Sashe 85
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***************
Bayan sati d'aya Alhamdulilah jikin Nnenna yayi sauki sosai amma har yau Bata dawo hayyacinta ba gashi idanun nata yadan washe daga jini-jinin zuwa fari tass amma Bata tashi ba jinya dai ake Mata sosai goggoji ta koma cikin gombe tabar Lahab a kauyen su,duk sati faruq na zuwa ya dubasa sannn Yana kawo Masa labarin irin Neman sa da ake Kamar me,dayake garin babu Network Sam tsawon sati d'aya kenan isheshen bacci Lahab baya samu sosai,zaune yake a kusa da ita hannunsa d'auke da kwaryar no-no Wanda aka dama da magani,iba take a ludayi Yana sanya Mata a baki a hankali in Kuma ya gangaro sai ya dau tsumman gefensa ya goge mata Inda ya gangaran a haka ya samu tadan sha kad'an,sai Kuma yaga ta Soma tari sosai tana kwarewa mikewa yayi ya dagata zaune ya jinginar da ita take ta Soma kwarara amai sosai take aman bakikkirin, kaman bakin Mai sosai tayi aman duk ta bata jikinta ta bata Masa jiki babu kyankyami ya Kamata harta gama kafun a hankali ya maidata kwance ya mike yadau babban tsumma ya goge wajen ruwa ya ibo ya wanke abinda ta batan ya Shanya ya had'a da kayan jikinsa ya wanke kayan jikinta matar malam ne tazo ta canja Mata don malam yace haka zatayi tayi ta aman har sai ta dawo aman abinda tasha wato in tasha no-no tayi aman nono.
A kallah Lahab yakai wata yanzun a kauyen Suna jinyar Nnenna Kamar kullum Yana zaune kusa da ita Qur'an ne a hannun sa Yana karanta mata,Kamar a mafarki yaga tana dan motsa hannunta Bai wani yi mamaki ba tunda dai ta Saba motse kawai dai Bata hayyacinta ne,sai Kuma yaga tana d'an bubbude idanunta harta budesu tar a hankali ta Soma magana Wanda yasa Lahab rufe Qur'an in ya matso kusa da kunnen ta Yana sauraron abinda take cewa Jin yanda take Kiran sunansa yasa sa damko hannunta jikinsa har rawa yake yake ce Mata"Nnenna ki kalleni ganinan kusa dake kinji Labiba"?
Hawaye ne ya Soma bin kumatunta da Sauri tasa hannu ta daura a jikinsa tare da jingina a kafadunsa tana kuka take cewa Lahab bata gani ya Bata glass nata da Sauri ya mike tsaye Jin tace bata gani kuka ta fashe dashi itama ta Mike tsaye tana lulubar hannnun sa kamo hannun nata yayi da Sauri ta damke hannun har tana kokarin faduwa na rashin kuzari,kamota yayi Yana cewa ta koma ta zauna amma Ina tace karya tafi ya Barta Dan Allah karya sake barinta"shigowa malam yayi sai Kuma ya tsaya Yana kallon su kauda fuska yayi yace Lahab ya zauna,Zama Lahab yayi itama ta zauna tana rike Masa hannu sai Kuma tambayar da ta jefo Masa"Lahab inane muke waya shigo dakin Nan? bana kallo Lahab bana kallo fa?Ina goggoji ta Miki min glass nawa.
Ki natsu shine amsar da malam ya Bata natsuwar tayi Lahab yadau wulan Fulani dake gefe ya aza Mata akai don gabaki d'aya gashin nata duk sun wargaje sunyi datti,kallon ta malamin yayi babu Wasa a fuskar sa yace"Zan tambaye ki Kuma Ina so ki ban amsa babu karya a ciki abinda Zaki cemin"jikinta har wani rawa take tasa hannu ta rike rigan Lahab da karfi ta gyada Masa Kai"ganin yanda ta rikice yasa Lahab sa hannu ya riko hannunta Yana dan Mata magana a hankali"ki natsu Mana babu abinda zai Miki kawai tambayar ki zaiyi fa"shuru tayi tana Jin abinda malam yake fada Mata.
