← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 154

Sashe 87

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanin baya jin dadi sai Dr Mum bata aika masa ita kai masa komaiba safiya ce taje ta jere komai a dining ta baro dan sunsan idan baya jin dadi ya saba baya buqatan kowace irin hayaniya ko magana dan hakan matarsa ta sabar masa indai bayajin dadi janyewa takeyi tace ya samu hutawa da kyau batareda tinanin ko yana buqatan kulawanba dan haka ya sabu da hakan ya zama dabiarsa.

Da daddare dakin Mommy ta kwana duk ta cika hancin Mommyn da wani qamshi daya hanata ita kam bacci mai karfi sbd yanda koina ta juya wani irin qamshi ne yake tashi a hatta gashin kanta dan haka gari na wayewa ta korota ta koma dakin Dr Mum acan taje ta qarasa baccinta na safe data kasa yi da daddaren itama sbd rashin dadin zuciyarta datake ji tin jiyan akan wayar datai kiranta data bata mata mood haryanzun.

Da safe Maamah ce ta hada masa breakfast da kanta ta saka Safiya ta dauka mata sukaje ta dubosa da kanta ya fito babban palonsa suka gaisa ta masa ya jikin ya amsa a natse ya warware sosai ba sauran ciwon kan dayake fama dashi amma a kame yake a soldier dinsa babu kowace sakewa ko kadan a fuskansa.

Bayan dawowan Maamah ya kira Dr Mum a waya sun gaisa itama bai fito ba sai yamma cikin wata black jallabiyar data fiddo haskensa sosai da zallan kwarjini da class da kamewa da lafiyan dake cikinsa sai black agogon patek philippe chrono watch dake daure a hannunsa wanda kudinsa zai siya wasu motocin hawan,takarmin arabian Russell and brombley ne a kafarsa black da suma suka saka fiddo tsantsar hasken kafafunsa da tsaftarsa da kaman basa taka qasa qamshinsa na tashi a natsen daya saba dan haka koda ya iso gurin mahaifinsa kwarjininsa tini ya doke ya rufe na mahaifinsa dan haka ko Mr Sideeq cikin girmamawa ya janye ya basu guri kafin suyi shirin shiga sallan magrib.

Bai rabu da Dad ba dai bayan sallar ishai dan haka kai tsaye bangarensa ya koma ya zauna yayi wata waya a natse ba hayaniya tsawon lokaci sosai yana gamawa ya shiga bathroom dan shirin bacci.

Itama gurin Dad taje takai masa tea bata wani jimaba Dad din yace ta tafi dan haka tana dawowa shirin bacci tayi tana gamawa ko gado bata haye ba Safiya taxo tace Dr Mum tana kiranta.

Faduwa gabanta yayi ahankali sbd yau kusan haka ta wuni da wani irin fargaba.

Kallan mommy tayi wanda bata dago ta kalleta ba duk da taji sakon.

Hijab dogo ta dauko yana fidda qamshinta a hankali ta saka ta fito tareda safiya din jikinta a mace.

A palo ta tadda Maamah wadda ta fito kitchen daga gama hadawa Raheem din komai ta miqa mata cup din madara mai kaurin gaske da zafinta data hado mata tace ta shanye sbd akwai sanyi yau.

Karba tayi sbd ta samu delay din zuwa gurin kiran Dr Mum ta fara sha ahankali tana dan zaunawa a dining safiya na mata surutu sama sama.

Duk yanda tayita slow haka ta gama ta miqe dole ta nufi gurin Dr Mum wadda tana shiga ko juyowa Dr Mum din bataiba ta kalleta tana duba waya tace

"Kije ki kaiwa Fleet tea da snacks gasucan da aka hada masa dan ba lallai yaci abinci yanxu ba da daren sbd da yamma aka kai masa abincin lunch nasa yayi"

Mutuwa jikinta yayi take sbd daga karshe dai batada mafita dole taje din ta fuskancesa.

