← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 122

Sashe 65

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamu da taji surutu na tashi kadan kadan a corridor nasu shiyasa ta fitowa ganin ba kowa ya sata koma daki,su Karan kansu Yan uwan sadeeq jikin su yayi sanyi ganin yanda aka tarbesu Sam basuga fuska a gunsu ba saisu Mami dake Nan da Nan dasu Mami ce ta bude jakanta tadau gudan dubu duba sabbi guda ishirin ta Basu a matsayin kudin tukuici,Adda ce ta Mike ta shiga kitchen da kanta ta Soma d'auko Robobin kaji dasu donot da eggroll tana shigowa dasu falo ganin hakan yasa sauran Yan uwa mikewa da Sauri Suka shiga kitchen in daman robobi biyar suka shirya musu ganin Adda ta fitar da uku yasasu zuwa Suka dau biyun Suka saka a store Suka rufe duk yanda Adda tayi tayi dasu akan su bada biyu a Kai amma Suka ki,mikewa bakin sukayi sunata godiya Mami da ummu da Adda su Suka rakasu har mota.

Mamu najin tashin mota daman tana bakin window da Sauri ta fito a dakin ta ta nufi falo,idanunta ne Suka sauka akan kawayen ta da Sauri ta karaso saboda Zama da sukai Suka tasa akwatunan a gaba shiya hanata gani magana ta Fara"Alhamdulilah yaudai Zan kwanta cikin kwanciyan hankali an kawo kayar diy...........kasa karasawa tayi kanin akwatunan da Sauri ta karaso tsakiyarsu tana nuna kayan da hannu tana tambayar su"wannan fa menene?Ina sauran akwatunan dakina fa za'a kai?da dariya Mai Kamar tura haushi Mami tace"kayan umaima ne da matan gidan Nan kaf bazasu samu irin Shiba shine aka kawo Kuma iyya kacinta kenan"jikin mamu har rawa yake tasa kafa tayi ball da akwatunan Kamar mahaukaciya tana rantse rantse wallahi sai an maida musu kayan su ita yarta ba Yar agwagwa bane da zasu aurar da ita haka da wasu shegun Kaya.

Mami Kam tafiyarta tayi Koh a jikinta ummu Kuma tayi dakinta taje ta kwanta,sauran kawayen Mami abincin Robobin suka deddeba Suka bar gidan Suna kananun magana bayan sun zuzzuga mamu akan karta yarda karsu karbi kayan,Koh sallama basuma mamu ba saboda haukar da ta ringa zubawa akan kayan auren karshe ma tace baza'a Kai Mata daki ba Addayiya ce tadau kayan takai dakin ta,har dare mamu na dakinta ta kulle kanta bata tabajin kunya irin na yau ba da tasan kayanda za'a kawo wa umaima kenan wallahi da bata gayyi kowa yazo ba dama bazata bawa kanta wahala wajen kashe kudin dafe-dafe ba,Abbu da yara tunda Suka dawo basu ga Mamu a waje ba Wanda hakan yasasu sanin tabbas akwai damuwa kasa hakuri Anwar yayi Saida ya tambaya,mikewa Addayiya tayi tabawa su zulai da muneera umurnin su dauko Mata akwatunan dake dakin ta,ba musu Suka daddauko ajewa tayi a tsakar falon Yan gidan duka na zaune a wajen umaima ce kawai Bata nan.

Nuna kayan Addayiya tayi tace"kaga kayan Nan umaru shi aka kawowa umaima shine uwarta ta d'aga hankalin ta har tana rantsuwa za'a maida musu"da mamaki Abbu yace a maida musu akan me kenan"?da Sauri ummu tace"akan bai Mata ba Mana Alhaji"girgiza Kai kawai Abbu yayi yace wa Addayiya"Ina ga yaran Nan zasu dau kayan sukai sa sashena su aje Zan rufe kayan a wajena bana bukatar wasu suzo da Suna ganin Kaya a gidan Nan bakuma za'a fitar da kayan ba sai ranan da aka daura auren"Yana gama maganar ya mike rai a bace yabar falon,Shareef ne ya ciccibi akwatunan da kannen sa Suka Kai dakin mahaifin nasu suka rufe.

