Sashe 91
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
juyawa yayi zai shiga gidan da Sauri ta kirasa cikin dan murmushi tace ga number ta Inka Isa Koh zaka kirani sai muna gaisawa?"la Aunty mubeena Ina da number ki insha Allah Zan kiraki sai Kuma ya d'aga Mata hannu ya shiga gidan, kuka mubeena ta Soma tana tafiya tana share hawaye,Allah sarki uwa uwace duk irin haushin Lahab da Mami keji kasa hakuri tayi tazo rakiyar sa Saida Suka iso airport kafun ta d'aga hannu ta maka Masa dundu Mai zafi Wanda ya sashi Kara Yana kallon ta magana ta Soma kamar haka"watoh Lahab harka Kai matsayinda zaka min abu inji haushi Kuma ka kasa bani hakuri Lahab zaka sa kafa kabar kasar Nan da haushin uwarka Kuma kana tunanin zakaci nasarar abinda kake bukata"
Rungumarta yayi yace"mamina Nina San kin Jima da yafemin Kuma sai hadamun fuska kike shiyasa na kasa baki hakuri"zungurar sa tayi yace"Koh da wuka nake rike dashi Lahab zaka kasa bani hakuri,girgiza Kai kawai yayi ya nemi yafiyar kowa daga danginsa sukayi sallama ya nufi jirgi, Ade dake gefe Suna buga rikici da papa don papa badon kudinsa daya kashe da kamawa Ade gida acan dayayi ba aradu da Ade bazai tafi da Lahab ba baisan da zancen tafiyar ba Saida ya hade da Yan gidansu yanzun a airport ganin Lahab ya nufi jirgi shiyasa Adewale mikewa yabi bayan sa bai damu da masifar papa ba, tunda sunyi sallama da mahaifiyarsa.
tunda Lahab ya juya Yana tafiya Bai Kara waigowa ba Koh sau daya Harya shiga jirgi shigowarsu Kenan ya Soma rarraba Ido Yana neman sit Inda Nnenna ke zaune don shu'aibu yace Masa yabar kome na tafiyar Nnenna a hannun sa har cikin jirgi zaisa a kaita amma Bai ganta ba saboda girman jirgin gajiya yayi da dubawa ya juya zai koma waje amma aka hanasa fita Ade kam na zaune baisan dawan garin ba don sit nasu ba daya da Lahab ba Yana gaban Lahab,Jin rikicin Lahab da ma'aikatan jirgi ya Sasa mikewa yazo Yana tambayar ba'asi da Kuma dalilin dayasa Lahab keson fita waje,kin basa amsa Lahab yayi ya koma ya zauna a filin sa shima Ade komawa yayi ya zauna.
Rumtsa Ido yayi da karfi gaske wannan shine karonsa na farko a jirgi Kuma zaiyi tafiya har wata kasa gashi baida tabbacin Nnenna na cikin jirgin.
Jirgin su Lahab ya sauka lafiya klau a babban birnin London cikin dare, passenger ne Suka Fara fita d'aya bayan d'aya mikewa Adewale yayi Yana kallon Lahab ganin baiyi niyar mikewa ba kala baice ba ya d'au akwatunan sa ya fita waje mikewa Lahab yayi ganin mutane nata fita,da mamaki yaga an bude private sit dake ciki saiga ma'aikaciyar cikin jirgin ta fito tana rike da hannun Nnenna waro Ido yayi da Sauri ya karaso wajen cikin farin ciki ya riko hannun ta da Sauri ma'aikaciyar tace"Kai ya haka ya zaka kama mata hannu?kafun ma yace wani Abu da Sauri Nnenna tace"shine Wanda nace ki dubomin kikace baki ganesa ba,au toh gata shine abinda tace tana Mika Masa jakunkunan Nnenna da shu'aibu ya Mata shopping sosai.
Sauka suke a steps na jirgin a hankali sunyi wani irin masifar kyau sanye take da abaya baki shi Kuma yana sanye cikin kananan Kaya jakunkunan su na hannun ma'aikatan Suna sauko musu dashi,Baki sake Ade yake kallon su daga inda yake tsaye Yana salati cikin tashin hankali ganin Nnenna tare da Lahab a London bai taba kawowa ransa wannan abun ba.
Juyawa yayi ya wuce ba tare da ya jirasu ba dayake Yana da address in Inda zasu sauka Hawa taxi kawai yayi ya Mika Masa address in,Lahab Kam Yana rike da hannunta Suka fito cikin airport in ya tare taxi shima ya hau ya d'ura kayansu Suka d'auki hanya,har sunyi nisa yace wa bature ya kaisu Inda zasu samu abinci watoh restaurant,abinci Lahab yayi order harda laidan Abraham, unguwa ne Mai kyau Mai d'auke da ginunuka iri d'aya akallah kofa-kofa yakai sama da hamsin Kuma Hawa uku,sauka Lahab yayi ya ringa dudduba number floor har Allah yasa ya samo numbern dakin nasu a Hawa na uku suke,nufar wajen Nnenna yayi Yana korafi a ransa wannan ai sai wata rana ya manta dakin nasu ace Hawa har uku dakuna sunkai sama da hamsin amma ace kome iri daya kamo hannun Nnenna yayi yabar jakan nasu a kasa ya Soma haurawa upstairs in da ita Suna taka steps in a hankali Hawa na biyu Suka hau gabaki d'aya taji ta gaji Zama kawai tayi tace zata huta,komawa kasan yayi ya dauko musu kayan su ya hauro dashi har lokacin tana zaune a matakalan,aje kayan yayi ya ciccibeta duk yanda tayita cewa ya sauketa ki yayi Saida ya kaita har kofar dakin su hannu yasa ya bude dakin ya shigar da ita,falone madaidaici sai wasu steps guda uku Wanda Koh ba'a fada Masa ba yasan kitchen ne a wajen ai dakuna guda biyu a falon sauketa yayi ta zauna akan kujera shi Kuma ya koma waje ya dauko bags nasu,kome akwai a falon TV fridge AC abubuwan more rayuwa duk akwai dakin dake hannun hago ya bude Adewale ne zaune akan kujera ya zuba tagumi Yana kallon gefe bude kofar baisa sa ya juyo yaga Wanda ya buden ba shima Lahab rufewa yayi ya bude na dama alamu shine dakin sa.
