← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 122

Sashe 31

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa yasan yanda ss 3 suke feeling lokacin da suke Sabon Shiga gani suke kansu daya da malamai ne yanzun gasu da gemu,gashi a lokacin yaran ke tashen balaga ji suke kashin su na daidai dana kowa,toh hakan take a wajen Lahab daman gashi da karfi Kamar doki Koh uncle muzammil dake jibgarsa albarkacin kanin uba yakeci,kwace kwalar sa yayi da karfi tare da bangazan coper in don bazai wuce 25 ba"Akan me Zan bar class in"?Lahab ya tambaye sa Yana haki.

Mari coper in ya wanke sa dashi tare da cewa,saboda bana ubanka bane.

Habawa daman Lahab a duniya ba abinda ya tsana irin a zagi ubansa Koh don uban bai raye ne oho,Amma shi gwara ka zagi uwarsa daka zagi ubansa,kafun coper(uncle physics) ya sauke hannnun sa tuni Lahab ya d'aga hannu ya sharara Masa Mari,a take suka rungume juna da fad'a.

Kacemewa ajin yayi da ihu Nnenna sosai ta tsorata ganin irin dambe da ake bugawa gabaki dayansu fada suke da dukkan karfin su Kuma bamai kwaran wani, Lahab bai basa daman da zai bugeshi,Kuka take tana tattara jakanta dana Lahab da laidan, ta ruga gefe ganin sun koma fadan akan bencuna.

Ihun dalibai shiya d'auki hankalin malamai dake makarantan da dalibai duk take sauran classes Suka fifita a ajujuwan su Suka nufi Nasu Lahab ciki harda su muneera dasu Adewale da Nabeel da rabon su da Lahab tun jiya,ganin fada ake da Lahab yasasu shigar Masa,take su ukun Nan Suka Soma jibgar coper Nan da karfin da Allah ya musu,daman ance sarkin yawa yafi sarkin karfe,zuwa lokacin Kare kansa coper Nan ya suma Amma baya iyya maida martani ganin malamai sun nufi ajin Yasa sauran students fara ihu suna ga principal ga disple Master.

da gudu Suka sake bawan Allah Suka nufi windonan hannnun daman ajin Suka hau Suka tsallaka daidai lokacin malamai Suka shigo da gudu suma Suka nufesu,Amma Ina kafun ma su sauka tuni su Lahab sunyi Nisan zango,sun dosi cikin gonakin makarantan Amma duk da hakan Basu hakura ba Suka rufa musu baya suma.

Ta bangaren class Kam kuka Nnenna take tayi don ita ta gama sadakarwa shikenan yau Lahab ya shiga ukun sa,daidai lokacin Rahab ya iso wajen bayan su muneera sunje sun Kai Masa rahoto sosai Shima ya shiga damuwa sanin da yayi lallai yau jikin Lahab zai gaya masa in aka kamasu,Yana Isa ya samu sun ma gudu juyawa yayi bai shiga ajin ba ya Kama hannnun zulai tare da muneera Suka bar wajen,warning ya musu akan karsu kuskura yaji sunyi hiran abinda ya faru Koh da Wasa Koh fadawa wani a gida,munira ce ya kallesa,insha Allah uncle bazamu fada ba Amma ni ina tsoron matakin da xa'a d'auka akan uncle Lahab?

Girgiza Kai Rahab yayi,karki damu munira abin zaizo da sauki Allah ya Mana Mai kyau.

Zulai dake kuka sai share hawaye take akai akai ita tayi magana,ni toh uncle Mai yasa yake haka ne.

Kin cika surutu zulaihat ya Isa haka kudai duk lokacin da kukayi sallah kusa uncle naku a Addu'a Allah ya shirye sa.

dukan su da Ameen suka amsa Masa kowa ya koma class nasu.