Kwance Lahab yake akan katifar sa sai Rahab dake gefe Yana assignment"yanzun Rahab da gaske baka kirani ba ka hadani da yarinyar Nan"tsaki kawai Rahab yaja baice kome ba sai Shan Kuma yace"eh ban hadaku ba in kanason magana da ita kaje da kanka Mana ba maka Kama da Dan aika ne"shuru Lahab yayi baice kome ba daidai lokacin Majid ya fito daga wanka don har lokacin bai koma gidan su ba bude wardrobe na Lahab yayi ya dau kayan baccin sa ya saka,sannan ya dawo Kan katifar tasa ya kwanta kallon sa Lahab yayi yace"Wai don Allah Majid kasan yarinyar Nan farida"?Jin maganar mace yasa Majid sauren tashi zaune Yana washe baki yace"wace yarinya kenan"am yarinyar Nan da mukaje birthday party saurayinta"Jin maganar da suke yasa Rahab barin abinda yake ya juya Yana kallon su da kyau.

Oh baby ferry kake magana haba Lahab me zakayi da wannan second hand in, karka bada kanka Mana bazaka nemi yarinya fresh one ba d'anta sai kilakin Nan ai taimaka girma wallahi abokai na da yawa sun hayeta fa"waro Ido Rahab yayi sai Kuma ya girgiza Kai yamike ya bar dakin tare da bugo musu kofa da karfi,Suma basu bi ta kansa ba sai Lahab yace"Kai tambayar ka nake ka santa bawai dogon magana Koh bayani nake so ba"

Eh na Santa mugun sani ba,amma Kai meyasa kake maganar ta"?tashi zaune Lahab yayi yace so nake na ganta don Allah Koh akwai wani party dakasan zata very soon"?eh toh gaskiya babu kasan fa ta wanke wani gara aure zatayi amma naji friends nawa nacewa za'a Mata na bankwana a Ranan za'a murzata na karshe"amma Kai meyasa kake son ganin ta?gyada Kai Lahab yayi ya cije baki baiso ace tonawa farida asiri yayi nisa har kusan aure ba, yaso ace tun yanzun kome ya kunce"karka damu kaide duk lokacin da aka saka date da venue na wajen ka sanar dani"ok shikenan ba yawa lahab, kwanciya sukayi dukan su biyu don Rahab Kam tunda ya fita a dakin Bai dawo ba.

Washe gari da safe sai ga goggoji Mai aiki ta dawo bakin aikinta daman girkin mamu ne gashi bata fito ba tun jiya hakan yasa tana zuwa ta fada kitchen bayan sun gaisa da mutanen gidan,bayan sunyi breakfast Abbu da kansa ya mike ya nufi dakin mamu hannu yasa ya tura kofar dakin ya shiga zaune take a bakin gado ta zuba tagumi sosai tayi nisa a cikin kogin tunani da ta shiga,Zama yayi a gefenta hakan ya sata dan birkita sai Kuma ta koma ta zauna tana kallon mijin nata Kamar yanda yake kallon ta,ajiyar zuciya ya sauke sannan ya Soma magana a tausashe yace"Halima meke faruwa ne"?

Kamar ya?tace Masa tana dad'a tamke fuskar ta"Kamar ya Kuma zakice ai a tunani na kinfi kowa sani miya faru, na tambaye ki Wai meke faruwa ne Naga tunda na dawo jiya har yau ban saki a idanuna ba gashi yanzun nazo na sameki acikin damuwa"?shuru tayi sai Kuma ta fashe da kuka ta Soma magana"gaskiya Ni wallahi a maida musu kayansu taya za'a ce yarka guda za'a kawowa lefe akwatuna biyar da wani banzan kit daya haba haba don Allah kofa zanin sama da dubu hamsin babu a ciki"?

