Sashe 92
Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru tayi da mamakin isarsa da ikon dayake nuna mata amma tinawa da matakin da suke akai na tashin hankalin dayake neman jefasu akan auren SANAAH din ya sakata saka slippers masu kauri ta nufi bangaren nasa dan daman doguwan abaya ce a jikinta da mayafinta tinda sune kayanta.
Ko data isa a kofar shiga bangaren taga Imran a tsaye yana waya take ta san RAHEEM yana ciki kenan shima dan haka fargaba taso kamata amma ta fuska tareda kame fuskanta.
A zaune Raheem yake a palon farko wanda sanyin qamshinsa ya doke na mahaifinsa ya kame niimar palon gabaki daya.
Qarasowa tayi ta zata wuce ciki a natse tareda kallan RAHEEM din kadan tana amsa gaisuwan daya mata a tsanake a kame duk da waya yake amsawa cikin iko.
Tana shiga palon da Dad din yake zauna ta qaraso ta zauna ta dan dago ta kallesa tana dan bude baki ta gaidasa shima ya amsa fuskansa a daure sosai ya bude baki bayan ta zauna tana sauraransa yace
"Likita kina sane da inada maganar jiran takardar sakin SANAAH amma kika aikata 'dan ki ya dora mata iddarsa??
Me kuka maidani?
Me kuke nufi da hakan?
Menene amfanin hakan bayan bai gama amincewa da bata matsayin matarsaba?
Rainani kukayi da maganata batada mahimmci ko me?
Da mamaki mai girma dr mum ta dago ta kallesa tana jin zancen kaman saukan haihuwa ta ji wani sanyi ya ratsa zuciyarta da kwanciyan hankali tareda tsananin tausayin SANAAH din wadda kenan halinda take ciki ne yau.
Murmushi ne ya kufcewa dr mum din wanda ya sake kular da Dad ya daidai nan RAHEEM din ya shigo palon da sallamarsa mai bayyanarda kamewa da nutsuwarsa ya qaraso ya zauna Dad daya gama yanke hukuncinsa sbd tabbas maida SANAAH macensa da RAHEEM yayi ba shine samun yancinta na zamowa cikakkiyar matarsa me yanci ba tinda matarsa haryanzu bata saniba kuma duka sun kasa sanar da ita yayita basu lokacin hakan amma basu cika ba sai kawai yaxo ya maida masa 'ya cikakkiyar mace wadda dagashi ubanta har ita basusan cikakkiyar makomar aurenba da yanxu kam ta tashi daga budurwa...wannan ne ke sake cin ransa dan haka ya maida kallansa cikakke akan RAHEEM din ya bude baki babu sauki ko rahama a sautinsa yace
"Fleet admiral a yanxu anan nake baka umarnin bani sakamakon auren SANAAH"
Dagowa RAHEEM din yayi ya saukewa Dad din idanuwansa cikin nutsuwa da kwanciyan hankali tareda kamewa da mamakin yanda koyaushe iyayensa basa gajiya da zama akan magana daya tin asalinsu farko hakan suke haryanzu bayan sunsan shi sam baa zama daya ayi biyu ayi na uku dashi duka akan magana daya sbd baida time din batawa akan abu daya koyaushe amma a wannan karan suna neman wuce huruminsu da Allah ya basu akansa.
Dr Mum kallo daya tayiwa yanayin RAHEEM din tayi shiru dan tasan nasa hukuncin zai fada wanda take fatan taji abinda bazai sakata samun bugawan zuciya ba.
Dad kuwa kallan RAHEEM din ya sake zai sake maimaita maganarsa a zafafe
Kalaman Fleet din suka ratsa shirun palon da cewa
"Tana dauke da aurena haryanzu akanta da i don't know wani sakamon da ake jira da hakan Dad,
She is my wife,
She still is,
She will still will be,
Tana dauke da igiya ukun auren da aka daura,
Tana amsa sunan iyalina,
Tanada matsayin iyalina,
Na kirata sa kalman iyalina akwai wani sakamon daya rage bayan hakanne??
