Sashe 12
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ranan tare Da Anwar lahab ya kwana gado d'aya, da safe ma shiya taimaka masa yayi brush harda karyawa ya basa a baki dayake bazashi Office ba, lahab ma zama yayi a dakin ya d'auko wani English novel yana karanta wa Anwar duk jaraban Mamu saida ta barsa.....
*************
Nnenna na bin mutumin A baya har suka shigo cikin gidan da sallama a bakin sa.
amsa masa wasu yara dake zaune a tsakar gidan sanye da uniform Suka mike da gudu suna oyoyo baba, jin Abinda yara ke cewa yasa matar gidan saurin fitowa daga bayi hannunta d'auke da buta.
Fuska ba walwala take kallon mijin nata sai kuma ta kalli Nnenan dake gefe kama baki tayi hade da cewa mijin nata, kai shayibu menene haka zaka shigo gida daga kai sai wando da vest duk datti ga wata Arniya da guntun riga tana binka a baya wanan shegen kulenfa uban me yasa aka shigo mini dashi cikin gida?
Girgiza kai mijin yayi yana kallon Ma'u, haba ma'u ya daga dawowa na koh waje baki bani na zauna ba baki bani ruwa koh wani abu da zansha na dawo hayyacina ba, zaki tareni da irin wa'innan xantuka, keda tun daren jiya nace miki ina hanya Amma kika ga shuru ban dawo ba, koh a jikin ki?
Eh koh a jikin nawa wani abin kake tsinana mini ne da in ka dawo zan damu sannan wacece wannan tace tana nuna Nnenna.
Bai bata Amsa ba sai kallon yaransa da yayi wa'inda suka sakesa da sauri suka koma kusa da Nnenna suna lakutar jikin kulenta sai kuma su ruga da gudu su koma baya suna dariya, sai kuma su sake dawowa su taba duk sun cika gidan da ihun su, daka musu tsawa ma'u tayi, kai shegu ku rufe mana baki kun cika mini kunne?
Kai ma'u Allah ya shiyeki nace miki banason kina zagen yarana da shegu Amma baki ji, sanan meya hanasu zuwa makaranta har yanzun suna zaune da uniform a jiki?
Tsaki ta sake hade da kallon su, kai me ya dawo daku ku fad'a masa da bakin ku? Ba musu suka sanar da baban su an koresu kudin petiA ne basu biya ba aka korosu.
Girgiza kai kawai yayi don kudin kwata kwata naira 100 ne, koh wani mutum daya shi kuma yau koh sisi bai dawo dashi ba dan kudin daya tara a kudun ma gashi ya hadu da iftilahi.
Kallon Nnenna yayi cikin turanci yake ce mata ta zauna bara ya ibo mata ruwa sai tayi wanka koh, gyada kai tayi ta nemi gefen dakali ta xauna shima boket ya d'auka da sauri ya nufi kofar gida.
Cikin masifa ma'u tace kai shayibu ban gane ba?me nake ganin yarinyar nan ta aje min gindin ta a dakalina?
Wa'iyyazu billah dake ma'u da rashin iyya magana, toh zama zatayi bakuwa ce tare muka samu iftikahin barayi a hanya?
Bata da gidan yan uwane da bazata tafi ba zata biyoka gida?oh na gane watoh sabon iskanci ne kenan daka saba xa'a kawo mini har gida toh wallahi bazata zauna mini a gida ba, sai dai ka zaba koh ni koh ita, wannan daga ganinta ma karuwa ce........... .
✨Ruqeenjalal✨
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🤹🏿♂️ *ALKAWARIN MASOYA* 🤹🏻♀️
~ Na ~
🍃 *Rukayya Ibrahim*🍃
Free page🤧
*EXQUISITE WRITER'S FARUM*
page1⃣7⃣&1⃣8⃣
Juyawa shayibu yayi yana kallon ma'u, shikam Allah ya gani rashin kudi da bin umurnin Iyaye,sune silar da yake hakurin zama da ma'u Amma wannan karon zai nuna mata ikon Miji akan matar sa, Ma'u baki da hankali a gaban yaran ki babu kunya kike irin wannan magana, toh bara na gaya miki koh kibi Abinda nace koh kuma ga kofa ki tafi duk inda yafiye miki nan.
