Sashe 137
Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaunawa tayi kirjinta nada tsananin ciwo da radadin tareda baqin ciki har lokacin amma maganar Hajiyar Samad ta ratseta dan haka dole a yanzu zata koyi dannewa da riqe kanta dan cimma burinta dan haka shiru tayi a zaune tana rintse idanuwanta dakeda ja sosai har lokacin tanajin kaman ta qyasta ashana da sauran gas din ya tashi kowa ya mutu ta huta da abinda takejin amma dai ta danne dan haka ta ringa sauke ajiyan zuciya me zafi a jere idanuwanta na cikowa da wasu irin hawaye masu tsananin ciwon yanda rayuwarta ta sauya a dare daya a lokaci daya bayan girma ya fara zo mata.
Bata fito dakinba a ciki ta wuni har dare ko abinci bata fito taci ba tana jiyo yar hayaniyarsu amma baqin cikin ganinsu kadai ya kasa barinta iya fitowa.
Sai dare ta fito bayan tayi wanka ta sauya kaya yanayinta ma ya dan sauya dan haka tana fitowa kai tsaye palon datake jiyo muryansu ta nufa dukansu suna zaune banda Mommy datake kitchen ta hadowa Dr Mum ginger mai dadi da kamshi sbd lamarin take ya koma mata mura mai karfin gaske.
Kaman a mafarki ba tsammani suka ganta ta iso gurin yanayinta baa gane yaya yake sam sbd idanuwanta dai har lokacin jajir suke sedai jikinta yayi sanyi a mace yake duk da hannuwanta na dan rawar da tin kwanakin haka take.
Dr Mum bata kalli inda take ba Mommy data iso da tray gabanta ta kalla tana bude baki da kulawa tace
"Sannu zainab"
Murmushi mommyn tayi tana juyawa gurin Maamah tace
"A kawo miki ne Maamah?
Girgiza kai maamah tayi tana cewa "aa" kafin ta maida kallanta kan Meenah data zauna ahankali tana dago kanta kadan batareda ta kalli kowannnensu ba dan idan ta kallesu zata iya jin ta kasa riqe kanta daga tsananin tsanarsu dake cin zuciyarta.
Mommy ma meenah din ta kalla tana bude baki da kulawa tace
"A kawo muki ginger tea din??
Girgiza kai tayi tana dan yin shiru da rasa abin fada saida maamah ta bude baki idonta akanta tace
"Meenah lafiya dai ko?
Akwai wata matsalar ne?
Girgiza kai tayi tana dannewa ta bude baki tace
"Hakuri nakeson baku nayi kuskure shedan yayi nasara akaina amma insha Allah na gane zan gyara ina neman gafararku akan komai"
Qarasa maganar tayi tana kallan inda Dr Mum ke zaune tana fara shan tea dinta ahankali da nutsuwa zuciyarta fes da wata sabuwar nutsuwan data dawo rayuwarta ayau da Hakeem yayi abinda ya kamata yayi shekara da shekaru.
#MAMUH
09033181070
[23/06, 10:34 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
136
Shiru gurin yayi tsit kaman babu kowa a gurin dukkaninsu abune da basu taba tsammanin ji ba musamman Maamah datasan babu hakura akan kishiya a lamarinsu hakama da safen nan taso sake aikasu lahira amma kuma yanxu tana cewa ta gane ta tuba,
Dr Mum da ko kadan ma bata basu hankalinta ba bare tinaninta daukan cup dinta tayi ta miqe tabar gurin batareda ta kalli ko bangaren da Meenah din take ba.
Maamah ajiyan zuciya ta sauke tana jin jikinta na mutuwa hakama ta rasa abin fada daya wuce karban hakurinta tayi ta kalli Mommy wadda itama shirun tayi tana dan dauke idanuwanta daga kallan Meenah din wadda itama har lokacin bata kalli kowannesu ba.
