← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 122

Sashe 68

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Motar umaima ne yayi parking bude kofar tayi ta sauko tare da daukar school bag nata ta rataya Yi tayi Kamar Bata gansu ba ta Kama hanyar shiga ciki,baki sake sadeeq yake binta dashi don gaskiya tayi mugun rame Masa sosai ta Kara haske Kamar dai maijin yan gaskiya Alhalin Kuma damuwa ce kawai ke cinta,ai ganin ta giftasu yasa sa binta da Sauri yasha gaban ta cikin damuwa yace"umaima lafiya kwana biyu bana samun ki ya jikin"?a gajarce tace lafiya da sauki sosai"sai Kuma ta yunkura zata Kara step da Sauri Kuma ya sake tareta haba umaima ya Kamata mu samu waje mu zauna akwai maganar da nake so mu tattauna dake ne"?

Shekeke take kallon sa tace"yanzun dai makaranta na fito Kuma Banda isheshen lokaci bazan iya magana da yawa ba"da saurin sa yace toh shikenan amma dan Allah meya faru Inna Kira wayarki Baki d'auka daga baya Kuma na jisa a kashe na shiga damuwa sosai wallahi"wayar ce ta Bata ban ganta ba shiyasa"da mamaki yace haba umaima in waya ya Bata bazaki d'au Koda na muneera bane ki sanar dani in yaso na Aiko Miki da kudi kisai wani"wani kallo ta Masa a fakaice,Wai ya turo kudi ta sai sabo Ina shi Ina saya Mata wayar da take rikewa tunda ya kasa had'a kayan auren azo a gani"ka Bari kawai Abbu yace nabar maganar wayar zai saimin sabo"ah ah umaima Nina dace Dana saya Miki,yanzun dai duk ba wannan ba so nake muje mu samu waje kiban Koh 10 minutes ne muyi magana akan programs Inda zakiyi anan gombe da Kuma kudaden da Zan Baki na gyara da dinki"shuru ta Masa Saida ya gama maganar kafun tace"basai ka kashe kudinka ba na gode duk abinda nake bukata an riga an tanadar mini dinki ma na riga na Kai maganar programs Kuma guda uku zanyi Kuma duka ango baya zuwa so ba bukatan ka sani tana karasa maganar ta zagaye sa ta wuce abinta har lokacin Yana tsaye Yana kallonta Harta bude kofa ta shiga ta maida ta rufe.

Lahab dake tsaye a bayan su kad'an kallon su kawai yake Bai zakud'a daga wajen da sadeeq ya barsa ba,juyowa yayi ya dawo wajen da Lahab ke tsaye yace"Wai Lahab akwai abinda ke faruwa ne Koh yake damun umaima"?kafada Lahab ya d'aga Masa irin shima Bai sanin Nan ba,karban number wayan sa sadeeq yayi kafun ya tafi.

Komawa cikin gidan Lahab yayi direct ya nufi kitchen abinci ya Iba a plate shinkafa da Miya sai cabbage Zama yayi akan dinning Yana ci,goggoji ne ta fito daga sashen Addayiya d'auke da kwanuka masu datti tazo zata shiga kitchen ganin Lahab a dinning yasa ta tsayawa Suna gaisawa tambayar ta labarin d'anta yayi da jikin sa tace Masa da sauki harma an basa Mata a garin su sosai ya Taya ta murna harda tsokana Wai zata Zama uwar Miki Banda sawa surkuwa Ido"da Wasa da dariya ta wuce kitchen.

