← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 122

Sashe 52

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ok toh nidai babu abinda ke damuna maganan Lahab Kuma wallahi koni banjin labarin sa jiya ma naje gidan su aka cemin Wai ba'amasan Inda yake ba wallahi Lahab zai kashe Yan gidansu duk ya d'aga musu hankali Kuma Nina tabbatar Lahab ba b'ata yayi ba iyya shegene kawai ke damun sa.

Uhmmm lallai Kam amma kana nufin ba'ama San Inda Lahab yake ba kenan?

Kwarai ma kuwa Nabeel hakan nake nufi.

toh yanzun gidan wa Lahab yashiga kenan?

Wallahu alamu Ina Zan sani Nabeel

Kallon sa Nabeel yayi Jin yace wallahu alamu watoh Koh Yaya Christian ya zauna a cikin musulmai sai ya kwaikwaye maganar bakin su,ok bara na wuce Allah ya sauwaka don nasan dai tabbas baka da lafiya kawai boyewa kake.

Yanzun bazaka zo mu shiga ba?

No Ni bazan shigaba kaga ma tafiya ta sai anjima,Nabeel yace ya Kama tafiya abinsa.

Toh ka gaida Inna.

toh zataji,komawa Adewale yayi cikin gida su.

MAFARKI.................
Assalamu Alaikum wani mutumine kyakkyawa fari tas sanye da farin Kaya hannunsa d'auke da Sanda Yana dogarawa yayi Masa sallama.

Waalaikumu Salam ya amsa Masa sallaman nasa daga zaunen da yake tare da d'aga Ido zai kalli tsohon amma Ina ya gaggara saboda hasken dake kashe Masa idanun.

bazaka iyya kallona ba Hassan tsohon yace Yana wani irin murmushi Mai dan Sauti.

Sosai zuciyar Sa ya tsinke har Saida ya dafe kan kahon zuciyar tare da kokarin d'agowa daga duke da yake Yana son tashi tsaye Kamar yanda tsohon yake a tsaye amma Ina ya kasa ji yayi gabaki d'aya jikinsa ya wani irin daskarewa waje daya sosai yaji wani tsoro ya mamaye Masa zuciya.

Bazaka iyya mikewa ba saidai wani ikon Allah Hassan ka kwantar da hankalin ka bazan cutar da kaiba,magana nake so nayi dakai.

Jikinsa na rawa ya daina yunkurin tashi daga wajen sai dan dago kansa da yayi ya kalli gaban sa katon kogi ne fari tass Mai d'auke da ruwan koramu masu gudana daaga cikin dutse Mai tsawon gaske hannu ya Mika a hankali zaisa a cikin ruwan kogin saboda tsananin sha'awa daya basa yaji an hanka d'asa tare da amon murya ana Masa gargadin kada ya kuskura ya taba ruwan,ja da baya yayi ganin ruwan ya rikide daga fari zuwa ja jazer dutsen dake wajen sun koma bakake.

Hassan kaga kogin Nan?tsohon dake bayan sa har yanzun ya fada.

"Eh na gani"

toh haka kaddarar ka take abu Mai kyau zaka gani ka zata abin sone amma fa ka sani kaddarar kace kaddarar kace tana tinkaro ka tabbas abinda Allah ya tsara dole ne saiya faru amma Ina Mai baka shawara akan duk halin da zaka tsinci kanka Nan gaba kayi hakuri ka dogara da Allah kasawa ranka kome jarabawa ne daga mahallincin mu,kayi kokarin ganin ka cinye jarabawar ka insha Allah Allah zai musanya maka da Mafi Alkhari akwai zazzafar kaddara a rayuwar ka haka zalika akwai kyakkaywar sakamako amma sai kayi hakuri sai kayi hakuri kayi hakuri Hassan.......ka zamo Mai tawakkali.....Allah na tare da Masu hakuriiiiiii...............wani irin zabura Lahab yayi ya mike zaune daga mummunan mafarkin dayayi duk zufa ya jika Masa jiki.

