Sashe 117
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gyada Kai Lahab yayi ya koma ya kwanta abinsa shi Kuma Ade ya sake cewa"Wai Lahab bazaka ci abincin bane"?Nan ma Bai basa amsa ba ya juya ya gyara kwanciyar sa........................
*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*
Washe gari da safe Yan team in su Lahab sukayi bankwana dashi zasu dawo gida yayin da Ade ma yabi jirgin London ya rage saura shi kadai washe gari shima ya d'aga daga Egypt xuwa Libya,saukar sa kenan daga jirgi yaji wani irin duka da kirjinsa yayi haka kurum yaji wani irin kwanciyar hankali da natsuwa daya tako kasar,sunan sa da yaga an rubuta a jikin wani karamin board a hannun wani balarabe yasa shi d'aga hannu Yana nufar wajen mutumin da Sauri mutumin ya gyara tsayuwar sa Lahab na fitowa ya Kama bag na kayan sa sai sannu da zuwa yake Masa Suka fita daga cikin airport in,mota Mai zafin gaske baka ya budewa Lahab ya Shiga shima ya shiga Yaja motar Suka bar airport in.
Babban gidane Mai shegen kyau Wanda Industry ta basa ya zauna a ciki har su kammala meeting Inda ya kawosa akwa kome na bukatar dan Adam a ciki ga masu aiki Kota Ina,Suna Isa wanka yayi Suka Soma jajjera Masa abinci kad'an yaci ya kwanta,sai Kuma ya zaro wayar sa number Abbu ya Kira Suka gaisa Yana tambayar sa ya kafar Addayiya don kwana biyu ance Masa batajin dadi ba kafarta na ciwo sannan ta kirata itama.
washe gari da safe dayake meeting in Suna dashi ne karfe 10 na safe shiyasa bai tashi ba sai kusan 9 na safe wanka ya Shiga ya shirya cikin wani Arnen suit wando Baki sai rigan ciki fari kana ya daura baban rigan akai,ba karamin kyau yayi ba kannan nasa ya tajeshi sosai kana ya dau bakin glass ya kwaba a fuskar sa Sabon labcoat nasa ya d'auka ya rike a hannu kana ya bude kofa ya fito haraban gida da gudu drive yazo ya bude Masa mota shiga Lahab yayi da Bismillah gateman ga bude gate Suka bar gidan ,tafiya suke hankalin sa nakan wayar sa Yana dannawa Koh xai samu sukuni don kwata kwata yau ya rasa sukunin sa.
Suna ssa industry sosai yake bin wajen da kallo bawai kallon kauyanci bane ah ah sai kallon naira tayi kuka daya Mata, labcoat in ya sanya kana ya gyara zaman glass nasa ya sauka a mota,yayi cikin meeting room in dake cikin wajen.
Zazzaune suke akan kujerun a kalla pharmacy da Kuma pharmacology da likitoti akallah sun Kai ishirin Amma gashi goma da wani Abu yayi na safe an kasa Fara meeting in adalilin mutum daya dabai iso ba Wanda Lahab baisan Koh wanene ba guntun tsaki yaja don shi a duniya ya tsane African time bare har zaizo yana jiran mutum d'aya,mikewa yayi da niyar barin dakin hakuri manyan ma'aikatan suka Soma bashi akan yayi hakuri Wanda ake jiran ma ta karaso,ransa ne ya Kara baci Ashe ma macece ya tsaya Yana jira badon yanajin kunyar idon mutane ba yau Babu abinda zai sashi cigaba da Zama a wajen Nan,komawa yayi ya zauna yasha mur dashi.
Turo glass na kofar akayi da Sauri gabaki d'aya jama'ar dakin suka juya Dan ganin Mai shigowa sabanin Lahab da kansa nakan wayarsa Yana dannawa Yi yayi Kamar baisan da halinta ta shigo ba,wow Masha Allah taku take daya bayan d'aya macece Mai cikar Kamala natsuwa da haiba ga wani irin kyau dake tattare da ita Mai sanyi da sanyaya zuciya farace Sol Kuma tass dogowa Mai jiki daidai fuskar ta d'auke da medicate glass, suit na Mata ta sanya ruwan toka wando da riga ta daura lab coat akan kayan ta farin hijab data sanya karami iya wuyanta Wanda Harya bata daman da gashin gaban koshinta kwantattu Suka dan leko,kafarta sanye da takalmi Mai tsini kujerar da aka tanadar dominta ta zauna ta Soma gaggaisawa da sauran jama'ar dakin,muryarta ta dan makale kad'an lokacin da idanunta sukaci Karo da Lahab Wanda ya sata kasa karasa gaisuwar data Mika Masa shikam kansa har lokacin na kasa Yana Jin duk abinda ke gudana amma bai dago ba.
Jawabi aka Soma da tattaunawa kowa kokari yake ya zuba bajintar sa Kuma ya nuna kwarewarsa a harkar sanin magunguna,Deyana Abbas Ali shine sunan da Lahab yaji an ambata da sunan ta mikewa tayi a hankali ta Soma jawabi sai a lokacin ya d'ago ya kalleta had'a ido sukayi a tare dukansu suka kauda idanun su ana juna, meeting yayi zafi kowa mikewa yake Yana jawabin sa,har aka zo Kan Lahab.
