← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 122

Sashe 105

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waro Ido Nnenna tayi sai Kuma taji ranta ya baci wato ma kokonton zaman nasu ake kenan"mama wani irin magana ne haka"kiyi hakuri yata in maganar ta Miki zafi Naga tunda nake daku Banga wani naki ko nasa dayazo kasar nan da sunan zuwa duba yara ba haka zalika babu Wanda ya bugo waya a idanuna"kuka Nnenna ta Fara ahankali sai yanzun tunanin yazo Mata lallai Suna da Kura a gaban su shin Menene makomar yaranta,mama Kam shuru tayi Bata Kara magana ba har Nnenna tayi kukan ta ta gaji.

Washe gari Suna babu kowa a gidan sai Muhammad dasu Lahab da iyalinsu sune Suka hadu sukaci abinci tare da gifts da Suka baiwa yaran,bayani Suna Lahab ya cigaba da zuwa makaranta haka ma ball ga Mama na zaune Masa da matar sa tana baiwa yaran kulawa sosai da gyara Masa Mata kome ya daidai ta a tsakanin su sun koma Kamar da ana Raha Wasa da dariya yaransu na samun kulawa na ban mamaki,a sannu sannu kwana na tafiya har Nnenna ta kammala wankan jegon ta Lahab ya koma dakin matar sa yayin da mama ta koma kasar nageria da tsaraba Mai yawa da Lahab ya mata,badon ranta yaso ba sai don Kiran da tsohon mijinta ke Mata akan taje ta zauna a tsakiyar yara,yanzun rainon yara ya koma wajen Nnenna da jidda da Suka kasance makwanta kawaye Kuma masu zumunci sosai,don wani lokaci in Lahab yabar kasar sai jidda ta dawo gidan Nnenna su zauna suyi girki su wuni sai dare ta ibi abinci a kula ta wuce gidanta dashi.

Yaran Lahab sun girma sosai yara kubul kubul dasu Kamar yaran turawa ga haskensu sosai ya karu fuskar Nan Kamar na mahaifinsu, don yanzun har tafiya Suna Yi babu Inda bada gudu Lahab ya Zama cikekken mutun magidanci Dan shekara 20 a duniya da yara Yan shekara 1, Nnenna tayi kiba ta waye duk Wanda yasan ta a Nnenna obinna a kauyen su inya ganta yanzun ba lallai ya gane ta ba,su Lahab sun samu hutun karshen shekara yanzun haka sun kammala part 2 saura musu shekara daya su kammala digree nasu anyi hutu Adewale yayiwa Lahab zancen tafiya nageria Amma Lahab ya murza Ido yace sai ya kammala makaranta zai je nageria,babu irin yanda Ade baiyi dashi ba yace bazashi yabar matar sa da yaransa ba.

Yau Ade baije Koh Ina ba kwanton Lahab yake yabar gidan Amma Ina dayake yau baida Wasa Koh training Yana gida da iyalan sa don haka yake in baida abinyi baya fita in Kuma zai fita toh da family sa,Jin motse a compound yasa sa mikewa yazo bakin windown sa ya bude labulen,Lahab ne tsaye da Nnenna Suna sanye cikin kananan Kaya gabaki dayan su jeans ne da t-shirt sai yaran su dake sanye da Kaya irin daya Lahab na rike da daya Nnenna na rike da daya ya sanya facemask a fuskar sa don haka yake indai zai fita da family sa sai ya rufe fuska gudun kada a daukesu hoto a yada a duniya ya Shiga uku,tsaki Ade yayi ganin sun shiga motar sun bar gidan tsake labulen kawai Ade yayi Yana mamakin halin Lahab nason Kai ace mutun nason yayan sa da matar sa haka Amma bazaiyi tunanin ya tasa mahaifiyar take kewar sa ba a zatonsa in Lahab yaga yaransa zaiyi hankali ya Fara natsuwa Amma baiga alamu ba Sam.

Washe gari lahab ya fita training hakan yasa Ade nufar kofar lahab ring na door ya Danna kana ya tsaya Yana jira ta bude Saida ya Jima sosai Harya juya zai tafi sai Kuma ya tsaya Jin an bude kofar"ah ah Uncle in twins Kaine sannu da zuwa shigo Mana"tace tana matsa masa,shigowa yayi da fara'ar sa ya karaso falon Zama yayi da sauri nazeefe dake zaune a kasan phalorn Yana Wasa ya mike da gudu Wai zaizo wajen Ade sai Kuma ya Fadi take ya sanyara Kara da Sauri Ade ya mike ya dagasa yana rarrashen sa"ba rawan Kai ba haka yake a Rana saiya Fadi sau uku ma"dariya Ade yayi Jin abinda tace yace"kin manta jinin Lahab ne in baiyi ba sai Allah ya tambaye sa"had'a fuska Nnenna tayi tana tafiya kitchen tace"gaskiya Uncle bazamu shirya dakai ba husband nawa kake fadawa haka"?sai Kuma ta shiga kitchen abinci ta ibo Masa ta dawo falon aje Masa tayi da drink's,Jin nazeefa tana sanyara Kara a daki Daman bacci take yasa Nnenna mikewa ta shiga daki jawo abincin Ade yayi ya Soma ci Yana baiwa nazeefi dake ta sa hannu a plate in Wai zai Iba Daman gashi yayi hakori hudu.

