← Book details Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 154

Sashe 95

Ganin Ido Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bathroom ya shiga bayan ya kira Imran a waya yana fitowa itama ta shiga dan fitsari ma takejin ya matseta jikinta babu karfi ko kadan.

Tana bathroom Imran ya kawo musu wasu kayan wainda tana fitowa ta saka batareda tsayawa bata lokaci ba wasu black English gown ce mai kyau da tsadar gaske shima nasa kayan black ne.

Ko data gama yana waya a natse da sabon yanayinsa da bata taga gani ba ko sani,

Yana wayar aka kawo musu snacks masu tsadan gaske da light abinci da drinks da wasu ruwan.

Sama sama sukaci suna gamawa bada jimawa ba time dinsu ma na tafiyansu yayi yanata wayoyi dan haka ya kashe wayarsa gabaki daya suka sake fitowa hannunsa na cikin nasa sanye da black prada shades sai hanbag dinta dake hannunta dan tafiya.

Babu wani bata lokaci kuwa aka gama komai jirginsu ya daga zuwa Morocco.

Sai tsakar dare sosai gap da asuba jirginsu ya sauka motoci daga gidan Kakansa Abbu wanda baya nan yayi tafiya checkups nasa sukazo daukansu airport.

Kai tsaye gidan iyayen Ms Meenah suka nufa sbd kai SANAAH din wadda tace acan takeso gurin fammah hakama tinda mansion din kakansa da anan bangarensa yake ba kowa su dr mum da abbun dika ba kowa yasan zata ji kadaici sosai dan haka ya hakura da barinta zuwa gurin famman tata.

Kafin su isa gidan ya kira numbern fammah wadda da mamaki ta kalli kiran nasa da time ta dauka kalma daya ya fada mata ya kashe wayar.

Saukowa gadonta tayi tana janyo riga mai girma ta dora akan kayan baccinta ta fito.

Tana fitowa harabar gidan mai tsananin girman gaske dan kusan kaman villah ce suma taga motocinsa suna shigowa harabar gidan a ajere.

Parking akai take aka bude aka fiddo kayan SANAAH din wadda tana ganin fammah ta sake narkewa ta fito motar batareda ta iya sake juyowa ta kallesaba tayi gurin fammah wadda tana ganinta taji sanyi ya ciketa itama ta ware mata hannu tazo ta shige jikinta.

Bai sake kallansu ba aka rufe motocin sika bar harabar gidan take batareda ma fammah ta isoba wadda ta shiga mamakin hakan sosai sbd kaman sunyi laifi itada Mum dinta tin ranar da suka rabu dasu a Nigeria basu samu sake fuskansa ba ita mum ma sam bata gane hakan ba sbd hidimarta datake gabanta.
#MAMUH
09033181070
[06/06, 9:13 am] Dasoo: GANIN IDO 2026
Mamuhgee

90
SANAAH datake jin zuciyarta na cika da wani farin farin cikin daban na ganin fammah sake riqe hannunta tayi tana jin kuma jikinta na sanyi amma dai tasani zatafi sakewa da samun nutsuwa a tareda famman aduk inda take dan haka fammah na kallanta taga yanda take samun nutsuwa da ganinta sai ta ajiye tinanin fushin Dad dinta a gefe tinda bawai ta tabbatar bane kawai dai taga kaman hakan ne ko dan yanzu da bai jira ta qaraso ba suka bar gidan.

Ciki suka nufa fammah na janye da akwatinan SANAAH din farin cikinta na bayyanuwa da wata murna take ta sakewanta tana kallan SANAAH din da murna a fuskanta tace

"Kuda sai next week amma kuka taho yanxu,Dad ne ko??

Dan dago idanuwanta tayi ta kalli Fammah din batareda bada amsa ba ta fada wani zancen a kasalance da yar gajiya da cewa

"Daman bakusan mun taso ba kenan??

Yar tafiya sukai mai dan taku kafin suka isa wata babbar kofar da fammah ta tura suka shigo wani makeken palo mai tsananin girman daya dauki set din kujeru har uku masu kyau da tsari irin na larabawa da manyan pillows komai na palon brown ne,

Kana kallan palon kasan gidan taro ne ka taho wanda kusan kila kaf zuriar gidan a ciki suke dan tin daga harabar gidan zaka san family house ne sbd bangare banagren dake cikin gidan da kuma tsananin girma da zurfinsa hakama gate din farko babba ko securities babu maigadi daya ne wanda idan gari ya waye ma a bude yake barin kofar gate din daya sbd yawan kaida kawon yawan jamaar cikin gidan dan haka sai dare ake rufe gari na wayewa a sake budewa sai kuma wani daren amma dai bawai kowa shigowa yake ba iya zuriar gidan ne sai baqinsu idan babu sani babu yanda zaayi ka shigo harabar gidan,

Kusan ahalin zuriar kaf suna cikin gidan dan haka ne yake da girma sosai kuma gidane dayake tin na asalin kakanninsu duk da akai akai suna yi kowa na dan gyara ana masa tsarin zamani dan hakanne wasu bangarorin sunfi wasu bangarorin tsarin zamani da kyau kowa dai da yanda yake gyara bangarensu,
Ita Ma Meenah a bangaren asalin kakansu da shine main baban bangaren gidan suke tareda sauran kakarsu daya data rage da wasu daga cikin yan matan gidan da mazansu suka rasu ko aurensu ya mutu da yayansu harma dan yanmata dan haka anan bangaren ma akwai mutane sosai.

Mutum hudu suka tadda a palon suna kallo suna firarsu da wayoyinsu da alama dai ba yanzu ne zasu shigeba.