1:20 cip aka tashi meeting in a hankali aka Soma fita one by one abinka da cikakkun Yan boko wa'inda suka San abinda Suke Babu wani hayaniya Koh ture ture Lahab da Deyana duk Basu mike ba sai da jama'an dakin Suka fifita saura bai wuce mutum biyar ba Suma Suka mike a tare kamar haden Baki,itace a gaba yana baya Suka Soma tafiya sosai ya zubawa jikinta Ido Yana kallon duk wani taku da take,yayinda ita Kuma kafafunta sai hardewa suke na rashin sabo.
Suna fitowa haraban wajen yaga wasu manyan bodyguards a kallah sunyi goma manyan maza majiya karfi sai Mata guda biyu,d'ayar ta bude Mata mota zata shiga kenan ya ratsa tsakanin su, ba tare da yayi magana ba yasa hannu ya Kama nata hannu tare da juyar da ita da karfin sa"tamkar wasu mayunwatan zagi haka Suka yunkura Masa da Sauri ta d'aga musu hannu,Kuma sukabi umurnin nata Suka tsaya, kallon hannun nata tayi fari tass dashi ta Kara d'ago idanunta ta kalli fuskar sa"irin kallon Nan na tambayar dalili"?ganin baice Mata kome ba yasa ta fizge hannun ta ta juya ta Shiga motar aka ja Suka barsa a wajen a tsaye da Sauri yaji an dafasa,dagowa yayi ya kalli mutumin a kalla zasuyi sa'o'i Kuma ya shaidaishi Yana daya daga cikin likitotin da sukayi meeting yare"kaga bawan Allah kada ka wahalar da kanka aka baiwar Allah Nan ba irin naci daban nuna Mata ha amma Koh kallo ban isheta ba tsawon shekarun Nan Koh haduwa mukayi nunawa take bata taba kallo na ba alhalin Kuma a hospital d'aya muke aiki"kala Lahab baice Masa ba ya juya shima yabar wajen.
Yana Isa gidan sa waya ya d'auka ya Kira Ade Ade na d'auka yace Masa"duk abinda kake ka bari pls kazo Libya Zan turo maka address na wajen da nake yanzun"keet ya kashe wayar ba tare daya jira abinda Aden zai fada ba"tsawon kwana uku Lahab na sintirin neman information akanta Amma ya kasa samun hakan Adewale yazo amma Lahab baice Masa kome ba, sosai yaji haushi sai masifa yake ma Lahab shidai Lahab baice kome ba sai visan sa daya dauka ya boye,yau tunda Suka tashi da safe ya shirya ya tafi meeting Inda za'a sake, yau sai xuba Ido yake ya ganta amma har aka tashi batazo ba.
Jikinsa a sanyaye ya dawo gidan tura kofar falon yayi ya shiga Ade ne zaune da wani balarabe Suna hira,ganinsa da Bako yasa sa bude muryarsa yayi sallama amsa Masa sukayi dukansu kana ya karaso falon nufar bedroom yayi da Sauri balaraben ya mike Yana sake gaidashi dawowa Lahab yayi ya zauna akan kujeran wajen Nan balaraben ya gabatar da kansa amasayin sa na coach khamaludeen saboda kaunar da suke Masa shiyasa Suka had'a Wasa dan Allah Suna so ya hallarta wasan ya buga da yaran su in Basu takurasa ba zasuyi farin ciki inya amince,da fari yaso yaki zuwa Saida Adewale yasa Baki sosai yayita basa Baki akan Bai Kamata mutane su nuna Masa kauna sannan Yana banzarar dasu ba hakan yasa sa hakuri suka saka Rana da venue.
Monday afternoon Lahab ne sanye cikin kayan ball farare tass har takalmin kafar nasa farine,sai Adewale dake rataye da sport bag na Lahab, shikam sanye yake da kananan Kaya,mota Suka shiga a tare driver yaja Suka bar gidan.
****************
Stadium cike yake da larabawa especially yara matasa sun cikane makil har wajen Zama yama wasu kad'an,shigowar Lahab filin wasan wani irin ihu wajen ya d'auka ana Kiran sunan sa,karasowa yayi ciki gurin da aka tanadar na zaman Yan Wasa Zama yayi Nan Yan Wasn Suka ruga wajen sa wasu suna sanye da Jan jese wasu Kuma Kamar na jikin sa watoh fari kenan, Nan suka Masa caaa kowa nason su musaba'ha dashi hannu kawai yake Basu Suna musaba'ha.
Wasa aka Fara cikin nishadi sosai su Lahab ke Shan yaran Wasa duk da yaran ma na bugawa iya kokarin su don sai su Lahab sunyi da gaske suke Shansu,an tashi Wasa su Lahab nada 3 goal yayin da yaran Suka tashi da 1 ihu wajen keyi da karfi ana Lahab Lahab Lahab da gudu wata balarabiyar yarinya sanye da jese sak na jikin Lahab sai dogon wandon roba pencil shima fari kanta dauke da hulan sanyi Babu Koh hijab a jikinta a kallah zata Kai shekara 13 don harta Soma Zama budurwa ga kirjinta cike da no-no tsallakowa tayi Kamar namiji ta hayo inda aka saka tsakanin Yan Wasa da Kuma yan kallon Wasa rugowa tayi da gudu duk kokarin tareta da ake kin tsayawa tayi ta nufi Lahab da gudu cikin larabci tana cewa akheeeeeeeeeee.