Sashe 47
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"bazan sa ba a hakan kikeso nasa kayan ne Koh Yaya nidai kiban abinci naci"mikewa Nnenna tayi ta dau cup guda daya ta Iba Masa tea in tasa spoon ta Mika masa,"make kafada yayi tare da kallon ta Yana Wani shugwabe fuska"nifa bazan iyya Sha da kaina ba Kinga dai hannun damana ne"?Kika tsagamin.
Zama tayi a kusa dashi a bakin gadon ta aje cup ta dau takeAway in kwai dana doya soyayye da Miya duk ta kawo ta aje masa tayi sosai sannan ta dau cup in tasa Masa a Baki kurba yayi a hankali Yana kallon fuskarta itakam Koh kallon sa batayi ba ta yago wainar kwai in tasa Masa a baki,atakaice dai Saida Lahab yaci ya koshi kafun Nnenna ta Mike daga Kan gadon laidodin abincin ta aje a jikin drower ta dauki Kaya ta shiga bandaki wanka tayi ta daura towel Inda Lahab ya cire tare ruwa tayi a bucket tayi ta soma wankewa harda na Lahab tas ta wanke kayan ta tsame a bokati,kayan da ta shigo dashi ta saka wandone da riga t-shirt ta dau bucket in tare da bude kofar toilet in ta fitoh.
Lahab Kam tunda Nnenna ta shiga ban dakin ya koma ya kwanta ba tare da ya maida ruwan daya cire a hannunsa ba,haka kawai sai Yana Jin wani irin shauki ji yake Kamar rayuwar aure suke da Nnenna Suna rayuwarsu a daki daya ta basa abinci ta Masa wanka duka da ace matarsa ce janta kawai zaiyi su kwanta tare yaji yanda masu aure suke ji ashe haka rayuwa da mace yake da dadi"Allah ka aurar damu"shine abinda Lahab yace Yana gyara kwanciyarsa Jin Karan bude kofar toilet daidai lokacin aka bude kofar dakin da sallama aka shiga,d'aga Lahab har Nnenna dake bakin toilet dago Kai sukayi sukaga Mai shigowar .................
******************
Ruky ta Jima a tsaye a bakin titi bayan wucewar mubeena ajiyar zuciya ta sauke itama ta tare Keke tare da sanar dashi sunan unguwan su shiga keken tayi Mai keken yaja Suka cillah 30 minutes Keke yai parking a bakin lungun su Rukayya saboda cabalin da unguwar tayi ga ramuka shiyasa masu Keke basa yarda su shiga sai dai a sauke su a bakin lungu,sauka tayi tadau 50 kudin keken ta Mika Masa gangarowa tayi cikin layinsu tana tafiya tana bin Koh Ina da kallo kowa harkan gaban sa yake unguwane na masu karamin karfi sosai,kallon gefen wani madalisa dake gabanta tayi cike yake da jama'a tim,sai tebur dake d'auke da manya manyan kuloli akai kannen Rukayya ne su biyu Wance take binta tana zuba abinci dayan na karba tana rarrabawa matasan dake zazzaune a rumfar,share hawayen fuskar ta kawai tayi ta wucesu ba tare ma da ta d'aga Ido ta Kara kallon madalisan ba suma basu wani lura da wucewar Yar uwar tasu ba saboda ciniki da suke.
tafiya taye kadan kafun ta iso kofar gidansu,gidane irin na da mai Jan block Koh kofa babu sai wani yamutsetsen taburma da aka Kare kofar shiga gidan dashi sai wani tsohon shagon gugan babanta dake kusa da gidan su leka shagon tayi tama baban ta dake guga da dutsen cakwal,baba sannu da aiki?
da fara'arsa ya juyo fuskarnan sharkaf da zufa,yauwa mamana harkin dawo gidan kawar Taki dazun da nashiga gida mamarku kece min kinje gidan kawar Nan taki mema sunan ta farar Nan?
Hhh sunan ta mubeeena baba?
