← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 122

Sashe 88

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lahab tunda ya tare machine ya shiga ya nufi unguwan su zuciyarsa ta Soma bugawa wallahi baisan amsar da zai Basu gamshashiya ba akan Inda ya Shiga gashi bayason musu karya Koh kad'an a hankali ya sauka a keken Yana bin kofar gidan nasu da Ido kudi ya baiwa Mai keken a hankali ya nufi kofar hannu yasa ya kwankwasa sai Kuma ya tsaya Jin muryar Mai gadi na cewa wanene Yana bude kofar sai Kuma ya tsaya Yana kallon Lahab da kayan jikinsa sai Kuma yayi shuru kwata kwata yanda Lahab ya fige Bai Masa kama da Rahab Inda ya gani d'azun a cikin gida ba da Sauri yace Lahab?

Murmushi Lahab yayi ya gyada Masa Kai aiko da Sauri ya bude kofar ya Soma salati cikin Al'ajabi ya ruga cikin gidan da gudu Yana kwalama Abbu kira da iya karfinsa Lahab Kam binsa yayi a baya a hankali,Yana tura kofar ya dan tsaya ganin kattafanin jama'ar gidan su a tsaye Suna jiran karasowar su don Mai gadi tuni ya kusa ya tsaigunta musu sunkuyar da Kai yayi lokacin da yayi Ido hudu da Abbu bawan Allah har wani Rama yayi na rashin amanar sa,da gudu Rahab ya tawo yazo ya rungume dan uwan nasa dan dukawa Lahab yayi a hankali ya Kara makale dan uwan nasa da karfi kowa yaga kaunar Nan yasan na sakanin jini da jini ne,da Sauri ya sakesa Jin Addayiya na salati fitowarta kenan daga dakin ta hannunta rda canula.

Kuka ta fashe dashi ganin Lahab a hankali ta Soma takawa tana nufo su da Sauri Lahab ya mike ya nufeta fadawa kawai yayi a jikinta ya sake kuka Wanda shima baisan kukan menene ba,zazzaune suke sun tasa Lahab a gaba tun ana lallaman sa ya fad'a musu Inda ya shiga har ran muzammil ya baci Wanda zuwan sa kenan yau don B'atan Lahab in tun ana daukar Wasa Abu ya Zama gaskiya sannan anzo ana Masa tambaya ya mannawa mutane hauka mikewa yayi Rai bace Yana zare bell in jikinsa ya Soma magana"wallahi Lahab inka kuskura ka batamin Rai jikinka ne zai gaya maka dan iska kawai"da Sauri Abbu ya d'aga Masa hannu tare da cewa kada Wanda ya sake tambayar sa Inda yaje duniya ce duk abinda ka shuka shi zaka girba sudai sunyi iya bakin kokarin su a kansa duk Wanda ya zagesu Allah ya Isa sai Kuma yace daga yau Kar Wanda ya sake tambayar Lahab Ina zashi duk Inda yaga dama yaje duk lokacin da yaso ya dawo Yana karasa maganar Rai bace ya mike yabar falon da d'add'aya kowa ya watse don Abbu baiya fushi amma in yayi abin Baya kyau Sam.

Zama Lahab yayi akan katifarsa lokacin da ya Shiga dakin nasu lumshe Ido yayi rabonsa da ganin haske haka Harya manta sai Kuma ya mike ya shiga wanka wanka yayi sosai ya kimtsa jikinsa cikin kayan baccin sa wando da riga kwanciya yayi ya lumshe idanun sa,turo kofar dakin akayi Addayiya ce d'auke da plate na abinci sai drink's mikewa yayi da Sauri ya karbi plate in ya aje a gefe itama Zama tayi tasa hannu ta shafa kansa a hankali ta Soma magana"Lahab Sam banji dadin abinda kayi ba ka d'aga Mana hankali haka zalika kasa mu a damuwa karka Kara Mana irin haka Kamar yanda yayan ka yace karmu sake tambayar ka bazan tambaye kaba amma dan Allah karka sake irin wannan?gyada kansa yayi ya kwantar da kansa a cinyarta hawaye na taruwa a idanun sa hannu tasa ta dauko abincin ta bude tare da d'aga kansa tana cewa ya tashi yaci ba musu ya karbi plate in ya Soma cin abincin daya Dade baici ba.

