Sashe 7
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Addar nabeel ne xaune a tsakar gidan tana banbaran masara, Amsa musu tayi ba tare da ta d'aga ido ta kallesu ba, lahab ne ya wuce d'akin yayin da Adewale ya koma kofar gida ya tsaya ganin irin kallon banza da mubeena ke masa,lahab na shiga ya samu nabeel sai bacci yake koh sallan asuba bai tashi ba, Ruwa ya ibo a randan inna yazo ya kwara masa a jiki, mikewa yayi cikin masifa yake zagen lahan, shima yana ramawa, sai da yayi da gaske kafun ma suka samu yayi sallah suka fita tare.
Da misalin karfe 8:00 lahab ya nufo gida jikinsa duk ya jike da gumi alamu dai dawowarsa kenan daga jogging, kofar get nasun ya bude ya wuce cikin gida, tura kofar falon yayi koh sallama babu, Rahab ne dasu munira da zulai ke karyawa cikin uniform na islamiyya yayinda rahab ke sanye da jallabiya fari da hula, su kad'ai ke zaune akan daining in, dayake Al'adan gidan su ne ranan weekend kowa na baccin safe sai su yara dake zuwa islamiyya, da ma'aikata hatta Addayiya bata tashi a weekend.
Good morning uncle?
Kallon xulaihat Lahab yayi kamar baxai Amsa ba Amma kuma saiya basar ya amsa mata da "lafiya " don karya yarfata, kawai ya wuce Abinsa.
D'aki ya shiga direct ya wuce toilet wanka yayi ya fitoh daure da towel wando kawai ya saka dogo, yad'au waya yakira mai aikinsu, ta kawo masa Abinci.
Ba'afi 5 minutes ba sai gata d'auke da tire zata kai shekara 50, da sallama ta shigo D'akin Amsa mata yayi, har gaban katifarsa taxo zata aje masa abincin.
"Subhanah Gogoji lafiya kuwa"Lahab yace da mamaki ganin saura kad'an ta xubar da abincin.
A sanyaye tace lafiya klau ta juya tana tafiya, harta fita A d'akin lahab kallonta yake, haka kawai yaji a ransa akwai abinda ke damunta.
Abincin ya bude macaroni ne da miyar kaxa sai ruwan tie, karyawa yayi yana kamawa ya d'an xauna kad'an Abinvin ya sauka before ya kwanta abinsa, A hankali har bacci yayi Ahon gaba dashi.
****************
Nnenna bata farka ba sai kusan 7 na safe dayake yau babu school share d'akinta da falo har waje tayi, tsummo karansu ta tattaro masu datti, bunu guda ta aje a waje, ta dawo falon kallon papa tayi dake xaune a kujera" good morning papa"
Morning daughter?
"papa abani kudi nasai omo zan mana wanki"?
Ah ah daughter ina naga kudin omo yanzun sai dai ki bari gobe na baki kudin in mun dawo church sai ki wanke?
Ok papa kawai tace tana mikewa tsaye.
Daughter ga wannan ki dafa mana doyane da manja sai magi?
Hannu tasa ta karbi laidan dake hannunsa sai doya dake gefe ta d'auka ta fita waje, kara-karan dake bola shita ibo tazo ta hura wuta dashi, d'aura tukunya tayi ta zuba ruwa tasa magi da manjan ta rufe, fere doyan tayi shima ta zuba.
Bayan ta sauke girkin ta ibawa papa nasa itama ta saka nata sai kulenta dake gefe ta zuba masa nasa, zama tayi a wajen tanaci tana kallon jama'ar dake zuwa wucewa in sun ganta a zaune sai su koma, gabaki d'aya tausayin kanta da kanta take don Abincin ba dadine dashi ba, in kuma bataci ba waxai bata.
Papa na karyawa yasa kafarsa ya fita a gidan, d'aki ta koma ta kwanta tama rasa me zatayi haka ta wuni har dare a d'akin sai kusan 11 papa da yadawo a buge Yau koh Abincin bata samu ya sayo mata ba haka ta kwanta.
Washe gari Sunday da safe lipton ya sai musu da sugar suka sha shayi baki, Nnenna na sanyi da wani kod'aden siket iyya gwuwa da riga, sai sandal na makaranta dake kafarta don bata da Wani takalmi sai wannan, kanta babu hula sai tsifeffen gashinta dake kwance babu gyara, hannunta d'auke da bable.
Papa ma sanye yake da kodeden suit nasa na gwanjo da wata kifefeyar takalmi da hula a kansa, rufe gidan sukayi zasu churchi, da gudu kulenta yataho kusa da ita ya tsaya,da masifa papa yace.
Nifa na fara gajiya da wannan cat in naki ace tsawon shekara goma kina tare da Abu bai mutu ba, sanan har magana ya fara ji, I swear bazaki fita dashi ba.
tsungunawa tayi tana shafasa"kiki zamuje church ka xauna a gida saina dawo", aiko kamar maijin magana haka ya koma gefe ya tsaya yana kallonsu har suka wuce, a tare suke tafiya da yarsa duk inda ta wuce sai a ringa gudu wasu su shanja hanya.
Da suka isa church in ma kin bari pasto yayi Nnenna ta shiga, Papa ya buga ya buga Amma yace bazata shigo ba, karshe haka ta koma gefe da bable inta dake hannunta ta zauna, Amma duk da haka pasto nan yace sai dai ta koma bayan church ba gaba ba kartana kallon yaran mutane daga nesa.
Ba musu ta koma shan bayan church ta zauna a kan wani dutse tana kuka ta rasa me yasa mutane suka tsaneta ne wai haka?
