← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 154

Sashe 14

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Acan fammah kuwa rayuwar tsaya mata tayi cak da zallar baqin ciki da radadin datake jin kaman zai kasheta,
Ta tsani hakeem ta tsani danginsa ta tsani duk wani ahalin jeerah da Nigeria tsana me girman gaske da ita zata mutu tabar duniya,
Tsanar da batajin harta mutu xata dena musu,
Mutum uku ne a duniya dake Nigeria da kawai take kauna da sune kadai suke hana ta tsinewa nigeria da wanda suke cikinta a kowane dare da rana wato Raheem dinta da fatima da nasir.

Mahaifintane yayi waya da fatima ya sanar da ita komai ya kuma qara bata amanar Raheem dan itace uwarsa itace dangin uwarsa kuma itace idonsu da zuciyarsu akansa suma dan fammah bazata nemesa a yanxu kusa ba saita samu lafiyarta da zaa nema mata.

Wannan shine sabon rudanin tashin hankali da damuwan da fatima ta shiga,
Bangaren Fammah suke haryanzu sbd an barwa Raheem bangaren mahaifiyarsa dasu masu renansa,

An sauya musu komai da komai na bangaren an zuba musu sabuwar luxuries tako ina wanda yafi na baya an wadatasu da komai kaman ba rayuwar duniya zasuyiba,

Kullum mahaifinsa na zuwa ya dubasa gashi an yaye su sosai hidimarsu ta qaru akan fatima dan yanxu sunyi wayo koina suna takawo suje da kafafunsu,

Lokacin auren captain yaja sosai tini rayuwarsa ta sauya ta koma wata irin me zafi sbd nutsuwan zuciyarsa daya rasa gabaki daya,
Baida farin ciki baida walwala ya koma cikakken asalin soldier dinsa da bayajin ma yanxu yanada buqatan kowace mace a rayuwarsa kawai aikinsa yake buqata da haka lokaci na sake ja ya tattara ya koma America komawan da baya dawowa sai lokaci mai tsananin tsayi.
Iyayensa da kwata kwata suka rasa Hakeem din baya yanzu soja ne kawai suke tare dashi dan kuwa ko su din yanxu babu sakewa a tsakaninsu dashi yayi nesa da kowa da komai,

Hatta 'dansa RAHEEM daya fara girma babu wata shaquwa a tsakaninsu ko bayyana soyayya sedai kokarin dorasa dayake yi akan rayuwar zama jarumi cikakken namijin fama da zai fuskanci kowace irin danger da rashin tsoro da bugun gaba dan haka ya zama a cikin wainda ake shakka fuskanta a familyn jeerah cikinsu da wajensu.
#MAMUH
#FLEET

GANIN IDO
Mamuhgee
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070
[09/05, 4:16 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

14
*_HARGITSI_*
By
*_TALATU ZAKI_*
+201031621512
*Duk maaboci kuma masoyin karatun littafin Hausa to karya wuce labarin nan bai karantasa ba sbd duk wani tsari da labari yake buqata to akwaisa tattare a cikin labarin HARGITSI Na TALATU ZAKI*🔥
https://chat.whatsapp.com/ERrtA3G4obwBQzBTiJUad3?mode=gi_t

*********
RAHEEM HAKEEM JEERAH yaron daya taso wani irin miskilin da baa taba yin irinsa ba a zuriar jeerahs shine kuma wanda Allah ya jarabci duk wani jinin jeerah da tsananin kaunarsa da son kulawa dashi hakama jini daya na Rear Admiral da kaf familyn jeerah suke alfahari dashi sbd matsayin da babu wanda ya taba takawa a zuriar jeerah tin ta farko wato Rear Admiral Hakeem Farouk Jeerah.