Nnenna dake zaune tun d'azun a kansa tana binsa da kallo ganin sai wani jujjuyawa yake da kansa ga zufa na sassafo Masa,saurin Mika hannunta tayi ta dafa sa ganin ya mike zaune a razane cikin damuwa take tambayarsa"menene mafarki kayi ne Mika gani a mafarkin naka"?kasa bata amsa yayi sai"innalilahi wa'inna'ilahu raji'un dayake ta maimaitawa,itama mikewa tayi da Sauri ta nufi wajen socket ta kunna wutan dakin tare dakai dubanta garesa ganin ya mike da Sauri zai nufi kofa,da gudu tasha gaban sa tare da nuna agogon bango dake makale a dakin"Lahab ka duba lokaci karfe 1:30am na dare Ina zakaje Kuma"?

"gidan mu zanje bansan meke faruwa dani ba a Y'an kwanakin Nan mummunan mafarki nake zanje wajen Mami na"ganin Kamar baya hayyacinsa yasa Nnenna kin basa hanya sai rungumarsa da tayi tabaya ta soma magana"ka kwantar da hankalin ka babu abinda zai sameka sai Rubuceccen Al'amari wannan bani da iko a kansa amma bazan barka ka fita a daren nan ba.

Fizge jikinsa yayi da Sauri ya nufi kof..............

🍀 *by Ruqeenjalal* 🍀

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 65&66

Nufar kofar toilet yayi ya bude ya shiga,komawa Kan gadon Nnenna tayi ta zuba tagumi,Lahab na shiga wanke fuskar sa yayi da ruwa sannan ya zauna akan toilet sit gabaki d'aya damuwa ne shimfide a ransa tunda yake bai taba ire-iren mafarkan Nan ba sai a 'Yan kwanakin Nan haka zalika yasan mafarki ba gaskiya bane amma mafarkin yau ya matukar rud'asa ya Kuma tsaya Masa a wuya,shiru kawai yayi yayi Jim dashi a zaune shi bai fita ba Shi baiyi kome ba.

Nnenna kallon agogo tayi sannan ta Mike ta nufi kofar ban dakin tasa hannu tadan tura kofar Jin a bude yasa ta dakata wa kafun ta soma magana"Lahab lafiya har yanzun baka fito ba"shiru bai amsa ba itama tura kofar tayi ta leko cikin ban dakin Allah ma ya sota akwai wuta,har lokacin Yana zaune shuru,takowa tayi ta shigo ciki a hankali take tafiya Harta iso kusa dashi hannu tasa a hankali ta kamo hannun sa lafiyayyen"Lahab meke faruwa mafarkin me kayi"?

Kallon ta yayi sai Kuma yaji baison sanar da kowa abinda yake mafarki especially na yau,mikewa tsaye yayi har lokacin hannunta na nasa ya nufi fita a kofar binsa tayi a baya har Suka fitoh Zama yayi a bakin gado tare da kallon ta ya nuna Mata gefen sa gyada Kai tayi ba musu ta hau ta kwanta,kashe wutar yayi shima ya kwanta gabaki dayan su shiru sukayi amma kowa yasan dan uwansa baiyi bacci ba.

Har asuba Basu rumtsa ba kowa da abinda ya damesa Wanda rashin baccin nasu lokaci daya ya saukarwa da Lahab da zazzabi a jiki,da asuba ma da taimakon ta ya samu yayi alwala ta shimfida Masa sallaya yayi sallah Yana idar da sallan Dr ya shigo ya daura Masa ruwa da Alluran bacci ganin jikin nasa yayi zafi ga rashin bacci yayi musu fad'a sosai ,bacci ne ya d'auke sa itama Nnenna bacci tayi akan kujera.

*******************
a gidan su Nnenna bayan dady ya dawo da yamma har dare baiga wullawan Nnenna ba gashi dai weekend ne bare ace taje school kasa hakuri yayi ya tambaye mom anan take ce masa tun jiya Friday Suka nemi Nnenna Suka rasa ,Sarah taje school nasu akace taje amma tashi da ita.

