← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 122

Sashe 82

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page 1
Innace muku hankalin Y'an gidan su Lahab ya tashi toh yafi gaban tashi yayi sosai suka shiga rudani duk yanda Abbu yaso su Masa bayani tun a cikin gidan sukace ah ah saidai yabisu office nasu aiko take ya shiga ya dau keyn mota Rahab da tunda yaji ance za'a tafi da dan uwansa yake ta faman rusa kuka yazo ya rungumi Lahab,amma babu Imani aka fincike sa tare da tasa Lahab a gaba suka bar falon ji kawai sukayi timmmmmmm Rahab ya sulale a wajen,hankali tashe Abbu ya d'aga waya ya Kira ya jafar ya samesa a office in jami'an ya barwa su Shareef Rahab shi Kuma yabi bayan jami'an.

Bayan isar su Abbu anan ne yaji dalilin Kama Lahab akan wata yarinya da tayi kisan Kai Kuma ana zargin dasa hannun Lahab,aiko Nan Abbu yace uban kuturu yayi kad'an bare na makaho kaninsa Koh kuda bazai iyya kashewa ba bare tai guda,Kuma babu abinda ya had'asa da wata Yar arna,magana ta Zama babba Mami da Rahab na gado don gabaki d'ayan su faduwa sukayi,lokacin da labari ya riske mubeena Aljanunta ne Suka tashi rike-rike sai ihu take daker aka samu aka daddan neta Suka kwanta,daga baya Kuma sai aka koma asibiti ganin ciwo ne ya nufeta lokaci d'aya,su Inna sunyi mamakin surutun da tayi lokacin da take cikin kukan iska akan a fito Mata da Lahab kaza-kaza tunanin da yazo ma Inna taima tausayin sane ya sata haka tunda case na kisan Kai ba Wasa bane.

Papa Kam sosai ya dawo gida Yana ta masifa akan baga abinda yake gujewa Ade ba akan yaran hausawan nan makiyansu ne Amma baya ganewa gashi yaro ya kashe Cristian duk yanda Adewale yaso Kare Lahab a wajen iyayen sa abun ya gagara don Yana tare papa zaiji an buga Masa baki,kowa yaji zancen Nan sai ya karyata duk da Lahab bayaji amma wallahi kowa ya shaida Lahab bazai kashe mutum ba Koh taimaka wa wata ta kashe mutum.

Duk yanda Yan Sanda sukayi da Lahab akan ya sanar dasu Inda Nnenna take amma ya murza idanun sa akan shi baisan Inda take ba,gashi an Hana taba lafiyar sa da karfin iko da kudi yayun sa Suka daukaka Kara za'ayi shariya akan kazafin da ake son d'aurawa kanin su,duk wani masoyin Lahab ya Shiga tashin hankali lokacin da zancen yaje kunnen Nnenna goggoji ne ta dawo tana sanar Mata hankalin ta tashe ta Soma kuka tare da mikewa tsaye tana cewa zata,tace musu babu ruwan Lahab basai an Shiga kotu ba,hankali tashe goggoji tace bazaiyu ta barta ta fita ba Lahab bazai yafe Mata ba ta fahimci Yana kaunar yarinyar sosai ita da faruq Suka yita nutsar da ita tare da Bata tabbacin insha Allah Lahab xai fito ai Yan uwansa nada kudi Kuma Godwin bazai iya winning akan suba in zancen kudine zuriyan su Lahab sun damasu sun shanye daker dai da sudin goshi Suka samu ta yarda zata zauna laptop nata ta dauko ta baiwa faruq ya sitting na kome a ciki ta Fara Hawa yanar gizo tana kallon abubuwan dake gudana a duniya da Al'amarin case nata kowa na fadin Albarka cin bakin sa.

Mami tafi kowa Shiga tashin hankali Allah sarki uwa gabaki d'aya ta rame ta fige duk da an sallamota amma bata Jin garau Kamar dai mubeena itama ta Dan warware ga Kuma bikin Ahmad da Ruky da ake a wannan satin duk abubuwan sun hadu sun Mata yawa,Lahab ya wahala zaman gidan yari Koh babu duka ba zagi azabane, ya Kara Baki ya rame sosai sai Ido da hanci da tsawo duk sun fito sosai amma saboda taurin rai Lahab yaki ya basu duk information da ya sani akan yarinyar.

Monday morning kotu ya cika makil da Jama'a Koh matsakan tsinke babu sosai sai dan surutai dake tashi kasa-kasa shigowan Alkali shiya nutsar da Al'umma kowa yayi shuru tare da mikewa Harya zauna kafun jama'ar Suma Suka zauna Yan uwan Godwin (Dad) dana mom sai Family Lahab Suna da yawa sai Yan jaridu da Kuma Yan kallo after few minutes lauya ne ya Mike ya gatabar da kansa na lauyan dake Kare Wanda ake tuhuma sannan lauyan su mom shima ya mike ya gabatar da kansa tare da Neman izini ya matsa kusa da Lahab ya tsaya sannan ya kalle sa yace" Koh zaka iyya fadawa kotu cikekken sunan ka"?