Su Lahab Kam da gudu Suka fasa cikin gonakin makarantan ganin har lokacin ba'a daina binsu ba yasa su Kama katangan makarantan Koh tsoron wayan danger dake mammakale basuji ba Suka d'ale da gudu Suka dirka ta bayan makarantan,Inda Allah ma ya sosu yashine a bayan wajen suna dirka Suka Kara gaba abinsu ,dole tasa malaman juyawa ganin su Lahab dai sun tsira.

Koran yara a ajin su Lahab teachers in sukayi sai Yan aji kawai aka Bari,Kama coper dake sheme akasa sukayi don gaskiya ya daku wallahi dole tasa aka nufi clinic dashi.

Nnenna Kam komawa tayi kan des nata ta zauna har lokacin jikinta baibar rawa ba don it's Sam duk abin tashin hankali bason sa take ba.

Su Lahab Kam d'aga Nan hankalin su kwance don harma sun manta sunyi fada tsakanin su su biyu da Nabeel,hirane ya barke tsakanin su sunayi Suna dariya,Amma wallahi Lahab baka da mutunci wai ma tsaya uban me ya hadaku ne wai?

Cikin dariyan shekiyanci Lahab ya dubi Nabeel dake Masa wannan tambayar"Kai za'a tambaya d'aga kanin Muna fada sai kawai kuzo ku shiga abinda ma bakusan kansa ba.

Hararan sa Adewale yayi toh sai mu Bari a jibgeka ne Koh Yaya?

"Wallahi kunsan nafi karfen muyi dambe aci zalina"ya karasa maganar Yana kallon Nabeel Yana dariya Shima Adewale kwashewa yayi da dariyan tunawa da dukan da Lahab yamasa last time.

Aiko Nabeel ya Shaka sosai har ya kasa hakuri ya yunkura zai kaiwa Lahab naushi da gudu ya zura tare da fashewa da dariya Nabeel ya Mara Masa baya Suka ringa guje guje a titi Kamar tababbu.

tun da abin ya faru ba teacher d'aya daya shiga ajin su Nnenna, don malaman sun rantse bazasu sake shigaba harsai an dauki kwakwaran matakin akan su Lahab don bazai yu suna matsayin malamai har dalibi ya samu daman dambe da malami abarsa ba hakan raini ne sosai Kuma in aka bar abin a haka toh tabbas an bawa dalibai satan amsa ne,duk Wanda malami ya buga zaice zai rama tunda Lahab ma yayi ba'a Masa kome ba,suma daliban Koh a jikinsu saima Dadi da sukaji yau babu lesson,sai hirar abinda ya faru suke duk an cika ajin da surutu group group akayi wasu mata zallah wasu Maza da Mata,wasu na zagin Lahab wasu nacewa ya burgesu daman copern haushi yake Basu wasu Kam labarin gagarancin Lahab suke musamnan Yan kusa da Nnenna Kuma sunayi Suna gaurayawa da turanci hakan yasa tana dan fahimtar abubuwan da suke cewa.

10:00pm dai dai aka buga break duk daliban ajin Suka Fara fita da d'ad'aya har gabaki dayan su Suka fita,sai Nnenna dake zaune rakube Kuma wallahi sosai takejin yunwa rabonta da abinci Mai kyau tun Wanda Lahab ya saya Mata jiya sai Kuma cake da taci shikuma ba abinci bane Mai nauyi bare ma ita data tashi d'aga jinya Koh magani anfison aci a koshi kafun asha,kwantar da kanta tayi a des in sai Kuma ta tashi jakanta ta bude ta fito da kulen nata a hankalin ya ajesa akan bincin da Sauri Kiki ya sauka ya nufi laidan Lahab dake aje a kasan bincin tun lokacin da ta sje batabi ta Kai ba kansa yasa Yana tsuntsuna laidan Yana soka kansa.