da mamaki Abbu yace"toh Halimatu yanzun ya kike so ayi indai maganar lefen ne baiyi ba babu damuwa Ni Zan iyya Kara Mata wasu set ma a had'a Mata da wannan,wani irin kayane umaima bata daura ba a gidan nan,abinda nakeso dake dan Allah ki kwantar da hankalin ki inke kin nuna irin wannan dabi'ar ita Kuma diyar taki ya kike so tayi kenan,amma in Kika nuna Mata albarkan aure yafi kayan tarkacen Nan na tabbata itama bazata nuna bai mata ba"

Wani zabura mamu tayi ta tashi tsaye ta Soma magana a harzuke"kasan Allah Alhaji nifa bazan yarda ba haba don Allah akwatuna 6 Kamar Wanda zai aure Mai tuyar awara da sakel gaskiya da sakel a maida musu da kayan su in Kuma bazasu Karo wasu ba saidai a sauke maganar auren Nan ai bashi bane kadai autan Maza kanaga fa,wannan yarinya Jamila ita da ba kyau ne da ita ba kaga gidan ubanta Koh gate babu amma ka dube kayan auren da aka kawo Mata sai tawa Yar za'a kawowa wannan tarkacen"shima Abbu tashi yayi ya nuna mamu da yatsa yana magana cikin fada"kee halima bafa tsoron ki nakeji ba karkiga Ina binki da lallama kice Zaki takani yanda kike so zancen aure Kuma Koh kiso Koh kiki wallahi baza'a fasa ba Koda kuwa yaron baiyi Kaya ba bare yayi sai in shine yace ya fasa,Yana karasa maganar yabar dakin cikin bacin rai.

Lahab Kam fita yayi a gidan hannun sa daure sai Mai lafiyar dake d'auke da kulan mubeena da niyar zai kaimata, ya gangara layinsu Nnenna da kafa don bazai iyya tuka Keke ba gwara ma in hannun hagune yake da matsala ba dama ba,Zama yayi a kofar gidan dake kallon nasu Nnenna sosai ya zurawa tsakar gidan ido Yana jiran fitowar ta duba agogo yayi karfe 7:12 ne daidai,Harya Soma tunanin Koh dai Harta wuce makaranta ne,amma saiya tsinci kansa da kasa tafiyar,sai kusan 7:30 yaga an turo kofan nasu tunda daman gidan nasu ba'a kewaye yake da gini ba, karafuna ne mutum na tsaye a wajen Yana hango cikin gidan.

Abraham ne ya fito yasha wanka cikin wasu arnan wando da riga na gogaggun Yan iska masu tashen kwaya, Nnenna na binsa a baya rataye da jakan makarantan ta bude mota yayi ya shiga itama ta bude gefe ta zauna yaja Suka bar gidan har sunzo saitinsa zasu gifta Kamar ance ta kalli gefen glass sukayi Ido hudu dashi da mamaki ta waro idanunta,shima bai tashi ba ganinta da yayan ta,har Suka share kwanar layin Yana zaune bai tashi ba"brother nayi mantuna nabar assignment book nawa a gida gashi yau zanyi summit pls ka tsaya Zan koma na d'auka"tsayawa yayi ya juya Yana kallonta yace"basai kin sauka ba bari mu juya mu koma saiki d'auka"da Sauri tace"ah ah ka tsaya dai na koma da Sauri Zan dawo karna baka wahala Bata jira mai zaice ba ta sauka da Sauri ta nufi layin su hangosa tayi a zaune har lokacin ya sata Kara Sauri tana dan gudu gudu kad'an hakan ya baiwa sassan jikinta daman kadawa da kyau,ganin ta yasa sa mikewa tsaye Yana murmushi Harta karaso Inda yake fuskar ta d'auke da murmushi itama tace"Lahab Kaine kaji sauki kenan"?hararan ta yayi irin na wasan Nan yace"eh nine lallai baki da kirki Labiba ace kin karyani amma baki nemi sanin yanda na Kaya ba nasan Koh Shakka banayi baki koma asibiti dubani ba"
Chapter 65 · 0% Book details