Bayan isha'i zazzaune suke gabaki dayan su a falo Abbu ya karkato su dukan su,sai dai har yanzun umaima da mamu Basu fitoba,wayarsa dake gefe ya d'auka cikin bacin Rai ya Kara a kunnesa Saida ya kusa tsinkewa mamu ta d'auka"keda yarki ku fito yanzun Nan maza kafun na Bata muku rai"Bai jira abinda zatace ba ya kashe wayar sa, ba'a dau lokaci ba saiga Mamu da umaima sun fito Zama mamu tayi a daya kujeran Kamar yanda ummu da Abbu da Addayiya ke Kai umaima a kasa ta zauna,Anwar Shareef uzaifa ku fita compound ku bude booth na motar dana shigo da ita akwai Ghana must go manya guda uku kowa ya dau d'add'aya ku shigomin Nan dashi,mikewa sukayi da Sauri Shareef sai zumbura Baki yake Yana hararan tagwaye dake zaune su ba'a ce musu suje ba.

Shigo da kayan sukayi Suka aje a tsakiyar falo umurni Abbu ya Basu su bude bags in su fiffito da abinda ke ciki,zannuwa ne manya manya masu tsada hadaddu da lufaya lace harda materials a daya Ghana must go in dayan Kuma shadodene tirim da hula da takalmi sai Kuma daya bag in dake d'auke da zannuwa colour uku Amma sun Kai turmi hamsin a ciki,kallon Addayiya yayi yace ta xabi turmin zani a cikin bakko dayan da bana anko ba matsowa tayi ta xabi zanuwa masu kyau kala uku Abbu yace Mata ta Kara Amma taki tace wannan ma ya isheta Allah yayi albarka itakam zanuwa ai Wanda take dasu ba'a dinka bama yawane dasu gasu can make a wardrobe.

Mamu itace na biyun zaba kala bakwai ta d'auka harda less dasu materials ta hada,sai ummu ita Kuma tadau kala biyar,anko abbu yace muneera ta zulaihat suzo su d'auka duka kala ukun Suka d'auka Koh wanne d'add'aya sai lufaya da Suka d'auka cikin bakko su Mamu da gyale da takalmi,sauran ankon Abbu yace su d'auka su rabawa Yan uwa gida gida kafun bikin su tabbatar sun kaiwa su nanne nasu gobe goben Nan sai Anwar ango kala goma Abbu yace ya d'auka shadda dasu boyel sauran yaran Suka daddauka Lahab Saida yadau kala biyar biyu nasu Adewale uku nasa,umaima ki Kira goggon ki na tura Mata kudi saikuyi magana zata Miki order Kaya daga Kano za'a dinka Wai a Shan don haka saiki kirata ki gaya Mata kalan kayan da Zaki saka a biki da Wanda za'a Kara Miki ta waya,sannan wa'innan Kuma Haleema kidau goma kema haka ummu sai ku baiwa Addayiya sauran zata rarrabawa kawayen ta Kuma haka sai kudin dinkin daya Basu Amma Anwar yaki karba shida Shareef sunce zasu biya a aljuhun su, Yana karasa maganar ya mike yabar falon Addayiya na binsa da sanya albarka.

Mikewa Lahab yayi ya dau shaddan ya Kai dakin su ya aje wanka yayi ya kwanta,washe gari a makaranta sunyi Math's da chemistry dayake sunada paper uku ne harda Islamic aka had'a musu,dayake makarantan basa bada paper a rarrabe sai an gama CA duka suke hadawa gabaki d'aya a raba a Rana daya.

Bayan ya dawo gida da yamma sadeeq ya kirasa tare da rokon sa akan ya fito wajen gate don baison shiga gidan sako zai basa ya baiwa umaima zai wuce bauchi ne,bayan ya fito kwalin waya ya Mika Masa tare da rokon sa akan ya taimaka ya baiwa umaima sannan dan Allah ta kirasa,ba musu ya karba hade da Masa alkawarin insha Allah zata kirasan,bayan wucewar sadeeq cikin gidan Lahab ya dawo har dakin umaima ya shiga hannu yasa ya tura kofar dakin nata zaune take cikin kayan bacci wando da riga sai dai ba Mai bayyana tsiraici bane Yana da duhu da laushi,kanta d'auke da holan bacci rike take da wayarta Kiran iPhone 11 chatt suke da goggon ta sumayya da Abbu yace ta nemeta suyi magana hotonan materials da zata sai Mata dasu purse da sauran surutun da zata saka a program's take turawa,taji an turo kofar a tunanin ta muneera ce Koh zulai don Mamu bata cika shigowa ba saidai ta kirata ita taje ta samesa hakan yasa bata bar abinda take ba har Lahab ya shigo dakin Zama yayi kusa da ita yasa hannu ya karbi wayar hannunta Yana jujjuya wayan hade da kallon ta.

