Sashe 2
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Addayiya dake zaune har lokacin fuska a hade, nufar kanta gadan-gadan Lahab yayi da azabebben gudu.
ai mikewa Addayiya tayi jiki na rawa ganin sa ya nufota da gudu itama gudun tasa ta nufi.............
*******************
ENUGU STATE.........
zaune take a kan bench ita kad'ai, kuma benchin a kusurwan aji, ita kad'ai aka ware wa wajen tana zama, gabaki d'aya ta tattara hankalin ta akan malamin dake koyar dasu Math's duk da ba kallonsa take ba.
sanye take da wani kod'aden uniform dogon rigane wanda ya tsaya mata iyya gwuwa, farace irin farin nan da ake kira light, kyakkyawace na bugawa a jarida siririya ce Amma fa Akwai kaya duk da tana zaune akan kujera hakan bazaisa mutun ya kasa gane irin baiwar da Allah ya mata ba, kirjinta a cike yake tam wanda yasa gaban rigan matseta har gaban kirjinta ya kasa rufuwa har ana kallon farin vest inta datasa a ciki shine ya hana ganin Kirjinta a waje, kanta ba hula sai gashinta mai yawa da aka masa kitso uku ya zuba har gadon bayan ta.
Ebo ce irin fararen masu kyau innan toh haka take ita ma, bakinta jajazur maikyau ga hanci mai tsaho, duk da idanunta na boye a cikin medicated glass, hakan bai hana ganin kwayar idanunta dake kallon Allo ba.
masha Allah idanun nan ne irin wanda ake kira da cat eyes kwayar idanunta sky blue ne, gasu masu girma, wanda sanadin su wasu ke kara gudun ta.
kiliilii....killiiliii bugun bell shiyasa malamin fita a ajin, ya rage ita kad'aice a class babu kowa, yamusheshen jakanta ta zaro a lokan benchi budewa tayi ta leka ciki.
kulenta(magge koh kenwa)zaune a kan takardunta abin tausayi, shima jin An bude boron yasa sa kallon ta.
sosai ya bata tausayi yanda bata karya ba, haka shima yau babu abinda yaci, hannu tasa a gefen jakan ta zaro naira talatin jujjuya kudin tayi a hannunta, aje jakan tayi ta mike tsaye ta fita a ajin.
tafiya take kanta a duke fuska a hade sosai, wanda hakan dabi'arta ne bazaka taba ganinta cikin fara'a ba, koh kaga tana surutu da wani, duk inda tazo wucewa haka yara zasuna watsewa Inda sabo ta saba, hakan yasa abin bai damunta sosai.
tun kan ta karaso wajen mai kayan shagon tuni ya ruga a guje ga fita a keus nasa, itama bata wani damuwa ba hannu tasa daga wajen shagon ta ballo madaran 20 da pure water 10 aje masa kudin tayi ta juya ta koma class.
zama tayi a inda ta tashi hannu tasa a boron ta d'auko kulen ajesa tayi akan kujeran, bude madaran tayi ta bula ruwan ta zuba a madaran saida yazo har bakin laidan madara, kafun ta aje pure water kallon kulenta tayi yana zaune kamar mutum ya kurawa madaran ido, d'aukarsa tayi ta aje akan cinyarta tana basa madaran.
sai da ya kusa shanyewa kafun ya Rufe bakinsa Alamun ya ishesa, sauran kad'an in ta shanye batare da taji kyeman bakinsa ba.
haka a daddafe take saboda tsananin yunwar da ke cinta, karfe 2 Aka tashi a school, duk yara suka fifita, itakam zama tayi a class taki fita saboda tasan mundin ta fita, haka yara zasuyita gudu har su shiga kauyen su, shiyasa take jiran su d'anyi nisa kafun itama ta kama hanya.
2:27 ta fitoh a class nasun hannunta rike da jakanta wanda kule ke ciki da takardu, yaran makarantan duka sun watse koh malamai babu, A haka take tafiya A hankali, Nnenna irin mutanen nan ne masu saib'i.
tafiya take Da kafa hankalinta gabaki d'aya yayi gida, ganin yanda hadiri ya hadu sama yayi bakikkirin sai iska dake kad'awa, doguwace sosai tana da wadatantun mazaunai masu d'aukar hankali, iska na kad'awa sai suka kara fitowa sosai.
babu kowa a hanyar wanda hakan bai dameta ba sanin yaune Ake biki a makwantan kauyen su, lokacin da ta tsallake ruwa tazo wajen gonaki.
ji kawai tayi an fizgota ta baya a matukar kid'ime ta juya wazata gani? wasu yan iskan kauyen sune chukwudi da onyebuchi akalla zasu kai 25, fizge riganta tayi taci gaba da tafiyan ta hankalin ta a tashe, sanin halinsu gashi yau babu kowa a hanya.
binta sukayi Chukwudi cikin yaren Ebo yake mata magana, ke Nnenna Mayya mufa ba ruwan mu da maitancin ki, cinki yau zamuyi saboda kin hadune bana wasa ba, gashi bamu taba samun target namu yatafi daidai ba irin yau.
jikinta na rawa ta kara sauri onyebuchi ne yasa hannu ya damko gashin kanta, fusge kanta tayi, da sauri ya wanketa da mari wanda yasa glass nata faduwa.
rumtsa kyawawan idanunta tayi cikin tashin hankali ta sake budesu, gabaki daya dishi-dishi take kallo sam bama zata iyya kane fuskar su ba a yanzun.
da sauri ta tsunguna a kasa tana lalubar glass nata, chukwudi ne yasa kafa ya take glass in dake gefe.
