← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 154

Sashe 91

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanda ta bada amsar ya sakasa dauke kansa daga kanta yana yin shiru tareda sallamarta yace Mr Sideeq ya rakata zuwa mota.

Sallama tai masa ta fice bayan ya bata kyautar 1k dollars a hannu yanayinsa na sauyawa sosai da wani irin bacin rai da fushin gaske daya gama tabbatarda Fleet ya manta shi waye.

Tana fitowa security din Imran dake tsaye ya bude mata mota ta shiga ya rufe daman Imran din na ciki ya ja kai tsaye ya fice villah din.

Fleet kuwa koda ya sake komawa dakin ya taddata tana bacci mai karfi a cikin mutuwan jiki da fuskanta datai laushi sosai kaman babyn data sha kuka.

Zaunawa yayi akan sofa din dake facing gadon ya jinginar da bayansa a jikin kujeran yana dora kafansa daya akan daya cikin nutsuwa yana cigaba da kallanta da rashin kowace motsi,

Akwai yanayi dayake jin kansa a ciki na rashin iya bude baki sam ya furta kowace kalma idanuwansa kaman suna kamuwa da wata obsession ne da baitaba sanin yaya yake ba akan kallanta da baisan me hakan ne nufi ba.

Bacci tsawon awa biyu tayi ta farka sbd zazzabin daya sauko mata a cikin baccin dan haka tana bude idanuwanta akansa suka sauka yana zaune a inda suke facin juna idanuwansa a lumshe fuskansa tayi wani irin haske tana fidda wani sanyayyan kwarjini da sirrintaccen kyau da class da wata irin kamewansa dake bayyane.

Lips dinsa da sukai wani irin light ta kalla wanda duk wanda ya kallesu zai iya fahimtar abinda suka ringa yi ne,

Rufe idanuwanta tayi ahankali cikin kasala da gabalaita tana jin yanayinsu da suka ringa sauka a kowane sako na jikinta taji zazzabinta ya qara karfi da fargaba.

Tashi tayi zaune ahankali cikin sanyi da rashin hayaniyan dogon motsi ta ziro kafafunta qasa tana miqewa tsaye wani zafi taji ya ratsa tsakiyarta ta rintse idanuwanta da karfi tana dan komawa ta zauna kadan tana hana hawayenta sauka cikin karfin hali.

Miqewa ta sake yi tana gyara rigarsa dake jikinta da dogon wandon kayanta ba bacci da rigar ta tashi aiki ta daga kafarta daya tana kokarin fara takawa bataji motsinsa ba sai jin hannuwansa tayi sun zagayota daya baya zuwa gabanta ya hade kirjinsa da bayanta yana sauke wata ajiyan zuciya mai zafi a bayan wuyanta da kakkauran muryansa mai dakar zuciya ya furta

"How are you feeling???

Rintse idanuwanta tayi ahankali tareda budesu tana jin hankalinta na sake tashi da yanda zata fuskanci iyayenta.

Zamewa tayi tana son sake takawa yayiwa tafiyan tata wani kallo kafin ya saka hannuwansa biyu ya dagata jikinsa yayi sama da ita yana nufar kofa yace

"Ina ne zaki??

Kallansa tayi da wani irin damuwa ta bude baki daqyar tace

"Zan tafi"

Kallanta yayi ta dauke idanuwanta daga kallansa.
##MAMUH
09033181070
[04/06, 1:11 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

85
Kallanta yayi a natse da kyau kafin ya nufi hanyar bedroom dinsa da ita wanda yake a yanda suka hargitsasa.

Sauketa yayi a natse kafin ya dauko wayarsa ya kunna datake a kashen tin juyan ya nemo numbern Maamah wadda take bacci ta dauka a natse tareda ambatar sunansa ya bude baki kai tsaye yace

"Good morning Maamah,pls a turo Maid dinta yanzu ta kawo mata something hot and light,thank you"

"Ok ba damuwa" Maamah tace ya kashe wayarsa yana kallanta da ajiye wayar ya zaunar da ita a gefensa tana dunqulewa sbd zazzabi sosai.

