← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 122

Sashe 22

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***************
Lahab basu suka farka ba sai kusan 11 na safe suna farkawa suka tarar da addayiya na zaune har lokacin a d'akin, watoh dai gadin su take, Lahab jiki yayi sauki da kafar sa ya shiga toilet duk da kafar bawai ya daina tsami bane, wanka yayi da ruwan zafi da addayiya ta had'a masa yana fitowa ya samu ta zuzzuba musu abinci a plate.

Zama yayi a bakin katifar tare da jinginar da jikinsa a jikin ginin dakin, da sauri ta kawo plate in ta aje masa a gaba, kallon plate in yayi shinkafa ne da salad sai miya,"gaskiya nifa addayiya bazan iyya cin abincin nan ba bakina ba dadi"

Ok toh lahabu mekake son ci?

"Kwai kawai zaki kawo mini soyayye sai ruwan tie ba madara"

Da hanzari ta mike ta fita a dakin, abincin da lahab yaki ci shi Rahab ya d'auka ya kama ci, koh 30 minutes ba'ayi ba saiga addayiya da tiren abinci aje masa tayi a gaba ga dukkan alamu yanzun ma ta d'aura tie in harda suyan kwai.

Kad'an lahab yaci ba yawa ya koma ya kwanta tare da d'aukar wayar sa, nabeel ya kira amma har ya gama ring bai d'auka ba haka ma adewale abun ya basa mamaki don da wuya ka kira d'aya baka samesa ba.
Aje wayan yayi kawai ya lumshe idanun sa yana sauraron hiran da addayiya keyi da rahab.

****************
Nnenna a rana d'aya tayi winning na heart in yara, daga malaman har daliban saboda kwakwalwar ta da kyaun da Allah ya bata gashi students mata sai janta labrary koh cafe suke ayi ciye-ciye, koh suce suje ta musu wani Assigment, duk da ba fuska ta sakar musu ba tana d'ari-d'ari da kowa kuma abinda ya bata mamaki shine sam yaran musulmai basu rabeta ba gwara maza wasu sun mata magana albarkacin zaman tare, amma matan kam kowa d'aga kai tayi abinta kamar basu san da ita a class in ba.

Yayin da bakin ciki ya gama gashe jennifer ganin rana d'aya Nnenna ta kwace mata kawaye, da aka tashi makaranta da driver yazo d'aukar su jennifer hanata shiga tayi driver yaja mator ya barta a tsaye.

Haka Nnenna ta ringa takawa da kafarta tun daga school har gida, gashi 3 aka tashi koh karyawan kirki batayi ba gashi taki cin abinda students suka sai mata, ga tafiya duk da hanyar sabone a wajen ta hakan bai hanata gane gida ba sai kusan 4:30 ta isa gida.

Tana tura kofar falon ta tarar da Mom zaune a falo sai sarah dake duba book nata koh kallon ta mom batayi ba, harta shiga d'akin ta wanka tayi ta ibo kayan uniform nata ta wanke su a waje ta shanya, kitchen ta nufa zata ibi abinci haka mom ta hanata iba, akan tunda Jennifer ta dawo makaranta ta kulle kanta a d'aki koh abinci taki ci sai kuka take don haka itama bazataci ba.

Sai dare aka samu Jennifer ta bude kofa anan take sanar da mom nata abinda Nnenna ta mata aiko mom ba karamin bacin rai taji ba, amma tace ta bari gobe in Allah ya kaimu zasu je school in tare ayita ta kare.

Haka koh akayi washe gari da safe Mom da kanta taje school in su Nnenna ita da jennifer yayin da suka bar Nnenna a titi tana takowa da kafa, Nnenna batasan me su mom sukazo suka kulla mata ba, tadai tazo school late har anso korarta gida, m amma daga baya principal yace a barta jin dalilin late in nata, sannan ya shaida mata tabar A class an maidata B.

Haka ba musu ta koma B da zama, amma sam ta daina jin dadin makaranta saboda mugun tsanar ta da aka soma ba gaira ba dalili gashi wulakanci jennifer take mata sosai, wani lokacin sai dai ta buya tasha kukan ta koh zaman aji bata iyya wa in aka fita break saboda ihu da ake mata da hausa wanda bata san mema suke cewa ba amma ta tabbata zagine.

A haka ta ringa zuwa school a kafa kuma a wahale kullum sai ta buga late allah ma ya sota ba'a duka a school in sai dai horo mai tsanani irin su wanke toilet da dai sauran su.

Daga an buga break kuma sai dai ta tafi bayan ajujuwa wajen gonakin makaranta ta xauna abunta ita kadai sai kulenta har a dawo break.

Gidan ma ba dadi yake mata ba sai in Abraham nanan koh dad suke d'an shiga harkar ta kad'an, nan ma ba sosai bane ga yunwa dake cinta abinci ba koh yaushe take samu taci abinda ranta ke so ba, har wani tari ta fara wanda bata san kansa ba in tanayi kirjinta har zafi yake mata haka numfashin ta ke fita da sauri sauri.

****************
Lahab sai da ya kwashe kwana 3 Rahab da addayiya suna jinyansa kafun ya samu ya murmure har yana zuwa masallaci da kansa muzammil yaso su koma makaranta amma addayiya tayi kukan kura ta dire tace jikin lahab bai warke ba, shikam da wannan yayi amfani wajen kara longo bewa don da gaske ciwo kan sun bushe sai dai baza'ace sun warke ba.

Yau dai yana fita sallan asuba bai zarce koh ina ba sai gidan su adewale, Amma maigadi yace masa adewale baya nan, sai ya gangara gidan su nabeel don shikam gaskiya yasha mamaki kwarai wallahi ace yau kwanan sa hudu basu gansa ba su kasa zuwa neman sa koh suje gidan su.