tunda ya kwanta yake juye juye Sam ya kasa bacci tunanin matar sa yake"Lahab yaji Rahab dake katifar sa ya kirasa"amsawa yayi tare da mikewa zaune shima Rahab mikewa yayi ya ce"bakayi bacci ba har yanzun"eh banjin bacci ne dan uwa"uhmmm kasan me"ah ah saika fada"Abbu ya Mana registration na weac da neco insha Allah zuwa next week za'a Fara waro Ido Lahab yayi yace kana nufin yanzun an rufe biya kenan"?kwarai ma kuwa.

Rumtsa Ido Lahab yayi yaci burin ya biyawa Nnenna duk da Bata kallo sai ya bada a Mata duk da yasan hakan prohibited ne a exam,komawa yayi ya kwanta Rahab ma kwanciyarsa yayi Bai Kara cewa kome ba ba,a cikin kwanakin Nan da Lahab yayi babu Wanda ya Kara tambayar sa Inda yaje Mami ma batazo ba shima ya kasa zuwa wajen ta saboda tsoro gashi yau satin sa daya ya muzammil ma ya koma a yau Suka Fara jarabawar neco babu Wanda ya sanar dashi zancen jarabawar Koh yaje yayi sai Rahab don yanzun Abbu baya Masa magana Koh gaidashi yayi baya amsa wa,sun cigaba da zuwa school harda Adewale Nabeel ma duka Yana zuwa duk da Lahab baisan waya biya Masa kudi ba yadai ganshi shima a hall Kuma ya tambaye sa Inda ya shiga sharesa kawai Lahab yayi Bai ce Masa kome ba Kuma sosai yaji ya Kara son Ade watoh duk da sun samu rashin jituwa akan Nnenna amma babu Wanda ya sanar wa da labarin auren sa.

Kamar kullum yau sun tashi jarabawar har yamma Suna fitowa lahab ya dan kalli Adewale ganin Nabeel hankalin sa baya kansu yasa sa kama hannun sa Suka zagaya bayan exam Hall shidai Ade Ido kawai yake binsa dashi Jin abinda yace"dan Allah so nake ka daukomin Nnenna ka kaimin ita garden City mu hadu a acan bayan mangariba dan Allah"wani kallo Ade ya Masa kafun yace"Kai me yasa bazaka je ka dauketa ba?kaga Lahab ka daina Sakani a shirgen ka da yarinyar Nan fa bana so"

Kawa Allah kayi hakuri Ade kasan Abbu yace naje duk Inda Naga dama ya cire security na gidan mu Amma abinda na gano wallahi yasa ana bibiyata duk Inda na shiga muddin aka ganni naje gidan goggoji za'a sawa zuwan ayar tambaya"shuru Ade yayi sai Kuma yayi tsaki ya juya yabar wajen murmushi Lahab yayi ya shafa kansa sannan yabi bayan abokin nasa, Nabeel ya hango tsaye Yana dubasu ganin su yasa sa matsowa kusa dasu yana cewa "muje gidan mu ka gaida Inna duk ta damu a kanka ga Adda mubeeena kamma ba'a magana"girgiza Kai Lahab yayi yace"kayi hakuri Nabeel bana fita tunda na dawo amma in Allah yasa muka gama exam lafiya zanje.

