← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 122

Sashe 73

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tura kofar falon yayi ya shigo sai Kuma yayi turus ya tsaya ganin Wance ke tsaye a tsakar falon,a hankali ya karaso ciki mamin sane zaune akan kujera sai Alhaji sulaiman shima a zaune yake ga Rahab a zaune akan carfet,farida(budurwar Anwar na da)ce tsaye kallo daya zaka Mata kaga ainahin Kamar ta na rashin mutunci gabaki d'aya ta zafge sanye take da lafcecen hijab har kasa sai nikaf data daga shi sama fuskar ta a bayyane,nuna farida yayi da yatsa Yana yamutsa fuska yace"wannan Kuma wacece Mami me take a gidan Nan ba auren ance an fasa da ita ba metake mana anan"

Juyowa farida tayi fuska jawur idanunta a kumbure sumdum ta Soma magana Kamar haka"wallahi tallahi Lahab tunda ka rabani da farin ciki ka rabani da walwala ka Haddasa min bakin ciki na rantse da Wanda Raina yake hannun sa Koh zanyi yawo tsirara Lahab saina Haddasa maka kaima bakin ciki ka rubuta ka ajiye nazone na baiwa uwarka sallahu tunda har kayi sanadin da bakin ciki ya kashe mahaifiyata ta bar duniya jiya Kuma akan abinda kayi bazan barka ba.

Mikewa Mami tayi tace"ke karamar Yar iska, ya kashe Miki uwa Koh bakin cikin ki ya kasheta shasha Sha karamar Yar bariki zakizo kice bazaki bar dana ba a gabansa, toh wallahi bazan bar maganan Nan ba sai mun danganta da kotu sai an rubuta Kamar yanda Kika ce duk abinda ya Sami d'ana kece sula ba Baki da mutunci ba Zan gwada Miki yanda ake rashin mutunci Mami na karasa maganar da Sauri ta shiga dakin ta,ganin hakan yasa farida barin gidan da Sauri tana rantse rantse bazata barsa ba.

Lahab Kam da Rahab duk shuru sukayi suna mamakin yanda farida tasan Lahab ne ya tona Mata asiri,fitowa Mami tayi a dakin tana waya da wani barrister akan zata Kai kara station yanzun za'a turo su kotu,kofar falon ta nufa hannun ta d'auke da hijab har lokacin hannun ta Kare da waya a kunne,da Sauri Alhaji ya mike Yana dakatar da ita akan babu Inda zataje ta koma ta zaune bude Baki Mami tayi tace"taya zanyi na zauna wannan shegiyar yarinya Harta Isa ta shigo gidana a gabana tana ma yarona warning harda Shan Alwashin bazata barsa ba kasan me zata Masa gaskiya ban yarda ba wallahi dole nasan abunyi.

Nace ki dawo ki zauna Amina Kika San Koh zafin mutuwar mahaifiyar tane yasa ta fadin haka dame zataji yanzun da mutuwar Koh da abinda Zaki Mata yanzun"d'aga Masa hannu Mami tayi cikin masifa tace"wani irin Bata hayyacin ta Bata hayyacinta ne zata gayamishi haka watoh nabar maganar ta wuce,daga baya nazo Naga d'ana cikin wani Hali bada Ni ba"

Kinji na rantse Amina babu Inda Zaki na gaji nagaji wannan wani irin abune haka fisabililahi,ban Isa dake ba kenan Koh ban Isa nace kibar Abu ki Bari ba,sai Kuma ya mike tsaye cikin bacin Rai yasa Kai yabar gidan,komawa tayi Kan kujera ta zauna ta dafe kanta,da Sauri Lahab da dan uwan sa Suka nufi mahaifiyar tasu ganin Kamar kuka ta Fara rungumar ta Lahab yayi a rikice,da Sauri ta turesa tare da wanke sa da Mari ta Soma magana cikin kaushin murya"matsa min daga jikin Lahab ya zanyi da Kai ya zanyi da Kai duk abinda na fada maka bashi kake aikatawa ba kwata-kwata Bakaji Koh don mahaifin ku baya rayene,ni Kuma bana tare dakune shiyasa kuke abinda kuka ga dama so kake hawan jini ya Kamani nima na mutu na barku.............