Aiko ranan mom taga bala'in Dad Wanda bata taba gani ba ta Inda yake shiga batanan yake fita ba sai cewa take daman bata son Nnenna taimama ita ta b'atar da ita Wasa-Wasa fada ya zamo na manya station dad yaje yakai kara Yar d'an uwarsa bakuwa ta bata,sun karbi hoton ta da suna aka Kai gidan TV Koh Allah zaisa wani ya ganta tunda ance bakuwa ce kilan bata tayi Abraham ma daya dawo daga Lagos yaji wannan labari hankalin sa ya tashi sosai.

Nabeel na barin gidan su Adewale shagon dinkin su ya nufa da sallama ya shiga shagon ogan sane da sauran yaran shagon Suka amsa masa Suna binsa da kallo rabon shi da shagon har sun manta sai dai yazo da abokan sa suyita hira,Zama yayi akan keken sa bayan yadau wani tsumma ya kakkabe kuran dake Kai ganin haka yasa ogan sa mikewa tsaye ya Soma magana,kaga Nabeel Mike tsaye bazaiyu kazo ka zauna a shago ba don nasa d'ayan biyu ne wata kil watace zata kawo maka dinki shiyasa kazo ka zauna watoh ka karbi kayan jama'a ka yanke zuwa shago daga karshe yara suzo Suna min rashin kunya a shago tare dajan Allah ya isa,don Kai Allah ya isa bai dameka ba don hakan Mike kabar shagon Nan.

Sunkuyar da Kai Nabeel yayi,don allah oga kayi hakuri wallahi dinki ne zanyi daman akwai wasu Kaya da nake son dinkawa ne.

Wa???badai a shagon Nan ba sai dai kadau keken naka ka tafi gidan ku dashi kaje ka dinka acan bazan iyya ma halinka ba Nabeel.

don girman Allah kayi hakuri oga wallahi dinki zanyi kudi nake su a Yan kwanakin Nan Inna bar shago Ina Zan samu tsoffen customers nawa.

Kai Nabeel wani tsofen customer Kuma bayan bana tunanin akwai Wanda xai sake baka dinki indai yasan ka kayan jama'a guda nawa ne a wajen ka na Allah ya isa?watoh kana son kudi Koh,shiyasa ka dawo ka yago kudin mutane?

Haushi ne ya tsoma Kama Nabeel hakan yasa sa mikewa ya fita a shagon baijima ba sai gasa da Mai bairo Kan keken sa ya d'auka da bodyn keken duka yasa a bairo wasu turaman zanin daya aje a shagon duk ya tattara ya loda a Keke,baibi takan maganan da ogan nasa yake Masa ba ya Soma tafiya Mai bairo na binsa a baya.

Suna isowa kofar gidan su wangale kofar yayi Mai bairo ya shigo da keken cikin gida,mubeena dake zaune ta tasa tuwo a gaba amma bataci ba don kwata kwata taji bata sha'awan cin kome musamman data ji labarin b'atan Lahab don zuwa lokacin labari ya guma unguwan kwana uku ba'a gansa ba,sai Inna dake zaune tana tatan kamu,dukan su da Ido Suka bi Nabeel har ya shigo tsakar gidan sauke keken sukayi damai bairon kudi ya zaro naira 30 ya mikawa Mai bairon.

gaskiya abokina talatin yayi kadan kadai ban 50,kallon sa Nabeel yayi a karkace cikin dan Jin haushi daman ya gama kuluwa da abinda ogan sa ya Masa,Kai da Allah karba ka Ware wani irin na baka 50 daga shagon mu Nan nan kasan layin Nan xaka wani CE na baka 50 sata kake Koh neman kudi kajimin almajiri da iyayi.

ran Alamajirin ne ya baci shima cikin zafin yace,kaga malam ban 50 na ai hakki nane in Kuma bazaka bani ba na barka da Allah.
Chapter 52 · 0% Book details