Duk tsananin kauna da soyayyar da familyn jeerah kewa Raheem bai taba sakewa ko sabo dasu ba sbd yanada wata irin miskilancin da baya ko san rabar mutane kwata kwata,

Bai dauki dangin mahaifinsa da girman daya dauki Maamah dinsa ba wadda ta qarar da kuruciyarta da lokacinta da lafiyarta da zuciyarta a gurin kulawa dashi da mahaifiyarsa wadda bata tareda su sama da shekaru goma a yanxu,

Maamah itace wacce aka ajiye kamar baiwa a jeerah villa dan kawai kulawa dashi tin yana yaronsa har zuwa yanzu daya fara sanin kansa yasan itace uwar da harya mutu bazai sauya matsayinta a gurinsa ba duk da mahaifiyarsa ma tana tareda su a waya bayan shekarun data dauka tana jinyar data cinye mata lokacin rayuwarta dan kuwa jinyar jiki data zuciya data kwakwalwa tayi duka dan kusan saida tayi qaramar hauka sbd damuwa depression da komaima kafin Allah ya saka ta fara dawowa Dr fammah dinta dake kokarin daidai career dinta yanzu sbd sai data koma tayi wani karatun program na shekara biyu kafim ta sake samun damar komawa career dinta data dawo sabuwa.

Maamah bata taba barin kauna da soyayyar mahaifiyarsa da girmanta mai tsanani ya fita daga ransa ba koyaushe a cikin cusa masa kaunarta da girman matsayinta take a gunsa wanda hakan ya kasa ya taso da kauna da tausayin mahaifiyarsa tareda tsantsan son kasancewarta a rayuwarsa daya san haka bame yiyuwa bane har abada sbd wani irin zazzafan raayi da zafin da mahainfinsa yake dashi.

Fatima manyanci yafara hawa kanta sbd wahala data debo tana yi tin a baya duk da yanzu sun girma wahalar ta rage mata amma kuma kaf babu me dawainiyar Raheem idan ba itaba sai kuma dan uwansa rabin jikinsa da kusan shine yanzu yake masa wasu abubuwan duk da komai nasu daya amma sbd shi ya taso tamkar me ciwon damuwa bayada wani walwala ko sakewa bare farin ciki,

Maamah itace uwarsa da babu komai dayake buqata daga uwa har uba amma kuma wannan yanayin da kadaicin na kanada uwa kanada uba amma baka tareda kowane a cikinsu hakama babu wanda ya taba yi masa maganar wani a cikinsu dan kuwa sun goge juna da gaske daga rayuwarsu babu sauran alaqa da fili ko kadan da suka rage a rayuwarsu duk da hakan ya kashe Hakeem gabaki daya ya koma wani sabon mutum.

Nasir shime rabin jikin dan uwansa Raheem da yake tamkar jinin daya da aka haifesu tare,
Shine mafi kusanci da Raheem duk duniya sbd yanda suke jin juna kaman yan biyun da aka yankewa cibiya daya,
Babu ma'aunin da zai iya auna girman kaunar da suke tsananin yiwa juna,
Babu kowace rai dayafi so sama da Nasir dan a yanzu duk da basu wani girma ba ko Maamah bata gane abinda raheem yakeso fiyeda dan uwansa Nasir din,

Nasir ya taso mai karfin hali da naci da qwazo da tsananin son Raheem fiyeda kansa sbd Maamah bata boye masa ko su din waye ba,ta fada masa matsayinsu a gidan da zaman da sukeyi,

Nasir bai damuba baiji komai ba jin koshi da uwarsa waye,
Abu dayane ya sake ninkuwa ya qaru a zuciyarsa da ransa shine kaunar dan uwansa dayake jin zai iya komai da bada rayuwarsa a akansa.

Fatima lokaci yaja itama tasan lokaci yayi daya kamata ta tattara ta koma inda ta fito duk da har lokacin babu labarin ibrahim sedai khalil ne haryanzu yake bibiyarsu akai akai itada Nasir yana jin lafiyarsu.

Babu Alh babba a duniya ya rasu a shekarar data fita sbd ya manta sosai tsufa yazo yayi jinyar watanni kadan Allah ya karbi ransa.