jin karan fashewan glass yasa da sauri tasa hannunta ta saitin wajen tana laluben glass in, tana najinsa ta d'auka, tattabasa tayi, Kawai saita fashe da kuka ganin idanun glass ya bararraje.
dariya suka sake a tare cikin iskanci onye yace mata, yaufa koh Jesus ne ya sauko bazai ceceki ba(wa'iyyazu billah) bare mutum gwanda ki bimu a hankali mu gama abinda muke so, a wajenki mu barki ki wuce, koh kuma mu kasheki kika mana gardama ya karasa maganar da zaro sharbebbeyar wuka.
dubansa tayi idanunta na zubarda ruwan hawaye, sam ba kallonsu take sosai ba, tadai san gasu a gabanta Amma bata kallo normal kamar kowa
"Tabbas kowa zai mutu Amma fa ka sani kai yau kwanan ka ya kare, kafun na mutu kai zaka fara mutuwa, Ajalinka na kusa wannan ALKAWARI ne, ALKAWARIN mutuwa"ta karasa maganar cikin tsantsan bacin Rai.
jin Abinda tace yasa chukwudi sake wanketa da mari mai zafi saida ta zube a kasa, jakarta ya fade Allah ya sota ba'akan jakan ta fadi ba data illata kulenta, jinine ya balle a hancinta.
A take ruwa ya sako da karfin gaske, hannu yasa yajawo riganta sai da ya yage,da karfi ta turesa ta kwashe jakanta da gudu ta ruga.
suma binta sukayi sosai suke tsere har sukazo bakin titi koh gabanta bata kallo saboda rashin glass, gudu kawai take wanda ta fadi yafi a kirga haka zata daure ta mike, da gudun tsiya ta tsallaka titin daya ratsa kauyen su.
suma da gudu suka zo tsallaka titin, ji kake kauuuuuuuuuu wata babban roka tabi ta kansu .
Nnenna dake gudu jin karan yasata tsayawa da sauri ta dafe kirjinta tuno warning inda papa ya mata kafun ta fitoh..............
SANARWA!!!!SANARWA!!!!SANARWA!!!SANARWA!!!
BABU UPDATE NA ALKAWARIN MASOYA
EVERY WEEKEND
✨Ruqeenjalal✨
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🤹🏿♂️ *ALKAWARIN MASOYA* 🤹🏻♀️
~ Na ~
🍃 *Rukayya Ibrahim*🍃
Free page🤧
*EXQUISITE WRITER'S FARUM*
Page3⃣&4⃣
in bata manta ba papa yace mata mundin ta fita gida, sannan ta d'auko masa magana jikinta zai gaya mata, asalima umurni ya bata akan ta rufe bakinta, har taje ta dawo karta kuskura tayi magana da kowa, gashi tajawo wani rigimar kuma.
kuka ta sake mai karfi gashi sai ruwa ake ga rashin glass ga iska na shigar mata ido, gashi bata ganin gabanta sosai,
tafiya kawai take hankalinta a tashe, ta rasa ina zata nufa ba ganin hanya zatayi ba sosai ga ruwa, tafiya take a hankali ga jakanta a sakale a kafad'arta, gajiya tayi ga yunwa yasa ta zauna a jikin wani bishiyar da batasan bishiyar menene ba.
kamar minutes 5 da xaman ta taji abu ya fado a jikinta da sauri ta kwala kara ta matsa gefe, don ta tsorata ainun zuciya mai sake-sake harta saka mata wani abin cutarwa ne.
jin abin bai motsa ba yasata lalubar jakar ta ta bude kulenta dataji yana kuka, aiko tana budesa da gudu ya nufi inda Abin nan yake d'aukowa yayi da bakinsa ya matso kusa da ita ya aje mata a jiki, hannu tasa ta tattaba jin ayabane yasa ta murmushi, duk da ita a d'abiyarta sam batacin abinda ba'a bata ba koh yayane, Amma yunwar da takeji bazai saurara mata ba rabonta da abinci tun jiya.
barewa tayi a hankali tana kai dubanta zuwa ga kulenta mika masa tayi Amma taji bai karba ba alamu dai bazaici ba, daman tasan Bayacin Ayaba, cin Abinta ta shigayi dayake bari guda ya fadi kusan k'walli 15 ne a manne waje d'aya.
bayan ta gama cin ayabar ta, zuwa lokacin ruwa ya d'auke mikewa tayi da jikekken uniform nata a yage, jakanta ta bude ta saka kulenta a ciki shima duk ya jike, tafiya ta cigaba dayi tana kallon dishi-dishi dayake hanyar ba bakonta bane koh babu ido garanti zata gane kauyen su.
tunda ta shigo kauyen jikinta ya fad'a mata ba lafiya, sanin da tamusu war yanzun suna bakin bishiya wasu na caca wasu nashan giya, Amma yau sit kakeji, duk inda ta wuce binta ake da ido wasu yaran kam gudu suke suna bata hanya.
a haka ta iso kofar wani yamusheshen d'akin falange wanda akayishi ciki da falo, sai tsunmokaran su a rarrateye a jikin kwanukan gidan kome nasu a waje yake kama daga bandaki wajen girki kamar dai gidajen inyamurai babu katanga koh makewayi daga an fita a daki toh kamar an fita a kofar gidane.
tura kofar d'akin tayi kamar yanda ta tsammani hakance watoh a bude kamar kullum, da takalmi a kafarta ta shige ciki.
falone d'an kankani sai kujera da katifa mai masifar datti a gefe da tufafi a rarrateye sai risho da takalma da kwalaban giya, wucewa tayi kofar dake tsakar falon, tana shiga dakine karami babu kome sai taburman ta karami da kullin kayanta data d'aure mai datti tamai dashi filo.