← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 122

Sashe 51

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page 63&64
da Sauri Nnenna ta sauka akan Lahab tare da kallon kofar dakin, nurse in jiya ne a tsaye ta Kura musu Ido,kunya ne ya Kama Nnenna sosai akallah nurse in zata Kai shekara 30 shima dai Lahab tad'anji kunyan kad'an amma saiya basar ya lumshe idanunsa tare da juyawa dakin baya tare da lullube jikinsa da bedsheet,d'an gyaran murya nurse in tayi cikin mamaki don ita ta kasa gane menene tsakanin yaran Nan guda biyu wallahi,kun sai maganin da likita yace min ya rubuta maka?

Nnenna ce ta bata amsa"ah ah yanzun ne zanje na Sayo"tana maganar tadau bucket na kayan tare da daukar pepar da card na Lahab ta juya zata tafi"Kinga zonan Labiba"Lahab ya Kirata dawowa tayi kanta a kasa don har lokacin nurse in na dakin tana had'a Masa magangunan sa"kidau abinci kici sanan banason ki fita a haka kizo ki zauna in ruwan ya Kare Zan fita da kaina na sayo"

kallon Lahab nurse in tayi sannan ta kalli Nnenna kafun tayi magana"sister jeki dau breakfast naki kici ashe baki karya bama,Kai Kuma Hassan bai kamata ka fita ba kadai barin ta karya sai taje pharmacy in Naga ma harda Kaya takeson ta Shanya Koh?

gyada Kai Nnenna tayi sannan ta aje bucket in ta zauna akan kujera ta jawo laidan abinci ta soma ci"gaskiya sister nafi dai son ta zauna in ninaje na sayo Kuma na Shanya kayan"?

Kallon Lahab ta sake,saboda me bazata fita ba?

"Kalli kayan jikinta fa a hakan takeson ta fita"

dan zaro ido Nnenna tayi kafun tace"Kai Wai Ina ruwan ka da shigena ne Kam"?

"Keee Ina ruwa na kikace?toh a kwai ruwana Kuma wallahi bazaki fita a hakan ba"

Shuru Nnenna tayi tana cigaba dacin abincin ta murmushi nurse in tayi wallahi ita sosai take mamakin yaran Koh menene tsakanin su don basu Mata Kama da Yan uwa ba especially datazo taga Nnenna akan lahab hakan ya Kara tabbatar Mata ba Yan uwa bane,meyasa baka son ta fita a hakan?

"Sister ki kalle kayan jikinta fa Kai Koh dan kwali ma babu"

Juyawa nurse in tayi ta kalli Nnenna Jin abinda Lahab yace"toh ke meyasa Zaki fita haka bazaki sa dankwali da Kaya Mai kyau ba?

Nnenna hadeye doyan dake bakinta tayi kafun ta bata amsa"nifa Christian ne bansan meyasa ya damu saina sa Kaya irin naku ba"

Jin abinda Nnenna tace yasa nurse in dan waro idanunta tana kallon Nnenna dawalakin goro a miya ashe shiyasa tun jiya take yawo da gajeren sikit toh shi Kuma wannan a Ina yasamu Yar inyamuran Nan kauda tunanin tayi da Sauri tana sauraron abinda Lahab kecewa Nnenna"toh saiki fadamin a Ina akace ku ringa shigen banza donke ba musulma ba sai akace ki ringa yad'a alfasha"?kaga Hassan tsaya menene haka ya zaku zauna Kuma cecekuce akan addini Maison gyara ai baya fada Koh zuciya.

