← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 122

Sashe 98

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da nutsuwar sa ta samu kokarin tashi yake a kanta da Sauri tasa hannu ta Kama waist nasa gam,Wanda hakan ya fahimtar dashi cewa itama tana bukatar nutsuwarta duk da akwai mutuwar jiki da gajiya a jikinsa hakan baisa sa kasa tallafawa matarsa ba sosai ya tallafeta har ta samu natsuwa,mikewa yayi a hankali ya d'auki towel NASA wanka yaje yayi kana ya fito mikewa tayi itama ta shiga toilet in kafun ta dawo Harya chanja zanin gadon ya kwanta,tana fitowa Zama tayi daga ita sai towel,shuru shuru yaji Bata hau Kan bed in ba kallonta yayi kana yace"lafiya bazaki kwanta ba kinsan karfe nawa yanzun"?shuru ta Masa Bata hauro Kan gadon ba,shima Bai Kara magana ba ya gyara kwanciyar sa so yake ya samu bacci kafun asuba don gobe Suna da training da sassafe,amma kasa baccin yayi ya sauka akan gadon d'aukarta yayi gabaki dayanta yazo ya kwantar akan gadon ba tare da ya damu da towel in jikinta ba ya lulluba Mata blanket.

************
tashi tayi ta zauna again Wanda hakan ya saka sa sake tashi agogo ya gani kusan 2:30 na dare tsaki kawai yayi yace"Wai don Allah wannan ai d'aukar alhakine ya Zaki kasa bacci ki hanani nima"?a fusace tace"toh ninace maka karka kwanta ne"toh Taya Zan kwanta kina zaune"a hankali tace"yunwa nakeji"wani kallo ya Mata sai Kuma ya tashi tsaye hannu yasa ya taba jikinta Jin sanyi babu zafi yasa sa komawa ya kwanta abinsa Bai Kara magana ba ya barta a zaune bacci barawo yayi awun gaba dashi.

da asuba Lahab daya farka da mamaki Nnenna ya gani d'aure da towel Kamar yanda ya kwanta ya Barta idanunta biyu da mugun mamaki yake tambayar ta Wai Bata kwanta ba?kin amsa Masa tayi yasa hannu zai tabata kawai ta turesa Saida ya koma Kan katifa ya kwanta,bata Kara magana ba shima gyada Kai yayi irin lallai innan ma, ya mike Alwala yayi yazo yayi sallah duk tana zaune,Kaya ya chanja ya fita waje da asuban amma shuru babu kowa shaguna duk a rurrufe dakin wani makwancin sa ya shiga yadau fresh milk guda biyu ya kawo Mata kin karba tayi Wai tayi fushi daker ya samu ta karba tana Sha Koh aje goran batayi ba ta Soma amai Kamar zata amayar da hanjin cikinta sosai tayi aman lokaci d'aya wani irin zazzafi ya rufeta,daukarta yayi ya Kai toilet tare da wawwanke Mata jikinta ya fito da ita, Kaya ya sanya Mata ya kwantar da ita akan gado kafun yazo ya gyara wajen da ta batan.

Wanka yayi da misalin karfe 6 zuwa lokacin wani irin bacci yayi gaba da ita so yake suje asibiti Kar ciwon yayi tsananin amma ganin tana bacci tunda bata samu na daren jiya ba sai yayi tunanin bari ya barta sai ya dawo,kayan ball yasa wando da riga sai takalmi ya fita a dakin, direct training ya wuce basu Suka bar wajen ba sai kusan 9 na safe daga wajen wajen Saida abinci ya wuce kaza yasai musu sai kayan ciye ciye na laida Incase kada ta bukace Abu lokacin da bazai samu ba shiyasa ya sama Mata irin su cake su pizza duk ya sassaya sosai ya Mata sayayya.

Lokacin da ya dawo ya samu ta farka zaune take gabaki d'aya ta jirkita ganinsa da laida Koh barin ya ajiye batayi ba ta kwace tare da budewa cake Inda ta gani a ciki shita warware da Sauri ta Soma ci ci bana Wasa tama cake in ba,shidai Lahab idone nasa ba bakin magana amma yasan tabbas Bata da lafiya wallahi irin wannan haukan cin Kamar Wanda ta shekara da yunwa,Kamar d'azun da asuba tana gama ci sai amai,ganin haka yasa Lahab cewa ta tashi su tafi asibiti amma kai da fata Nnenna tace ita lafiyarta klau babu Inda zata,taba jikinta yayi yaji babu zafi Kamar d'azun, tambayar ta abinda zataci yayi tace apply,mikewa yayi yaje ya jido apply kwali guda fresh dasu yazo ya jera Mata a daki Aiko shikenan Nnenna ta samu abinci Bata da aiki saicin apply tunda kome taci amai yake sata Amma Banda shi.

Lahab yaga ikon Allah gabaki d'aya Nnenna ta sauya ta Zama mabukaciya don tun tana kunyarsa tana jiran shiya Fara tabata Harya kasance ita ke nuna tana sonsa a aikace ba'a bayyane ba,shima Yana iya bakin kokarinsa wajen sauke nauyin da Allah ya daura Masa akanta Koh da kuwa baya mood,ga cin apply ga fad'a fushi da mita duk yanzun Nnenna ta koya cikin satin da sukayi harta chanja Sosa ga yawan zazzabin asuba da kuma yamma, sai yace su tafi asibiti tace bazata ba suyita fada Harya hakura ya kyaleta.