Fitowa Nnenna tayi da ita ta zauna akan kujera tana Bata Madara a feeder,ture plate na gaban sa yayi ya kalleta"mun wuni lafiya maman twins"? lafiya klau"Masha Allah Daman akwai wata magana da nake son muyi dake ne in ban takuraki ba"babu kome Ina jinka Allah yasa lafiya"?

Gyara Zama yayi yace lafiya kalau kawai dai aKan mutumin ne nace bari nazo ta wajen ki Koh Allah zaisa kisa baki,wallahi Nnenna Lahab baida hankali tunda mukazo kasar Nan waya wannan in ba Yan nageria ne suka kirasa ba sai sa'i da lokaci yake Kiran su,wancan shekara akayi hutu yace bazai koma ba saboda cikin ki daya girma toh ga wannan shekara yace bazashi ba,abinda Ni nagani Kamar abinda yake Bai Dace ba ace shekara biyu baka koma gida ba bayan Kuma kana da dama,hakan zai jefawa family sa cikin tunanin Abu biyu"na farko ko don Lahab yayi kudi shiyasa yake kokarin zame kansa a cikin su Koh fifita aikin sa akan su hakan Kuma zai iya saka manyan yayunsa sa Ido akansa a cikin kasarnan tunda Suna kudi ba Basu dashi ba, Kinga za'a gane kome akanku,Abu na biyu Kuma mundin aka gano kina tare dashi ne za'a daurawa alhakin rikon nasa Akan ki,Kuma daker su barku tare tunda sunga yanda ya iya Zama dake ba tare da yayi tunanin gida ba Wanda ada ba haka yake ba,don haka nazo na Baki shawara ki sa Baki Koh Allah zaisa yaji naki tunda yanzun kun riga kun Zama daya"?

Ajiyar zuciya Nnenna tayi ita kanta tana tsoron randa asirinta zai tonu"yanzun Ade kana ga duk Randa family sa suka San da auren mu zasu barmu tare kuwa wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba"?uhmmm kedai kiyi Addu'a kawai shine abinda yace Yana mikewa da nazeefi a hannun sa,Aiko da Sauri nazeefa tasa kuka ganin zasu bar falon Wai itama a dagata"dawowa yayi ya ciccibeta da boron madaran su harda feeder da flasks a ciki na ruwan dumi karami ya bar falon dasu duka.

Goshin mangariba Lahab ya Isa gida tura kofar falon yayi ya shiga da sallama falon tsabtsab sai kanshi dake tashi Nnenna ce ta fito kitchen hannunta d'auke da kuloli tana jerawa a dinning,sanye take da guntun siket da riga karami kannan nata yasha gyara sosai wallahi mutun ya ganta zai zaci Koh Bata had'a jini da kasar bakaken fata ba,saukowar tayi Akan steps biyu dake wajen dinning in,ta karaso kusa da mijinta dake zaune akan kujeran falo tsungunawa tayi tana warware Masa igiyoyin dake makale a takalmin ball dake kafar sa ta zare dogon socks in,kana ta Mike ta sabe jakan sport nashi ba tare da tace Masa kome ba ta haura upstairs,binta yayi da Ido harta Haura saman Ya shafa kansa yana mamakin wannan cicin maganin da take innan fa yasan dai lafiya suka rabu, gashi yaga yau sama ta haura alhalin Kuma tunda yaransa Suka Soma tafiya yace Mata bayason amfani da upstairs gudun kada yaransa suce zasu hau Koh a hau dasu suce zasu sauka suje su illata a banza a wofi.

Mikewa kawai yayi ya bita saman dakinsa na saman ya bude ya shiga a gyara yake Kamar Yana kwana a ciki alhalin Kuma sai yafi wata bai hau sama ba,Jin motsinta a bandakin yasa sa tura kofar ya shiga,wanka ya fito daure da towel kana daya na hannunsa yana goge ruwan dake kansa,mikewa tayi tazo ta karbi na hannun nasa shi Kuma ya zauna ta Soma goge masa,kafun ya tashi ta Mika Masa zallabiya da wando Yasa ta shimfida Masa sallaya ganin lokacin sallan mangariba ya kusa calbin sa ta sauka ta dauko a dakin kasa ta kawo Masa lokacin Harya Fara sallah ta aje Masa a gefe,ta koma ta zauna akan kujera ta jawo wayar sa tana dannawa.

Yana idar da sallan Addu'a yayi kana ya d'aga Ido ya kalleta sai Kuma yace"Wai Ina yaran Nan ne tunda na dawo Banga su ba Koh bacci suke kuma kinsa nace Miki banason kina barin yaran Nan Suna baccin yamma bashi da amfani kwata kwata Kuma baida kyau"bafa bacci suke ba Kuma tunda kace bakason Suna baccin yamma nadaina barin su Suna bacci Koh sunyi ta dasu nake"gyada Kai yayi"in kawo maka abincin Nan ne"?no Zan sauka naci a dinning Amma Baki bani amsa taba Ina suke kinsan banson yaran Nan kina kaisu gidan Muhammad da sunan barma jidda raino fa"?

Mtwsss ikon Allah waika ka fini son yaran Nan ne Inka tashi sai kayita min fada Kamar nika Haifa Basu ba,kafasan Ni na girmeka baikamata kana min magana haka ba"wani zabura Lahab yayi ya tsaya Yana Mata wani kallo kana yace"keee niii Kika girma inji wani makaryacin..............................

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*
Chapter 105 · 0% Book details