Shuru Lahab yayi Kamar yanda Nnenna itama tayi duk Suna sauraron holon da nurse in ke musu,Kunga duk ku rufemin baki ke Kuma kina bibiye Masa bayan Kinga ba lafiya bane ma dashi kinsan Mai jinya da rawan Kai,amma fa abinda yace baiyi laifi ba bai Kamata ki fita a hakan ba nan Arewa ne Muna da al'adu da kunya,don haka ki tsaya bara naje na kawo Miki abaya ta danake zuwa da ita Ina daurawa akan uniform saiki sa da dankwalin sa ki fita ki Shanya kayan kije pharmacy duka,ba shikenan ba na raba gardaman?

kallon Nnenna yayi sannan ya kalli nurse in"eh shikenan ki kawo Mata ta saka mungode sosai"ba kome Hassan Amma bara muji daga bakin ta Koh ta amince karma takurata?gyada Kai Nnenna tayi alamun itama ta amince,fita a dakin nurse tayi bata Jima ba sai gata ta dawo da abaya baki da igiyan sa sai dankwalin sa karba Nnenna tayi tana Mata godiya,ba kome tace sannan Kai Kuma Hassan ya Kamata ka rage b'uruntun Nan haka kaji da lafiyar hannun ka.?

Insha Allah Zan kiyaye"fita tayi a dakin ta barsu itama Nnenna mikewa tayi bayan ta gama karyawa rigan ta zura a jikinta ta daura da igiya sai dan kwali data makala a kanta tadau bucket in kayan da card tayi waje.

Bayan fitar Nnenna baccine ya d'auke Lahab bayan yasha magangunan da nurse ta aje Masa bacci ya dauke sa baima San lokacin da Nnenna ta dawo ba.

da misalin karfe 8:20am na dare Lahab ne zaune akan gadon sa Yana cin gasheshen kaza da ya aike Nnenna ta soyo Masa bayan masifar da ya rufeta dashi akan bata iya kula da Mara lafiya ba ya za'ayi ya samu tsagen Kashi ace tun safe baici nama ba,shine fa ta fita ta sayo Masa gasheshen kaza biyu sai milk ita Kuma ta saiwa kanta fruit salad data gani a bakin asibitin don duk abinda ake sai dawa a restaurant na wajen akwai nama a ciki,kallon Nnenna yayi sannan ya kalli Naman sa so yake yace Mata tazo suci amma Kuma inya tuna abinda ta Masa sai yaji bazai bata ba daurewa kawai yayi ya yagi cinya ya Mika Mata,ganin bata masan yanayi ba yasa sa Mata magana da baki"ki karba ungo"?

Kallon hannun nasa Mai lafiyar tayi sai Kuma tayi murmushi tare da mikewa d'aga Kan kujeran da take ta matso Kan gadon Zama tayi a bakin gadon tasa hannu ta amshi cinyar kaza dake hannun sa har lokacin, bakin sa ta nufa da naman,girgiza Mata Kai yayi tare da nuna Mata bakin ta watoh ita zataci"kaci samun kashinka ya koma yanda yake"

Hararan ta yayi"ce Miki akai Zan iyya cinye kaji biyu ne duka d'ayan ma bazan iyya ci duka ba shiyasa na tsammiki"

"Kaga Ni Kuma banacin nama"dan zaro ido yayi Yana kallonta"kina da ciwon hanta ne"?girgiza Masa Kai tayi.

"Ciwon hanji"Nan ma girgiza Masa Kai tayi"toh Koh Naman kazane bakici bakinki ya Saba da naman karnuka da aladodi"?wani kallo ta Masa Jin kalar tambayar da ya Mata bata ma basa amsa ba ta Mike zata bar bakin gadon,da Sauri ya Kama hannunta,kallon hannunta daya kamata tayi ta kalli nasa sannan ta dago ta kalli fuskarsa fuska a hade "yau tun safe kina Kan kujera why not yanzun ki kwanta ki huta"?

A Ina Zan kwanta na hutan"?

Nuna Mata gadon yayi"toh Kai Kuma ka kwanta a ina,"gefen gadon ya sake nuna Mata"oh so kake mu kwana tare kenan koh"?eh haka nake nufi"

fizge hannunta tayi ta rike kwankwaso tana kallon sa kafun ta soma magana"d'azun da safe a dakin nan ka Kare min tanadi kace Ina yawo ba Kaya Mai kyau gashi Kai Kuma yanzun kana cewa nazo mu kwanta? nima bari na tambaye ka a addinin naku ance ku kwana da mace gado daya ne ba aure"?

