan bikin dake trending saratu ta nuna mata a waya ta zubawa wayar ido zuciyarta na kasa yadda har lokacin daga karshe ma jintane da ganinta suka dauke dan haka da gaggawa Fatima da itama ta kasa yadda ta kira hakeem din.

Kafin hakeem ya iso gidan daga inda yake nesa sosai mummunan kiran daya qarasa dakatar da rayuwar fammah cak ya shigo wayarta Na rasuwar Mahaifiyarta Ammi.

Mummunan halinda ta shiga dole akai gaggawar kiran ambulance wadda dole itace zata iya kaita asibi sbd ta sanqame.

Duk inda ake shiga tashin hankali fatima ta shiga ta firgita ta rasa inda zata saka kanta.

Kowa ya shiga fargaba da tashin hankalin ganin halinda fammah ta shiga dan haka aka fara gaggawan hada tafiya da ita Morocco din.

Shi kansa hakeem tashin hankali da damuwa kashi kashi yake ciki dan haka ya matsu yaga ta farfado.

Fatima dai bata wani shiga cikin ahalim jeerahs dinba tana gefe da Nasir da Raheem da baya wani yadda da kowa idan ba ita ba sai mahaifiyarsa da baima san itace cikakkiyar uwar data haifesa ba.

Fammah jikinta yayi nauyin da bata farka ba sai washe gari kuma tana bude idanuwanta akan Hakeem suka sauka wani abu yaxo ya danne maqoshinta da kirjinta sedai rashin uwarta datai a yanzu shine abinda yake gabanta dan kuwa ta rasa duniyarta kenan.

Bata cewa hakeem komaiba ko kalma daya bata iya furta masa ba abu daya ta nema daga iyayensa da kanta shine tafiya gida a cikin wannan halin datake ciki taji ta gani.

Iyayen nasa sun tausaya mata sun kuma jajanta rashin mahaifiyarta.

Babu wanda tayiwa maganar auren Hakeem kaman yanda bata bawa kowa damar yi mata maganar auren ba har iyayensa kuwa.

Da zatai tafiyar akace tabar Hakeem tinda ya isa yayewa kuma daman ba wani sosai yake shan nonon nata ba sbd yanayinta da kuma jinyar da zatai ga rasuwan Amminta.

Wani nauyi ne mai tsananin gaske ya sake danne kirjinta kaman zuciyarta zata kama da wuta haka take ji dan haka bazata iya hayaniya ba tinda ba lafiya a tattare da ita kwata kwata.

Fasa tafiya da fatima tayi tace ta zauna da Raheem a matsayin yar rainansa tukuna.

Fatima ta shiga tashin hankali sbd tsoron abinda take gani a zuciya da idanuwan fammah akan duka abinda yake faruwa amma batada zabi haka ta zauna aka tafi da fammah tabar mata 'danta RAHEEM wanda zatai zaman renansa a jeerah a matsayin Nanny.

A daren da zasu tafi sai a wannan daren ne fammah ta fasa wani irin kukan daya saka fatima sauke kai itama tana tayata kukan datake jin yana ratsa dakin da tsananin tsima.

Washe gari da asuba jirginsu ya daga da fammah da Hakeem dama su Daddy da ummah da zasuje gaisuwa dukansu.
#MAMUH
#FLEET RAHEEM JEERAH
#MUHAMMAD NASIR IBRAHIM
#S.A.N.A.H

GANIN IDO 2026
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070
[09/05, 4:16 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

12
*_HARGITSI_*
By
*_TALATU ZAKI_*
+201031621512
*Duk maaboci kuma masoyin karatun littafin Hausa to karya wuce labarin nan bai karantasa ba sbd duk wani tsari da labari yake buqata to akwaisa tattare a cikin labarin HARGITSI Na TALATU ZAKI*🔥
https://chat.whatsapp.com/ERrtA3G4obwBQzBTiJUad3?mode=gi_t

