← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 154

Sashe 85

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi yayi yana ajiye tasa wayar shima da sake tabbatarwa da kansa akwai dan sauran lokacin daya dibarwa auren yana cika tabbas sauya rabasa koda hakan na nufin kowace bacin rai da kowa zai shiga tinda itama SANAAH din 'ya ce kuma mace ce kaman kowace.

Washe gari dukansu suka fita tareda Mum din wadda itama zatai siyayyar abubuwa da dan dama da kuma gyaran da zata fara yiwa kanta na tafiya qasarta a cikin familynta da itace star a kaf ciki yanzu sbd itace matar wanda yakeda tarin arzikin da babu a familyn da kuma wata irin power da suna hakama dukiyar gaske take sakarwa familyn nata na kusa da nesa sbd nunawa duniya irin daula da rayuwar datake ciki wadda sai mace mai girman saa ce zata samu kanta a cikinta shiyasa kaf familyn suke bata girma da tsantsar tarairaya kaman zasu bauta mata duk da sunada zafi sosai amma ita kam ta zama star din da babu kamanta a familyn duk da akwai maza masu kudi sosai a familyn amma basu kai mijinta ba.

Shopping suka fara yi sosai kowa da abinda yake buqata da kuma so dan haka suka jima tukuna suka gama Mum ce ta biya kudin komai da card din Fleet daya basu kafin suka baro suka nufi spa wanda bayan sun isa Mum tayi magana dasu kudi sukai magana akan a gida zaa ringa zuwa kullum ana musu komai tsawon kwanaki biyar tukuna sukai payment na komai suka bar gurin.

Koda suka iso gida yamma ta dan yi dan haka a gajiye SANAAH ta fada wanka tanayi ta fito tayi sallah tana idarwa fammah na fitowa daga wankan itama taxo tayi sallah a daidai nan Safiya da SANAAH ta kira a waya ta shigo dauke da madara me zafi data dafo mata da zuma da sabon coconut bread daya gasu ta ajiye musu a gabansu tana kallansu da dariya labari kala kala a bakinta ta zauna tana bubbude kayan da suka siyo tana dubawa tana fitarwa tana cewa

"Ni idanma kukai tafiyar nan jikina mutuwa zaiyi kilama hadda zazzabi sai nayi"

Da dariya fammah dake kai bread din mai dadi a bakinta tace

"Ai Saffy kila hadda mutuwa sai kinyi kin dawo tsabar bakida wanda zaki bawa labaran gulmanki musamman na hajiyar Uncle da babu ranar da bakida su a baki"

Dariya safiyar tayi tana qara fidda kayan gabaki daya tana kallan famman da wata sabuwar gulman tana cewa

"Ai ko dazu na ganta ta fito tana waya zata fita a mota sai tsinewa wasu takeyi daman babu ranar da bata tsine tsine fa"

Sai a lokacin SANAAH tayi murmushi mai hade da yar dariya mara sauti tana kallan safiya tace

"Safiya duk ranar da hajiya ta kama ki kila dukan da zata miki akanki zata sauke haushin kaf familyn nan"

Wata dariya me kyau Fammah ta sake wadda ta fiddo wata irin kyakkyawar kamarta da Dad dinta sak musamman idanuwanta sbd yanda zancen SANAAH din ya sakata kwatanto ranar dan haka dariya takeyi da wani irin sakewa itada Safiya din wadda tace

"Wayaga sakwara dan kuwa wlh nima nasan uban duka zanci gashi banda me amsana dan kafin Dad yazo na koma kaman wadda tayi hadarin mashin a digar jirgin qasa"

Wata dariyar Fammah ta sake tana jin kaman zata shide.

SANAAH data kasa dauke idanuwanta ahankali daga kan fuskan famman zamewa tayi ahankali tana jinginar da bayanta jinin kujera daga qasan datake zaune a kasalance tana sauke wata ajiyan zuciya mai sanyin gaske tareda dan lumshe idanuwanta tana ajiye cup din hannunta ahankali tareda kama jikinta guri daya a natse tana kasa dauke idanuwanta daga famman cikeda wata irin kauna da sanyayyar yanayin dake yaduwa a kirjinta tana jin kaunar fammah har cikin jininta.

Sake wata maganar Safiya ke yi tana dariya itada Fammah wadda take jin idanuwan SANAAH akanta ta juyo ta kalleta kadan da kulawa zatai magana SANAAH ta girgiza mata kai cikin wata irin slow da shagwabanta dan tasan abinda famman zata fada.
#MAMUH
09033181070
[02/06, 11:18 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

79
Dare sosai Safiya takai a dakin nasu tana musu fira suna nishadinsu kaman yanda suka saba tukuna ta baro bayan ta jere musu komai da suka siya a inda tasan ya kamata harna toilet takai ta jere dana gaban mirror da dai komai tukuna ta musu saida safe ta fice.

Fammah kallan SANAAH tayi bayan sun kwanta tana lafe har lokacin a narke batason hayaniya da doguwan magana da kulawa tace

"Ke are you okay wai?

Girgiza kai SANAAH tayi alaman eh bayan ta kalli famman ta dan rufe idanuwanta kadan.

Da mamaki famman ta sake kallanta tana wata dariyar data zo mata tana da neman jin amsa tace

"SANAAH are you inlove? I mean did you fall for me or wat????? Ta qarasa maganar da dariya sosai da tsokana.

Harararta SANAAH ta bude idanuwanta tayi cikin rashin karfi tana kai hannunta daya ta daketa a kafa tana cewa

"You crazy fammah??

