← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 122

Sashe 102

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma Lahab tunda Allah ya hore maka why not ka samu wata dattijuwan baturiya ta zauna ta kula maka da ita ko haihuwarce ya tashi ai akwai wata a kusa"wani banzan kallo Lahab ya Masa irin na baka da hankalin Nan"Ade taya Zan bar matata a hannu bayahudiya salon a haifamin yara biyu ta sabe daya ta gudu Koh ace sun mutu saboda da Bata da tsayaye gwara Ina Nan"shuru Ade yayi h?ar Lahab ya gama surutun sa kafun yace"toh nidai Ina kewar kasata Kuma zanje Naga iyayena"Allah ya bada sa'a babu Inda zani harsai Naga gudan jinina a doron kasa"yanzun me zakace musu a matsayin excuse naka"

Cewa zanyi Muna da wasa a France kawai"uhmmmm shine abinda Ade yace Suka cigaba da Hira Nnenna dake cikin kitchen tanajin duk abinda ke faruwa sosai taji zuciyarta tayi sanyi Jin Lahab har yanzun ya damu da lafiyar ta Koda yake ai ya damu da lafiyar ta ya bai damu da lafiyarta ba ai da ta Jima bata gidan sa,ta yarda Lahab na sonta baba Wasa ba.

Allah sarki Lahab bai sanar da gida bazai dawo ba har Saida Adewale ya koma nageria kafun ya sanar dasu sosai ran Mami ya baci tayita fada Akan wasan banza zaiki dawowa hakuri kawai ya Bata,yau tun safe lahab Suka shirya dashi da Nnenna zasu hospital cikin Nan gashinan tirim a gaba sanye take da polon wando sai riga bankacece har gwuwa Mai dogon hannu cikin Nan a gaba gyale tayi rafen nasa a kanta,ta sanya boot a kafarta,Lahab ma sanye yake da kananu kaya,motar ya bude Mata ta shiga Suka wuce hospital,Suna Isa facemask ya d'auka ya sa gudun kada mutane su Soma daukarsu hoto a watsa a duniya ya shiga uku tunda yanzun shima ya Zama popular Koh Ina ya Shiga hotuna ake masa,yauma anyi sa'a sun hadu da mutumin da suke yawan haduwa dasu in sunje asibiti awo matar sa mai ciki Amma ayau sun hadu dasu ne lokacin da suke Shirin shiga mota sai ga Matar da mijinta sai wata tsohowa da baby a hannunta daga gani haihuwa matar tayi Kuma an sallame su,Suka nufi motar su Suma ba tare da sun kula dasu Lahab ba duk da daman duk haduwar su basa magana duk da bakaken fatane sai dai su ringa kallon su Lahab shikuma kallon ke hanasa musu magana tunda barikine kowa zaman kansa yake ba irin Naija bane mutun zaice wane ya ganni Bai gaisheni ba"

Shiga Nnenna tayi Lahab ya shiga Harya tada motar bayan ya zare facemask in fuskarsa sai Kuma ya tsaya ganin motar gayen Taki tashi gashi lokaci d'aya aka Fara yayyafi fitowa sukayi daga motar zasu koma cikin hospital in,da Sauri Lahab ya fito a motarsa hade da musu sallama,da mamaki mijin ya amsa hade da basa hannu Suka sake gaisawa,kafun Lahab yace in babu damu suzo su shiga ya rage musu hanya,tsohowar taso ki amma data ga Nnenna a cikin motar saita amince suka shiga baya gabaki dayan su Lahab yaja mota.

