← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 122

Sashe 16

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanke-wanke tayi a kitchen lokacin gari ya fara waye wa 5:30am na asuba saiga Peace ta fito a kofar d'aken kusa dana Nnenna sanye da kayan kitchen, bin falon tayi da kallo sai kuma ta sake kallon Nnenna da kyau, ke wace irin wawo yace ya zakizo ki jika tiles haka da kumfa?

Nnenna kam shuru ta mata don ta rasa me yasa take da bakin jini ne, koh ina taje bata farin jini, karban mopper in Peace tayi ta gyara tiles in falon tare da nuna mata yanda zatayi mooping in kayan falon karta narkawa kayan wuta ruwa.

Tana aiki peace na girki a kitchen, tana gama aikin d'auraya peace ta lafta mata a waje,ta had'a mata da sabulu da omo ga dam a gefe na ruwa.

Tun tana tsammanin gamawa da wuri har d'aurayan ya fara shiga jikin ta, wanki take tun safe tana kallon yanda yara 'yan makaranta keta wucewa daga musulmai har Christian da ma'aikata, har lokacin da Dady ya fita shima ba'a jima ba saiga momy itama ta fita aiki, jennife ma ta fitoh zata makaranta ita da sarah tana sanye da uniform a jikinta, Abraham ne karshen fita, yana fitowa wajen da Nnenna ke zaune ya nufa zama yayi a bakin barandan kamar yanda tayi, beauty kin tashi lafiya Am sorry da abinda na miki daren jiya?

Kala batace masa ba sai mikewa da tayi tana shanya kaya a igiya, shima mikewar yayi sai magana yake mata yana binta Amma taki kulasa, peace dake tsaye tun d'azun a bakin falo sai binsu take da mumunan kallo especially ma Nnenna, tsaki taja da karfi wanda ya jawo hankalin su duka harda Abraham.

Amma baice kome ba ya juya ya shiga motar sa yaja yabar gidan, itama wanki ta cigaba dayi sai kusan 12:00 ta gama sauran omon ta wanke kayanta kala biyu da sukayi datti daman kayan kala hudu ne, uku shayibu ya sai mata da wanda ta shigo gari dashi.

Cikin gidan ta nufa a gajiye direct ta wuce kitchen don yunwa take ji sosai, peace ce tsaye tana had'a lunch, koh kallon Nnenna batayi ba itama bata wani damu ba ganin kula a rufe yasata nufar wajen ta bude farfesun kazane, rufewa tayi da sauri ta bude d'aya kwanon taga taliya ne, rufewa kawai tayi ta had'awa kanta tie a kofi sai kulenta data ibawa naman kazan kadan a kwano, ta fita a kitchen in bata damu da tsakin da peace ke bugawa ba.

Tana shiga d'akin ta ajewa kulen abincin sa itama ta kama shan shayin ta, turo kofar akayi koh excuse babu, d'aga kanta tayi ganin Abraham ne yasata maida kan kasa taci gaba da abinda take.

Shigowa yayi ya zauna a kujeran mirrow hannun sa rike da laidodin kaya, hiii baby yace yana murmushi.

Nuna masa kofa Nnenna tayi da hannu.

Da mamaki yace korina kike Nnenna?

"No fita zakayi don baka nemi excuse nawa ba ka shigo"

Amma ai naga gidan mune koh?

"Na sani koh d'akin momy ne ya dace a nemi excuse "

Ba musu ya mike ya koma bakin kofar ya nemi Izini ta basa kafun ya shigo, direct bakin gadon yazo ya zauna kusa da ita, da sauri ta matsa gefe tana hararan sa.

Sorry yace yana d'aukar laidan ya aje kusa da ita, kallon laidan tayi tare da tambayar sa menene?

Kayane na sai miki masu kyau da kayan amfanin ku na mata?

"Bana bukata"

Saboda me?

"Nawa ya isheni"

Amma menene laifi don Brother ya sai ma sistern sa kaya?

"Toh ai kai ba brother na bane cousin ne"

Amma ai duk d'aya ne koh?

"Ba d'aya bane kowa da matsayin sa"

Nidai kiyi hakuri d'an Allah ki karba"

Kallon sa tayi sai kuma ta tuna in fa bata karba ta wata rana kaya zai gagare ta, amma bata son ta basa kofar da zai na shiga jikinta"OK thank you"tace tana d'aukar kayayyakin ta maida gefe mikewa tayi tsaye hade da ce masa zata shiga wanka.

Ba damuwa ki shiga ki fita ina jiran ki kinga ma saiki gwada kayan na gani?

Wani mummunan kallo da Nnenna ta masa baisan lokacin da ya mike ya bar dakin ba, yana fita da sauri ta bisa ta rufe kofa, laidodin ta bude kayan ta juye akan gado, tana dagawa tana dubawa jeas ne pencil kusan hudu sai t-shirts harda towel da brush da maclen ga shampoo duka, dasu turaru ka, tad'an ji dadi kad'an jera kayan tayi ciki wardrop harda vest da lagies.

Wanka ta shiga tayi brush, tana d'aure da towel ta wanke kayan da ta cire a toilet in ta fitoh dashi a boket, mai ta shafa ta sanya wando tasa vest ta d'aura riga akai, duk wanda ya ganta yasan bata saka brz ba saboda yanayin yanda kirjinta ya fitoh sosai gashin kanta dake tufke koh warware sa batayi ba saboda wahalar kimtsawa da yake bata, boket in ta d'auka cikin jin dadin shigarta na yau don bata taba saka kaya mai kyau irin na yau ba, gashi tana jinta free ba kamar kananun siket ba koh dogon riga wannan wandone har kasa, ga silifas na roba mai flower a kafarta irin na yayin nan akalla zaikai 3k.