d'ago jajjayen idanun sa yayi ya kalli lauyan yace"Sunana Hassan Al'hassan dogo Mai Naira"jinjina Kai lauyan yayi sannan ya Kara jefo Masa tambaya"Koh zaka sanar da kotu wace alakace tsakanin ka da Wance ake zargi da kisan Kai Nnenna obinna"?sunkuyar da Kai yayi sai Kuma yace"bamu da wata alaka ta jini friend nawa ce a makaranta"wani shegen murmushi lauyan yayi ya gyara rigansa kafun yace"kana nufin bakwa haduwa sai a makaranta sanann duba da a'ladunku na Arewa babu friendship tsakanin mace dana miji"mikewa lauyan dake Kare Wanda ake tuhuma yayi Yana cewa"objection my lo... barrister Yana kokarin cusawa Wanda ake zargi magana a baki taya zaice a Arewa babu abota tsakanin namiji da mace"gyada Kai Alkali yayi yace wa lauyan a kiyaye,sannan yaci gaba dama Lahab tambayoyi Yana basa amsa har aka gangaro Kan na Randa abin ya faru"Koh Hassan zai iyya sanar da kotu a ranan 30/1/202.........meya fitar dashi da misalin karfe 20:20am daga gidan su, alhali Kuma dokan gidan su yara basa fita muddin 9 na dare ya gotta.?

Sosai zuciyar Lahab ta tsinke bama Kamar lokacin da ya dago ya kalli Mami da Abbu da Suka zuba Masa Ido Suna jiran amsar da zai bada,a hankali yace"da misalin karfe biyu na dare Nnenna ta kirani a waya.......................tsab ya Fadi abinda ya faru a ranan har hotel Inda Suka sauka a ciki amma bai sanar dasu yasan ana tuhumar Nnenna da kisan Kai ba haka zalika baice musu ya kaita gidan goggoji ba yadai ce sun bar hotel in ya bata kudin mota akan zata koma garin su"jijiga Kai lauyan yayi sannan ya nemi izinin zama ya koma ya zauna.

Koh lauyan dake Kare Wanda ake tuhuma Yana da tambaya Koh shaidan da zai nunawa kotu Hassan bashi da hannu a kisan Abraham?mikewa lauyan yayi ya sake rusunawa kafun ya dawo wurin Lahab ya Soma magana"a ranan da akayi kashe Abraham Wanda ake zargin Yar uwarsa Nnenna obinna ce ta kashe sa,abisa binciken likita sai da aka raunana gawar da duka akai kafun bayan Yan minutes aka daba Masa wuka daidai karfe 1:30 na dare Wanda anan Kuma Mai gadi ya tabbatar ma da kotu karfe 2:21am Lahab ya bar gidan su,kotu in tayi duba da wannan al'amari Lahab bayida hannu a kisan Abraham duba da cewa Saida aka kashe Abraham kafun ya bar gidan su.

Yana karasa maganar Alkali yace Yana da takardan hujjan likita amsawa yayi ya mika aka mikawa Alkali,sannan yaci gaba da bada gasheshen bayani akan babu abinda ke tsakanin Lahab da yarinyar sai abota Kamar yanda yace duba da cewa ajinsu daya a makaranta,haka zalika yarinyar da aka bibiye tushen taa korarta akayi a kauyen su saboda zargin maita da ake binta dashi,Kai a takaice dai an fafata shariya sosai kowa yanason yaga ya kada d'aya, Alkali ya d'aga shariyar sai Nan da sati shida sannan lauyan su mom ya tabbatar daya nemo hujoji masu karfi Wanda zai tabbatar wa da kotu Lahab nada hannu dumu-dumu Koh boye Nnenna,bayan kammala shariyar aka maida Lahab Inda aka d'auko sa don Abbu yayi yayi a sakosa su dawo gida Amma kotu Bata bada dama ba.

Bayan sati shida Zama na biyu,tsaye lauyan su Abraham yake a gefen Lahab daya gama kodewa ya Zama wani iri dashi ya jefo Masa tambaya"shin Koh zaka sanar damu dalilin da yasa kuka fasa kwana a hotel in alhalin Kuma kudin kwana ka biya tun farko"?gyara tsayuwar Lahab yayi yace"saboda a hotel in ba'a Kama wuni sai kwana sannan na jawota ne don na ajeta daidai safiya na maidata gidan su Don ni bansan cewa ba iyayenta take tare ba"

Kana nufin duk abotar ku da ita bata sanar dakai cewa ba iyayenta bane Mr Godwin da matarsa ba"?

"Kwarai Ni Bata sanar Dani ba"

Amma me tace maka bayan sanar dakai cewa ta bugawa Abraham lamp"?cemun tayi ya shigo dakin ta cikin dare Yana kokarin afka Mata shine garin Kare kanta ta buga Masa lamp"ok a lokacin kasan cewa ba yan uwa bane Koh Kuma tace maka menene a tsakanin su"a kufule Lahab yace nace maka bansan bada parents nata take tare ba Saida abin ya faru.

Murmushi barrister yayi sannan ya nemi izinin gabatar da shaid'an sa na biyu, peace ya Kira ta taso tazo ta tsaya gabaki d'aya idanunta a kumbura kallo daya zaka Mata kasan cewa wannan mutuwar ta shigeta ta Soma amsa tambayar da aka jefo Mata,shin akwai wani Abu na rashin fahimta Koh tsana Koh Kara tsakanin Abraham da Nnenna,girgiza Kai tayi sai Kuma hawaye ya cika Mata Ido tasa hannu ta share ta Soma magana a hankali"babu wani Abu a tsakanin su sai dai Kuma Nnenna batason shishige Mata da Abraham keyi Kamar ma ta tsane sa,sosai dai akayi ta fama da shariyar aka Kira mom Dad Jennifer Sarah sukazo sukayita bada shaidan gaskiya da karya akan Lahab bayan kammala nuna hujjojin barrister Solomon jefau ya koma ya zauna,mikewa lauyan Dad yayi ya matso kusa da lahab.
Chapter 82 · 0% Book details