Waro ido tayi tana kallon shayibu sannan ta maida kallon ta gun Nnenna dake xaune gabaki d'aya kanta a duke duk da ba Hausa takeji ba, Amma daga Kaga muhawaran da suke kasan fad'a ne, toh wallahi bara kaji xama kam daram dam, in ma burinka kenan na tafi na barmaka gidan kuji dadin iskanci toh bazan tafiba tace tana shigewa daki Abinta.
Shima bai kara magana ba ya d'auki jamfansa a igiya ya saka, ya fita bai jima ba sai gasa da ruwa a boket d'aya hannun nasa d'auke da sabulu sai take Away a Abinci.
Da sauri Nnenna ta mike ta karbi boket inda ke Hannun sa ta aje a gefe,nuna mata bayan gida yayi cikin turanci yace ta kai ruwan ciki ba musu takai ta aje.
Yaran sa kam kulen suka tasa a gaba suka maida abin wasa,Abincin ya mikawa Nnenna yayi yace mata taci, ba musu ta karbi take Away in tana budewa da sauri yaran suka rugo zuwa inda take alamu dai suma ba karyawan sukayi ba, Aje laidan Nnenna tayi a kasa ta bude, shinkafane da miya sai nama d'aya akai da sauri ta kauda fuskar ta, iba tayi a laidan takeAway in ta mikawa kulenta sauran ta baiwa yaran Shayibu.
Da mamaki yake kallon ta sai kuma ya kasa hakuri ya tambaye ta dalilin da yasa batacin duk abinda ya sai mata?girgiza kai tayi sai kuma a hankali tace masa ita batacin nama koh abinci mai nama.
Da mamaki yake kallon ta sai kuma ya wuce d'akin matar sa, zani da riga ya d'auko harya fitoh da sauri ma'u ta biyosa da gudu tazo ta fizge kayan kuma tace Nnenna bazata saka mata kaya ba.
Fita yayi bai jima ba sai gasa da siket da riga na gwanjo har guda hudu, ya baiwa Nnenna ta shiga wanka, Alele ya sayo mata ba musu taci ya nuna mata dakin yaransa akan ta shiga ta kwanta tunda jiya basu samu bacci ba, ba musu ta shiga ta kwanta abinta sai bacci.
Bata farka ba sai kusan 3:00 na yamma nan ma masifar Ma'u ne ya farkar da ita akan bazata ci Garin kwaki ba yau ta gaji sai dai ya bata kudi ta sayo musu Shinkafa a dafa koh dafa duka ne(jalof).
mikewa tayi ta fitoh a d'akin jin ma'u ta shiga ciki kallon Shayibu tayi sai kuma tace, "sir pls in zamana ne Bataso sai na tafi"?
Murmushi yayi watoh mutun koh baya jin yare Allah ya basa baiwar gane abinda ke gudana, haba Nnenna bafa akan xamanki bane?
"Toh akan menene sir tunda nazo kuke fad'a"?
Kudi ne takeso na bata ta sai Abinci ni kuma bani dashi shiyasa kinji ki koma daki koh?
"sir haba ka d'auki kudin dake hannunka kasai abinda ya dace"
taya zanna taba miki kudi, badon bani dashi ba da dasafen nan ma hidimar ki duk ni zan d'auka basai na taba kudin ba?
"No sir nikam na bar maka kudin ka rike a hannunka ni damuwata kawai ka kaini wajen uncle nawa"?