Dr Mum da ita kanta kalamansa suka sakata kafesa da ido maida kallanta tayi kan Dad da dan sauri sbd tanaji a jikinta irin tafasar dayake yi da yanda kalaman suka zafafesa dan kuwa babu abinda yaji wanda yakeson ji kafin ya bude baki yayi wata maganar sbd a yanzu ma ya fasa kowane sassaucin dayake da niyar yi RAHEEM ya miqe tsaye tareda sake bude baki a natse kaman bai taba furta komaiba yace
"Nagode Allah ya qara lafiya ya saka da khairan"
Juyawa yayi ya nufi kofa Dad da zuciyar sojoji ta gama ciyosa ya dago idanuwansa jajir zai furta kalamansa Dr Mum tayi saurin dawowa gurinsa tana miqa hannunta bakinsa zata dora cikin mantawa da matsayinsu sai kuma ta dakata cak batareda hannun ya qarasa sauka akan bakinsa ba sedai yana dap dan kuwa hatta saukan numfashinsa mai zafi tana ji a fatar tafin hannunta ta dago da idanuwanta da a karan farko suka shiga cikin nasa gap da gap ya saka idanuwansa da suka sauya sbd bacin ran dayake ciki a cikin nata yana jin asalin qamshinta tin na shekarun kuruciya suna shigarsa direct da tareda numfashin bugawan zuciyarta.
Janyewa tayi baya cikin nutsuwa da dan kamewa da qin sake kallansa ta bude baki tace
"Dan Allah tinda ta riga ta zama matarsa ka kyalesa yayi yanda zaiyi"
Kafeta da idanuwansa yayi yana qin furta kalma ko daya sbd da yawa sun bace daga kansa da bakinsa a yanxu dai.
Juyawa tayi tabar palon tana jin itama gabaki daya kalamanta sun bace mata.
Tana komawa bangarensu bata iya fuskantar kowaba sai data shiga dakinta ta nutsuwa ta dawo daidai tukuna ta nufi gurin SANAAH wadda Maamah ta rufe ido ta sake gasata dakyau da abubuwa tana kuka tana jin kaman zata mutu sbd kunya harta galabaita tayi bacci gwanin tausayi.
Yaso nemanta sosai sbd yanayin lafiyarta amma ba wayar hakan hakama iyayen nasa yasan idan har bata warware ba zasu bata kulawa dan haka ya barta kawai ko bangaren bai sake zuwaba sbd ganinta zai iya basa matsalar rashin jinta din dan haka kwata kwata babu wanda ya sake ganinsa.
Washe gari ba laifi ta tashi sbd ta samu sauki sosai dan ba qaramin gasuwa tayiba hakama dr bushrat ta sake zuwa dubata,
Wani tattali da kulawa take samu daga Maamah da Dr mum mommynta ta kawo ido ta saka kawai.
A waya fammah tasan batada lafiya sosai dan haka ta ringa tarairayanta a wayan mum kam anyi busy bata wani bawa rashin lafiyar mahimmanci sosaiba ta bari idan taxo tukuna.
Bata fitowa palo koyaushe tana bedroom sbd batason tsautsayi yasa ya shigo tana palon ta gansa dan kaman bazata taba iya sanin kallansaba take ji.
Dad ma ya dauki mugun zafin da shi kansa Raheem din zuwa yanxu ya shedar da hakan sbd dai da gaske auren zai rana dan haka ya hana kowa daman ganinsa a cikin iyayensa kaf dan su Dr Mum ma hankalinsu ya tashi yanzu kam.
Imran dayake shirin tafiyarsu Morocco ya gama kammalata amma dayake akwai sauran kusan sati kafin tafiyar sai bai siya ticket ba ya sanar da Fleet din komai ya kammala batareda ya dago ya kallesaba ya bude baki a natse yace
"A siya tickets gobe koman dare zuwa gobe da safe zamu wuce"
"Aiit Done fleet" Imran ya fada yana daga wayarsa yabar gurin yana fara aikinsa kawai.