*********
Bayan tafiyar Fammah daga Nigeria fatima jin tayi tana rasa nutsuwarta da kanta dan kuwa kadaici ne ya sakota gaba da kewa da damuwa,

Babu wanda aka bari a tareda ita a bangaren daga ita saisu Raheem da nasir sai kuma saratu,

Babu me zuwa bangaren kwata kwata sedai duk safiya idan tayiwa su Raheem din wanka suka sha nono ta hada musu da cereal da sukesha zata kai Raheem can gurin su Ummah sbd abinda akace mata kenan.
Acan zai dan wuni saiya gaji yayi bacci a dawo dashi sai kuma washe gari ta sake kaisa.
tin tafiyar batai nisa ba rayuwar ta sauya mata kwata kwata musamman da duka su biyun qyuya ne dasu basa wani yadda da mutane ko Raheem dinma daga baya yadda da kowa a cikin familyn bayan Mamma dinsu fatima da ita suka sani.

***Isar su Dr fammah qasar Morocco har lokacin babu wanda tacewa komai dan kuwa kwata kwata idanuwanta a rufe suke ma ruf babu alaman idonta biyu dan hakane kowa ya qyaleta ta samu dan rintsawar sbd tana buqata ko dan yanayinta dakuma damuwar rashin mahaifiya.

Hakeem dake zaune a kusa da ita ya san idanuwanta biyu dan kuwa yanada tabbacin babu baccin da zai dauketa a rayuwar dasuke kai yanzu,

Duk yanda yaso mata magana ganin suna tareda iyayensu yayi shiru shima dan kuwa ko jirgin dasuke cikinsa zai juye dasu yayi fata fata bazata taba tankasa a yanda yasan zuciyarta.

Kallanta yakeyi a kai akai harya hakura ya dena kallanta ya kama nasa girman sbd kada ya zamana kaman yana shakkarta ne.

Ita dai a nata bangaren batajin akwai wani a cikinsu dama danginsu dake gida da suka rage da kowace qima ko daya a idanuwanta jinsu takeyi tamkar wainda zama guri daya dasu yana danne numfashinta.

Motocin da familyn Jeerahs din suka tanada ne suka taho airport suka daukesu guda uku na alfarma kai tsaye gidan iyayenta suka nufa.

Suna isa koda fammah ta hada ido da mahaifinta wata irin rawa jikinta yafara ahankali kafafunta na kasa daukanta sbd sama da shekaru uku kenan bata sakasu a idanuwanta ba tin wani zuwan datai ganin gida ta koma,

Kasa iya daga kafafunta tayi ta sauke kanta ahankali wasu irin hawaye masu tsananin zafi suna gangaro mata abbun da kansa ya taso ya iso gareta daidai Hakeem ya miqa hannu zai kamata sbd har lokacin daman bata iya tafiya ita kadai da kanta sai an taimaka mata.

Abbunta ne shima ya miqo mata hannunsa ta kama a sanyaye batareda ma tako kalli inda Hakeem yake bare ta nuna tasan da mutum,

Kuka ne mai karfin gaske ya taho mata take mahaifinta ya rungumeta yana lumshe ido tareda sauke ajiyan zuciya.

Ciki sukai gabaki dayansu zuwa palon Abbun da babu mutane sbd basa zaman gaisuwa tinda akai janaizar ta aka kaita kowa yayi gaisuwansa ya watse dan haka koda aka kwana zuwa yau babu kowa duk anyi gaisuwan an watse sai iya qanwar Ammin data taho daga Cairo da babban 'danta.

Zama akai tsakanin Abbu da familyn jeerahs sukai gaisuwa tareda jajantawa da nuna kulawa kafin suka tafi masauki bayan sun dan jima sosai a gidan.

Tinda suka taho ciki akai da fammah dan haka har suka tafi basu sake ganinta ba Hakeem dake tsananin son ganinta da magana da ita haka yaga babu alaman ma zai iya maganarta dan haka suka tafi.

