← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 122

Sashe 107

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwance Lahab yake da Rahab a daki sai Hira Rahab ke Masa ya Masa na wancan ya Masa na wannan shima Lahab ya sake jiki sai Hira yake har bacci ya dauke rahab,wayarsa Lahab ya zaro ya kunna ganin karfe 12 na dare ne yasan zuwa yanzun safiya ne Kiran ta yayi da sauri ta d'auka vedio call Suka ringa Hira ta jera Masa yaransa a screen ya kalle su kafun sukayi sallama lokacin har 2 na dare yayi ya kwanta bacci ya dauke sa,washe gari da safe bayan dawowar su sallah Lahab bacci ya koma bashi ya tashi ba sai kusan 10 na safe ya fita ya karya tare da gaida jama'ar gidan.

da yamma ligis Lahab na kwance a falo sai Jin surutan samari yake a kofar gida ba'a Jima ba saiga Mai gadi Wai dandazon yaran dake team nasu Lahab ne suka had'a zuga sunji Hassan Lahab ya shigo kasa amma Mai gadi ya hanasu shiga Koh tsakar gidan,mikewa Lahab yayi ya sauya Kaya ya fito Aiko Yana turo gate in wani irin ihu matasan Suka sake har Saida suka cika unguwan da muryoyinsu Wanda yasa wasu Mata masu gulma fiffitowa su baiwa idanunsu abinci.

Kudi Lahab ya zaro ya mikawa wani babba a cikin su yace a raba Aiko zo kaga Kura shikam tuni ya wuce cikin gida ya barsu Suka gaba gurnanin su suka watse.

Lahab ya zaga cikin dangi sosai babu Inda Bai zaga ba har wajen mama yaje(maman Muhammad) Kuma duk inda yaje sai ya Mika musu wani Abu duk da suna da arziki Amma akace Mai baka yanaso a basa haka Mai arziki baikin kyauta duk dukiyar sa, Adewale yazo wajen Lahab Yana tambayar sa Koh Nabeel yazo wajen sa, amma Lahab yace ah ah baizo ba,Ade yayi yayi dashi akan suje su gaida Inna amma Lahab yace bazashi ba,sai ya zauna sosai yake kewar matar sa don a kalla Suna waya sau biyar a Rana wani lokacin in Bai samu lokaci ba cikin dare ma suke waya.

Satin Lahab daya a nageria ya tada maganar komawa Nan Abbu yace waneshi Bai Isa ba sai ya kammala hutun sa duka amma Lahab yace shikam gaskiya zai tafi Yana da wasa,Mami ta rantse bazai koma ba sai yayi wata biyun nan,anyi auren Shareef a idon Lahab Kuma Alhamdulilah biki anyi an gama lafiya satin Lahab yanzun uku da zuwa nageria,kawai su Abbu suka waye gari babu Lahab ya tattara yanasa yanasa ya gudu basuma San da zancen ba sai da suka ga Bai kwana a gidan ba,ran Mami ya mugun baci bana Wasa ba lokacin da Rahab ya sanar da ita,Kuma ta kudiri aniyar Lahab na kammala karatu bazai cigaba da Zama a wajen ba.

Nnenna Karan kanta Bata san da zancen dawowar sa ba kawai cikin dare ta gansa ya diro ba karamin mamaki Tasha ba,da ta tambaye sa lafiya yace lafiyar kenan kewarta yayi.

Babu Wanda ya Kira Lahab daga gida akan gudun nasa haka zalika shima Bai Kira kowa ba sai dan uwan sa hatta Ade baisan da maganar guduwar sa ba sai bayan ya tafi,Kuma Bai kirasa ba.

Adewale ya kammala hutun sa lafiya ya dawo sun cigaba da karatun su yaran Lahab sai girma suke dad'awa da wayo.

*****************
Yau tunda Nnenna ta tashi takejin zuciyarta na tsinkewa Wanda Bata San dalilin ba, breakfast suke a dinning su biyu sai yaran su dake zaune a falo Suna Wasa,kallon ta yayi yace"Wai wife meke faruwa ne tunda Muka tashi da safe Naga Koh kuzari Baki dashi wanka wannan yau Nina ma yaran Nan gabaki d'aya na ganki lagwas"?gashi yanzun ma tunda muka zauna breakfast na kusan tada plate nawa ke Koh spoon biyu Mai kyau bakiyi ba"?Dan ajiyar zuciya ta sauka kana ta zame tagumin dake kumatunta tace"wallahi dear tunda na tashi yau nakejin wani irin faduwar gaba da damuwa Wanda Ni Karan kaina bansan dalili ba"?

Uhmmm toh Allah ya rufa asiri kinsan wani lokaci shedan ma na haka sai ya saka maka faduwar gaba"gaskiya ne amma wallahi na rasa peace of mind Ina ji Kamar wani Abu na Shirin faru..........."kul karki Soma babu abinda zai faru damu sai Alkhari"gyada masa Kai tayi Suka cigaba dacin abincin badon hankalinta ya kwanta ba mikewa Lahab yayi bayan ya goge bakin sa ya dau school bag nashi Yana Mata sallama Harya sa hannu zai bude kofa yaji anyi knocking,budewa yayi da mamaki Muhammad ne da gani Kuma hankalin Sa a tashe yake"Lahab kana da labarin abinda ke faruwa kuwa? da Kai kuwa a nageria"rass rass haka gaban Lahab ya Fadi amma yayi ta maza yace"subhanallah meke faruwa"?

