← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 122

Sashe 112

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin mamaki da Yan Sanda Suka koma gidan don duba abincin wani shago aka saya Amma abin mamaki gidan a bude Suka samu Daman su Lahab Basu rufeba anyi Neman duniya ba'a ga abinci ba sai jinin da yake zuzzube a kasa da Kan gadon na Rahab,waya Ade ya d'auka ya Kira Abbu Yana sanar dashi abinda ke faruwa hankalin Abbu a tashe ya Kira ya jafar da mijin Mami ya sanar dasu akan zasu hau jirgin yawo zuwa London Amma kada ya sanar da Mami abinda ke faruwa harsai sunje London in sun dauko gawan sun dawo hatta jama'an gidan Abbu bai fada musu ba.

Alhaji sulaiman daman Suna falo da matarsa tunda ta tashi da safe Koh abinci bataci ba haka kawai take yawan cemai zuciyar ta na tsinkewa,shiyasa Bai fada Mata ba yadai ce Mata zashi emergency meeting a kwara state,dashi dasu Abbu suka wuce London a ranan sai washe gari Suka Isa zuwa lokacin Lahab duk Mai Imani inya gansa sai yaji tausayin sa gashi Dr yace sai an Nemo babba namiji zaiyi magana dashi ganin su gaba daya kuka suke Inka cire Lahab daya zamo mutum mutumi.

Lokacin dasu Abbu suka Isa anan likita ke sanar dasu cewa poison yaci Kuma a take ya tsintsinka Masa hancin cikinsa Allah ya Masa rasuwa innalilahi mutuwar mahaifinsu sabuwa ya zame musu yau sosai mutuwan yasasu tunawa da baban su,ya jafar har hawaye Saida yayi bincike aka shiga gadan gadan don sunki bada gawan sukace a tsaya ayi bincike amma su Abbu sukace Ina su zasu tafi da gawar kasarsu amasa sallah a binne sa.

CCTV camera dake gidan Lahab da Kuma cikin area aka bibiya tabbas anga wani da masks bayan fitansu Lahab ya shiga ya dau laidodin abincin saidai ba'a ga fuskar sa ba an bibiye camerori harna motar daya saukesa da Kuma Wanda ya dauke sa bayan ya fito a gidan haka zalika an dau wayar Lahab an dudduba anan aka ga shagon da akayi order anje shagon amma Waiter dayakai abincin ance tunda yakai ma su Lahab abinci Bai dawo ba bincike yayi bincike karshe aka rufe shagon kwata kwata magana tayi girma a garin sosai.

Su Lahab sun dau gawar zasu dawo nageria anan yayun sa sukace ya zauna a London bai Kamata ya dawo nageria yanzun ba Amma Lahab Koh amsa Bai Basu ba kuma Bai fasa Shirin binsu ba sufa abin nasa ya Fara basu tsoro tunda Rahab ya rasu shikenan Bai Kara furta Koh eh a bakin Saba sai dai kayi magana ya baka amsa a aikace.

*****************
Allah sarki uwa abinka da social media tuni zance ya karade Koh Ina ba Wanda baiji mutuwar Rahab a jikinsa ba Babu ma Kamar na kusa dashi wa'inda Suka San halinsa bazakaji wani ya aibata bawan Allah Nan ba sai dai kaji ana fadin Alkharin sa,Mami kan tunda taji labarin faduwa tayi a take marabanta da tun tana budurwan rabon dasu dashi toh a ranan sun tashi kame kame akayi da ita wallahi duk Wanda ya ganta saiya tausaya Mata ana samu iskan ya sauka sai Kuma ta kom Suma Kan Suma akayi asibiti da ita.

Dirowan dare su Lahab sukayi cikin NAGERIA duk da dare ne gidan su Lahab makil da Yan uwa na nesa da kusa sun cika gidan tab, shimfidasa akayi a falon Abbu,a daren Abbu ya Soma ma mamacin wanka Lahab na falon Yana taimaka Masa Suka shirya dan uwan nasa har lokacin idanunsa gangataran a bushe, Qur'ani yayun Suka d'auka duka Suna karantawa shima Lahab Yana rike da nasa karatu yake,kwanan ketso da akai Saida Suka sauke Qur'ani cip kafun safiya.

Jama'a sun cika gidan nasu da unguwan gabaki d'aya jama'a ne, a ranan Koh mutum baisan Lahab ba in yaji labarin su sai kaji yace zaije zana'ida Yan garin gombe Basu taba ganin mutuwa Mai jama'a a yanzun ba irin Wanda suka gani a mutuwan Rahab,Mami dake hospital tana farkawa za'a sake Mata Allura ta ringa kuka da magiya akan a barta taje taga gawan danta ta Masa addua ta Masa kallo na karshe, Dr yaso yaki amma sulaiman yace a barta,da taimakon sa aka baro hospital in da ita,tunda ta fito daga cikin mota wasu Mata suka fashe da kuka ganin yanda Amina ta koma Rana daya sai kaji ana ga mahaifiyar mamacin Allah sarki.