Su Alh husain ma tsufa yazo sosai daddy ne ma yakeda saura,

******Raheem da Nasir nada shekaru goma sha hudu a duniya Dr fammah da Shakur suka nema a basu Raheem bayan komai nata ya dawo daidai ta koma dr fammah dinta ta baya rayuwa ta sauya mata tazama hamshakiyar macenta mai ilimi da da yanci da abun kanta,

Babu wani tashin hankali da akai aka bata damar kasancewa da 'danta wanda zai ringa zama gurinta yana kuma dawowa gurin dangin mahaifinsa.

Tafiyarsa ta farko dr fammah taso a taho da fatima kamar me amma sbd neman Ibrahim mijinta da khalil yakeyi sosai dan tinanin ko baya raye ya saka bata tafi ba dole suka tattara itada Nasir suka koma gida.

Raheem ya shiga mummunan hali sosai bayan rabuwarsa da Maamah da Nasir sbd tinda yake a duniya sune kadai wainda yake tareda su ya rayu dasu baida sabo da shakuwa da kowa bayansu biyun,

Jinya yayi sosai bayan zuwansa Morocco tsawon lokaci kafin ya fara kokarin sabawa da mahaifiyarsa da danginta da suma suke tsananin kaunarsa.

Fatima ta koma gida da Nasir suka fara kokarin fuskantar sabuwar rayuwarsu wadda take tattare da qalubale dan bata wani taho da abubuwan rufin asiri masu yawaba tinda babu kowa a tsakanin Fammah da hakeem da zasu bata dukiya me yawa.

Daddy ne ya bata kudi sosai da motar abinci wadda suka siyar da rabi dan babu gurin da zasu ajiye.

Kadan kadan kudin suka fara shigewa gurin neman Ibrahim da sukeyi ido rife,

Nasir yana ci gaba da zuwa makarantarsa da aka sakasu mai tsananin tsadar gaske shi da Raheem bayan yayi tasa jinyar shima ta rashin dan uwansa.

*****Raheem dauki lokaci sosai a gurin mahaifiyarsa harma yafara karatu yayi nisa a karatun mahaifinsa ya sake dawowa aka dawo dashi Nigeria nan Hakeem da kansa ya aiko aka dauko fatima da nasir suka koma jeerah.

Daga nan rayuwar Raheem ta koma tamkar jeka kadawo baya Nigeria hannun mahaifinsa baya Morocco hannun mahaifiyarsa,

Yanayin rayuwar sai yafara zamar masa wata babbar damuwa data sake saka rayuwarsa abin tausayi dan kuwa karatunsa ma wani wasa ya koma acan da nan,

Da haka suka sake girma babu sauyi ko daya a rayuwar Raheem da iyayensa dan haka mahaifiyarsa ta tattara danta ta karba bata sake barin ya dawo ba,

Barin Raheem rayuwar fatima da nasir suka dawo gida kwata kwata gabaki daya ya saka suka duqufa sanaa kala kala ga khalil nata kokarinsa gurin kulawa dasu da dora Nasir a sanaoi daban daban dan rufawa kai asiri.

Suna waya sosai da fammah amma fatima bata taba yadda ta fada mata halinda suke ciki ba sbd duk wata tana aiko mata kudi masu yawa na karatun Nasir da komai nasa dan ta dauke kowace irin lalurarsa.

Suna gama karatun secondary Dr fammah da suke cewa Dr Mum ta saka ayiwa Nasir takardu da komai dazai dawo hannunta acan Morocco yayi karatu tareda dan uwansa da suke tsananin kewa da mugun son juna sai kwatsam Admiral Hakeem jeerah ya aika Raheem karatun Soja kamarsa America.

***acan Nigeria su fatima sun wayi gari da wata irin gobara me tsananin data saka rayuwarsu sake sauyawa sbd sun rasa komai hadda takardun nasir din da akagama hadawa dan haka komai ya lalace ya dawo baya ta bangare daya kuma sai ga Ibrahim ya dawo gida da kansa cikin yanayi na ciwo baiyi kwana uku da dawowaba ya rasu.

Duk yanda sukaso neman Dr Mum ba dama sbd hatta wayarta da numbern take ciki basu tsira da ita ba bare Raheem da shikenan bazaa taba magana dashiba ko samunsa ba sai ya fito.
Chapter 14 · 0% Book details