Bude baki maamah tayi da nutsuwa da samun nutsuwa da jin dadin hakan tace
"Masha Allah da kika gane hakan kuskure ne kikeyi Meenah hakama mu daman abinda mikeso kenan tin kafin lamarin yayi nisan da komai zai lalace kuma tinda babu ran da aka rasa allah ya yafe mana gabaki daya ya kuma kara miki hakuri da juriya da tawakkali"
"Amin" Mommy ta fada a natse tana dan kallan Meenah din wadda idanuwanta suka ciko da wasu hawayen da suka gangaro ahankali ta goge tana miqewa tabar gurin sbd kowace lokaci zaa iya ganin ta danne maamah din ta shaqeta har lahira idan bata bar gurin ba.
Dakinta ta koma ta shige.
Mommy ce taje ta hada mata abinci a try ta bawa safiya takai mata har daki sbd ita yanzu babu wannan a tsakaninsu sai komai ya sake daidaita zuwa gaba kila.
Safiya data kai abincin itama a tsorace take da shakka dan haka tana ajiyewa ta juyo ta fito.
Daqyar ta iya tura abincin cikinta tana jin kaman zata amayosa amma hakanan ta tura tana buqatan koyan karfin hali da taurin rai na munafurcin da bata iya dan su basu iya munafurci ba sam shiyasa ko kishiyar akai basa boye kishi idan sun zauna kenan dan basa zama sedai ka zaba daya a ciki ko su ko wata.
Maamah har cikin ranta taji farin cikin hakan da kuma godewa Allah daya kawo sauki a cikin lokacinda basu taba tsammani ba.
Mommy ma da duk hankalinta yake tashe a boye akan yanda SANAAH zatai rayuwa da meenah a matsayin abokiyar zama yau din jin tayi dan wani sauki yafara shiga zuciyarta sbd ba qaramin tashin hankali da tsoro take a cikinsa ba dan idan har meenah zata iya sakawa rai hudu wuta kai tsaye a bayyane baa boyeba sbd kishi tabbas babu abinda bazata iya ba.
Washe gari da sabuwar Meenah aka tashi dan kuwa har daki taje ta gaida kowannensu duk da koda ta shiga dakin Dr mum tana waya a natse bata amsa mata ba dan haka haka ta gaji da zama ta miqe ta fice daga dakin.
Maamah kuwa sosai ta dan sake mata tana sakata tsayawa cikinsu taci abinci tana kokarin cigaba da riqe kanta itama.
Haka ko bayan cin abincin ta dan zauna cikinsu batareda iya cewa komaiba sbd maganarta na daidai da iya kasa riqe kanta.
Maamah ta roka tai mata iso har gaban Dad wanda yayi mamakin ganin Maamah din da Meenah suka basa hakuri akan Meenah din ta tuba tana neman gafara.
Zuciyarsa Sam bata amsa da kowace maganar meenah dinba amma sbd yarta saiya amsa gafarar tata amma duk da hakan sam bazata taba cigaba da zama a Nigeria ba gidansa dole zata koma Morocco ko America wannan shine hukuncinsa da bazai taba janyewaba dan kuwa ta taba rayuwar macen da bai taba rayuwarta data komai da kowa ba dan kuwa harya bar duniya bazai manta yanayin da idanuwansa suka gani na halinda Dr fammah ta shiga ba akan idanuwansa data kusan konewa har lahira hakama wannan daren shine tsoron da rayuwarsa bata taba shigaba tinda yake a rayuwarsa dan haka abune da har mutuwansa bazai iya mantawa ba.
Hakanan dai jiki a mace Maamah ta sake bata kwarin gwiwan taci gaba da addua da danne zuciyarta zataji komai yazo da sauki insha Allah.
Haka Maamah ta ringa kokarin janta a jikinta tana sake tausarta da nuna mata kulawa da kauna dan bata sassaucin abinda ta lura haryanxu tanaji a zuciyarta na kishi wanda ya saka meenah din itama jin tana samun karfin hali da juriyar iya dannewan tana hana kowa iya gane abinda yake kirjinta da fuskanta.