Imran na fita wayarsa dake gefensa tana fidda hasken shigowan kira ya dauka yana decline na call din ya saka kiran Maamah wadda take zaune tareda Dr Mum sun gama magana da Abbu a wayarta taga kiran Raheem din ta dauka a tsanake.
"Maamah da asuba insha Allah zan wuce Morocco maid ta shirya mata komai"
Ajiyan zuciya Maamah ta sake tana cewa
"Zan hada mata da kaina insha Allah"
Kashe wayar yayi yana kashewa gabaki daya ya aje ya miqe ya shige bedroom dinsa.
Dr Mum maamah ta fadawa wadda itama wani nauyi ne taji ya sauka kirjinta sbd zuwa yanzu sun gama shiga tsaka me wuyar HAKEEM JEERAH dan da shi kansa Raheem din bai hango sauki ba ko kadan.
Maamah ce ta miqe taje dan kiran safiya ta hado mata kayan SANAAH din ita zata hada sauran duk da ba wasu kayan zaa daukan mata ba acan ayi siyayyar wasu yafi sauki.
Dr Mum kuwa batajin zata iya barin Dad ya sani gwara dan haka zata tabbatarda bata bar SANAAH taje masa sallama ba tinda tasan yasan da tafiyar batasan tashin hankalin da ake ciki ba sam sam ita.
#MAMUH
09033181070
[05/06, 9:56 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
87
Dr Mum ce ta samu SANAAH din har dakin Maamah data koma da zama ta kalleta da kulawa tana zaune cikin kujera ta dan kwanta kadan tana sauraron Safiya dake mata firar nishadi sosai tana murmushi tana sauraronta da kallanta.
Ganin Dr Mum din ya sakata dan tashi zaune a natse tana gaidata da cewa
"Sannu da zuwa Dr Mum"
Zaunawa tayi gefenta kafin ta amsa da kulawa tana dan sake fuskanta da murmushi mai tsananin kyau daya bayyanar da kamannin fleet a fuskanta tace
"Fira safiya kike bawa Yata take wannan murmushin da jin dadinsa"
Dariya safiya tayi tana kallan SANAAH din wadda itama murmushin ta sake yi tana dan kasa kallan Dr Mum din sosai.
"Yaya jikinki Baby?
Yanxu bakya jin kowace rashin jin dadi dai right??
Gyada kai tayi tana cewa "eh thank you Dr Mum"
Murmushi dr mum din tayi tana maida kallanta kan safiya tace
"Ai Maamah ta fada miki zaki hadawa SANAAH wasu daga kayanta yau da Asuba ne tafiyarsu Morocco an dawo da ita kusa"
Da jin dadi Safiya tace
"Eh zanje yanxu na hado mata su"
SANAAH kuwa dagowa tayi ahankali da yar faduwan gaba da shakka ta kalli Dr Mum din kadan sbd bata gama jin tafiyar ma ta kamata kwata kwata ba gashi ana maganar yau da asuba,
Wani numfashin tashin hankali da rashin jin dadi ta sake na abubuwa da dama da suka bata son tafiyar kwata kwata bata kaunar yinta,
Batasan tayaya zata iya hada idanuwa da Fammah dinta da Mum ba dik da babu wanda yasan abinda yake tsakaninta da Dad din famman amma hakanan take jin tsananin nauyi da kunyar kai kanta gabansa ta iya kallansu musamman fammah datake jin tafi jinta a cikin zuciya da kirjinta,
Hakama batasan tayaya zata kasar da babu wanda zata iya sakewa dashiba a cikin yare da al'adar da ba nata ba ga uwa uba shi wanda bazata iya sake hada idanuwanta da nasa ba sbd har yau basu taba sake ganin junaba bata kuma shiryawa sake hada fuskanta da nasa ba ko a kusa.