Cikin kulawa suka kalli Fammah datake janye da Akwati kafin suka maida kallansa akan SANAAH wadda take cikin hannun famman suka sake fuska sosai suna ambatar sunanta kaman wadda suka taba sani sbd kawai sun san da zuwanta daga bakin Fammah dan haka sannu da zuwa da barka da hanya sukai mata batareda kowannensu yataso ba.

Amsawa tayi a hankali tana dan gaidasu itama batareda tabar fammah ba itama.

Wucewa ciki sukai zuwa wata hanya yar gajera suka fada wani palon daga can suka sake shigewa wata kofar tukuna suka isa inda bedrooms dinsu suke kai tsaye wanda yake kaman nata ta isa da SANAAH din suka shige tareda rufo kofar.

Sanyin ac ne da qamshin Fammah din ya kame dakin komai a fes a tsare kaman yanda suke da tsantsar tsafta da tsari dan haka ajiyan zuciya mai sanyi SANAAH ta sauke tana zaunawa a sofa ahankali tana ajiye handbag din hannunta tareda dan warware qaramin veil din kanta tana dan lumshe ido ta bude na jin samun sabuwan nutsuwa.

Bathroom ta shiga bayan fammah ta tayata fara unpacking kayanta na akwati duk da ba duka zata fitar mata dasu ba ta jera.

Wanka tayi da ruwan zafi sosai tai brush da alwala tana fitowa kayan bacci ta saka bayan ta dan shafa mai kadan sallah tayi tana idarwa fammah na shigowa dakin dauke da tray data zubo mata gasashen flat bread da baa jima da gama gasawa ba sbd masu aiki a cikin daren suke fara rage aikin breakfast din safe da safe warming wasu abubuwan kawai zaayi bread din kuma koda zaa gama yanda ake ajesa har safe lfy kalau zaka cisa kaman lokacin aka gamasa.

Tea da madaransu mai kauri datake full cream ta hado mata da fruits sbd tasan sauran abincin bama iya cinsu zatai ba.

Tasha tea din sosai sai flat bread din kadan sbd ba wani sosai takejin yunwaba sbd so biyu yana sakawa ana kawo mata abinci a cikin jirgi duk ba wani ci tayi ba sai data bude baki dole tace abarsa bata buqata.

Mum tayi bacci sbd yau tinda ta futa tin safe bata dawo gidan ba sai dare dan haka maganin ciwon jiki ma tasha ta iya samun bacci dan haka koda SANAAH ta tambayeta fammah tace saidai kuma da safe.

Kwantawa sukai take bacci mai karfin gaske ya dauke SANAAH din sbd gajiya da rashin sakewan data shiga tinda suka baro gida sai yanxu ta dan warware.

Washe gari da Asuba bayan sunyi sallah sun gama SANAAH bata iya komawa bacci ba ta dauki wayar Fammah ta saka kiran numbern Dad wanda tayi ringin harta yanke baa dagaba dan haka ta saka kiran Dr Mum wadda tana xaune a palo tana tinanin isa gurin Hakeem tagano ta kuma jiyo meke faruwa da shirunsa duk da kaman bai gane SANAAH bata gidanba kila har lokacin harma da Raheem din batajin yasan qasar ya bari.

Kallan wayarta tayi tana ganin numbern fammah kai tsaye tasan SANAAH ce insha Allah sbd a daidai wannan lokacin yanzu acan Morocco asuba ne kuma fammah basu taba kiranta a wannan lokacin ba dan ko bayan tafiyarsu so daya suka kirata har ita har Mum dinta dan haka tasan waye me kiran.

Dauka tayi a natse tareda cewa

"Assalam alaikm"

Amsawa SANAAH tayi da nutsuwa da jin dadin saukan muryan daya daga cikin iyayen nata a kunnenta tace

"Barka da asuba Dr Mum,ina kwana??

Numfashi itama dr mum ta sauke cikin hadiye wani mamakin jin SANAAH a gurin fammah wanda yake tabbatarda ba gurin Raheem kenan zata xauna ba,
Takaicine ya taso mata amma ta danne tana tinanin SANAAH dince tafi son hakan kila dan haka da kulawa da kauna tace

"Lfy kalau alhamdllh baby yaya hanya?
Ya gajiya?
Anan kika sauka kenan gurinsu Fammah??

Bata iya amsa tambayan karshe ba ta farko kawai ta amsa tana tambayar Dad dinta dasu Maamah.

Duka suna lafiya tace mata tana shiga wani zancen da ita suka dan jima suna magana kafin Maamah ta karbi wayar itama suka amsa kafin aka kira safiya takaiwa Mommy wayar itama suka gaisa suna kashewa Safiya ta kirasu da wayarta tafara musu mitan duk batajin dadi da basanan su duka.

Sai da suka gama wayoyin ta kwanta nan bacci ya sake daukanta mai nutsuwa.

Bata farka ba saida rana ta dan fara fitowa dan haka tana tashi wanka tayi a natse ta fito ta shirya cikin skirt da rigan Bahnab black masu kyau da suka dan lafe a jikinta kadan amma koina a ruge dan har qasa sosai skirt din yake sai rigar itama mai dogon hannu ce da turtleneck.

Milk silk scarf ne a kanta qamshinta me sanyi na tashi fammah ta jata duka fito suka fara zuwa dakin kakarse Amma duka gaidata ta nunawa SANAAH din kulawa sosai kafin suka zauna aka sakata breakfast anan wanda shima bata wani ci sosai ba sbd abincin ba wani abinda zata iya ci bane sosai so tea tasha kawai.

Suna dakin mutanen gidan ke shigowa daya bayan daya akai akai suna gaida Amma din dan haka da yawansu anan ta gaisa dasu da turanci kawai suke iya communicating sbd bata wani gane larabcinsu su kuwa daman basuma san hausa ba.
Chapter 95 · 0% Book details