"****************
Kamar nasan fuskar nan taka in ban manta ba Kamar Hassan Lahab Koh?"gyada Kai kawai Lahab yayi,wow gaskiya naji dadin haduwa dakai Ni Sunana Muhammad Auwal wannan iyalina ce Hauwa amma ana kiranta da jidda sai mamata gata ?"nima haka" shine abinda Lahab yace,shuru mutumin yayi ganin Kamar Lahab baison hiran,tsohowar Kam kasa hakuri tayi tace"yaro wannan Yar uwarka ce"saboda ita haka kawai taji ta Kosa Taji menene a tsakanin su tunda matar d'anta tace Mata ai Suna haduwa dasu a hospital sa'i da lokaci Suna zuwa"har Lahab ya bude Baki zaice matar sane Nnenna ta rigashi da cewa"kaninta ne"wani kallo Lahab ya Mata amma baice kome ba yaji matar na hausa da d'anta don a zatonta ko su Nnenna basajin hausa don Basu Mata Kama da Yan nageria ba Nnenna tafi Mata Kama da Yan Ethiopia harda Lahab in ma duk da bakine amma kyakkyawa ne sosai,gulmansu ita da matar suka Fara tana cewa ai wallahi itama Saida tayi tunanin Koh Yan uwane amma meyasa kullum Lahab ke rakota,da Sauri mijin yace"gaskiya mama ya Kamata kuyi shuru babu Dadi Kuma cikin mutane kuma yare zasu tsargu bare Kuma wa'innan da kuka jefawa tambaya.

Murmushi Lahab yayi don yasan Nnenna ba wani fahimtar hausan take ba"mata tsohowan ne tasake jefowa Nnenna tambaya tace"aiko gaskiya yayi tsawon kafa dubeshi Kamar wani yayanki amma ku Yan Ethiopia ne"?haba dan Allah mama kiyi shuru Mata"yaron ya tareta da Sauri Lahab ma juyowa yayi yadan kallesu kana yace"munata tafiya Baku fadamin address naku ba"fada Masa sukayi da mamaki yake kallonsu don kuwa gidan sane manne dana mutumin amma baice musu Suna waje daya ba don baya fatan yayi makwantaka da tsohowar Nan sarkin surutu.

Wuce kofar gidan sa Lahab yayi ya tsaya a kofar gidan mutumin bude kofar sukayi Suka fiffito mikawa tsohowar laima Lahab yayi dake cikin motar sa gudun sanyi kada ya Kama babyn,sai a lokacin ya musu barka da samun haihuwa itama Nnenna ta musu barka harda karban baby tayi ta kalla kafun ta maida musu, number Lahab mutumin ya karba Yana ta godiya kana Suka shiga ciki Lahab Kam reverse yayi ya nufi nasu gidan.

tunda cikin Nnenna ya shiga wata tara shikenan Lahab ya tattara wasan kwallo ya aje a gefe ya koma zaman gida tunda babu makaranta Suna jiran lokacin haihuwarta,yau tun safe lahab yace Nnenna ta shirya bayan sunyi breakfast shiryawa sukayi ita dashi Suka fito zasu fita sayyayyan kayan yara da zasu sayo yayi-yayi ta Masa list yaje shi kadai tace shida baya kaunar yaran yake ba tasan bazai sayo Abu Mai kyau ba,lokacin da Suka fito compound ganin da gaske zata bisan yasa da tsayawa yace"Amma so kike kije ki haihu a hanyane Koh"ai Dr yace saura 2 weeks"da dariya yace waike kin amince da maganar Dr Koh yau in Allah ya nufa Zaki haihu"da masifa tace koma me zakace kace sai make"abinka da gidan turawa na wancan gidan na kallon na wannan kawai cikin magana sukaji an kwala Masa Kira Yana juyawa da mamaki ba kowa bane sai tsohowar Nan tsaye a baranda tana murmushi tare da tafa hanneye daga nesa yaji muryarta Kamar Ansa lasfika tsabar karfi tana cewa"daman Nan ne gidan ku D'an ball ban sani ba ai dana ringa shigowa na huta da zaman kadaici, Kanna kowa saina ringa zuwa wajen mamanka...............................