Koh Zaki sanar dani sunan ki"Sunana Nnenna obinna"ke wace kabila ce"a hankali tace Igbo"toh tambayar da Zan Miki yanzun shine menene halakarki da Mafi'a(secret code)"zaro Ido Lahab yayi sai Kuma yace"haba malam ya zaka..........d'aga Masa hannu malam yayi yace"karka kuskura na sake Jin bakinka a cikin tambayar da Zan Mata karka kuskura"shuru kawai Lahab yayi Nnenna Kam jikintane ya tsoma rawa a hankali ta Soma hawaye sai Kuma ta fashe da wani irin kuka ta koma da baya timmm kakeji ta yanke jiki ta Fadi tayi wani irin sandarewa"salati Lahab ya sake yayi Sauri ya matso gareta ya tallafo kanta Yana Kiran sunan ta amma shuru bata amsa masa ba.
Mikewa malam yayi ya dauko wani magani yazo ya Shaka Mata a hanci saiga jini ya Fara bulbulowa Kamar bakin fanfo Kara Lahab ya sake Yana kuka yana cewa a taimaka Masa karta mutu"Kai ka kwantar da hankalin ka wannan jinin dake fita a jikinta warakane a gunta ka natsu sosai,natsuwa yayi aka maidata Kan shinfidar da ta tashi ,fita malam yayi yace Lahab ya biyo bayan sa bayan sunfita Zama yayi a kasan bishiyar tsakar gidan Zama yayi a gefen sa,magana malam ya Soma Masa Kamar haka"Lahab a gaskiya yarinyar Nan tana cikin gagarumin hatsari bana Wasa ba wanda in aka cigaba da hakan zata iya rasa ranta gabaki daya Dan soyayya ya Fara tasiri a zuciyarta.
Waro Ido Lahab yayi yace"mutuwa fa kace malam dan Allah ka taimakamin kada ta mutu don Allah fa"tabbas Lahab zata iya mutuwa in ba dai wani ikon Allah ba muddin ba'a samu ta dawo hayyacinta ba hakan Kuma bazaiyu ba harsai ta samu wani muharraminta kusa da ita wato miji muddin aka d'aura Mata aure karfinta a kungiyar su zai raunana rauninta zaisa ta samu sassaucin ciwon da take ciki in ba haka ba naman daya wuce cikin tannan zai iya Zama ajalinta......................
*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*
🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀
Waro Ido Lahab yayi yace"malam kana nufin bazata tashi ba sai an Mata aure"?gyada Kai malam yayi yace eh tabbas aure zai rage Mata hatsarin da take ciki, ya Kamata a Nemo Yan uwanta suxo asan abinyi,a hankali Lahab yace"gaskiya malam bansan Inda Yan uwanta suke ba Wanda na sanin ma yanzun nemanta suke ruwa ajallu"anan take yabawa mallam labarin haduwarta dashi sosai malam ya jinjinawa kokarin Lahab tare da Masa Nasiya akan bijirewa dokar da aka kafa musu a gida da yayi ya rage rashin jin magana"sannan daga karshe Lahab yace a daura Masa aure da ita"kallon sa malam yayi yace"gaskiya Lahab bazan iya hadaka aure da yarinyar Nan ba tare da izinin mahaifan kaba gudun Shiga hakkin su a matsayin su na iyaye zasu iyya tuhumata akan waliyin auren ka danayi bada izininsu ba.
Hawaye Lahab ya share cikin alhini yace"yanzun malam sai a barta ta mutu kenan baza'a taimaka Mata ba dan Allah"za'a taimaka Mata Lahab,shine a Nemo iyayenta suzo da kansu kaga yarinyar Nan ba musulma bace auramaka ita sakaka a matsala za'a Yi kaga ita ma bada izininta ba da Sauri Lahab yace"dan Allah malam a daura Mana auren kaga iyayenta sun mutu haka akace a kotu Kuma Yan uwanta bana tunanin zasu taimaka Mata a yanzun"in ma maganar auren ne babu damuwa inta farfado sai na saketa ba shikenan ba in batason aure.