rike baki Muhammad yayi yace"Ina wayar ka"a fusace Lahab yace wani irin Abune haka in zaka gayamin ka fadamin Ni wayata tun daren jiya da aka damen da Kira cikin dare na kashesa Kuma yanzun makaranta zani"uhmmmm wayar sa Muhammad ya zaro ya daddanna kana ya mikawa Lahab,amsa Lahab yayi sai Kuma ya zare Ido sosai Yana kallon screen in, a hankali ya koma baya-baya ya Mannu da jikin kofar falon wani irin zufa na karyo Mata a hankali ya Soma furta kalmar innalilahi wa'inna'ilahu raji'un,tare da sulalewa ya zauna Muhammad ya karasa Masa"Adewale ka cuceni"shine kalmar da ya Fara fitowa daga bakin Lahab ransa yayi mugun baci har jijiyoyin fuskarsa Suka tashi baro baro.

da gudu ya fito daga flat nasa ya nufi nasu Lahab hannun sa d'auke da waya cikin tashin hankali turus yayi ganin Lahab zaune dabas a kasa ga Muhammad a tsaye a kansa,nufar Lahab yayi Yana cewa"mun shiga uku Lahab kasan cewa................kasa karasa maganar yayi saboda wani irin mugun kallo da tunda yake da Lahab bi taba tsammanin Yana da irin Saba,shiya maka Masa tare da mikewa ya cakumo kwalarsa da karfi..........................................

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

Adewale meyasa zakamin haka meyasa"sakeni Lahab muyi magana wallahi kaji na rantse maka Ni bansan yanda akai hotunan Nan suka fita ba"in baka sani ba toh waya fitar kenan waya fitar kenan"?Kaine dai ka d'auke hotunan Nan Kuma a wayar ka suke wazai fitar"?

Muhammad sai kokarin kwace kwalar Ade yake a wuyan Lahab amma Abu ya gagara Jin ihun tsawar Lahab shiya saka Nnenna saurin fitowa,da gudu ta nufesu tasa hannu tana ma Lahab magana akan ya sake Ade amma Lahab yaki data shiga tsakani suma bangajeta yayi harta kusa faduwa"don Allah Lahab ka sakeni a zatona jimawar da mukayi Koj Wani akace maka nama haka bazaka yarda ba Kuma zaka tsayamin akan gaskiya ta amma yau Ni nake rantse maka ka kasa yarda har kana rikemin kwana"Ade yace cikin damuwa don shi yasan dai bbu Wanda ya nunawa hoton Nan.

Jikin Lahab yayi sanyi a hankali ya sake Masa kwalar sa ya koma ya zauna anan bakin baranda ya rike kansa"tambayar abinda ke faruwa Nnenna tayi? wayar hannun sa Ade ya Mika Mata,amsa tayi"hoton sune ita dashi lokacin da take da ciki Suna tsaye a tsakar gida sai Kuma wanda aka d'auka a hospital ranan da ta haihu duk su biyu da yaran su, sai Kuma Wanda aka d'auka Suna zaune a falo Koh wata biyar hoton baiyi ba, posted nasu akayi tare da dogon sharhe Kamar haka"shahareren dan wasan kwallon kafan Nan Wanda akafi sani da Hassan Lahab mazaunin America a yanzun an gano yana tare da wannan makashiyar Nnenna obinna tsohowar class mate nasa Wance aka taba kamasa akanta na zargi, Suna zaman dadiro harda yara biyu ba tare da sanin iyayen su ba.

Kuka Nnenna ta sake da karfi shikenan abinda suke gudu ya faru amma Koda sunan Wasa Bata taba tunanin ta wannan tsigar asirin nasu zai tonu ba"matsowa yayi kusa da Lahab tasa hannu ta rike nasa a hankali ta Soma magana"Lahab ka sani daman irin wannan Rana na zuwa duk boye boyen mu Koh guje gujen mu amma nima banji dadi datazo ta wannan tsigar ba,amma ka sani dai-dai da Rana daya ban taba kawowa raina Ade zai aikata Abu makamancin haka ba,wata kil wani ne ya aikata hakan saboda ya shiga tsakanin ku karfa ka manta ba kowa keson ka da Ade ba bugu da Kari Ade ya riga ya zamo wani bangaren naka bai cancanci haka ba"

Tsungunawa Ade yake da niyar yi zai baiwa Lahab hakuri da Sauri Lahab ya tarosa hade da rungumarsa Yana bubbuga bayan sa a hankali yace"kayi hakuri abokina raina ne kawai ya baci amma tabbas nasan Wanda ya aikatamin wannan Abu Kuma na Jima da gane sa, fuska biyu garesa shiyasa na yakiceshi a cikin rayuwata amma wannan Karo Zan basa mamaki"da Sauri Ade yace"waye kenan"girgiza Kai Lahab yayi ya sake Ade ya Shiga cikin falon binsa sukayi a baya zaune suke dukan su Muhammad da kansa ya kulle tambayar su yayi daman ba aure Lahab sukayi ba?,anan Adewale ke warware Masa kome sosai yayi mamakin abinda Lahab yayi Kuma sosai ya Masa Nasiya akan rashin Jin da yake dakin Jin maganar magabatan sa,haka zalika ya basa shawara akan boye boyen Nan ya Kare ya tinkare iyayen sa da maganar kawai Kai tsaye ya fad'a musu gaskiya.

Amma Muhammad kana ga babu matsala kuwa kasan fa ita Nnenna zargin kisane akan ta komawar su nageria babban hatsarine fa gwara ya zauna anan maganar tayi sayi kafun Nan,hakaKo akayi Muhammad sosai ya musu wa'axi jikin Lahab yayi sanyi sosai haka itama ta shiga damuwa wayarsa Kam Sam Bai kunna tanaba daren ranan Koh bacci Bai samu ba washe gari ya tashi da zazzabi Mai zafin gaske da ciwon Kai duk yanda taso suje clinic ki yayi yace bazashi ba.
Chapter 107 · 0% Book details