Sashe 4
Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Samad ma daya san can din dole daman zasu fara zuwa take ya dafe bayan motar gaban suka nufi can din.
Isarsu maqabarta take securities suka tsaya waje suna bude masa hanya tareda tabbatarda tsaro daga waje dan kuwa daga shi sai imran da Samad ne suka saka kai a maqabartar bakinsa da yayi wani irin nauyi dauke da adduar ziyara idanuwansa na sauka akan daidai kabarin da suka tsaya wanda bazai taba manta gurin dayake ba take suka sauya ya sauke su akan sunan dayake kan kabarin..MUHAMMAD NASIR IBRAHIM.
Shekarun baya..........
#MAMUH
#BEST STORY
#FLEET ADMIRAL RAHEEM JEERAH
#MUHAMMAD NASIR IBRAHIM
#LOYALTY
#JEERAHs
#AGE GAP LOVE
#HOT+HOT+ROMANCE
GANIN IDO 2026
1k
Vip 5k
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
[09/05, 4:16 pm] Asia ahmd: GANIN IDO 2026
Mamuhgee
4
*_IMZEED ENTERPRISES LTD_*
07077532253
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Sisters na ce ba? Wai kuwa Kuna da labarin shahararriyar mai sayar da kayan yara da kayan kicin ɗinnan akan farashi mai sauƙin gaske fiye da kasuwa? Na san dai ko ban faɗi sunanta ba da yawanku kun santa, amma dai duk da haka bari in faɗa muku sunanta. Imzeed Enterprises LTD, ta shahara gurin siyar da kayan yara da kayan kicin kala daban-daban akan farashi mai sauƙin gaske. Sauƙaƙawarta bai tsaya a nan ba, tana yin adashin kayan kicin weekly da monthly ga ƴan'uwa masu niyyar siyan kaya amma basu da dunƙulallen kuɗin a lokaci ɗaya. Abin burgewar shi ne tana da branch a Jihar Kano da jihar Filato (Jos), sannan tana aika kaya cikin ƙanƙanin lokaci a faɗin Nigeria da Nijer. Ku tuntuɓeta a kan wannan lambar wayar domin ku kwashi garaɓasa...07077532253. Muna maraba da masu sayen ɗai-ɗai ko sari.
********
A zamanin da turawa ke kamun baqar fata daga Africa suna tafiya dasu qasarsu wasu ana maidasu bayin bautawa qasar wasu kuwa karatu ake sakasu wasu kuwa sojojin yaqi ake sakasu,
A cikin wannan zamanin ne cikin wainda aka kama aka tafi dasu aka tafi da wasu marayu su biyu da basada uwa sai mahaifinsu wanda ana tafiya dasu da karfi da yaji basu mara ko kwana biyu ba ya rasu yabar duniya.
Antafi dasu qasar turawa ta hanyar jirgin ruwa dan haka koda suka isa kusan da yawansu da aka taho dasu baqin cikinsu da tashin hankalisu yafara sanyi sbd yar nisa da tsarin tafiyar da kusan tin anan kowa yake iya sanin maaunin kaddararsa a hannun turawa.
ALIYU da ABBAKAR su kadai ne suke uwa daya uba da aka taho dasu dan haka kai tsaye suna isa da akazo rabasu sai aka saka Aliyu cikin sojojin yaqi shi kuwa abbakar sai aka sakasa a cikin masu karatu daga nan suka rabu amma suna haduwa sosai sbd camp din bordern qasa suke su dukan.
Aliyu na sauran da aka sakasu cikin bauta da ukubar koyan aikin soldier duk da shekarunsu basuda yawa sbd iyakacinsa shekaru goma sha biyar haka yafara fuskantar wahala da tsantsar azabar zama kurtun soja da ko a gurin yaqi iyakacinsu kai bullet da daukan gawa amma azabar tayi yawan da yakejin kaman bazai iya kai labari ba.
Da farko har abinci baa basu sai duka da bautar aiki kawai wanda ya saka da yawansu sun mutu sbd wahala da sallamawa.