Mika Masa hannu tayi fuskarta babu walwala tace"ka bani wayata baka ga Abu Mai muhimmaci nake bane"?eh Naga abinda kike amma fa ki sani duk muhimmacin sa baikai sadeeq bakoh"?

Mikewa tayi Rai bace zata bar dakin da Sauri shima ya mike ya Isa kusa da kofar da Sauri ya rufe hade da zare key in ya rike a hannun sa yace"umaima zauna magana zamuyi dake"hararan sa tayi tace Kai asuwa da Zan tsaya na saurare ka kaga nifa banson damuwa yanzun"hhh bakison damuwa nidai yanzun kawai ki zauna muyi magana malama"Zama tayi tana kallon wani direction daban"umaima Zan fada Miki gaskiya duk da da ciwo amma fa ki sani kaf duniya babu masoyin ka sama damai fada maka gaskiya Zan tambaye ki tsakanin ki da Allah umaima meyasa Kika chanjawa sadeeq"?

Shuru tayi bata basa amsa ba har lokacin bata Kara kallon sa ba"umaima tambayarki nake meye faru a tsakanin ku har Zaki Masa karya kice wayarki ya bata Alhalin Kuma gashi a hannunki kin Sasa ya sai Miki wani haba umaima duk wannan na menene"?Koh akan kayan auren ne kema Bai Miki ba"?hawaye ne ya cika Mata Ido a hankali tasa hannu ta goge wa'inda Suka zuba Mata cikin shesheka tace"haba Lahab ya zanyi da Raina ne Taya za'a ce sadeeq zaimin Kaya haka a ganina Yana da kudin da zaimin fiye da hakan amma ya kasa"toh ke umaima yanzun abinda ya dameki shine kankantan kayan?a tunanina babu kayan da za'a Miki ya d'aga darajan ki bayan Wanda Kika saka a gidan Nan sannan kinsan dalilin sa nayi Miki kadan inne"?kuka ta fashe dashi tana magana"Ni duk ba kankantan kayan bane yafi Bata min rai Kamar d'aukan kayan da akayi a waya aka had'a da hotona ana yadawa a online Wai duk girman kaina ga lefen da aka min,sannan haka maganar yake ta yawo a school namu abin shiyafi mini ciwo wasu kawayena ma don su tabbatar yasa su zuwa da sunan kallon Kaya,amma Basu samu kallo ba don Abbu yahana a fitar,shine suke cewa Wai kunya ya Hana a fitar jama'a su gani"

girgiza Kai kawai Lahab yayi yace"ke dai umaima sai kace yarinya karfa ki manta yanzun fa 25years kike dashi Amma kin kasa magance dan matsalan Nan"ke Banda abinki yanzun a tunanin ki in sadeeq ya Miki wannan Kaya har abada bazai Miki Wanda ya fisa bane Nan gaba karfa ki manta Mata da yawa sun samu kayan aure na bugawa a jarida amma auren baiyi lastic ba meye amfanin sa,ba yawan Kaya bane aure ah ah albarka ake nema kawayen ki masu Miki dariya yanzun haka a cikin su wata da sadeeq zai nemi auren ta Koh babu lefe ba goro sadaki kawai in zai tabata da gida wallahi tanason,kina ga guy kyakkyawa dashi ustaz ki tsaya kina Masa yanga,amma shikenan in Baki so ni Zan iya zuwa na samu Abbu a fasa bikin kawai sai yayi lefe 24 box's shikenan"?ya karasa maganar tare da jefa Mata kwalin wayar akan gado da wayan ta duka.
Chapter 68 · 0% Book details