Sashe 38
Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mai aiki daya aka basu bangaren wadda zatai hidimar komai na bangaren har dafa abinci wanda shima an cike musu store din dayake lafiyayyan kitchen dinsu da abinci da duk wani abun da zasu buqata naci dana sha da katan katan na ruwa da soft drinks.
Sitirar sakawansu ma sbd magana ce ta kudin da baa san zafinsu ba babu bata lokaci aka tanadar musu sitira da duk abinda akasan zasuyi amfanin dashi.
Mr S ne ya kaisu har bangaren tareda mai aikinsu wadda itace ta shiga har ciki dasu ta gabatar musu da komai a natse da girmamawa.
A palo suka zauna shiru babu wanda ya iya magana tukuna har saida Al'amin yayi karfin halin magana yana boye damuwansa da bayyanarda farin ciki sbd kawai suma su samu kwanciyan hankalin jin dadin yafara yabon Dad din da masa addua yana basu tabbacin a yanxu dukansu zasu samu nutsuwa insha Allah kuma kaman gobe ne zasu ga ya gamo karatunsa ya dawo garesu.
Yanda yake kokarin nuna musu ya sake daga kowace damuwa dan kawai suma su sake din ya sanyasu kawar da damuwa suna nuna masa nutsuwansu da kwanciyan hankalin da zasu samu.
Mai aikinsu da sunanta yake Safiya ta fito daga kitchen ta nufi dakin Mommy ta faro aikinta daga can ta gyara mata duka kayan da aka kawo aka ajiye a kan gado zuwa cikim wardrobe ta jere komai tsaf ta qara gyara dakin ta kunna ac ta fito.
Dakin SANAAH ta nufa wanda shi komai dayake cikinsa na daban ne wanda yake na duka jin dadi da tsarin budurwa mai gata da aji itama kayan ne a aje kan lafiyayyan babban gadonta dayake shirye da tsadaddun beddings ta fara jere mata a wardrobe tana hada kowace riga da gyalenta sbd duka kayan luxury abayas ne kaf masu kyau da rashin hayaniyar ado sai tsada.
Bayan jere kaya turaruka da shoes ne da suma babu abinda akai delay duka an siyosu na amfaninsu da zasu fara kafin idan an nutsu a siya komai akan tsari.
Tana gamawa nan ma tafito lokacin ne SANAAH ta shigo dakin a natse wani sanyayyan sanyin ac ya ratseta ta rufe idanuwanta ahankali sbd har lokacin zazzabi ne a jikinta sosai kuma jiri take gani mai tsananin gaske dan haka daqyar ta isa toilet batareda ta iya tsayawa qarewa dakin kallo ba.
Tana shiga toilet amai me karfi ya kufce mata ta qarasa da sauri tafara yinda a cikin toilet seat tana dafe cikinta dake ciwo sosai.
Sosai tayi aman tana gamawa a galabaice ta zare kayan jikinta ta isa gurin shower ta sakarwa kanta ruwan da batamasan masu zafi ne ta kunnoba sai da suka ringa sauko mata taji dadin hakan ta rufe kyawawan idanuwanta da sukai laushi tana jin ruwan na ratsa fatar jikinta da ita kanta tana buqatan ruwan.
Ta dan jima ciki tukuna ta fito da alwalan sallan laasar da akai tana ciki da jiri har lokacin ta iso tsakiyar dakin daidai nan Safiya ta shigo dauke da tea me zafin gaske dayaji madara sosai ba suga ko kadan ta qaraso ta ajiye akan table.
Bude baki SANAAH tayi cikin rashin kuzari ko kadan tace
"Ki kashe mun Ac banajin dadi sosai"
Cikin kulawa da girmamawa Safiya tace to tana daukan remote ta kashesa tana juyawa ta fice.
Tana fita SANAAH bata iya komaiba sallah tayi daqyar tana gamawa ta zube a gurin dunqule take baccin zazzabin wuya ya dauketa.
Mommy ma wanka tayi mai kyau ta shirya tayi sallah hakama Yaya Al'amin wanda shima hadda shi a kayan sakawan dan haka yayi fes anan yayi sallah bai fita ba sbd baisan koina na cikin villar ba tukuna.
Abinci lafiyayye safiya tayi ta gama bayan magrib tana gamawa ta jera a dining taje har daki ta sanar da mommy,
Basuda zabin daya wuce fitowa cin abincin wanda akai sbd su kawai kuma mai rai da lafiya a tsarin da basu taba cin abinci ba wato kan dining.
Sai a lokacin suka san halin da SANAAH ke ciki dan haka yaya Al'amin dole ya fita a natse da kame kansa sosai tareda bayyanarda irin karfin nutsuwansa ya tafi hanyar zuwa bangaren Dad ya dakata daga waje ya kira mr s a wayarsa cikeda girmamawa ya sanar masa SANAAH ba lafiya sbd baisaniba ko zasu iya tafiya su kaita asibiti.
Mr S baya nan amma saiya kira likita wanda zai taho ya dubata a cikin gidan ba buqatan zuwa kowace asibiti.
A cikin daren kuwa likita mace taxo ta duba SANAAH din tareda bata magani masu kyau bayan tasa ankawowa SANAAH din abinci da tea tasha tukuna tabata magani tasha kafin ta wuce da basu tabbacin gobe zata dawo.
Da damuwan jikin SANAAH suka kwana wadda ta danne damuwan kasancewansu inda suke ganin rayuwar tayi musu nauyin da kaman bazasu iyaba.
Baccin nutsuwa me karfi ne SANAAH tayi a daren wanda yake tattareda kwanciyan hankalin gangar jiki da ruhi dan haka sai latti sosai ta farka a kasalance.
