← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 122

Sashe 19

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***************
Nnenna tun asuba ta farka da sauri tayi brush ta sanya d'aya daga cikin kayan da Abraham ya sai mata, dogon riga ne bai iso koh gwuwa ba, sai hulan sanyi data saka, fitowa tayi cikin murna ta fara aikin ta, watoh share-share da goge-goge har tsakar gidan ta goge tiles duka, wanke-wanken dake kitchen duk ta tattara ta wanke tas.

Daki ta shiga tai wanka, uniform in ta sanya siket ne nevy blue sai riga mai dogon hannu, stokin na rigan tayi a cikin siket in, hannu tasa tadau nect-tie nata blue ta sanya dayake tasan yanda ake nade abin tunda papa na makalawa, socks tasa fari sai boot nata nevy blue, empty jakan ta nevy blue shima ta d'auka, amma babu takardu a ciki kulenta dake gefe ta d'auka ta sanya a jakan, barect nata ta kafa akai daman gashin ta a tunkushe yake bata warwarewa ma bare.

Agogo ta kallah karfe 7:00pm daidai ta fito a d'akin taku take a hankali tanajin ta wani iri cikin kayan uniform nata, tana isa falon gabaki d'ayan su suka bita da ido, ganin wani irin azabebben kyau datayi kamar dan ita akayi uniform in, jennifer turmude fuska tayi cikin hassada, Abraham kam kamar ya taso ya rungume ta haka yakeji koh zaiji sanyi.

Tsungu nawa tayi akan gwuwar ta tana gaida dady dake zaune akan daining, Amsawa yayi sai kuma ta gaida Abraham ya amsa da sauri haka ma sarah ta amsa ba walwala, sabanin momy da Jennifer da sukaki Koh amsa mata ma.

Kallon ta dady yayi, daughter gashi yau dai zaki fara zuwa makaranta, abinda nake so na fad'a miki shine kinga makarantan da zakije ba irin na kauye bane? wannan makaranta ne na birni sannan Muslim and Christian ne, babu ruwan ku da yaran hausa wa kar naji kar na gani, kika kuskura naji labarin an ganki da yaran Hausa wan nan, toh sai na cireki kuma banda kawayen banza,kiyi abinda ya kaiki kinji koh?

Dukar da kai tayi sosai"i promise u Dad bazaka sameni da sab'anin hakan ba"

Ok daughter ni zan fita ga Abraham zai kaiku school na basa kudin da za'a cherge ku.

"Thank you Dad"

Ur welcome daughter yace yana mikewa tsaye ya sabe jakan dake zaune akan kujera ya bar falon, kallon ta abraham yayi, Beauty kije kitchen ki ibo abinci time na gudu.

Mikewa tayi da sauri mom ta daka mata wata uwar tsawa, koma ku zauna yar iska bakauyi ya, babu inda zaki duk rawan kafarki yau bazaki school din nan ba,nuna jennifer tayi ke Jennifer tashi brother ya kaiki school karkuyi late.

Kallon ta Abraham yayi, haba mom ya haka bakiji Dad yace na kaita school ba?

Naji, ni kuma nace bazata ba, kuma wallahi ka kuskura ka sanar da mahaifin ku saina saba maka.

Jin abinda mom tace, yasa Nnenna sake kuka da karfi shikenan murnar ta zai koma ciki.....................

✨Ruqeenjalal✨

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🤹🏿‍♂️ *ALKAWARIN MASOYA* 🤹🏻‍♀️
~ Na ~

🍃 *Rukayya Ibrahim*🍃

✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki tuntube ni ta layin nan whatsApp only 07044407979👌

Free page🤧

*EXQUISITE WRITER'S FARUM*

page2⃣5⃣&2⃣6⃣
Kuka Nnenna take Amma koh tausayi babu haka mom tasa Abraham d'aukar Jennifer zuwa school sarah ma makaranta abinta ta tafi, mom yau koh aiki bataje ba, dole tasa Nnenna komawa daki ta kifa kanta tana kuka sosai, koh karyawa batayi ba a haka tayita zama a daki.

Shima Abraham da sauri ya aje jennifer a tunanin sa mom ta tafi hospital, amma me yana zuwa yaga mom xaune a falo, haka ya sake komawa da baya yabar gidan kawai.

Har azahar Nnenna na xaune a dakin tana kuka koh kayan bata cire ba.

Dad dake wajen aiki ne, Abraham yaje ya samu ya sanar dashi abubuwan dake faruwa, sosai yaji Ransa ya baci matuka bai taba zaton yawan amsa wa mom bukatun ta babu musu shiyasa ta d'auka koh tsoron ta yake ji.

A fusace ya nufo gida cikin bacin rai...

*******************
Lahab kam suna isa makaranta haka yayita bin makarantan da ido rabon sa da zuwa school tun komawar muzammil barrack, suna isa makarantan daman shike zaune a baya dasu muneera Rahab na gaba tare da muzammil in.

Yana packing duk suka sassauka, hannun Rahab muxammil ya kama suka nufi office in principal, yayin da su lahab suka shishige Ajujuwan su.

Lahab na shiga ajin wajen da Rahab yafi zama watoh benchin gaba agun ya zauna tare da fiffito da takardun Rahab ganin maths teacher nasu ya shigo.

Ta bangaren Rahab kam suna shiga office in Muzammil ya bada sanarwa akan so yake a shanja ma Lahab aji a ciresa daga A zuwa B class sannan su saka masa ido duk lokacin da ake lesson baya aji a kirasa kuma a tabbatar ana binciken littatafan sa, yayi rubutu koh ah ah, 20k ya baiwa disple master nasu akan lahab, zaina zaman extra lesson da hadda, in yazo tun safe sai 5 na yamma zaina komawa gida.

