Sashe 75
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A bangaren gidan minister Suma sunsha mamaki da sukaji an baiwa Alhassan Mata a zaton su ma babbace tsohowa Kamar Addayiya,amma duk da hakan Addayiya ta nuna kin amince warta akan me zai Karo Mata Amarya bayan Saida Suka riga Suka tsufa da Yaya da jikoki wannan ai abin kunya ne Amma me rumtsa Ido yayi yace yaji ya gani y'ay'an sa gabaki d'ayansu sun nuna basa kaunar auren Amma yaki hakura dan uwan sa Saida ya bashi shawaran hakura ganin gidan nason rikicewa,amma yace babu Mai hanasa auren Amina.
Zancen aure ya kankama Kaya na Alfarma minister yayi ma Amina Wanda yasa Yan kauye Suka ringa CeCe kuce akan inno zata saida Amina saboda tsabar son kudi irin nata amma inno ta toshe kunnen ta ta musu ta uwar shegu,saura sati daya biki duk Wanda yaga Amina sai ya tausaya Mata ta rame ta zabge tayi kuka tayi kuka harta fawwalawa Allah lamuran ta amma fa bawai ta hakura bane, sosai take Jin wani irin tsanar Alhaji a ranta tare da kudurta irin abubuwan da zata shuka Masa in yayi gangancin auren ta.
tirkashi ana wani ga wani cikin wannan Hali sulaiman ya Fado a cikin rugan su yazo ya tarar da wannan mummunan labari sosai ya birkice Kamar tababbe da kansa ya shigo har cikin gidan su Amina yazo ya dafa kafar inno Yana rokonta akan kada su rabasa da Amina amma inno tace aikin gama ya gama wajen kawu shehu yaje amma Ina babu alamun nasara don ba karamin kudi Alhaji ke sakarwa inno ba,yaso ya rusa gidan su Amina kafun aure ya musu na zamani amma inno tace a Bata kudin kawai abin magana baya kad'an a kauye har jikokin su sai amma gori.
Sulaiman tunda ya dawo yake bin Koh wani hanyoyi don ganin ya hadu da Amina amma inno ta datse Amina Koh Nan dashan Bata fita ta kasa ta tsare,sulaiman bai samu ganawa da Amina ba sai a daren da za'a daura Mata aure misalin karfe Sha biyu na dare ta farka don da Rana kanwar sulaiman tazo ta sanar da ita akan yayan ta zai jirata a Sauro da daddare ta fito zaiyi magana da ita a sirri karta fadawa kowa,tun karfe 9 na dare take son fita tana tsoro, gudun kada wasu su ganta Koh inno ta farka ta Kamata zata fita.
tafiya take a hankali cikin duhu gudun kada a jiyota kofar gidan su ta nufa a hankali taji muryar mutum a bayan ta da Sauri ta juya hade da kwala ihu da Sauri sulaiman yace nine Amina karkiyi a jiyo mu,jikinta ne ya daina bari anan Suka zauna Suka soma tattaunawa Suna muhawara don sulaiman cewa yayi ta tashi su gudu daga rugan suje suyi aure a can Inda yake NYSC,ita Kuma tace bazata jawa iyayen ta abun kunya ba akan me zata bisa suje suyi aure su shiga duniya ita bata yarda ba amsar da ta basa shiya kuntata Masa Rai, anan fad'a ya barke a tsakanin su sosai sulaiman ya gaggasa Mata magana akan itama tana son auren Alhaji shiyasa ta Fadi haka Ashe ba soyayyar gaskiya take Masa ba taga Mai kudi zataje birni.
Komawa cikin gidan tayi tana kuka ta shiga dakin ta ta kulle wani irin zafi takeji a ranta har Addu'a take Allah ya dauke ranta kafun gobe ta huta Kar taga wannan Rana da za'a ce an daura Mata aure da tsohon nan,.
*********************
Rana bata karya saidai uwar d'iya taji kunya ayau dubban al'umma Suka shaida dauren auren Alhassan Muhammad dogo Mai naira tare da Amaryar sa Aminatu kabo jibril Akan sadaki naira dubu Ashirin,tunda aka kafa rugan ba'a taba daurin aure irin na ranan ba jama'a mn Kamar kasa Yan birni sosai Suka cika kauyen hatta yaran ango da jikokin sunzo daurin auren kakan su,Amina dake daki,kafa yasha yaben bakin lalle da hannu sai kuka take tunda gari ya waye Koh wanka taki tashi tayi Jin lasfikan masallaci iska ya kado zancen daurin auren nata dib taji ta d'auke wuta bata Kara sanin me ake ciki ba Saida ta farka ta ganta a cikin mota ana tafiya da ita,watoh ashe data Sumama bata tsira ba a sumen aka sata a mota bama ta lafiyar ta ake ba ta zancen aure suke sai yanzun take takaicin rashin yarda da abinda sulaiman yace Mata tayi,data bisa Koh bangon duniya ne suje.
****************
tafiya suke sosai ganin haka yasa ta hakura da iFace iFace da take ta nutsu waje d'aya har lokacin hawaye baibar bin kumatunta ba idon Nan Kamar garwashi,tsayawa motar yayi itakam har lokacin bata dago taga Inda suke ba bude motar akayi da Sauri wata goggon ta ta lulube Mata fuska Wai gudun kada a ga fuskar tata ba'a sayi Baki ba.