Ajiyan zuciya mara sauti ta sake a sanyaye tace

"Ok Dr Mum"

Juyawa tayi ta fice.

Dining ta nufa ta dauka babu kowa a palon taso tace Safiya ta dan rakata sbd ta samu dawowa da wuri amma ba kowa.

Sanyaye ta nufi kofa ta fice ta nufi hanyar bangaren tana fidda wani mayen qamshin daya gama kama jikinsu dan kuwa hatta tafin hannuwansu da kafafunsu qamshi yake fidda sbd abubuwan da aka basu suna amfani dasu duk da bata wani amfani dasu sosai sbd kamshin yana wani irin yawan dayake saka jikin duk mai shaqa sanyi da samun nutsuwa.
#MAMUH
09033181070
[03/06, 8:17 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

81
Tana isa bakin kofar shiga bangaren dan dakatawa tayi tana dan sake sauke ajiyan zuciya a sanyeye kafin ta miqa hannu daya ta bude dan tasan ba amfanin bugawan tinda babu wanda zai bude mata kuma shi yana kurya ba lallai yajita ba.

Tana shiga bayan rufe kofar sake dan jan numfashi tayi kadan a sanyaye har lokacin kafin ta daga kafafunta a natse tayi tsakiyar palon ta nufi hanyar palonsa zuwa lokacin babu sauran faduwan gaba sbd ta riga da ta saddakar da ganinsa tinda dai batada zabi ko mafitar kaucewa hakan duk da tana fatan ace yana bedroom dinsa baya palon ta yanda zata ajiye ta juyo ta fito.

Tana isa kofar itama a natse ba kowace hayaniya ta bude ta sako kai tareda dan sake sauke numfashi mara sauti da karfi sbd qamshin daya ratseta daya isa har kirjinta zuwa cikin zuciyarta.

Takowa tayi tana isowa cikin tsakiyar palon da babu motsin komai bayan flat screen tv dake aiki ba murya ma sosai.

Jin kamshin na sake ratsa hancinta da kirjinta ya sakata dagowa a tsanake da sanyi ta kalli inda ta doso idanuwanta suka sauka akansa yana zaune sanye da black silk pajamas na Fernandos Miami da suka saka wani haskensa da kwarjininsa fitowa suka cike idanuwanta da sukai nauyi mai tsanani a take tareda nauyin kirji ta dan daukesu daga kansa tana qarasowa cikin natsar da kanta da kamewanta me sanyi.

Ipad ce a hannunsa da farin eyeglasses na ragewa idanuwansa hasken screen din daya sake sakasa mai tsantsar fixgan hankali da nutsuwan duk macen da zata samu nasara da saar ganinsa a irin wannan lokacin dayake shi dinne da bayyanar fitinannen hot jikinsa.

Kafafunta kusan kokarin kasa qarasowa da ita sukeyi sbd wani irin nauyi da sukai tareda sauyawan kowane bugawan kirjinta duk tayi taku daya.

Gabansa ta tsaya tareda dan durqusawa a natse ta ajiye tray din hannunta akan table din dayake gabansa ta dan dago batateda ta iya dora idanuwanta akansa ba ta bude baki da wani sautinta mai sanyi da ratsawa tace

"Ina wuni"

Bai amsata ba sai kusan da maganar tai seconds masu yawa kafin ya dan kalli kayan data ajiye ya amsa a taqaice yana ci gaba da duba abinda yake dubawa.

Wani iri taji tana kasa motsawa daga inda take din ta dan dan dago ta kallesa idanuwansa sam basa kanta ta sake bude baki a natse da sanyin da jikinta yake tsanantawa tace

"Ga tea da snacks inji Dr Mum"

"Thank you" ya furta shima a qataice yana dan juyawa ya kalli wayarsa dake gefensa data fara ringing daga America ne numbern ma fuskansa a kame kaman yanda take ta asalin FLEET ADMIRAL RAHEEM HAKEEM JEERAH dinsa.