Ganin fiyeda rabin wainda akazo dasu din sun mutu sai turawan suka sauya tsari aka fara koyar dasu hadda ilimin yaren turanci wanda hakan ya fara sassauta zuciyar wainda ke rayen daga sallamarwa dasuke kokarin yi ga rayuwar.
Wannan dan qarin da aka samu ya saka Aliyu fara kokarin daukan jarumtar kowace irin wahala da azabar training sbd samun dan ilimin koda baida yawa zai taimaka masa gurin kasancewa da dan uwansa wanda bayan lokacin daya dan ja anrabasu dan kuwa su abbakar din tini akai cikin qasar gabaki daya dasu dan tabbatarda samuwan iliminsu da turawa zasu ringa amfani dasu dan juya duk baqaqen fata ta hanyar amfani da yan uwan nasu.
Aliyu da Abbakar lokaci yafara ja na rayuwarsu sun gama tabbatarda babu wani sauran maraici da quncin daya rage bayan su dage su zama abinda akeson su zaman matiqar hakan zai saka su samu daman ringa gani da kasancewa a rayuwar juna.
Alkawari ne da suka daukawa junansu batareda sun sake ganin juna ba suka fuskanci komai da karfin zuciya da son cimma manufa,
Aliyu ya tsaya tsayin daka yana koyan duk wani aikin wahalar dake cikin zamowa bawan soja kuma ya kwantar da hankalinsa sosai ya bude kansa dan fahimtar duk wani darasi da koyarwa tareda ilimin dake cikin kowace ukubar da ake basu tamkar dabbobin da basuda rayuwa a jikinsu.
Jajircewansa da qwazonsa tareda wata irin jarumtar shanyewa da hadiye duk wata azaba ga shakaru marasa yawa ya saka ya fara samun attention daga masu kulawa dasu suk maiyar da hankali akansa sosai azabarsa na ninkuwa wanda a nasa bangaren kowace azaba qarin karfin zuciya da juriya a garesa dan kuwa iya bushewa zuwa lokacin zuciyarsa ta bushe sosai.
A ranar da aka fara fita yaqin farko dasu irin tashin hankali da gawarwaki da yanda mutane ke mutuwa mara kyan gani a gaban ido ya saka Aliyu shiga mummunan halin daya suma saida ya kwana biyu kafin ya farfado sbd mummunan abinda ya gani daya saka kukan da baitaba yiba kafin daga baya ya tabbatarda saiya sake zama mai bushewan zuciyarda babu kowace irin tsoro ko fargaba acikinta zai iya tsira harma ya rayu rayuwar da zai iya zama sanadin yancin dan uwansa dan kuwa abbakar daya shiga qasar ya gama zama bawansu na har abada dan kuwa babu wanda zai iya fidda sa qasar.
Tin daga wannan lokacin Aliyu ya fara zama abinda suke son su zama din babu sauki ba tausayi zafi da wuta kawai batareda sanin kowaba da komai bayan qasar turawan.
A bangaren daya kuma kusan shi kadai ne ya tsira da ilimin turancin da ake basu,
Shekaru masu yawa suna sake tafiya Aliyu na sake zamowa cikakken sojan yaqin turawa dan kuwa ya gama sadaukar da rayuwarsa gabaki daya tarihi da kaddararsu yake son sauyawa na tsayawa ya zama soja mai cikakken yanci ba bawan soja ba da zaa kashe a banza ko gurin binnewa bazai samu ba sedai a qona gawarsu kaman yanda ake qona kara.
A lokacinda aliyu yake gwagwamarya da gawarwaki da harbe harben zamowansa soja a filin yaqi a wannan lokacin Abbakar nasa ilimin yayi zurfin da tasa rayuwar shima ta sauya gabaki daya dan kuwa an gama saka masa mummunar akidar tsanar baqar fata yar uwarsa da babu abinda iliminsa bai koyar dashiba na yanda babu amfanin kowace baqar fata a duniya bayan zamowa baiwa.