Kama baki yayi Yana kallonta sai Kuma yace"ah ah

"toh don haka in kanason na kwanta na hutan ka amshi waya ka Kira gidan ku Koh ka ban address na gidan kun tunda kace a unguwan mu kake,sai yanzun naje na sanar kaga nima saina samu na koma gida yau kwana daya kenan ban bawa Kiki na abinci ba Ina tsoron Kar yunwa yasa ta Kama dabbobi taci fa"?

Komawa yayi ya kwanta Yana mita"aiko saidai kiyita kwanan kujera karki huta in indai nine Zan Kira Yan gidan mu Koh aikan ki tunda dai ke Kika karyani ya zama Miki dole kiyi jinyata,Kiki Kuma inyaga dama yaci mutane ma ba dabbobi ba"komawa tayi ta zauna taci gaba dashan fruits nata har karfe 11 idanun su dukan su a bude basuyi bacci ba Nnenna Kam gabaki d'aya taji bayanta da hips nata har wani kamawa suke ta gaji da zaman kujerar bata samun isheshen bacci Mai dadi akai, gashi bata San kasuwa ba da sai taje gobe tasai taburma da filo,ga tunanin Kiki da take da halinda yake ciki,amma bata damu da Yan gidan su ba tasan babu Mai damuwa da rashin ta tunda dady baya Nan.

12:11am ta Mike a hankali ganin Lahab ya sake sosai gashi sai sauke numfashi yake Kamar Mai bacci,alhalin Kuma idanunsa ras suke ba bacci yake ba,leka fuskarsa tayi ganin idanunsa a kulle sai sauke numfashi yake a hankali hannu tasa ta kashe wutan dakin a hankali cikin Sand'a ta hau Kan gadon kwantawa tayi a bayan sa wajen dan filin da ya rage hannunta ta nade tayi filo dashi Koh minutes 10 batayi ba bacci ya dauke ta,mikewa zaune Lahab yayi duk da duhune amma Yana kallon ta filon sa ya matsar kanta a hankali ya d'aga Kan ya daura akan filon tare da gyara Mata hannayen ta shima kwanciya yayi yasa kansa a filon ya Zamanto dukan su biyu ke kwance akai, Addu'an bacci yayi baijima ba bacci yayi gaba dashi.

******************
Nabeel bai zarce Koh Ina ba sai gidan su Ade yana Isa gidan hannu yasa ya kwankwasa kofar Mai gadi ne yazo ya bude ganin shine yace bafa zai bude Masa ba don papa yace karya sake bude Masa shida Lahab,ganin da gaske bazai buden ba yasa sa rokonsa akan Yama Adewale magana Yana waje yanason magana dashi,daker dai Mai gadin ya yarda tare da nufar cikin gidan.

Bai wani Jima ba saiga baigadin sai Ade daken binsa a baya bude kofar yayi cikin fara'a,ah ah shegen yaka saya a waje kashigo Mana Yana maganar Yana wangale Masa kofar shiga gidan,Nabeel Kam sosai ya kurawa Adewale Ido ganin yanda yayi mugun rama daga gani kasan baida lafiya ne,ah ah Adewale Nan ma ya Isa basai na shigo ba.

Kama Isa kazo mu Shiga kawai guy?

dan Jim Nabeel yayi bawai gidan su Adewale bane baison shiga ah ah yau weekend ne taima baban sa na gida yaje yaci Masa mutunci a banza don baida matsala da maman Adewale,no Ade Nan ma is ok daman nazo na tambayeka labarin Lahab ne nayi missing nasa kwana biyun nan Koh na Kira wayarsa baya shiga shine nace bara nazo wajen ka Koh zamuje gidan ya jafar mu dubo sa amma Naga kaima Kamar Bakajin dadi ba ma amma Koh notice babu nazo na dubaka.

Sai murmushi Ade keyi Yana sauraron zuban da Nabeel ke Masa ba gaggautawa sai da ya bari yakai Aya kafun yace,toh yanzun dai wanne Zan amsa a cikin tambayar Nan naka?

Koh ma wanne ka Fara amsa wa.
Chapter 51 · 0% Book details