Ajeta yayi a bakin gadon kana ya aje akwatunan su a gefe,Zama yayi a bakin kujeran dakin ya zare takalmin Boot dake kafarsa ya zame black socks in duka kayan sa ya cire ya rage daga shi sai wando dogo toilet ya shiga yayi wanka da Alwala ya fito bude jakansa yayi yadatu darduma tare da kallon Nnenna dake zaune a bakin gado Yana cewa ta jirasa bari yayi sallah ya kawo musu abinci"gyada Kai tayi tace"so nake nayi wanka tukun na"ok yace ya tada sallah yana idarwa had'a Mata ruwa yayi a toilet kayanda zata sa tare da nuna Mata ma ajiyinsa,fita yayi falon ya d'auki laidan abinci dakin Ade ya bude ya aje Masa laida daya baiyi magana ba ya sake fita.
Kitchen ya shiga shima kayatance Mai dauke da dinning a ciki irin tsarin turawa haka yake plate ya d'auka da cup ya fita dakin nasu ya Shiga har lokacin bata fito wanka ba bude akwatinsu yayi yadau maganinta yasa Mata a cikin fresh milk daya sayo musu, yasa nasa maganin ya aje juye abincin yayi duka ya zauna ya Soma ci Sam abincin Bai Masa dadi ba saboda dandano daya banbanta da cimarsa sosai amma saboda gayu haka yake taci,bude kofar toilet in akayi Nnenna ta fito da towel tana tafiya tana tattaba waje dakatawa Lahab yayi ya daina motse harta shigo dakin Kan gadon ta zauna tana tattaba kayan da ya aje Mata d'auka tayi sai Kuma ta Soma warware towel in jikinta da Sauri yayi gyaran murya itama a rikice ta Kara tamke towel in da Sauri ta nufi toilet Wai zata koma kawai ta gwaro da jikin wardrobe Kara ta sake ta durkusa tana dafe goshinta.
da Sauri ya mike yazo ya Kama goshin Yana ta masifa wai ai zata hallaka kanta a banza fita yayi a dakin ya jirata tasa kaya kafun ya dawo ciki Suka ci abinci dayake darene kwanciya sukayi tana Kan gado Yana Kan kujera.
Washe gari da safe,har 9 Lahab na bacci tunda ya koma bayan sallan asuba Bai tashi ba Nnenna ta farka amma saboda kartayi motse ta tadashi ya sata kin tashi tana kwance akan gadon,bubbuga kofar akayi da karfi,shiya farkar da Lahab mikewa yayi Yana tsaki ya nufi kofar budewa yayi Ade ne tsaye cikin Shirin tafiya makaranta Yana bin Lahab da mugun kallo sai Kuma yace"zakaje ne Koh nayi tafiya na"?da mamaki Lahab yace"haba dan Allah jiya fa Muka diro kasar Nan ka Bari gobe muje school in mana"juyawa Ade yayi yace"course namu daban Kai zaka iya Zama sai goben"da Sauri Lahab yace dan Allah d'an jirani Ina zuwa"?,dakin ya shiga da Sauri ya Wasa ruwa ya sanya Kaya da Sauri ya dau school bag NASA ya fito,a falo ya samu Ade na zaune Yana jiran sa kallonsa yayi yace"Wai Ade haka Zan tafi bazan karya ba"nuna Masa kitchen da hannu Ade yayi da Sauri ya Shiga bude abinci yayi sai Kuma ya dauka da gudu ya nufi dakin su aje Mata yayi a kusa da gado ya kawo ruwa ya aje Yana gaya Mata ya tafi school, sanan ya fito a dakin kala Ade baice ba Suka wuce makaranta.
Ranan Lahab na farko a makaranta ta Masa dadi don yaga chanji da school nada nada sosai anan babu takura babu tsawa Ade ya wuce department nasu yayin da Lahab ma ya wuce nasu dan Adewale zai karanta engineering me yayin da Lahab xaifara karanta pharmacy daga zuwan Lahab class har yayi abokai guda uku yayan turawa,biyu maza d'aya mace,Suna fita a class dayan yaja Lahab wajen training na football nasu a school babu kauyanci Lahab ya shiga cikin yaran turawa ana buga ball dashi,cikin sati guda Lahab ya sassaba da mutane da yawa haka zalika abokan sa masu son karatune shiyasa Koda yaushe yake cin serious Kuma ba laifi sosai suke ganewa gashi yanzun ya Zama daya daga cikin members na yara masu kwazo wajen football ga kyakkyawan horo da suke samu daga coach nasu haka zalika Yana yabawa da gogarin Lahab.