Sallah tayi tareda zaunawa tana adhkar har gari ya qarasa wayewa sosai.
Miqewa tayi sanye da doguwan rigar sallar dake jikinta a natse da sauran rashin karfin jiki sosai ta nufi bedroom din Mommy.
Koda taje itama mommyn tana zaune tana lazimi dan haka ta zauna ta jira tagama tukuna ta gaidata cikin kulawa da kauna.
Amsawa mommyn tayi tana shafa bayanta cikin kulawa da kauna me karfi tana cewa
"Yaya jikinki?
Kin ji sauki sosai?
Lumshe idanuwanta masu kyau tayi tana dan jin jikinta na sake sakewa tace
"Naji sauki kawai rashin karfi sosai nakeji"
Gyara mata rufar kanta tayi tana kallan kyakkyawar fuskanta datai duhu da rama tayi tana cewa
"Shima zai dawo karfin jikin naki indai saukin ya samu"
Yaya Al'amin ne yayi knocking kofar dakin kafin ya bude ya shigo da sallama yana kallansu da kulawa da kauna me karfin shima ya qarasa ya zauna gefen mommyn yana gaidata idonsa akan SANAAH da sai yanzu yake ganin ramarta sosai da duhun datai.
Yaya jikinta ya tambaya bayan ya amsa gaisuwanta.
Maganganunsu sukai na tsawon lokacin daya saka basu samu komawa baccin safe ba saida sukaji shirun yayi musu yawa babu kowa ba motsin komai hakama koina tsit ba wata hayaniya dole kowannensu ya koma ya kwanta baccin daya daukesu mai tsananin karfin da basu san ya akai hakan ba.
Safiya ce kadai take ta kaida kawon ayyukanta na gyaran koina har dakunansu ta gama tayi breakfast ta jere a dining ta koma kitchen tana qarasa gyaran koina a kitchen dan zatai snacks da zaa ajiye naci idan buqatan hakan ta taso.
Sai karfe goma sha daya kusan dukansu suka tashi shima sbd zuwan Dr Zulaihat ne wadda ta sake dawowa duba SANAAH din.
Safiya ce taje dakin SANAAH a natse ta sanar da ita dan hakanne ta tashi tareda saukowa a gado ta nufi toilet tayo wanka da brush ta fito ta shirya cikin doguwan riga ta fito batareda wani shafe shafen mai ba.
A natse da rashin hayaniyarta da rashin karfin jiki sosai ta iso gurinta tana gaidata da muryanta mai sautin daya hana Dr zulaihat gane ita din ba yar asalin familyn bace dan babu garaje da rashin nutsuwa a sautinta dazai saka ka gane a inda ta taso.
Sake fuska dr zulaihat tayi tana amsawa da cewa
"Masha Allah SANAAH jiki ya dan samu sauki ba kaman jiyan ba"
Murmushi ta sake mai kyau a natse tana cewa
"Alhmdlh kawai karfin ne bana jinsa sosai,thank you"
Cikin kulawa da kokarin fira da ita Dr taci gaba da mata tambaya ta sake tabbatarda jikin ya samu sauki sosai tukuna tabarta.
Tana kokarin miqewa ta tafi mommy ta fito itama sanye cikin doguwar riga mai mayafi babba da taushi tana ganin dr din itama ta dan sake fuska tana mata sannu da zuwa.
Gaida mommyn tayi suka dan qara tattaunawa tace insha Allah SANAAH taji sauki itama mommyn godia tayi mata.
Dr na wucewa Abinci suka ci a kan dining din da suke jin lamarin wani iri amma dai ba zabi ba kuma wanda suka gani bare magana ko neman tambaya dan haka suka rungumi duk rayuwar da aka basu a bangaren da hannu bibbiyu.
Gurin gaida Dad jeerah zasu tafi amma baa kirasu ba sai dare bayan Sallar ishai sai ga kiran Dad din da kansa a wayar Al'amin dan haka suka fito dukansu a natse zuwa inda ya kirasu.
Koda suka isa palonsa tin daga tsarin da komai nasa daban yake wanda kana gani kasan na shugaban gidan ne kazo.
Bude kofa Al'amin yayi a natse da sallama a bakinsa ya shiga su mommyn na bayansa SANAAH ba gefen mommy sanye da wata doguwan rigar daban data nade kanta da mayafinta ta nutsu a jikinta da kyakkyawar fuskanta data rame,
Kallo daya zakai mata ka tabbatarda nutsuwanta da tarbiyarta tareda kame kanta da rashin daukan hayaniyarta.
Tinda suka shigo palon Dad jeerah ya dago ya kalleta a natse da dukkanin kulawan data sakata shiga ransa irin shigar daya kamata ace yayiwa Nasir da yana raye amma bai bawa Nasir kauna da kulawan daya kamata ya samu daga garesa ba sbd irin sadaukarwar da mahaifiyarsa tai musu tun tanada cikinsa har haihuwansa da girmansa,
Shine ya kamata ya zama uba na alfaharin da Nasir bai taba samu ba haryazo ya sadaukar da ransa a garesu..
SANAAH itace halittar da daace Nasir zai dawo duniya zai bawa kowa amanarta da bakinsa,
Itace halittar da zai kaunata a yanxu duk duniya ya maida Alkhairin sadaukarwar Nasir.
Bayan Nasir ita kanta kai tsaye kamewan kanta da nutsuwanta dake bayyane tai masa yaji yana jin radadin abinda Samad yayi mata wanda ya sakasa haramta aurenta dashi har abada amma tabbas zai zo SANAAH a cikin ahalinsa dan hakan yake jin nutsuwan hukuncinsa na karbansu suka dawo hannunsa.
#MAMUH
09033181070
[01/05, 9:35 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee