← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 122

Sashe 116

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aiko Nan code ta cika da mamaki aka hau salati bana Wasa ba ganin waje yaki natsuwa yasa alkali wanke peace tare da bimata hakkin ta ga Kuma tara da Nabeel zai biya ta.

lokacin da aka juyo za'a Kama Alhaji sulaiman wayam kamar walkiya ba'a gansa ba,babban magana su dai police dake gadi basuga wucewar Saba,Nan aka Soma kus kus Ashe Dan kungiyan asiri ne, Nan aka d'auki ummu da Nabeel aka wuce dasu tare da d'aga shariya sai Nan da sati biyu kotu ta bada belin Lahab zai iya komawa gida, mutane da yawa sun babbawa peace kyautar kudi masu mugun yawa ana Kuma tsinewa su Nabeel Sunsa yarinya zaman yari harna shekara biyu cip ba tare da hakkin taba dady shima hankalin sa ya tashi baisan a wace duniya Nnenna ta Shiga ba ya kasa riketa a matsayinta na Yar dan uwan sa Wanda ya turota wajen sa gashi yanzun baisan Inda zai sameta ba,Mami Kam saida aka fitar da ita don kasa fita tayi sai kuka take tana ta Cuce kanta.

Kutu ta bada umurnin kafun shariya ta gaba tanason a durkusar Mata da Alhaji sulaiman da Kuma farida a kotu a duk Inda Suka Shiga Yan Sanda su Nemo su.

Mami Saida ta kwanta a gado gabaki daya ta gama rikicewa sai cewa take ta cuci kanta ta ruguzawa yaronta rayuwarsa ta rabasa da matar sa da yayansa Anya Allah zai yafe Mata kuwa sulaiman ya cuceta,ana ta Bata hakuri shidai Lahab ba uhmmm ba uhmmm uhmm Amma dai yaje ya dubata sai cewa take Hassan ka yafe min ban maka adalci ba a matsayina na uwa shidai kansa a kasa harta gama surutun ta ya mike ya fita.

Yaje wajen Inna gaskiya halinda ya ganta ita da mubeena ya saka sa a damuwa sosai Inna ke fama da ciwo bana Wasa ba asibiti ya chanja musu zuwa Mai tsada yadau d'awainiyar jinyar ta ita dai mubeena duk lokacin da ta gansa sai dai kawai mutum yaga tana kuka.

Cikin sati biyun Nan abubuwan da dama sun faru ciki kuwa harda rasuwar Inna da Kuma kamo farida da akayi amma Alhaji sulaiman ba'a Yi nasarar Kama sa ba haka kotu ta yanke mutu hukunci daidai da abinda Suka shuka Allah sarki mubeena Suma Kan Suma ta ringayi ta rasa dame zataji da mutuwar Inna ne ko da rabuwa da Nabeel dan hukuncin kisa aka yanke Masa ta hanyar rataya shida farida ita Kuma ummu a bisa lura da akai Bata da niyar kashe Alhaji Kuma bata San zai mutu ba a dalilin abinda ta saka Masa, yasa aka sassauta Mata hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai,ga maraicin rashin uwa da uba,lokacin da yazo Kan gawan Inna zai Mata bankwana ba karamin kuka yaci ba ya nemi yafiyar mubeena duk da yaso ace Inna na ra'ayi yazo ya nemi tata yafiyar amma sai ya kasance shine ajalinta,tabbas duniya budurwar Wawa ce shikam tasa ta Kare,duniya tama mubeena zafi jau yayin da Mami ma ke fama da rashin lafiya Wanda hakan ya Hana Lahab komawa London.

Mubeena maraici ya Mata yawa sosai yanzun tana gidan bappa Ado ana fama da rayuwa amma kwata-kwata rayuwar ta baya Mata dadi kwata-kwata tana cikin bakin ciki da damuwa bama Kamar inta tuna saura kwana kaza a rataye dan uwan nata.

Mami taji sauki kana ta tattara ta koma gidan da ta sayawa mahaifiyar ta da yaranta donta rantse bazata Kara Zama a gidan sulaiman ba yaran ma badon badon ba da dangin sulaiman zata mayarwa suje can su karata amma data tuna Y'ay'a dai nata ne Kuma itace gatansu hakan yasa ta rungume abinta,Lahab ya taso da zancen komawa London Wanda Mami ta nuna Bata son hakan ya zauna a Nigerian in ma karatu zai cigaba yaci gaba anan don ita yanzun kaf duniya Babu Wanda takeso a kusa da ita irin Lahab yanda taga ya chanja gabaki d'aya dabi'arsa da halayen sa Suka sauya, hankalin ta atashe yake gabaki d'aya yaron ya koma Kamar wani baki a cikin familyn sa baya sakewa da kowa magana wannan bayayi sai yaga dama yake,Kuma duk a dalilinta ta rabasa da duk wani yakini nasa akanta,da ciwa yarinyar da bataji ba bata gani ba mutunci,yanzun burinta Bai wuce aga Nnenna ba.

*****************
Abbu ne yace bata Isa ba Lahab ya koma ya jona masters nasa yaci gaba da karatu in ma ball inne yaje yaci gaba da bugawa Allah ya bayyana Masa iyalansa,bazasu sake Bari Mami ta karasa shiba a banza, inya zauna a gidan ma hankalinsa bazai kwanta ba tunda kullum tunani yake matarsa na kasar,haka Koh akayi Lahab ya tattara yanasa yanasa yabar NAGERIA shida Adewale don Ade Yama samu aiki a London yanzun Kuma har gobe ba'a ga sulaiman ba.

*********************
BAYAN SHEKARA GOMA
Ihune ya cika cikin stadium in dake kasar Egypt,Wasa ne ake bugawa tsakanin NAGERIA da EGYPT Kuma a lokacin wannan gorzon footballer yayi winning nasu Yan NAGERIA dake zaune tuni suka mike Suna ihu ana Kiran"Hassan Lahab Hassan Lahab gabaki d'aya sunan ne ya cika stadium in Mai girman gaske dake dauke da dandazon Al'umma na kasashe daban daban,jarumi Kuma sadauki shiya bayyana a tsakar filin Yan uwansa bakaken fata kuma Yan team nasu sun dagasa sama ga coach nasu dake ta murna hannun sa d'auke da wani tafkeken cup an Masa Ado a ciki sai walwale yake Golden colour,kowa ka gani indai bakin fatane fuskarsa a washe yake sabanin Wanda yaci kwallon babu alamun fara'a Koh alamun Jin dadi a fuskar sa Wanda jama'a basu damu da hakan ba don Inda sabo sun Saba da wannan dabi'ar tasa,Saukesa akayi a hankali ya Soma tafiya sanye take da kayan ball wando da riga damtsen hannun sa d'aure da shaid'an Captain na Yan Wasa, Yana fita a stadium kwata-kwata mutum ya gansa bazaiyi zaton Yana da wannan kuzari na buga kwallo ba sai dai Yana dauke da manyan 6pack ga muscle nasa masu girma sosai tafiya yake kansa daya sha aski irin na Yan kwallo Yana duke a kasa Bai dagowa bare yaga Yan jaridu dake binsa Suna jefo Masa tambayoyi,matashi ne a kalla bazai wuce shekara 30 zuwa 31.

Zaune yake a cikin hotel Inda aka Kama musu shi kadaine a dakin sa a zaune ya zubawa waje daya Ido,turo kofar akayi amma Bai wani dago ba,wani kyakkyawan matashi brown colour dashi kudi dajin Dadi sun ratsa shi sosai fuskar sa d'auke da farin ciki ya shigo dakin cikin Jin dadi baiyi wata wata ba Koh shakkan Wanda ke zaune fuska a hade ba yazo ya rungumesa da karfi,amma Koh gizau bawan Allah nan baiyi ba.