Mubeena Kuma mamana wannan Suna ai sunan yan gayu saiku zaku iyya rikewa.
dariya kawai Rukayya tayi ta nufi kofar gidan nasu d'aga taburman tayi da sallama ta Shiga.
Addanta bazawara dake duke tana sana'an wankau ce ta amsa sallamar ta tare da Mata sannu da zuwa itama Rukayya sannu da aiki tama yayar tata ganin uban wanki da take tana ta shashanyawa,Zama tayi a bakin dakali,mamar tane ta fitoh kitchen da Sauri hannunta d'auke da kullin awara data tsame yanzun daga tukunya ajewa tayi a bakin dakali tare da daura Masa babban dutse akai.
Sannu da aiki mama?
Yauwa Rukayya sannu harkin dawo?
Eh na dawo mama,yauwa tunda Kim dawo ga kwanuka da tukanen abincin Nan kije ki wankesa kafun lokacin fitar kanwarki tuyar awaran yayi kin kimtsa kayan aiki,mikewa Ruky tayi ta Shiga dakinsu ta Kwabe kayan jikinta ta sanya wani kodadden zani ta fitoh bucket ta d'auka ta fita gidan ruwa ta ibi kafa uku saboda yanayin yawan kwanukan abinka da gidan masu abinci da tuya kwanuka bana Wasa bane buhun omon su ta dauko ta aje tasa kujera ta Fara wanke wanken.
Sai can yamma kannenta guda biyu Suka shigo gidan, Almajirai nabinsu da robobi da kulolin abincin nasu,faggawa Almajiran sukayi a mawanki ita Kuma Yar autarsu ta dau awaranta a bucket da abubuwan tuyanta ta fita kofar gida, cefene maman su tama Rukayya saboda itace Bata sana'an kome sai aika da wanke wanke da zuwa cefene in bataje school ba Amma su biyar Mata kaf su hudun Suna da abin yi.
Bayan sallan mangariba zazzaune suke gabaki dayansu a tsakar gidan sauran abincin da bai Kare ba na sairuwa shi gabaki dayan su suke ci shinkafane da Miya sai Kuma tuwo da miyar alaiyahu da aka duma, Ruky duk da abinda ke damunta kokarin boyewa take bata son kowa a gidan su ya fahimci halin da take ciki,Jin ana kiraye kirayen isha'i yasa baban su mikewa ya fita masallaci sauran yaran ma duk Suka mimmike Suka dau buta Suna Alwala.
Bayan sallan Isha zazzaune suke ana Hira a tsakar gida ita Kam Ruky rike take da handout nata tana karatu hannunta rike da dan wayarta Abba gida-gida,yaro ne ya shigo da sallama tare da sanar dasu wai wani na sallama da Rukayya a waje kallon kallo akayi don rabon da azo ace a Kira Rukayya ai an kusan shekara kenan,kaje kace wanene Addan Rukayyar tace,juyawa yaron yayi baijima ba sai gashi ya dawo Wai inji Ahmad,mikewa zaune Ruky tayi duk da tana danjin kunyar babanta dake wajen,ta fahimci wani Ahmad ne cikin sanyi tace kaje kace bana Nan?
Ke tashi dan Allah Mara hankali wani irin aje ace bakenan Mike Maza,-maza Kafun tacewa yaron kai jekace tana zuwa maman ta tace tana zarewa Ruky Ido,mikewa Ruky tayi tadau hijab nata cikin kunya ta fita a gidan.
tsaye yake a jikin ginin gidan su ya hade hannayen sa a kirjin duk da dare ne hakan bai hanata ganin raman da yayi ba, Assalamu Alaikum.
Waalaikumu Salam Rukayyar barka da dare?
Uhmm barka dai Ahmad ince dai lafiya na ganka a irin wannan lokaci Kuma a kofar gidan mu?
Hh lafiya klau Rukys menene zai kawo saurayi irin wannan lokaci wajen budurwa in bada maganar so ba?tukunna ma ba wannan ya Kamata ki tambaye Ni ba jikina ya Kamata ki Fara tambaya.