"Eeh naji amma ina ji a jikina you're obsessed with ne or my looks,
Kin fara soyayya ne ban saniba girl??
Fadamun waye da bansaniba ya kasheki haka kwata kwata bakida saura ko kadan aswear"

Juya mata baya SANAAH tayi ahankali tanajin tsigar jikinta kawai suna tashi ahankali daga kalaman Fammah din kawai ta lumshe idanuwanta bakinta na sanyin da bazata iya furta ko kalma daya ba.

Fammah na ganin hakan ta sake sake wata yar qaramar dariyar data bata tabbacin maganarta na iya zama gaskia.

"Prof ne??? Fammah ta jefa mata tambayar a kunnenta wadda ta sakata rintse idanuwanta ahankali tana dan qanqame bargon datake rufe dashi sbd tana bude idanuwanta fuskan famman ta gani a kusa da tata wadda murmushin dake kai ya kusan sakata tsayar da numfashinta sbd fuskansa ce sak ta shiga idanuwanta akan ta famman.

Sake maimaitawa fammah tayi da cewa

"Prof ne fadamun sbd idan shine muna cikin murna"

"Fam pls ki kwanta kiyi baccinki ba kowa a rayuwana"

Tsokanarta Fammah taci gaba da yi dan taji harta tabbatarda kaman ba kowa din dan haka suka kwana bacci zuciyarta cikeda sanyi da nauyi na abinda takeji a kirjinta gameda duk abinda famman ta ringa tambayarta.

Washe gari da safe bata fito ba sam tana daki har rana tukuna ta fito taje ta gaidasu Dr Mum tayi zamanta cikinsu har kusan yamma kafin masu gyaransu suka taho wanda Mum dake matar gidan datake ganin kusan duka su Mommy da Maamah harma da Dr Mum itace kadai matar gidan a cikinsu dan itace matar babban Dan Jeerahs kuma wanda yake da matsayin da babu wanda yake dashi a familyn dan haka take sake jin isa da iko masu gyran ma da suka taho haka suka ringa bata girmanta sbd nuna musu datai itace asalin macen Jeerahs family.

Bangarenta aka kaisu aka ware musu daki daya suka shirya komai na aikinsu sai da sukaci abinci suka gama jiranta ta gama yangarta tukuna taxo ta zauna aka fara musu.

Su uku akaiwa gyaran kusan har dare tukuna aka gama sai kuma gobe.

Ana gamawa wanka sukai dukkaninsu sukai sallar magrib da ishai sukaci abinci banda SANAAH da bata iya cin komaiba Dr Mum ta aiko safiya ta kawo mata dafaffiyar madara da zuma da kidney sauce taci tai brush ta kwantawanta.

Su Mum kuwa sbd ta nunawa Fleet adonta data fara acan bangarensa ma tayi wanka bata dawo ba sai washe gari.

SANAAH ko dataje ta gaidasu Dr Mum kai tsaye Dr Mum tace mata kada ta sake fitowa zuwa gaidasu ta zauna guri daya sbd gyaran da ake musun bayason ko yawon tai zamanta kawai sai angama.

Mum ma ta sanar mata hakan amma sam bata iya zaunawa ba sbd duk akai mata ta ringa kaida kawo kenan sbd yanda take ganin tana daukan idanuwan masu ganinta da glowing din data fara.

Maamah ma ta saka an dauko musu mai gyaran gargajiya da zata qara musu da nata idan an gama wannan dan haka a ranar da akai 5days aka gama wannan din a ranar washe gari suka iso daga maiduguri ta jirgi sbd tickets da aka siya musu.

Tin ranar da Dr Mum ta hana SANAAH fitowa bata kuma fitowaba sbd itama gabaki daya bata jin kuzarin yawon daman dan haka tin daga ranar babu wanda ya sake ganinta tana bangaren nasu bata fitowa koyaushe tana daki abinci ma anan take ciki ta dena zuwa sam dining ci tareda su dan haka basu sake ganin juna ita dashi ba tsawon kwanakin.

Ana gama wancan gyaran aka fara musu sabon wanda SANAAH din tace bata buqata sbd jin takeyi abin ya mata yawa amma ko kafin Dr Mum tai mata fadan hakan a waya Ms Meenah tai mata fada sosai tace sam sai anmata sbd bikin dake gabansu dan ita so take ma SANAAH din ta samu miji a can dan akwaima wani dan uwanta datake son hadasa da SANAAH din sbd ya samu shiga a gurin Dad jeerah da Raheem din daya dade yana neman hanyar shiga ahalin jeerahs din dan shima soldier ne matarsa ta farko ta rasu tabar Babynta daya namiji da baifi shekara tara zuwa goma ba dan haka take tsananin son SANAAH din taje kota yaya ne.

Mommy data saka SANAAH a idanuwanta data tafi ganinsu muguwan faduwa gabanta yayi sbd irin sauyin datai wanda ya saka fatarta har wani daukan idanuwa takeyi da kyau da glowing da wani irin fitinanniyar qamshin dake fita daga jikinta jin tayi hankalinta yane neman tashi da tsoro da shakka da fargaban wannan gyaran data ga Dr Mum din sun rufe ido ana mata wanda itaba yarinya bace ta fahimci dole hakan na nufin gyara ne na miji ake mata bayan ga matarsa itama tana cikin gyaran hakama tayaya zasu tafi da SANAAH din qasar da batada kowa batasan kowaba da kishiyar da batasan cewan kishiyarta bace ga kuma miji a tsakiyarsu duk da tasan babu ma abinda zai faru tinda haryanxu a kaman fammah yake kallan SANAAH din kokuma tace matsayin matar dan uwansa da baya raye.
Chapter 85 · 0% Book details