Sun samu nasara sosai Lahab Yayi bajinta a wasan da suka buga yasha musu sosai,hakan yasa sa daukaka sosai,sun koma gidan su,sannan team nasu sun basa kudi sama da million biyu cikin abinda Suka samu saboda bajintarsa cikin kudin ya baiwa Ade have million sannan ya turawa Rahab 300k ya baiwa uzaifa 200k tunda Sunsan Inda kudin ya fito lokacin da ya tura musu basuki amsa ba account ya Kai Nnenna ta bude ya zuba Mata kudin da shayibu ya basa nata kana ya Kara Mata 100k a ciki,Lahab a sannu sannu ya Fara Zama sannan ne a fagen kwallon kafa don sosai ya iya buga wasa hakan yaja Masa farin jini da daukaka har yasa wasu team Fara daukar sa haya Yana buga musu Wasa ba tare da sun damu da kankantar sa ba kudi kuwa sosai ya Soma damkarsu sosai Kuma Alhamdulilah Lahab mutum ne da baida gyashi kome ya samu sai ya tsamma Rahab dake India da uzaifa haka zalika zaisa wa Nnenna a account nata duk da Bata cin Koh sisi haka zalika Adewale don yanzun tuni Suka bar gidan da suke lahab ya Kama musu gida Mai zafi wadacece Suka koma ciki don wani sa'in sai afi wata Ade Bai hadu da Nnenna ba waje d'aya sai in ya shigo part nasu Lahab ga moto Lahab ya saya ya saima Ade duka rayuwa tayi Dadi bana Wasa ba tuni papan Ade yayi sanyi lokacin da ya kawowa Ade ziyara yaga yanda Allah ya daukaka Lahab Kuma Yana taimakon dansa har dawainiyar makarantan Ade yanzun Lahab keyi,Amma tuni ya manta da zancen wani Nabeel don tunda yazo kasan Bai taba kiransa ba saidai in Suna waya da Ade in Yana gun shine inya tambaye shi sai Ade yace gashinan su gaisa.

Lahab sun koma makaranta tuni har semester yayi nisa yaso yasa Nnenna a makaranta Amma babu Hali tunda Bata da shaid'an takardun Gama secondary,ga rigimar da take fama da ita nata na masifa ga yawan ciye ciyen kayan fruit don yanzun tabar apply ta koma kankana da mangoro Koh Kuma abarba.

Lokacin da labarin Lahab ya Fara zaga katsa tuni Yan nageria Suka Soma Jin labarin sa wani Dan naija best footballer Kuma very young a turai gashi da farin jini bana Wasa ba duk channel na sport ba'a rasa nasa a ciki,lokacin da labari ya Fara riskan Mami tunda ba kallon kwallon take ba sai Yan uwa ke kiranta Suna cewa sunga Lahab na ball a TV koransa tayi tana Masa fada akan an turasa karatu yaje ya Kama abinda bazai amfane saba Bata yarda ba,Aiko waya yayiwa Abbu ya sanar dashi dare da Masa Alkawarin insha Allah zai kammala karatunshi tare da sakamako Mai kyau daker dai Abbu ya sauko ya baiwa Mami hakuri ya cigaba da Wasa tunda sunga kokarin da yayi a karatu.

tun safe Lahab ya fita Bai dawo ba saboda Wasa da suke bugawa Mai zafin gaske bashi ya dawo gida ba sai kusan 2 na dare,shigowa falon yayi ba tare da ya kunna wutan ba ya wuce sait nasu bude dakin su yayi ya shiga da sallama,dan waro Ido yayi ganin wutar dakin a kunne ga Kuma Nnenna kwance a bargo"Kai amma yarinyar Nan bakiji taya Zaki kwanta da wuta a kunne"kashe wutan yayi ya zaro tafkeken wayarsa dake bag dake bayansa ya kunna hasken waya aje bag in yayi yadau towel ya nufi toilet wanka yayi kana ya fito,daure da towel in kayan bacci yasa ya fita a dakin kitchen ya wuce ya tare coffee nasa Mai zafi ya zauna a dinning dake cikin kitchen in ya Soma Sha Saida yasha Rabin cup kafun ya mike.

d'akin ya shiga tare da matsowa kusa da gadon hannun sa yasa ya warware blanket Inda ta lulluba zai kwanta da Sauri ya sake blanket in, saboda turirin da yaji ya fito daga cikinsa har yanajin wucin numfashinta Mai zafi Ashe idanunta biyu sai rawan d'ari take hannu yasa ya tabata da Sauri yaja baya zafi jikinta jaujau"subhanallah Labiba tun ba yauba nasan baki da lafiya amma rashin jin da Kika kakkabawa kanki yanzun ya hanaki Bari muje hospital"?kasa amsa Masa tayi bakinta ya bushe sosai hakoranta har haduwa suke da juna,mikewa yayi da sauri ya nufi wardrobe nata budewa yyi ya dauko Mata wando da riga amma irin bujennan masu Fadi yasa Mata hijab ya dauko cikin Wa'inda ya sai Mata duk da ba amfani yake dasu ba Kuma hijab in irin have Sunnah ne.

A daren nan Lahab ya dauketa sai Wani hospital Mai tsada, a cikin daren Nan aka amsheta zuwa lokacin zazzabine yaci karfinta sosai ruwa Suka daura Mata tuni tayi bacci sai gwaje gwaje da aka mata,a asibitin Lahab ya kwana tare da ita tana farkawa da safe ta Fara Neman abinci Kuma ta tashi garau abinta,fita yayi ya sai Mata abinda zataci taci kana aka sake daura Mata ruwa.
Chapter 98 · 0% Book details