Jikinsa yaso shigar da ita amma taqi yadda ya kyaleta yana jin wayarsa na vibration na shigowan kira amma bai dubaba sbd ba lokacin wayarsa bane yanxu.

Babu bata dogon lokaci safiya ta iso bangaren dauke da tray har palonsa ta ajiye sai a lokacin ya fito da SANAAH din wadda ta dane cikin azaba tana hana safiya datai qasa da kanta barin ta gane tafiyarta ko yanayin fuskanta daman jiran datai tazo sbd ta taimaka mata su koma tare dan bazata iya doguwan tafiyar ita dayaba.

Miqewa safiya tayi tana ajiyewa ta gaidasa da girmamawa mai girma kanta a qasa ta juya zata fice SANAAH ta bude baki daqyar ba karfi a muryanta tace ta jirata.

Cikin tilas tasha madaran da aka dafa mai kauri da zuma da kayan qamshi bada yawaba duk da zafinta daya ratsa cikinta taji dadin hakan sosai sbd karfinta ya dan karu da kuzarinta dan haka komai bata iya ci ba tafara hawayen son tafiya dole yabarta ta fice ya bita da kallo a tsanake harta fice batateda ta waiwayoba tana tafiyar da itace idanuwansa ke kasa iya dena kalla.

Tana fitowa babban palon Safiya dake can kofa tsaye tana jira dagowa tayi ta kalleta da kulawa sosai ta dan dawo gurinta dan bata daman jin saukin dataga babu shi a tattare da ita zuciyarta cikeda tinani kala kala dana farin ciki dana tsoro dana fargaba dan kuwa daga yanzu ta tabbata kishiyar Ms meemah amma dai ko menene tinda SANAAH ta samu zama cikakkiyar mata itama hakan yayi mata dan kaman yan uwan jini suka dauketa tintini kaman yanda itama ta daukesu sbd a yanxu daga mommy sai SANAAH ne nata sbd maraici.

Fitowa sukai babu kowa har lokacin babu wanda ya tashi suka nufi bangarensu mommyn suna isa babu kowa dan basu tashi ba dan haka ta tsaya cak tsakiyar palon cikin tsananin damuwa fargaban batasan dakin wa zata nufa ba dan a cikin iyayen nata ukun mata babu wanda take fatan yaganta ya iya gane halinda take.

Jajir idanuwanta sukai damuwa mai tsanani da mutuwan jiki na rufeta hawaye masu zafi suna ciko idanuwanta,

Safiya ce ta bude baki tace
"muje dakin Mommy"

Can suka nufa suka shige mommyn na bacci SANAAH din ta iso bakin gadon ta haye ta shige bargon jikinta na dan rawar sanyi.

Safiya fita tayi taje kitchen ta sake hado mata tea mai zafi da kauri sosai ba suga daga zallan madaran gari saita ruwa da condensed kadan ta kawo mata ta bata tasha itama kadan tace ya isheta ta dunqule safiyan ta fice.

Zazzabi mai karfin gaske ne ya sake taso mata ta ringa rawan sanyi tsawon lokaci kafin bacci ya dauketa.

Mommy ko data farka ta ganta kwance a gadon fuskanta ta kalla taga yanda ta kumbura tayi ja sai ta tashi zaune a hankali ta kalleta da kyau tana zuba mata idon taga ko a cikin baccin kaman a galabaice take yinsa sbd zazzabin daya sake sakata laushi sosai.

Dauke kai Mommyn tayi daga kallanta da sauri tana jin kirjinta ya buga kadan ta sauko gadon tana qin sake kallan SANAAH din ta fada toilet.

Bata sake bi ta kallanta ba harta gama duk shirinta bayan ta fito wanka ta fito palo tana nufar dakin Maamah wadda itama ta farka harta yi wankanta tana waya a natse.