Tana fitowa falo tayi kicibis da peace na jera kuloli a daining cikin haushi take binta da kallo itakam koh a jikinta shanya kayanta tayi a waje ta koma daki.

Da yamma lilis dady da jennifer suka dawo, aiko tana dawowa haka ta ringa masifa sai Nnenna ta cire kayan jikinta bazata saka ba saida Abraham ya mata kaca kaca kafun ta natso, sai kuma tace sai Nnenna ta tattaro kayan da ta wanke ta gogesu.

Haba jennifer muna da injin wanki menene nasa ta ta wanke sannan yanzun bazaki bari gobe ta goge ba sai kice yanzun.

Jin abinda dady ya fad'a yasa jennifer fashewa da kuka irin na sangartatun nan a take baban sa ya rikice ya fara rarrashin ta tare da baiwa Nnenna dake gefe umurnin taje ta tattaro kayan ta goge.

Mikewa tayi Abraham ya bita da kallon tausayi, taje ta tattaro shanyan dakin guga ta wuce taje ta fara goge kayan nasu daga ita sai kulenta suke zaune a ciki.

Har dare tana guga karshe ma bacci ne ya d'auke ta a dakin ba tare da ta gama gugan ba.

Washe gari ma da bautan ta tashi haka ta ringa rayuwa a gidan cikin bakin takura na Abraham da jennifer har gwara sarah sau dubu akan momy, ga dady baya cewa kome akan abinda suke mata.

Dady Ya tura ayi bincike akan Nnenna kuma ya samo cikekken bayanai akanta da abubuwan da suka faru da ita harta gudo zuwa gombe, sosai ya shiga shock karfa da gaske mayyar ce, amma bazai iyya kin riketa ba tunda shine kad'ai nata da ya rage.

Kasa fad'awa momy gaskiya yayi don yasan tabbas, zaman Nnenna bazai yuba tare dasu, sai dai ya kira Nnenna ya mata warning akan inta kuskura ya kamata da wani laifi na maita koh na illata wani zai d'auki babban mataki akanta,don nan birni ne ba kauye ba kana kashewa za'a kasheka bare suna Christian a cikin musulmai dumu dumu ta iyye bakin ta.

Kuka take tana gyada kai koh banza ya taimaka mata, tunda ya amince zai rayu da ita a karkashin sa, neman Alfarmar koma wa makaranta ta nema duk da ta sanar dashi ta gama SS 3 Waec ne batayi ba amma tana son ta cigaba da zuwa har lokacin waec yayi.

Ba musu yasa aka d'auko mata result nata a kauyen su, washe gari ya aike Abraham kasuwa ya sai mata kayan makaranta ya kai dinki,yasai mata sabon eye glass mai kyau da tsada, da sauran abubuwan da zata bukata akan zuwa Monday zasu kaita school a mata Interview duk ajin da ya dace a sata sai a sata, don su sun d'auka bata da kokari sosai.

Jennifer kamar ta wura wuta ta shiga jin Nnenna xata shiga school inda take sosai ta haukace wa momy akan ita bata yarda ba wallahi, momy ma ta nuna akan sai dai a sata a govorment school Amma Dady yace ya gama magana.

Wannan abu yama momy ciwo a karon farko dady ya bijirema bukatar ta, amma kuma tasan me zata kulla koh Nnenna ta shiga school in sai taji bata kaunar xama tare da jennifer.

************************
Lahab yau ball suka tafi tun safe bai dawo gida ba, daga ball suka je gidan su adewale da yake iyayen sa sunyi tafiya acan sukayi wanka suka saka kayan sa dukan su, suka wuce birthday party wani school mate nasu,

sai yamma lilis ya nufo gida tun daga nesa ya hango sa zaune, sai da gaban sa ya fadi sanye yake da 3quater na sojoji sai t-shirt baki, yana zaune a bakin get kan kujeran roba.

Ai da sauri yaja ya tsaya shikenan yau dai tashi ta kare, Amma yan gidan nan munafukai ne ace babu wanda zai sanar dashi uncle muzammil na zuwa yau, ya wuni a gida sai aki sanar dashi da yau ai ya kaima islamiyya ziyara.

Ji yayi kamar ya juya Amma babu hali dole tasa ya nufi get in zuciya na duka, Amma san koh nuna alamun ya gansa ma baiyi ba, ya sa hannu zai bude kofar.

Lahab!!!!!!! Muzammil ya kwala masa kira da karfin gaske.

Aiji yayi kamar an tsikare ransa da tsinke, cikin sauri yace"na'am uncle daman wallahi ban ganka bane"

Na tambaye kane lahab ka ganni koh baka ganni ba?

"Kayi hakuri don Allah uncle"

Hakurin uwar ka?ina kaje?

"Uhmmm naje lesson ne gidan su adewale"

Ina takardun?

Kallon hannunsa yayi sai da ya hadeye yawo"uncle nabar takandun a gidan su"

Gyada kai muzamminl yayi, oh watoh boko yafi Arabic kenan?

"Ah ah uncle"

Ok toh me kake nufi naga dai islamiyyar so biyu ake zuwa a sati kai kuma naga a karshen satin ma kaje lesson koh?

"dan Allah uncle kayi hakuri"?

Hakuri?meka mini ai duk abinda kayi kanka kama bani ba, ka wuce muje sallah bazaka shiga gida yanzun ba muje, yace yana nuna ma lahab hanya babu alamun wasa a fuskar sa, da sauri lahab yayi gaba muzammil na binsa a baya har bakin masallaci.
Chapter 16 · 0% Book details