Jidai kawai tayi Suna tafiya amma Bata San Inda take sanya kafarta ba har suka nufi cikin sashen nata ajeta sukayi akan gado Suna jin Mata sai shigowa suke Suna fita ana gaggaisawa da Yan uwa ta,abinci aka kawo musu aka aje duk matan dakin Suka fita aka bar amarya dayan uwan ta sosai Yan uwan nata Suka Soma cin abinci basu Koh damu da halin da Amina ke ciki ba Suka hau zagin mutanen gidan Wai Suna musu kallon wulakanci Kamar sunga Kashi ga wani d'add'aga hanci da uwar gidan take,ai maganin inno kenan ba kwadayi ba sai ta Kai yarta ga mahallaka Koh wajen yan Yankan Kai,inji wata tsohowa a cikin su itadai Amina har lokacin tana lullube Bata yaye mayafin ba.
da yamma akace za'a Yi budan ka gidan minister sosai ya cika da Baki duk da auren sirri yayi amma bai buyaba zancen auren Kuma kowa yaji sai yace zaizo yaga matan da Alhassan ya Kara da gangan aka kirkiro budan Kai don ayi maganin tsohowar d'aya aura,wanka Amina ta sake Alhassan ya turo matar Alhussan tazo ta kawo Mata kayan da zata sa don duk gidan babu Mai supporting auren Nan nasu sai ita hatta dan uwan sa baiso.
Ba karamin mutuwar tsaye goggo badawiyya tayi ba data ga Amaryar tsohon nan,amma batace kome ba haka ma bata fadawa kowa ba ta kawo Mata zani da Sabon mayafi ta yafa,tanama Yan uwan Amina da aminar jagora har tsakar gida wajen budan Kai,lokacin da aka bude Kan Amina kowa ya Sha jinin jikinsa Addayiya kuka ta fashe dashi tana cewa Alhassan ya kunyatata ya rasa wance zai kawo Mata a wannan shekarun sai jikarta?da jikarta zatayi zaman kishi sosai fa magana ya bazu a gari akan zancen auren nasu.
Bayan kwana biyu baki masu zuwa kallon Amina da Yan gulma duk sun dan ragu Addayiya har ciwo tayi akan zancen auren Amina kafun daga baya ta fawwalawa Allah,tsakanin Amina da Alhaji babu abinda zamuce sai dai muce rabon wahala ne ya sasa auren ta don ba karamin rashin mutunci Amina ke Masa ba a gaban kowa nuna wa take bata sonsa auren dole aka Mata ga rashin kunya takewa kowa a gidan,duk da ba halinta bane amma auren duk shiya birkitata sosai take nuna Masa kiyayya shima abin na Masa ciwo amma hakuri yake Yana danne zuciyar sa don duk abinda zata Masa bazai fasa Zama da ita a hakan yake sonta.
Alhassan fa yaga ta kansa don gabaki d'aya Amina ta birkita masa gida rashin kunya takewa mutane na bugawa a jarida Inka cire Alhussan da matar sa badawiyya don su basa ma zuwa Inda take bare tagansu tace zata musu rashin kunya, muzammil yayi mugu mugun tsanar yarinya ga Kuma abinda take musu,ummu bata fada da ita Saida babu abinda ke hadasu sabanin Addayiya da mamu sosai suke gaba gashi duk lokacin da akayi fada sai Alhassan yadau gaskiya ya bata cewa yake duk Mai son zaman lafiya dashi toh ya fita harKan Amina.
Amina bata da aiki a gidan sai dai taci ta kwanta tasha gwada gudu amma security ne birjit KoNan dacan bata iya zakudawa a cikin compound sai sun bita da Ido Suna duba Inda zata,Alhassa nada hakuri shiyasa yake zaune da Amina Yan garin su nadan zuwa kadan kadan ya musu hisani su tafi akwai wata Rana kanwar sulaiman tazo gidan ta a boye da letter (wasila) ta Bata akan sulaiman ne yace ta Bata sannan itama ta rubuta Masa reply kanwar tasa ta koma Masa dashi, Amina ta karbi wasikar shikenan tun daga ranan sai sulaiman ya dau kanwar sa suzo cikin gari don yaki komawa service,yan kitsa Mata rashin mutunci da zatana ma Alhaji ta yanda zaisa shi sakenta amma Abu ya gagara harsai wata Rana mamu ta Kamata suna magana da kanwar sulaiman plan in yanda zata fita su hadu da sulaiman, anan take ta sanar da Alhassa sosai ransa ya baci bana Wasa ba Kuma ya bincike dakin Nan ya samu wasikun da take Tarawa na sulaiman a ciki da durowan ta sosai Yama Amina fada akan martabar aure,da Kuma Hana security barin kowa daga kauyen su indai ba mutane uku bane, kawu inno da muneeru tunda har waya aka kawo aka Bata.
Yau surkin Alhassa sarkin katsina ya shigo gombe sannan ya iso gidan surkin nasa sauke sa a babban falo Alhaji yayi cikin mutunci kowa na gidan sai haba-haba yake da surkin nasa ana kawo abin Sha daci ana jerawa kowa Saida yazo ya gaidashi daman alhassan ya gargadi Amina don Allah kada ta kuskura tazo ,Aiko ita daman abinda zai kuntata masa shi take so tayi Masa,Suma tsaka da magana ta Fado falon mikewa Alhaji yayi Yana tare ta da cewa suje waje sai suyi magana amma Amina taki ta fita,saima ta hau Kan kujera ta kame.