Girgiza Kai kawai malam yayi Yana jinjina yarantan Lahab wato shi bai damu da abinda zaije ya dawo ba gaba gadi yake abinsa"kaga Hassan aure fa ba abin Wasa bane haka zaliki ba'a yinsa da niyar a sake,da kyakkyawar Niya ake da fatan raya sunnah manzon mu fiyayyen halitta dan haka karka sake furta saki da bakin ka"toh malam yanzun haka za'a rufe Ido dan Allah a barta ta mutu ka taimaka insha Allah babu abinda zai faru sai Alkhari"
Lahab kayi kankanta da zaka d'auke wannan kasadar haka zalika Inka aureta Ina zaka nufa da ita daga Nan"?malam saura min Yan watan Ni nabar kasar Nan gabaki d'aya so nake mubari tare da ita insha Allah kafun na dawo kome zai daidaita Zan sanar da Yan uwana Kuma Ina da tabbacin zasu amince"dadin Baki sosai Lahab yayita ma malam shidai malam kallon sa kawai yake baice Masa kome ba haka zalika Bai nuna Masa ya amince da bukatarsa ba yadai zuba Masa Ido kawai Yana kallon sane kawai.
Bayan kwana uku haryau malam baicewa Lahab kome ba shima Lahab Bai sake magana ba ana dai cigaba da jinyar ne har lokacin tana Nan Kamar gunkiya,yau tun safe Lahab yabi yaran dake tafiya kiwo sosai sukayita yawo da shanukai sai yamma likis Suka dawo cikin rugansu gabaki d'aya Lahab ya rame kowa ya gansa yasan a wahale yake daga abincin da yakeci ma ba cimarsa bane kwata-kwata d'add'aure shanukan sukayi sannan ya debi ruwa a kwalla yaje yayi wanka kayan Fulani wando da riga ya sanya sannan yazo ya zauna Yana cin tuwon da matar malam ta zuba Masa,babu abinda zaice musu sai godiya dan malam Koh sisi Bai karba ba na jinyar Nnenna haka zalika Suka juya Suna ciyar dashi.
bayan sun dawo sallan isha'i malam ya kirasa cikin dakin sa bayan ya zauna malam ya Soma Masa magana cikin serious note yace"Hassan in Allah ya kaimu gobe juma'a bayan sallah za'a daura muku aure tare da yaran rugan mu da za'a daura musu gobe in Allah ya kaimu da rai da lafiya Zan daura auren Nan ne saboda halinda yarinyar Nan take ciki Kuma Naga alamun da gaske ne Bata da wani tsayaye haka zalika bai Kamata kaci gaba da Zama anan ba"wani irin fara'a ne ya karade fuskar lahab sosai ya Soma godiya Kamar bakin sa zai taba kasa"haka zalika zaka d'auki yarinyar Nan in taji sauki ka kaita gidan ku ka musu bayani"?
da Sauri Lahab yace"wallahi malam gidan mu bazasu taba yarda da ita ba asalima sai an kaima hukuma ita"shikenan Lahab duk lokacin da kake bukatar sanar da gidan ku ka sanar dani zan tashi da kaina naje na Kara musu bayani"gyada Kai Lahab yayi cikin happy ya mike dakin da aka kwantar da Nnenna ya Shiga kwance take Kamar kullum matsowa yayi kusa da ita sosai yasa hannu ya janye gashin ta daya zubo ta gaban goshinta duk a hargitse hannunta ya Kama a hankali ya Soma Mata magana"Labiba in Allah ya kaimu gobe za'a daura Mana aure zamu dawo karkashin inuwar aure ki yafe min batare da Neman yardan kiba Ina Addu'an Allah yasa auren ya zame Mana Alkhari ya Zama silar warakarki"sai Kuma ya sake hannun nata tare da tofa Mata Addu'a ya fita a dakin.