da Sauri Rahab ya rufe Mata Baki hawaye na bin kumatun sa yace"don Allah Mami kada kice haka, ki sanya Mana albarka don shi mukafi bukata a Yanzun insha Allah Koh babu mahaifin mu a duniya zamu zamo abin kwatance da Alfahari bazamu taba yin abin Allah wadai ba Abbu ya jafar ya muzammil Suna iyya bakin kokarin su wajen ganin sun tsaya a Kan tarbiyar mu Mami in bazaki yaba musu ba,Bai Kamata kiga gazawar su ba akan muba.

Rungumar dan nata tayi Lahab dake zaune a kasa tunda ta turesa daya sunkuyar da kansa har yanzun bai daga ba,Saida yaji abinda mamin nasu ke cewa"Lahab tun farko Nika Fara kawowa zancen farida nace maka ka bar zancen ashe Lahab baka bari ba Saida ka bibiye yarinyar Nan,ka tona Mata asiri yanzun Kuma tazo tasha alwashin bazata barka ba meyasa kake son damuwa da wa'inda basu damu da kaiba kake son gwaninta wa wa'inda gwanintar taka ba ganin sa zasu Yiba meyasa-meyasa nace meyasa Lahab"ta tambaye sa da karfi.

dagowa yayi idanun sa jajer yace"Saboda d'an d'an uwana ne bazan so mugun iri a cikin zuriyar mu ba Kuma na tabbata Koh nine Anwar shine Ni sai Inda karfin sa ya Kare wajen Hana wannan aure, murmushin takaici Mami tayi tace"lallai yaro baisan wuta ba saiya taka da ace kasan wacece Halima da bazaka d'aga Ido ka kalli yaranta so biyu ba Halima ta musguna min a rayuwa Halima tamin sharri kala kala bata da makiyiya kamar Ni,amma nasan baka San tarihin gidan ku ba illa Suna da ka sani da yan uwan ku,a yau Zan baka labarin tushen aure na da mahaifin ku da Kuma dalilin auren nasa yana babban mutum Ina yarinya.

****************
WAIWAYE ADON TAFIYA...............

Alhaji Al'hassan dogo Mai Naira shine cikekken sunansa ainahin su Fulani gombe ne haifafun cikin gombe Alhaji Al'hassan tagwaye ne dattabai masu sananin Kama da junan su Wanda a lokacin zaiyi wuya kaga tagwaye tsofafe masu Kama irin shida d'an uwan sa Al'hassan tare Suka taso kome iri daya suke Hatta karatu course d'aya Suka karantaAlhaji Al'hassan nada Mata d'aya kwallin gwal,Hajiya Aisha Wanda yaranta suke kiranta da Addayiya auren saurayin da budurwan sukayi da ita har Allah ya azurtasu da Y'ay'a guda biyar Umar(abbu) sai da Umar yayi wayo ya Soma zuwa makaranta kafun aka haife jafar saboda haihuwar Aisha tana da tazara sosai Saida jafar ya girma kafun ta haifi sumayya (goggo) sai autan ta Muzammil (uncle).

Alhaji Al'hassan kudi sun zauna sosai haka ma Al'hussain shima yayi aure amma har tsawon shekaru matarsa bata taba haihuwa ba,duk da Al'hassan yasha basa shawara akan ya Kara aure amma kememen yaki yace haihuwa na Allah ne Kuma Koh baida rabon Y'ay'a a duniya y'ay'an Al'hassan Suma sun isheshi da haka yake kashe Masa Baki.

Umar yayi aure bayan ya kammala karatun sa har mahaifin nasu ya gina Sabon kamfani Kuma ya basa manager a company in yana gudanar da ayyukan ciki,Umar nada yara uku da matar sa Halima(mamu)d'ansu na farko Anwar sai Mai binsa Shareef da kanwar sa umaima,bayan haihuwar umaima ne ya Kara aure ya aure ummu ta Haifi d'anta na farko uzaifa a lokacin.