Kukan dukkanin baqin ciki da kunci da kadaicin dake cike zagaye da rayuwarta fammah ta sake tana jin rayuwa ta gama juya mata bangare mara dadi sbd a yanzu batasan tayaya zata fuskanci wannan masifar rayuwar ba babu Amminta,Amminta ta tafi tabarta a rayuwar da babu komai sai son zuciya da son kai tareda zalinci,

Irin kukan datakeyi da yanayinta da suka gani mai muni da tada dukkanin gashin jiki ya saka duk karfin halin mahaifinta da manyancinsa fasa wani irin kuka yana jin tsananin dacin mutuwar rayuwar yarsa daya tak hakama yana jin gwara da Allah bai nunawa Amminta ita ba a wannan mummunan yanayin data koma kamar wadda take dauke da qanjamau dan kuwa hatta haske da lafiyar farar fatarta duk sun tafi koina qashi ne a jikinta kawai yake gani.

Ita kanta qanwar Amminta Anne kuka ta fasa tana rerawa jikinta nawata irin rawar tashin hankalin ganin Fammah a hakan ma wai tana aure a familyn da suke billionaires a can qasar.

Ayau da suka ga yar Ammin a gabansu suke asalin kukan rashinta a cikin mummunan yanayi.

Kukan mahaifinta shine abinda ya qarawa yanayin muni da tashin hankali.

Kwana sukai a cikin damuwa me nauyi da qunci babu kowace irin farin ciki a gidan da mutanen gidan ga damuwar Raheem da aka baro data saka mahaifinta jin kaman ma zuciyarsa zata buga dan haka washe saida shima aka kawo masa likita ya dubasa.

Jeerahs washe gari ma sun sake zuwa suka wuni a gidan zaman gaisuwan da babu kowane sakewa a yanayin dan Abbu ba lafiya bai iya fitowa ba haka sukai zamansu suka tafi ko fammah bata fitoba sbd sunsan yanayinta.

Hakeem ne ya shiga har can ciki dakin Amminta ya dubota tana zaune ta dunqule guri daya idanuwata sunyi jajir sun kumbura ba kyan gani.

Duk yanda yayi magana da nuna mata kulawa ko kadan bata iya juyowa ta kallesa ba dan kuwa a duk lokacinda zai wanzu a guri zuciyarta da idanuwanta tareda jinta dauke mata sukeyi dan haka har yayi maganganunsa ya gaji ya miqe ya fice babu abinda taji bare juyawa ta kallesa.

Bayan tafiyarsu ranar saida suka kwana biyu basu sake zuwa ba gidan banda Hakeem da kullum yana gidan amma sam ko Abbun bai samun ganin fammah din kawai yake gani sai masu aikin gidan itama tin yana jin karfin gwiwa harya rasa abin fada mata sbd batama responding bare yasan akan matakin datake na ta fahimci abinda yakeson fada mata.

Sati biyu suka share a qasar suka tattara zasu koma suka tafi gidan sukai musu bankwana dan Abbun ya fito sun tattauna akan zasu tafi da Fammah daga nan zaa wuce da ita india ne asibiti.

Abbu bai musu ba ya amince musu da fatar allah yasa a dace dan bayason hayaniya a yanzu da rayuwarsa data yarsa suke cikin duhun damuwa da kadaici.

Bayan tafiyar su Alh babba masauki Hakeem ya shiga har ciki ya samu fammah ya sanar mata maganar tafiyarsu a jibi.

Dagowa tayi a karan farko ta kallesa da idanuwanta da suke jajir a bushe kaman yanda takejin ko zuciyarta ta bushe babu abinda takeji.

Kallansa datai ya sakasa sauke numfashi da ajiyan zuciya sbd yasan lokacin maganarta yayi.

Bude baki tayi a natse da sanyi tace

'Aure zakayi HAKEEM?

zuba mata ido yayi yana kasa bata amsa sbd bayason sakata a wani mummunan halin.

Bata dauke idanuwanta akansa ba ta maimaita tambayarta da cewa
Chapter 12 · 0% Book details