Ba kome shine abinda Nabeel yace Yabi bayan Ade Suka bar school in Lahab Kam gida ya koma wanka yayi ya tafi sallan mangariba daga Nan wani mall ya wuce sayyayyan Kaya ya Mata sosai ya had'a da kayan ciye ciye laida guda daidai ya fita a mall in ana Kiran isha'i tsayawa yayi yayi sallah kafun ya nufi wani tukuban nama yasai kaza sukutum guda biyu Keke napep ya hau Yana kallon motar dake binsa a baya tsaida keken yayi a kafar wani gida ya bude gidan ya shiga suturan jikinsa ya Kwabe yasa wani sabo daya saya sanin da yayiwa gidan Mai kofa biyu ne irin gidan Nan guda biyu da ake musu kofa a katangan tsakiya bude daya kofar yayi ya fita abinsa ta wani layi ma ya fito Yana dan dube dube ya tare Keke sai garden City.

Yadan jima kad'an kafun Adewale Suka karaso rike yake da hannun Nnenna had'a fuska Lahab yayi Yana kallon hannun har Ade ya karaso,cikin masifa ya Soma magana"wannan wani irin Abune ya zaka rike Mata hannu"?da dariya a fuskar sa duk da baison Yi amma wallahi Lahab ya basa yace"idan ban rike Mata hannu ba Lahab Ina Zan rike gani nayi Bata amfani da Sanda Kuma haka zalika bazan barta haka ba Koh ya kake so nayi maka ne Wai"hararan sa yayi ya fizge hannun ta ana Ade ya rike Yana magana kasa kasa Yana cewa matar aure zai rike kaza kaza shidai Ade wani table ya nema ya zauna nesa dasu ya zaro wayarsa Yana dannawa.

Zaunar da ita yayi akan dardumar daya shimfida musu a kasa Yana bin kayan jikinta da Ido kayan ya kode sosai,gaidashi tayi ya amsa Yana cewa"Labiba kiyi hakuri ki Kara hakuri da jarabawar ki Allah ya bamu ikon cinyewa kinji"amsa Masa tayi da toh kana ya bude laidan Kazan,Naman ya yago yasa Mata a baki bude bakin tayi ta amsa ta Soma ci,ya Kuma dauko hanken ya goge Mata gefen bakinta sannan ya sake yago wani Naman Yana Kai Mata Baki daidai lokacin yaji tsayuwar mutum a kansa da Sauri ya d'aga Kan nasa sai Kuma ya zaro Ido cikin mamaki Wanda ya gani agun............................

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀

Farida murmushi tayi tace lallai ma Lahab Ni ka shekemin tawa soyayyar Kai Kuma kana raya taka Koh? sai Kuma ta gyada Kai tare dayin kwafa tabar wajen binta yayi da Ido harta mule kafun ya maida kansa ga Nnenna data jefo Masa tambaya "Wai wacece?shuru yayi Yana daukar drink ya kafa Mata a Baki kin bude bakin tayi ta rufe sa gangataran d'an dakatawa yayi Yana kallon ta da mamaki yace"bazaki karbi juice in ba"?nace maka wacece"?dariya ya Soma cikin dakewa yace "kishi Koh"?

babu wani kishi kawai dai naji yanayin da tayi magana Kamar tana Jin haushin Kane duk da ba yarenku nakeji sosai ba"ba kome shine abinda yace Mata sannan ya Kara da cewa"Nnenna mun Fara exam naso na biya Miki amma Allah baiyi ba"ba kome Lahab hakama na gode matukar babu abinda zance maka sai godiya kamin goma Sha akan wannan basai ka ce kome ba"amma naso na biya Miki wallahi"dariya ta danyi tace toh Inka biyamin ka fadamin da wani idon zanyi exam"?kamo wani hiran yayi sukayita Hira har Saida Ade ya gaji da Zama ganin 10 na dare yayi yazo yace ma Nnenna ta tashi su tafi,kayan Lahab ya bata da sauran tarkacen Ade ya d'auke sai gidan goggoji.
Chapter 88 · 0% Book details