Rahab kam hawaye ne kawai yake bin kumatun sa lokacin da disple master ya tasa keyar sa zuwa B class.

Muzammil na komawa gida zama yayi ya karya,suna hira shida addayiya a falo, don matar sa ta tafi gidan su da yaran sa ba kowa a gidan sai su ummu suma suna daki,ji sukayi ana kwala sallama a bakin kofar falo, addayiya ce ta amsa duk da ta gane masu muryar amma bata nuna ta ganesu ba sai ma tambayar su datake akan su wane ne su shigo.

Muxammil kam mikewa yayi da sauri yabar falon, aiko suna shigowa suka soma gaida Addayiya, yamutsa fuska tayi ta amsa ba yabo ba fallasa, lafiya kuwa yan duniya na ganku anan?

Nabeel ne ya bata Amsa, lafiya addayiya munxo wajen lahab ne, da safe bai fitoh jogging ba gashi wayar sa munyita kira ba'a d'agawa da safen nan.

Ok toh ku shiga d'akin nasa ku duba taima yana aikin nasa watoh bacci.

Mikewa sukayi suka nufi dakin su lahab, suna shiga suka ga ba kowa a d'akin, toilet Adewale ya nufa hannu yasa zaiyi knocking kawai yaga toilet in ya budu, tsaki yaja mtwsss wallahi nabeel ba kowa a dakin nan, sai Allah ina ya shiga yau kuma tun safe.

juyawa sukayi zasu fita a dakin sai kuma suka ja da baya ganin Muzammil tsaye ya harde hannu.

Da sauri dukan su suka tsunguna suna gaidashi, d'aga musu hannu yayi ba tare da yayi magana ba ya musu nuni da hannun sa akan su biyo sa.

Fita yayi a d'akin suna binsa a baya saida sukazo falo, sai kum ya tsaya tunawa da yayi karfa ya fita dasu compound su arce a d'ari don halin sune dagasu har abokin nasu lahab gudu ba abin kunya bane a wajen su.

Kofar dake falon ya turasu wanda zai kaisu har garden, suna dai binsa a baya har garden yayin da ransu in yayi dubu ya baci watoh lahab yasan kwanan zancen amma bai sanar dasu boss ya dawo ba, bare ma nabeel ya shaka sosai.

Zama yayi akan d'aya daga cikin kujerun gabaki d'ayan su yasasu linkdown, kallon su yayi, meya hanaku zuwa makaranta?

Uncle munzo duba lahab ne koh lafiya yau bamu gansa da asuba ba, daman in muka dubasa sai mu wuce school.

Ok daman kun daina sa uniform ne?

Ah ah uncle daman in mun zo mun dubasa sai mu koma musa ne.

Makarya ta yace ana d'aukar bell nasa dake gefe, ya zubawa adewale da karfe,kafun ma nabeel ya ruga shima aka zuba masa aiko zurawa sukayi a guje yana binsu abinka da soja tuni ya shawo kansu, ya soma sakasu tsallen kwado daga bakin gate har garden.

Haka ya sasu a gaba sunayi yana binsu a baya akalla saida sukayi kusan 2 hour's har yakai basa iyawa suna farawa suke zubewa kafafu sunyi tsami, nabeel kam har kuka ya fara da gaske kafun muzammil yabar su hade da musu kyakkyawan kashedi akan wallahi gobe in yaje makaranta yaji labarin basuje ba, koh sukaje suka tafi geto koh yagansu tare da Lahab sai jikin su ya gaya musu, babusu babu haduwa da lahab sai an dawo makaranta.

Sudai amsa masa suke da eh kawai, nuni ya musu dasu wuce su tafi, wallahi haka suke tafiya a hankali kafafu duk sun mutu kafun su isa get sai da suka huta a baranda, suna fita ma saida suka huta a kwalbet na kofar gidan, kallo adewale nabeel yayi, wallahi adewale daga yau bazan kara yarda muxammil ya dakeni ba, daman ina rage masa ne Albarka cin lahab, amma tunda dai yace baya bukatar muna haduwa da kanin sa, wallahi daga yau na rabu da lahab kuma makarantan ne dai baxanje ba.

Haba nabeel karfa ka manta yanda xai iyya dukan lahab haka zai iyya dukan mu, menene innar ka da mubeena basama lahab ne?harda zagi amma kaga ya nuna bacin ransa, yar uwarka da shekara 2 ta girme lahab amma bai taba tanka mata ba, sau nawa dad nawa na xagin ku lokacin da muke yara ma sau nawa yana dukan ku akaina, in kuka shigo gidan mu amma na tabbata lahab bai taba cewa zai rabu dani ba, haba nabeel?

Kai kaga zaka iyya nidai nace bazan iyya ba, dukan mun nan munason zuwa school amma saboda lahab bazaije ba haka zamu ki zuwa duk saboda shi, shine yau shi zashi makaranta mukuma munzo muji lafiya bamu gansa ba,wani banzan yayansa ya mana irin wannan duka, lahab in ubana ne.?

Shuru kawai Adewale yayi don yasan wannan surutu da nabeel keyi duk cikin zafin ciwo ne da haushi, amma yana wuce iyya ka ya tabbata wallahi badon Albarkacin lahab ba yasan da sun dade da rabuwa dashi koh don yanda nabeel ke nuna masa banbancin Addnin wasu lokutan, amma lahab babu ruwan sa da nuna fifiko gashi baida zuciya sam koh yayi fushi da abu zai huce ya dawo.

Wucewa sukayi direct gidan su nabeel don kafar nan tasu sai an gasa ta, gashi adewale bayason komawa gida iyayen sa na hanya kar su dawo suga kafar su yasan ba karamin bala'i za'a buga da baban sa ba akan maganar nan.
Chapter 19 · 0% Book details