Sosai yaji dadin girmama sa da Nnenna tayi gashi dai yarinya kirista tana da Hali mai kyau da tunani, ok kawai yace yana fita a gidan tsintsiya Nnenna ta d'auka ta share musu gidan kwanuka masu datti data gani a watse duk ta had'asu waje d'aya haka ta wanken babu omo, tana cikin wanke wanken sai ga shayibu ya dawo da laida baki ajewa yayi yana kallon Nnenna da mamaki, Daughter kece haka da aiki?
"Ba kome sir is my pleasure"
Ma'u ma'u yana kwalawa matar tasa dake d'aki kira, Amma tayi biris dashi koh Amsawa batayi ba gashi yaransu sun dawo makarantan Allo sunyi jigon-jigon a gefe duk yunwa na damunsu ga mangariba ya kusa.
Fitowa tayi tana yamutsa fuska, gani lafiya kaketa kwalamin kira haka?
Kedai kika jiyo da halinki ga shinkafan nan saiki d'aura mana da wurwuri akwai wake yaran nan yunwa sukeji?
Ita wannan menene Amfaninta da bazata d'aura ba, sai ni zan daura ita kuma tana yawo da siket kai ba dankwali kana kare mata kallo, ta karasa maganar da nuna Nnenna dake xaune tana d'aureye kwanuka.
Amma dai kinsan yarinyar nan yar Kudu ce koh? Abincin mu daban da nasu haka ma yanayin girkin mu sannan koh da ace ta iyya ai bai dace ki sata aiki ba bayan wanda take miki.
Dakata shayibu banason maganar banza abinci ne nace bazan iyya girkawa ba.
Ya miki kyau kawai yace yana wucewa madafan Gawayi ya kunna daker lokacin ana kiran sallan mangari ba ya samu ya fara kamawa, wucewa yayi zuwa masallaci da yaransa maza biyu macen ma buta ta d'auka tayi Alwala ta shimfida sallaya tana sallah.
Nnenna sai kallonta take don Abin sabo ya xamo mata kauyen su babu musulmin da xaiyi sallah a sarari haka suna kallo, Asalima inka musulunta koranka ake a kauyen.
Ruwan xafi ta d'aura a gaushin ganin ya kama, sai ga shayibu ya dawo tire ya d'auka yana gyaran wake yayinda Nnenna ya bata dakan barkono yaransa na gefe da kule, gabaki d'ayan su suna zaune har bayan isha'i ya gama girkin, xubawa Nnenna yayi a kwano d'aya da yaransa ya zubawa kulenta a wani tsohon kwano ya xuba nasa daban ya xubawa Ma'u nata babu kunya tazo ta d'auka tayi daki.
Suna gama cin Abincin Nnenna tayi wanka yace musu su tafi daki su kwanta, suna shiga Nnenna ta tambaye yaran takardun makarantan su, firfitarwa sukayi tana ta musu lesson, tama d'ayar Assigment nata sai kusan 9 suka kwanta.
Washe gari da asuba shayibu yazo ya buga musu kofa yaran sukayi Alwala sukayi sallah Nnenna wanke-wanke ta had'a shayibu yasai musu omo da yawa yaran sukayi shara shi kuma ya musu karyawan taliya dafa duka da manja.
Suna karyawa yasa yaran a gaba zai kaisu makaranta, daga nan zai wuce GRA neman gidan Coulis Appa, Suna barin gidan Ma'u ta ibo kayanta masu datti dana yaranta tazo ta jugawa Nnenna a gaba hade da bata boket ta jido ruwa ta wanke musu kaya.
Haka koh akayi Nnenna tayi jidon ruwa tun daga rijiyan unguwan har ta cicika randa kafun tazo ta dukufa akan daurayan harda na shayibu ma'u ta had'a saban mugunta, Nnenna ba ita ta gama Aikin ba sai kusan 5:30 lokacin ta gama wankin jikinta duk yayi tsami gashi ma'u bata bata na rana ba tanaji tana gani ta gama dafawa ta zubama yaranta da suka dawo makaranta Amma ita kaman ajalinta, ga gajiyan d'auraya.