Ita kanta dr mum sbd yanda maamah ta dage da bata hakuri ya saka ta dan sassauto kadan duk da tariga tasani duk yanda meenah zata hakura matiqar SANAAH da Fleet suka dawo tana ganinsu bazata iya danne abinda takeji ba shiyasa suke tafiyarsu idan har bazasu iya ba dan shine maslaha da mafita tareda zaman lafiyan kowa amma meenah batada niya ko hakurin iya jure hakan.
A cikin kwanaki kadan Meenah ta dawo mutum dinta tsaf ta koma kaman ba ita ba dan kuwa yanzu ta tattara komai ta danna a cikin ranta ta boye ta iya controlling kanta musamman ganin yanda a yanxu duka ta gama saka kowa yadda da tubanta da yafe mata duk da Dr Mum bata gama koma mata kaman baya ba hakama shi Dad sam babu ko daman zuwa gaidasa datake samu,
Hajiyar Samad ta maida hankali sosai akan ganin Samad ya tattara ya koma dan haka ta tattara meenah ta watsar tana jiran ta fara ganin wucewansa tukuna ta waiwayeta ta gyara mata zama,
Itama meenah yanzu ta ajiye Hajiyar cak sbd bata buqatanta lokaci ma ta bata na bari gidan ita da danta.
Maganar maida auren Dad da Dr Mum yafara fita ahankali sbd irin yanda wata irin lafiyayyar soyayya mai sanyi da nutsuwa da manyanci ke gudana a tsakaninsu sbd babu ranar da likita bata zuwa ta duba masa lafiyarta hakama a waya ma yanda yake waya da ita akai akai ya saka ita kanta tafara jin lamarin ya mata nauyi dan haka ta hanasa ganinta kwata kwata dan irin kalla dayake mata duk wanda yake gurin zai iya jin nauyin hakan sbd baya iya riqe kansa daga mata kallan dayake mata tin a lokutan shekarun baya da rashin samun rayuwar kansu da basuyiba tinda sukai aure sbd tinda sukai aure basu zauna sosai ba akazo aka haihu lalura ta biyo baya daga karshe auren ya qare suka diba wannan shekarun ba tareba kwata kwata basu morewa tsantsar soyayyar da sukewa juna ba tinda sukai aure dan hakanne sai yanzu da manyanci yazo kila zasu morewa soyayyarsu ta hanyar zama da juna babu rabuwa saita mutuwa yanxu kam.
Tinda ta hana haduwansu sam kwata kwata yaji zuciyarsa batada sukuni da nutsuwa a ciki duk da a waje kame yake amma a ciki baida kowace nutsuwa dan haka a dan wannan lokacin ne ya shirya tafiya Morocco tafiyar da Umma naji duniyarta ta tsaya cak kirjinta ya kasa dauka haka ta kwanta ciwon hawan jininta daya fara hawa ahankali ahankali sbd damuwa mai tsananin gaske data kasa cirewa kanta.
Dr Mum kuwa dole itama tafara shirin komawa Moroccon tareda su maamah hadda Mommy banda meenah datace zata jira su dawo.
Kafin tafiyarsu aka kammala gyaran bangaren nasu daya kone zuwa sabon gini gabaki daya wanda yake sama da qasa kuma shine kadai ya fita daban da sauran bangarorin kaf,
Duniyar luxuries aka zuba a bangaren wanda ya sake banbanta bangaren da sauran na matan gidan dan kuwa komai nasa na daban ne dan nan ne bangaren Dr mum a matsayin matar gidan macen da Hakeem jeerah ya zuba shekaru yana jiran dawowanta rayuwansa da gidansa.
Fleet ne ya zuba duk wata duniyar dake bangaren yai abinda kowane da ko uba zaiyiwa 'ya ko uwarsa.