Jafar yayi aure shima ya aure Khadija (nanne) Yana aikin gonnati,Yana da yara hudu Hashim Fatima sai Aisha(Amaryar Anwar)sai auta Majid a lokacin ma Yana jinjirin sa,sumayya(goggo)tayi aure ta auri sarkin katsina tana zaman aure a shan, muzammil lokacin an Fara Zama saurayi har an shiga jami'a ana karatu a cikin gombe.

Al'hassan mutum ne Mai hakuri dattako dajan nasa a jiki sosai, An basa minister of labour and employment,kudi ya zauna sosai hakan yasa sa gina babban gida yadau 'Ya'yan sa da d'an uwan sa(Hussain)ya maida su cikin gidan,gidane da ake zaman lafiya Kuma babban gida sai abinda baza'a rasa ba mamu(halima)macece Mai masifar tsiya da kasa hakuri yayin da ummu ta kasance Yar ba ruwa na hakan yasa zaman su yayi sanyi don Koh mamu ta hau ummu Bata kulata, Addayiya akwai gajeren hakuri sai dai macece Mai tausayi matuka tana kaunar mijinta da Masa biyayya sosai sannan babu ruwan ta da sawa surkunaye Ido daman part nasu daban tsakanin tama dasu akwai rata shiyasa ba'a Jin kansu,gogo badawiyya(matar Alhussan)daman ita macece Mai sanyin hali ga yawan shuru shuru shiyasa gidan baida hayani Kamar gidan yawa.

A wata Litinin Alhaji Al'hassan da tawagan sa Suka je wani kauye na Fulani usul dake karamar hukumar bajoga dake cikin gombe,wani rikici ne daya hafko tsakanin Fulani da manoma,sosai akama Fulani barna Kuma ya mugun tausaya musu shiyasa ya taso takanas yaje rugan,minister ya mike ya shiga rarrabawa jama'a kudi sosai Yan kauyen Suka cika da murna ga kayan masarufi da aka sauke musu mota babba ana rarrabawa buhuhunan shinkafa da masara,tun daga nesa ya hangota d'auke take da Robobin nonon ta akai dawowar ta kenan daga cikin gari ta Kai tallan no-no tana dawowa su uku ne suke tafe tana tsakiyar su,ganin yanda ake rabon abinci da kudi yasa sauran abokan tafiyar tata Suka aje Robobin su da gudu sukayi wajen motar da Kuma dattijon dake raba kudi,tunda ta d'aga Ido ta kalli wajen bata Kara kallo ba tafiyar ta kawai ta cigaba dayi.

Mikawa PA nsa kudin hannun sa yayi ya cigaba da rabawa,ya nufi barin wajen da Sauri security Suka mimmmike zasu bisa,ganin hakan ya Sasa shiga mota kawai ya zauna amma bai rufe murfin ba Yana kwanton yaran da suke tare da ita,yafito security yayi ya sanar dashi akan ya Kira masa yaran da suka d'au buhun shinkafa ta gwannati akan sun Nan su biyu,Kiran su security sukayi duk da kowa yasan yan kauye da tsoro hakan bai hanasu zuwa ba,Jin Wanda ya raba musu kudine ya kirasu aje shinkafan sukayi da Sauri Suka nufi motar.

Kabo na Isa gida ta aje roban nonon ba tare da ta saurare masifar da innon ta ke Mata ba akan ta San ana raba Abu bazataje ta karbo ba ai in bata samu ba,yayan ta zai samu in Kuma Suka samu dukan su karuwan sune,daki kawai kabo ta shiga ta fito da soson ta sai sabulun sodan ta dan kankani taja ruwa a rijiya cikin k'walla ta nufi kewayen nasu,Aminatu shine cikekken sunan ta yarinya ce da bazata wuce shekara 16 ba kyakkayawar bafulatana ce Fara Sol da ita sai kauyanci daya Kara boye sirrin kyawun nata sosai.
Chapter 73 · 0% Book details