Bayan shekarun azaba da ukuba da nakasa da fargaba da tashin hankali da rashin bacci da rashin hutun jiki da zuciya da quntatuwa a hannun turawan yaqin kasar amurka ALIYU ya samu damar fitowa a cikakken sojan yaqin qasar mai yanci bayan da kuruciyarsa da samartaka da lafiya da ganinsa da duk suna qare a gurin bautar daya jure dan ganin wannan ranar da zai fito a cikin ayarin sojoji masu yancin da zai iya ganin yan dan uwansa wanda a yanzu yake rayuwar qasqanci a hannunsu.
Bayan duk wannan shekaru da suka shude sama da ashirin da biyar Abbakar ya samu ilimin boko sosai hakama manyanci yafara shigo masa amma baitaba fita daga zamowansa qasqantaccen baqar fatar da suke kalla ba wanda shima yake kallan baqar fatar qasqantattu aiki kawai yake a qarqashinsu kuma zaici gaba ne har qarshen rayuwarsa babu maganar yanci har abada.
Aliyu ya sauya sosai ya shima shekaru sun tafi amma a lokacinda ya amshi lambarsa ta zamowa cikakken soja wasu hawaye ne suka ciko idanuwansa da sukai jajir ya rintse ido yana komawa inda yake tsaye tareda dagowa idanuwansa ya kalli gefen daya tabbatarda ayarin baqar fatar qasar masu ilimi suke dan duba dan uwansa da shima tinda aka ambaci sunan Aliyu jeerah din a cikin sabbin sojojin da aka qaddamar wasu hawaye suka ga garo masa sbd bayan sama da shekaru ashirin kenan dayaji sunan dan uwansa harma idanuwansa suka sauka akansa dan haka kasa dauke idanuwansa yayi daga Aliyu wanda suka taho sunada kuruciyarsu amma a yanzu dukansu yau sun fara manyanta shekaru sun fara rufewa.
Shi kansa aliyu dayaga dan uwansa kasa dauke idanuwansa yayi daga kansa yana jin inama daga wannan yancin nasa su tattara su koma qasarsu wadda baitaba dena marmarin komawaba amma yasan har abada ne wannan.
Zamowan Aliyu Soja bai basu daman gani ko kasancewa da juna ba dan kuwa daga wannan ganin da sukaiwa juna basu sake ganin juna ba sbd Aliyu da aka maida kwata kwata border ta cikin daji sosai dan haka rayuwarsa ta sake zamowa kadaitacciyar da babu kowa a cikinta bayan zamowansa sojan da baisan komaiba bayan yaqi da rashin walwala da farin ciki ko kadan.
Abbakar yafi Aliyu shiga shekarun manyanci sosai sbd baya aikin wahala da gwagwarmaya kaman aliyu hakama lafiyarsa tafara ja da baya dan haka tinda ciwo ya sakosa gaba aka tattarasa aka maidasa inda din da ake aje irinsa can wani qaramin garin da baida kowane irin tsaro a cikin qasar.
Jinya sosai Abbakar yayi wadda ta saka ya samu aikawa Aliyu sakon yana rokon yaxo suga juna na bankwana.
Sakon na isarwa Aliyu ya samu isowa a washe garin ranar bayan doguwar tafiyar kwana biyu a hanya.
Koda ya iso nurses ne dake camp din suke kulawa dashi sosai amma yariga yayi nisan da babu wata doguwar magana a tsakaninsu Allah ya karbi ransa.
Aliyu duniyarsa tsayawa tayi cak sbd yasan shima a daidai yanxu baida kowace burin cigaba da rayuwa sbd duk abinda yayi yaqi ya zama yayisa ne sbd dan uwansa wanda gashinan sun rabu babu kowace sauran kusanci da sanin juna a tsakaninsu.
Ya shiga mummunan hali amma kuma a lokacinda yayi ido biyu da matar Abbakar din da dansa daya tak jin yayi ya samu sauran hope dan haka kai tsaye bayan kwana biyu ya tafi dasu inda yake sbd daman kusan acan din da yawansu sun dauko iyalansu sbd zamane daram a dajin babu ranar barowa shiyasa ya zama tamkar babban gari a tsakiyar jejin.