SANAAH jin tayi kirjinta yayi wani irin nauyin gaske da fuskantar wannan yanayin daga garesa jin tai idanuwanta sunyi nauyi suna cikowa da wasu irin hawayen da batasan daga inda suke kokarin fitowaba ta miqe tsaye tana kokarin juyawa ta bar gurin sbd kada su sauko sedai tana kokarin juyawan yana dan dagowa a cikin idanuwanta kai tsaye nasa idanuwan suka sauka a tsanaken daya hango tahowansu dan haka tana juyawa taku daya tayi ba tsammani taji anriqo hannunta daya da dayan hannunsa batareda ya motsaba daga zaunen daya ke...

Itama cak ta tsaya a gurin tana rufe idanuwanta ahankali hawayen dake cikinsu suka gangaro ahankali ta saka hannunta daya cikin nutsuwa ta goge tareda qasa da kanta sbd jin tasowansa ya tsaya gap da bayanta har suna dan gogan juna ta sake rufe idanuwanta tana jin zuciyarta na shiga daci gabaki daya.

Shiru sukai su duka biyu sbd shi kansa wani irin mugun nauyin da bayajin akwai abinda zai taba sauke masa shi yaje ji a kirjinsa tin jiyan dako ganin kowa a rayuwarsa bayason yi ita kanta zuciyarsa dake wannan zafi da nauyin bata buqatan ganinta sbd kaucewa illar da zai iya yiwa kowa idan zafin ya rasa yanda zai riqu....

Ganin hawayenta ya saka yaji wani sabon zafi da radadin kirjinsa ya qaru bazai iya shima dauka ba dan kuwa daga ranar daya tabbatarda Son dayakewa Nasir na jini ya dawo kanta batareda saninsa ba harya kai wannan matakin dayake kai ayanxu da baisan yaya yake ba zuciyarsa ta rasa kowace control cikakke akanta.

Bai saki hannunta ba kaman yanda bata juyoba hakama shima bai dawo gabanta ba tsawon seconds zuciyoyinsu na yaqi da tsananin abinda suke ji a cikinsu kafin ya juyo da ita cikin wani irin slow yana saukar da idanuwansa masu kaifin gaske akanta da wani slow shima kaman wanda ya zuqi cocaine.

Tashi tsigar jikinta sukai gabaki daya ahankali sbd yanda kallan ya ratseta ta rufe idanuwanta ahankalin da wasu sauran hawaye masu dumi suka qara gangarowa daga cikinsu ta bude idanuwan da wata sanyayyar sanyin daya sakasa bin hawayen da idanuwansa yanda suke tafiya haka yake binsu da idanuwansa har suka sauka zau diga ya saka tafin hannunsa daya suka diga a tsakiya ya zuba musu ido yayi musu wani kallo kafin ya dago idon ya sauke a fuskanta har lokacin taqi kallansa...

Bude baki yayi da wata sautin data shaqe bata fito duka ba yana sake matse hannunta kadan cikin nasa dayan hannun har sai data lumshe ido yace

"Bazaki taba sake amfani da waya ba sai bayan lokaci......

Lumshe idanuwanta tayi da wani irin nauyin kirjin daya ratseta sbd bata tsammanin jin hakan ba duk da tai tsammanin hukuncin...

Yanda ta lumshe idanuwanta da wani mutuwan jiki ya sanyasa sauke mata wani numfashi mai dumin gaske yana matsota sosai fuskansu na hadewa ta gefe yanajin har lokacin wani irin radadin gaske na soya zuciyarsa da jininsa ya rintse idanuwansa shima yana janyewa daga gareta tareda juyawa zai wuce bedroom dinsa wani sautin numfashinta dayake kokarin boye kukan daya taho mata na wannan hukuncin yasaka idanuwansa sake sauyawa sosai sbd har jininsa ne yake tafasa tin jiyan wanda a yanda yake tin jiyan idan ya shiga filin yaqin ruwa mutanen dazai raba da kansu da grenade sunada yawan gaske.
Chapter 87 · 0% Book details