Yana zuwa gidan su nabeel suka gaisa a inna harma tana tambayar sa lafiya baizuwa kwana biyu? (D'an mutum kenan duk yanda kake kinsa randa baka gansa ba sai kaji wani wuri naka sakayau)anan yake sanar da ita baida lafiya ne.

Tare da tambayar ta su nabeel, ce masa tayi ai sun tafi jogging, fita yayi a gidan ya nufi hanyar filin ball da suke zuwa exercise aiko yayi sa'a tun daga nesa ya hangosu suna motsa jiki, hannu ya d'aga musu yana kwana musu kira, amma gabaki d'ayan su sukayi kamar basu gansa ba abin yayi mugu-mugun basa mamaki lokacin da ya iso inda suke yaga nabeel na kokarin barin wajen, da sauri ya rike hannun sa "haba guys kwana biyu baku ganni ba amma kuka kasa nema na"?

Wani kallo nabeel ya masa cikin yaushi yace, mtwsss eh taya zamu neme ka bayan kana school sannan a gidan ku ba'ason mu rabe ka, toh muma yanzun m................

✨Ruqeenjalal✨

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🤹🏿‍♂️ *ALKAWARIN MASOYA* 🤹🏻‍♀️
~ Na ~

🍃 *Rukayya Ibrahim*🍃

✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki tuntube ni ta layin nan whatsApp only 07044407979👌

Last Free page🤧

*EXQUISITE WRITER'S FARUM*

page 2⃣9⃣&3⃣0⃣
Don haka muma yanzun bamu ba kai?

"Wai menene niban gane ba kunje gidan mune daman"?

Munje mana wannan d'an iskan yayan naka ya........., ai lahab bai bari nabeel ya karasa ba ya wanke sa da lafiyeyen mari cikin hakin bacin rai yace" wallahi karka kuskura ka sake zagan mini yaya kaji na gaya maka duk rashin kunyan ka a bayana kake, don uwarka na taba zagin wani naka ne don ya kuntata mini.

Hannu nabeel ya d'aga ya wanke lahab da mari shima jin ya zagi uwarsa, aiko take lahab ya shuresa ya buga a kasa take fad'a ya barke a tsakanin su, sosai lahab ke jibgar nabeel adewale yayi iyya kokarin sa don raba fad'an abu yaki lahab na jibgar nabeel, shikuma zuciya na cinsa yaki barin fad'an daga karshe dai har jama'an dake gefe suna exercise, aka zo aka kakka masu amma nabeel yaki barin fad'an sai zagin wa'inda suka rirrikesa yake, wai sai dai a barsa ya buge lahab.

Wani ne a cikin su yad'au waya ya kira Bappan sa a waya, akazo aka jasa aka tafi dashi kafun mutane suka watse, kallon lahab adewale yayi, gaskiya friend nayi mamakin abinda nabeel ya aikata maka?

"Manta dashi kawai adewale gani yake yafi kowa zuciya baisan akwai maza bisa kansa ba, wai ma meya farune Adewale ban gane abinda yake ma masifa akai ba, me uncle ya muku ne"?

Wallahi lahab munzo wajen ka kawai ya kikirbemu wai bamuje school ba, shine shi kuma nabeel yad'au zafi baka sanar damu yazo ba mukaje gidan ku neman ka, ashe ka shiga school koh note babu, nima banji dadi ba gaskiya?

"Am sorry amma ban zati don brother na ya buge nabeel zai hau haka ba, ka dube jikina"lahab yace yana kwabe rigan sa.

Jesus menene haka lahab mezan ganin nan?

"Wallahi kaga jikina dukan da muzammil ya mini kenan kwana biyu bakwa gani na"

Cap Allah ya sauwa ka amma guy ka daku fa iyya dakuwa ma kuwa.

"Ka bari kawai Adewale ai shiyasa nace wallahi bazani makarantan ba sai dai ya kasheni"

Da mamaki Adewale ke kallon lahab, gaskiya aboki wallahi kana da taurin kai na rantse nidai gobe school zani, bansan koh nabeel zashi ba?

"Kai karka sake kira mini sunan shegen nan a kusa dani"

Ok yanzun ina muka nufa kenan da sassafen nan lahab?

"kai muje gidan ku ka chanja kaya mu fasa gari wallahi na gaji da zaman banzan nan zama waje d'aya ba dadi sam"

Ok muje lahab amma fa kasan old man na gida fa?

"Toh ni ina ruwa na tsoron baban naka nake ne"?

Ah ah yi hakuri man muje.

Kama hanya sukayi suka nufi fita a filin ball in har sun bar filin kamar daga sama suka ga Muxammil a tsaye a gaban su fuska ba walwala, hade fuska yayi sosai yana kallon lahab, amma kai dai lahab Allah ne kadai zai gyara maka ka, shige mutafi tun raina bai baci ba.

Bin gefen muzammil yayi ya nufi layin su ba tare da yace kome ba, kallon adewale uncle yayi, ka wuce kaje ka sanya uniform wallahi naje school naku bakaje ba, nida kai yana maganar yabi bayan lahab da sauri gudun karya arce.

Lahab na gaba Uncle na baya a haka suke tafiya har suka shigo cikin gida yana tura kofar falon ya shiga, Addayiya ce zaune sai Abbu ga inna ma zaune sai masifa take.

Karaso mutumin banza, addayiya tace tana kallon lahab.

Hararan ta yayi"wallahi nidai ba mutumin banza bane atoh"
Chapter 22 · 0% Book details