Ba'a taso church ba sai 12:38 su kuma basu suka bar church in ba sai da jama'a suka watse duka wannan umurnin pasto ne.
Sai kusan 1 suka kama hanya har gida yauma bata samu na rana ba sai omo da papa yasai musu na 50 ya bata ta dawo tayi wankin a gida zai wuce , saida ya jaddada mata kar taje kogi wanki, amsa masa kawai tayi da "toh"ta karbi omo tace
Tana komawa gida wankin ta harhad'a gayyane guda tana tunanin ina omon hamsin zai isa Amma tuna a kogi zata wanke koh ba omo zata sa a ruwa ta cire, don basu da ruwa a gidan in kuma zatana ibowa a kogi harta cika jarakuna, Abin ya mata yawa gwara ta tafi da wankin kawai.
Tattara wankin tayi ta sabi kulenta tasaka sa cikin kayan wanki ta d'aura akan ta,kogi ta nufa kamar yanda tayi tsammani hakance watoh jama'a a tare a kogin kamar me,daga masu wanki masu kama kifi, gefe daban ta samu babu kowa sai yashi mai kyau da haske juye kayan tayi a gefe , tad'au boket ta ibo ruwa ta dawo ta zauna agun tana wanki ga kulenta a gefe yana zaune.
Sosai take wanke kayanta bata damu da marmatsawa da wasu masu dauraya sukayi daga gefenta ba, duk da suna da nisa da ita Amma haka suka kara marmatsawa sosai, tana cikin wanki kamar daga sama taga an tsaya a kanta.
Da mamaki ta d'ago tana kallon yaran, yan matane guda hudu, katti katti irin inyamurai manyan nan gasu bakake, gabanta ne ya fadi tunawa da yaran ba mutunci bane dasu gashi a kauyen su taji papa na cewa Yan zaman gindin dutsene sai sufi wata basu dawo kauye ba.
Kee kece mayyar da ake magana koh?
Shuru tayi bata basu Amsa ba sai raba ido take.
Haushi rashin Amsa wata taji a cikinsu, hannu kawai tasa ta kifar da ruwan omon Nnenna.
Da sauri Nnenna ta tsunguna tana tsine kayanta dake cikin ruwan omon kuma sun zubar a yashi, sai da suka bari ta tsine duka ta saka a boket, sai wata ta sabi boket in da gudu ta nufi kogi.
Da gudu Nnenna ma ta bita tana kuka tana bata hakuri don a cikin kayan harda school uniform nata, kuma shi kad'aine da ita tasan papa bazai taba sai mata wani ba gashi weac ma kasa biya mata yayi haka ta sake maimaita ss 3 don batason zaman gida kullum kewa na damunta shiyasa take zuwa makaranta, an koreta har an gaji an barta.
Kamata sauran yara ukun sukayi tana kuka tana rokon d'ayan akan ta dawo mata da kayanta Amma ina sai da ta juye su a ruwan kogi, tana juyewa suka saketa suna dariya haka jama'an dake kogin dadi sukeji ana wulakanta ta.
Da gudu tayi cikin kogin tana bin kayanta zata cire Amma ina ruwa kam sai tafiya yake da kayan ta, haka tanaji tana gani ruwa ya gudu da tufafinsu sai na papa data samo kala uku,Amma itakam na jikinta ne kawai ya rage mata.
Dawowa bakin kogin tayi tana kuka ga jikinta na tsintigon ruwa, boket nata biyu dake gefe ta d'auka zata tafi, da sauri suka fizge boket in,har suka jimata ciwo da karfen boket in a hannu,d'ayan ta had'ashi da dutse a take boket in ya fashe, cikin dariya tace bake mukaji anacewa mayya ba toh mu mun fiki Hassabibanci.
Kuka ta sake da karfi don ita a duniya babu abinda ke bata mata rai irin a kirata da mayya, abin na mata ciwo, hannu kawai tasa ta sabi kulenta, fizgo kulen wance ta zubar mata da kaya tayi ta wurwura kulen zata jefar a ruwa.
Da karfi Nnenna tayi tsalle ta taka kirjin yarinyar da kafarta, A take yarinyar tayi wani irin zubewa a kasa saida kasan wajen ya girgiza take ta sandare babu Alamun Rai a tatare da ita.........
✨Ruqeenjalal✨
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🤹🏿♂️ *ALKAWARIN MASOYA* 🤹🏻♀️
~ Na ~
🍃 *Rukayya Ibrahim*🍃
Free page🤧
*EXQUISITE WRITER'S FARUM*
page 1⃣1⃣&1⃣2⃣
Sam yarinyar bata motse idanunta sun kakkafe a sana ga hancinta na xubar da jini, ihu jama'a suka kwala aka rufu akan yarinya.
Hankalin Nnenna a tashe Don yau tasan ta shiga uku, gashi papa ya hanata xuwa Amma taki ji wai ita tabi sauki, gashi taje tasa kanta a masifa, da sauri ta sabi kulenta da ya jefo a gefe, ganin hankalin mutane baya kanta yana kan yarinyar dake kwance.
Yasata banbarawa a guje jikinta sai rawa yake tunda take bata taba jawo rigima kiri kiri irin na yau ba, sai dai taga an mata Aiki Amma yau ta baiwa kanta mamaki mai girma.
da gudu ta baro kogi har ta shigo cikin kauye direct gidan su ta nufa tana xuwa ta bude kofa ta mayar ta rufe jikinta na rawa tayi cikin dakin aje kulentayi ta zauna dabas a kasa ga kayan jikinta a jike.
Kuka take sosai gabaki d'aya hankalinta a tashe yake ta rasa meke mata dadi yau dai tata ta kare ta shiga uku.