Haba Lahab yaufa ranan murna ce dan Allah ka sake fuskar Mana friend"?hannu Lahab yasa ya ture Wanda ke bayan nasa har Saida ya kwanta akan gado kana ya dago kansa ya kallesa sau daya ya sake kauda fuskar tasa,shikam dayeke ya Saba da halin Lahab Bai wani Bata Rai ba sai mikewa da yayi ya zare P-cap dake kansa take yalwatancen gashin kansa ya bayyana harma da tabon sallah da yayi radau a goshin sa yayi bakikkirin Wanda ya Kara haska annurin fuskar sa"ya sake kallon Lahab in yace"kaga lokacin sallan mangariba ya kusa ya Kamata ka tashi kayi wanka mu tafi masjid time na wucewa"

Kin mikewa Lahab yayi tsungunawa guy in yayi ya kamo takalmin ball in kafar Lahab ya zare ya zare socks in, wandon ball in waist in Lahab yasa hannu zai zame wani irin damko hannun sa Lahab yayi hankali tashe cikin muryarsa Mai amo da girma yace"Kai Adewale a u out of ur sense"?kyalkyalewa da dariya Ade yayi haryana kwanciya kana yace"toh bagashi nasaka kayi magana ba ace mutum tunda ya tashi da safe banji yace kome ba"?tsaki kawai Lahab yayi ya mike ya Shiga toilet in bai Jima sosai ba sai gashi ya fito da towel lokacin Ade baya dakin.

Sanye yake da jallabiya fari sai hulama fari tas takalmi ya sanya kana ya fita a cikin hotel room in,laft ya hau ya saukesa kasa,fitowa yayi haraban Hotel in gabaki d'aya larabwa ne ke shawagi a wajen duk Inda ya wuce sai kaga ana nuna sa da hannu Koh ana kallon sa masallaci ya shiga anan ya hadu da Ade a ciki.

Bayan an idar da sallah har mutane sun watse lahab Bai fita ba hakan yasa Ade tashi ya fita sai da akayi isha'i kusan karfe 8:00 na dare lahab ya mike yabar masallaci,Yana Shiga cikin dakin nasa ya samu Ade zaune agaban system Yana dannawa amsa Masa sallamar yayi bawai don yaji sallamar ba sai sanin da yayi yayi kafun ya shigo dakin, Kwabe jallabiyar yayi ya kwanta akan gado,ga abincin Kanan ninaci nawa"Ade yace kala Lahab baice ba Kuma bai Mike ba shima Ade bai Kara magana ba har kusan 9:00 na dare Suna dakin bawai Hira suke Koh wani abuba ah ah Lahab na kwance Ade na aiki a system,d'an d'ago kai yayi ya kalli Lahab kana yace"Wai friend kasan gobe zamu bar kasar Nan Koh pls wannnan Karo kabi Yan team naku ku koma NAGERIA Mana shekara da shekaru ka bar kasa, Kai an zuba maka Ido ma bakasan anayi ba"

Shuru Lahab yayi again amma ya Kara tamke fuskar Nan tasa tamau Babu Koh digon fara'a"maganar gaskiya nefa Lahab wannan Karo ya Kamata ka d'aure muje naija Mana Kai baka gajiya da zaman London da sauran wasu kasashe amma baka tuna kaifa cibinka a naija yake"?karkaga shuru da Mami da Abbu Suka maka kazaci Koh Basu damu da Kai bane Koh basa sonka a kusa dasu Dan Allah ka musu adalci mana"

"Adewale gaskiya bazan je naija yanzun ba daga Nan Libya Zan wuce"da mamaki Ade yace"Libya Kuma Lahab wani wasan kake dashi ne a can don Ni na gaji da London Nan so nake na leka nageria"?MAXHEAL pharmaceutical's(Libya)Ltd, industry akwai wasu pharmacist da akeso nayi aiki dasu acan Suna so mu had'a hannu ne da industry nasu akwai wasu magunguna da sukeso su bugane"gyada Kai Ade yayi cikin happy Jin yanda Lahab yayi dogon magana yau kana yace"toh Allah ya bada sa'a amma Ni gaskiya Ina ga Zan wuce London daga Nan Zan wuce naija"?
Chapter 116 · 0% Book details