Kaga dan Allah Ahmad Ni wannnan Wasa ya isheni haka Ina son kawata Ina son alakarmu duk da Koh shekara bamuyi da haduwa ba kaika sani a makaranta muka hadu amma Ina jinta a raina sosai bazan so ka Zama tsilar rabuwar mu ba Koh Ni na Zama tsilar rabuwar ku.
Haba sau nawa Zan sanar dake cewa babu wannan zance na nine sula Koh kece tsila babu wannan magana abu daya na sani shine bamu sabawa shariya ba Kuma ita da kanta tace bata Sona tana da Wanda take so?
Eh hakane amma fa ka sani bazan iyya auren ka ba duniya zasu zageni.
Wani irin zagi?ana gujewa mutan ne Koh bayan aure zasu zo har gidanki su fiddaki ne,Koh zagi Yana mannuwa a jikin mutum ne? Ni abinda nake so dake Ruky ki sani bawai zanyi abin nan dan kuntattawa mubeena bane ah ah wata daya ya rage in ba haka ba baba na ya rantse sai ya auramin Yar kanwarsa Ni Kuma tarbiyarta baimin ba amma kefa na sanki tuntuni bana bukatar tsayawa tantance dabi'unki sai abinda baza'a rasa ba.
dan sauke ajiyar zuciya Ruky tayi,yanzun Ahmad y........baibari ta karasa ba ya dakatar da ita,Kinga Ruky ba zuwa nayi muyita maida zance ba Zan baki Nan da kwana uku kije kiyi shawara Zan dawo ranan talata na amshi amsata duk abinda Kika yanke wallahi bazan Kara akansa ba don haka ki shiga cikin gida Sai da safe.
gyada Kai kawai Ruky tayi ta juya ta shiga gida,tana shiga ta samu baban ta ya tashi yayi cikin dakin sa itama dakinsu ta shiga da Sauri taje ta zauna akan katifar ta ta rufe fuskarta da hannunta cikin damuwa.
Mikewa Addan Ruky tayi ta biyota dakin Zama tayi a bakin katifar ta dafa kafadar ta,Ruky meke faruwa meyasa tsawon shekara kina Neman mashinshini sannan yau kin samu wani yazo shine Zaki ki fita Ruky watoh har yanzun bakiyi karatun ta natsuba kin manta sake da kikayi da Nasir ya tsubce Miki,haba Ruky kinfiso dukan mu mu taru mu zauna kenan Koh me?
Uhmmm Adda Koh kinsan Ahmad Nan dayazo wajena shine zai aure mubeeena?
Rukayya wata mubeena?
Kawata mubeeena fa.
What??wannan ai shirmene akan me zaizo wajen ki bayan Yana tare da kawarki,Zama Ruky tayi ta warwarewa addan ta kome,toh kinji abinda ke faruwa.
Mikewa Adda tayi ta kalli Ruky, Rukayya indai haka abin yake toh Ina Mai Baki shawara ki yarda ki amince da Ahmad wannan shine Allah ya kashe ya Baki.........
🙄*Ruqeenjalal*
*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*
Page 59&60
Haba Adda wani irin Allah ya kashe ya bani? karfa ki manta banine a ransa ba mubeena ce wallahi Koh shakka banayi Koh na aure sa bazan samu kulawar da mubeena zata samu a wajen sa ba.
Uhmmm Rukayya kema har yanzun yarinyar ce Ina ruwanki da yafi sonta a kanki,shuru kawai Ruky tayi tana kallon Yar uwar tata sai zuzuta zancen take da Kara jaddada Mata akan ta amince dashi, Rukayya nidai Ina Kara gaya Miki wallahi kiyiwa kanki karatun ta natsu ai dukan kune zakuyi biyu babu ke baki aure sa ba itama ta rasa don haka nidai Ina gaya miki ki amince kinji?
gyada Kai Ruky tayi tace,insha Allah Adda Zan amince Masa Allah yasa hakan shiyafi Alkhari a garemu baki d'ayan mu.