*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

Murmushi yake Lahab yayi Aiko da Sauri Mata Kam ta zagayo daga cikin gidan su zuwa nasu Lahab tana washe baki, tace"Ina zakuje ne Koh asibiti ne"?Ah ah mama zamuje sayyayyan kayan babies ne"Nnenna ta Bata amsa Kama Baki tayi tace yanzun da cikin Nan Zaki fita wani sayayya ai saidai kuzo na rakaku muje ki zauna Ina zabar Miki"Lahab baiso ba Amma ba yanda ya iya haka matar Nan ta bisu tafiya suke sai surutu tane musu Kamar me Suna Isa mall Nnenna ta nemi waje ta zauna tsohowa da Lahab ne Suka Soma jidon Kaya"mama kayan tagwaye Zaki d'auka kome bibbiyu ganin ta Soma zaban suturan sawa"toh tace ta Soma d'aukan na jarirai biyu amma kayan da mace Koh namiji zai iya sawa shopping Lahab yayi sosai kama daga gadon yara kayan su bargo set na feeder duk abinda jarirai zasu bukata sai da Lahab Suka saya ya kashe kudi kusan million daya a kayan yara kad'ai sai Yan suturu daya sayawa Nnenna kala goma tsohowar ma ya sai Mata kayan yara yace ta kaima jikokinta inta koma nageria Aiko taji Dadi ainun sosai, yawo sukayi bana Wasa ba,sai kusan yamma ligis Suka kamo hanyar gida.

Mama na baya Nnenna na gaba da Lahab tunda Suka nufo layin Suka hango Yan Sanda a tsaye Suna magana da Muhammad da matarsa duk Suna waje da gani dai a cikin tashin hankali suke tunda motar ta nufi kofar gidan su suke binsu da kallo,bama Kamar lokacin da mama ta bude kofar da Sauri Muhammad ya nufeta Yana tambayar ta"mama Ina Kika shiga kinsa hankalin mu ya tashi haba mama dan Allah Nan fa ba nageria bane,fitowa Lahab yayi ganin yanda ran Muhammad ya baci sosai don mama kam bude boot na motarsu tayi tadau laidan da Lahab ya sayo Mata tana Masa godiya tayi cikin gidan tabar su tsaye a waje.

Hakuri Lahab ya baiwa Muhammad tare da fad'a Masa dalilin da yasa ta bisu,sai anan Muhammad ya sake ransa tare da cewa babu kome yasan halin mama sarai,sallaman yan Sanda yayi tunda anga Wanda ake nema,cikin gida Lahab ya shiga, Nnenna daker take taka kasa ta fito a motar kafafunta sunyi mugun kumbura Kamar me,takawa take a hankali harta shiga falon,kayan Lahab ya ringa daukowa one by one Yana ajewa yaje ya dawo Saida ya kwashesu tas kana ya rufe motar ya shigo gidan,har lokacin Nnenna na zaune a falo Bata tashi ba,dakinsa ya Shiga yayi wanka tare da daura Alwala yayi sallan mangariba,ya fito a dakin har lokacin tana zaune a falo sai had'a zufa take,matsowa yayi kusa da ita Yana tambayar ta lafiya"kafafuna kemin ciwo ga kirjina nauyi"toh ba Dole ya Miki nauyi ba Labiba Saida na hanaki fita Amma saboda tsabar taurin kai Saida Kika fita"ita dai batace kome ba hannu yasa ya zame wandon jikinta yajashi kasa cire Mata wandon yayi ya rage daga Ita sai polon riga don ta riga ta cire gyalen,takalmin kafarta ya cire ya zare socks duka,dukawa yayi ya d'auketa.

Ajeta yayi a bathroom ya had'a Mata ruwa wanka kana ya zare rigan nata da under wear itama Bata Masa musu ba don jikin nata gabaki d'aya batajinsa normal,rigan jikinsa ya zare ya rage daga shi sai dogon wando wanka ya Soma Mata,yana gamawa ya daura Mata towel kana ya ajeta,ruwan zafi ya had'a a baf ya dauko kafar yasa a ciki Yana dannawa,sosai ya dumama kafan kafun ya d'auketa sai cikin daki,ajeta yayi a Kan gado yadau pillow babba ya daura kafarta akan cream ya d'auka Yana shafa Mata Koh zataji saukin kafan,duk abinda yake matan Nan basu Koh ga maciji shurune kawai Kamar wasu kurmaye.
Chapter 102 · 0% Book details