Da Sauri Nnenna ta d'auke sa sai Kuma ta hada fuska ganin sai kokarin sauka yake zai koma wajen laidan"Kai Kiki menene haka ka daina Mana"tana maganan tana sake rikesa gam abinka da dabba maijin yunwa da kwadayi take ya Soma kukan Nan nasu na kuleluka,tsorata tayi gudun Kar wani yaji ta shiga matsala da Sauri ta dauki laidan ta bude da mamaki abinci ta gani sai dan paper karami dake d'auke da note,haka kawai taji ranta nason karanta abinda ke rubuce,hannnun tasa a hankalin ta dau paper warwarewa tayi,"wow shine abinda ya fito a bakin ta Ganin wani nice note dake rubuce, rubutune Mai shegen kyau Kamar na computer.

"Good morning Labiba(Nnenna)"

Shine abinda ta Fara gani a farkon shafin,murmushi tayi don tasan kaf duniya babu Wanda ya taba kiranta da sunan Nan sai mutum daya, amma Bata tsammani lettern nata bane.

"How was your night hope kintashi lafiya ya karfin jiki,meyasa Baki koma clinic ba alhalin kince min Zaki dawo a Kara duba lafiyar ki"?

"Ok fine ga break na kawo miki Yana laidan Nan pls karkice no and promise me zakisha maganin ki,nasan indai har na shigo ajin Nan ba lalle in samu magana dake ba shiyasa na tsaya na rubuta miki letter na shigo dashi""

"Kici abinci Kisha magani and kije clinic"

"See you tomorrow byeeeeee"

Hannnunta tasa ta rufe bakinta tana murmushi watoh abinda ya faru Nan daman Lahab ya riga ya tsara kenan kafun ya shigo,Jakarta ta bude a hankalin ta aje papern a cikin litattafanta, cire barrect nata tayi ta aje a gefe laidan ta bude tana maijin dadi Sam ta rasa meyasa indai Lahab ya Bata Abu har marmarin karba take,Koh Abraham dake dan uwanta bata karban abin hannunsa.

takeAway in ta fitar duka biyu budewa tayi ganin daya indomie ne dayan Kuma kwai hakan yasata aje kwai in ganin akwai bread ma,indomie ta bude ta zubawa Kiki a marfin roban ta aje Masa akasan binci ya sauka ya kamaci,flask in ta bude don tasan yanda ake budewa akwai irinsa a gidansu.

Tsiyaye coffee tayi a cup fork ta d'auka Shima na roba ne ta Soma cin indomie cikin happy tana hadawa da coffee inta hankali kwanci sosai taci indomin Harta rage don daman Saida ya cika roban dam,karshe rufe sauran tayi ta maida cikin laidan ta,Ana dawowa breakfast haka sukaci gaba da Zama babu malami har azahar musulman suka fita sallah itakam kwai da bread ta d'auka taci ta koshi.

Misalin karfe 3 na yamma aka tashi makaranta dayake yau ba extra lesson kasancewar abinda ya faru yasa su tun karfe ukun akace su tafi gida,duke take tana tattara litattafanta data fitar tana bitawa saboda ita dai abinda ya faru bai Mata dadi ba da asaran lesson nayau dabasu samu ba,Amma ta lura yan ajin Koh a jikinsu Basu wani damu ba.

Excuse me senior,taji muryar wata yarinya dake tsaye a kanta d'aga Ido tayi ta kalli yarinyar black beauty ce kyekkyewa sosai Yar doguwa bazata wuce 15 ba Koh kasa da haka"yes" shine abinda Nnenna tace tana kallonta don d'aga gani juniorn sune.

Am daman nace Koh jakan dake zaune a gaban des Nan naki ne?

Girgiza Mata Kai Nnenna tayi"no ba nawa bane na class mate nawa ne.

Murmushi zulaihat tayi,ok sister na uncle nawa ne Bari na d'auka.

"La ba kome Nnenna tace tana d'auka da kanta ta Mika ma zulaihat in don ganin yanda ta tsaya sai kallonta take Kuma tana magana idanunta akanta.

da Sauri zulaihat tasa hannu ta karbi boron tana kallon laidan abinci dake gefe Amma dai batace kome ba tama Nnenna sallama tabar ajin,Nnenna ma jakanta ta d'auka tare da laidan ta fita a ajin.
Chapter 31 · 0% Book details