Gaidata tayi kafin ta fito ta nufi dakin dr mum itama ta gaidata ta dawo ta wuce kitchen dan duba breakfast idan baa kammalaba.

A dining safiya ta gama komai ta jere dan haka Mommy sauran su drinks ta qarasa jerawa saiga su Maamah da dr mum din duka sun fito zuwa dining din.

Zama sukai a natse suna firarsu hankali kwance suna cin abincinsu banda mommy da hankalinta yaketa neman rabuwa biyu amma ta tattara ta watsar ta danne tana cigaba da firarta.

Sai da Safiya ta wuce dauke da tray na wani breakfast din daban zata nufi dakin Mommy maamah ta kalleta tace

"Ina zaki kai abinci safiya??

"Maamah SANAAH zan kawai batajin dadi ne tana dakin mommy"

Shiru mommy tayi tana ci gaba da cin abincinta ita kuwa maamah cikin kulawa tace

"Subhnallah,muran ce ko me? Amma ba sosai ba ko?

Gyada kai safiya tayi tana juyawa ta wuce

Dr Mum kuwa bata ce komaiba tana gamawa ta miqe tana cewa bara ta duba SANAAH din ko zata sauya mata maganin muran.

Koda Dr Mum ta isa daki SANAAH na toilet ta jima a ciki kafin ta fito daure da babban towel tana tafiya ahankali tana ganin Dr Mum ta gyara tafiyarta da sauri tana dan bawa kanta karfi da kuzari harda dan sakewa kadan tana daukan wani babban towel din ta rufe jikinta da bude baki tace

"Ina kwana Mum"

Amsawa Dr Mum tayi tana kallanta da kyau da ganin SANAAH din ta kasa dagowa ta kalleta ko kadan.

"Yaya jikinki? Muran ce?
Kin gama shanye maganin dana rubuta miki last time??

Gyada kai tayi ahankali tana dan bude baki tace

"Naji sauki dan zazzabi ne kadan kawai amma yanzu komai banaji ma"

Gyada kai Dr Mum din tayi tana sake kallanta kafin tace

"To ki huta zuwa anjima mugani idan bai dawoba zazzabin"

Miqewa tayi ta fice daidai nan Maamah ta shigo wadda kallo daya tayiwa SANAAH taji tinaninta ya tsaya cak sbd koda ta shigo SANAAH na tafiya zuwa gaban dauko kayan da zata saka.

Kallanta tayi da dan sauri da jin wata kauna da kulawa ta qaraso tana cewa

"Ki kula tinda bakyajin dadi ki zauna safiya tashi ki dauko mata abinda take buqata.

Miqewa safiya tayi tana isa gurin kayan ita kuma SANAAH din ta zauna sbd Maamah dake dakin kada ta gan tafiyanta.

Koda ta shirya cikin kaya marasa nauyi tana cin abincin kadan amansa tayi gabaki daya sai dai aka kuma bata abu mai ruwa tasha ta sake komawa bacci jikinta da wani irin zafi sosai.

Wasa wasa sai ciwo ya zama nata dan kuwa wuni tayi a kwance zazzabi mai Karfin yaqi sakinta babu gabar jikinta da bata mata wani irin tsami da ciwo dan haka dole mommy ta ringa kulawa da ita.

Har dare tana daki daga toilet sai gado,
Maamah ma itace ta hada mata abinci har so biyu amma babu wanda ya zauna cikinta dan haka dole dr mum tace zata mata dubawan likitoci dan sanin meyake damunta dan itace kadai bata gane asalin halinda SANAAH din take ciki ba.
#MAMUH
09033181070
[04/06, 1:12 pm] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

86
Kiran Dad ne ya shigo wayarta bayan sallar ishai datake kokarin zuwa duba SANAAH din.

Kaman ba zata dauka ba sai kuma ta daga kai tsaye nemanta ya furta yana yi yanzun nan.
Chapter 91 · 0% Book details