Kasa karasowa Kan gawar tahi sai da Addayiya dake gefe tayi kuka harta rasa Inda zata da kanta ta Mike ta Kama Mami Kamar makauniya ta ajeta a gaban gawan,hannu na rawa tasa ta bude fuskar sa Allahu Akbar kamar ka kirasa ya amsa fuskar nan tsab dauke da annuri,ya Allah kaji Kan wannan bawa naka ka Masa Rahama ka gafarta Masa, na yafe maka duniya da lahira d'ana baka tabamin abinda na kwana dashi a Raina ba yaro Mai biyayya,shekaran jiyan Nan ya kirani cikin dare Yana cewa na yafewa Dan uwan sa na daina fushi dashi,Ashe da rabon bazamu sake gamawa ba innalilahi wa'inna'ilahu raji'un Allah kaji kansa da Rahama ubangiji ka haskaka kabarin sa da rahamar ka ka bani hakurin rashin sa da dangana a cikin raina"ameen Ameen Yan falon suke cewa one by one yayun sa sukazo Suka Masa Addu'a.

Mikewa Lahab yayi a hankali Yana takowa kusa dashi Zama yayi ya Soma Masa Addu'a Yana nema Masa Rahama a wajen mahaliccin mu,kana aka dauko gawan a makara Lahab da Abbu sai muzammil da jafar su Suka rike sa aka Soma fita dashi Mami kuka ta fashe da karfi sai Kuma aka ga ta sulale a wajen Addayiya Kam salati take tana Allah ya jikan ka Allah ya maka Rahama yasa can yafiye maka Nan,Lahab Suna fitowa ana Basu hanya kofar gidan su Lahab yayi kad'an masallacin juma'ar unguwan aka wuce dashi don yafi fili Inda kasan sallan edi haka jama'a Suka taru.

Aje makaran sukayi daman an riga anyi Alwala aka Soma daidai ta sahu,juyawa da Lahab zaiyi saiya hange Ade acan gefen wani gida Yana zaune nesa dasu amma Yana hango duk abinda ake ga hawaye nabin gefen kumatunsa Yana sharewa juyawar da Lahab zaiyi wazai gani Nabeel ne tsaye a sahu wani irin super Lahab yayi yasa kafa ya taka kirjin Nabeel har Saida ya koma baya baya ya bugu da kasa ji kake Tim salati jama'a Suka Fara don a zaton su Koh hauka Lahab ya Fara fuskarsa cikin fushi har wani rawa Naman fuskar cikin rawan muryar sa daya kwana uku baiyi magana bane ta ratsa jama'ar cikin yakini da tsananin tsana ya nuna Nabeel kana yace"wallahi tallahi in baka bar wajen Nan ba zanyi ajalinka Kuma ka sani dan uwana Bai mutu a banza ba bakaci banza ba na rantse da sarkin daya busamin numfashi bazan barka ba.

Hayaniya aka Fara ana tambayar lafiya mikewa Nabeel yayi ya karkade jikinsa kana ya juya ya barwajen bisa umurnin wasu don an zati matsalan rashin Rahab yasa sa haka juyawa yayi ya shiga sahu aka tada sallan gawa,ana kammalawa aka d'auki gawan sai makabarta,Lahab da hannunsa ya Kama gawar aka saka a Rami lokacin da aka tura daidai lokacin jini ya Soma zuba ta hancin Lahab har Saida ya zuba a bakin Ramin a hankali ya d'ago sai Kuma mutane Suka soma salati ana cewa yayi Sauri yaje hospital wannan jini yafi karfin habo,kin zuwa yayi ya tsunguna aka binne dashi kana ya tsunguna agefen kabarin yanama Dan uwan nasa Addu'a gabaki d'aya jini ya Bata gaban rigansa Amma Bai damu ba.

Suna fitowa daga makabarta Lahab ya yanke jiki ya Fadi,Saida aka kwana biyar da mutuwar Rahab kafun ya farfado Mami duk tayi laushi tayi kuka tayi kuka harta gode Allah rashin lafiyar Lahab ya Kara daga Mata hankali Kai bama ga ita kadai ba har dangi sun tsorata kada tarihi ya maimaita kansa akan yaran nan,bare da akace Lahab ya samu heart attack shiyasa jini yake fita a hancin sa Kuma sun bada shawa Koda ya farfado don Allah kada aringa abubuwan da zai daga Masa hankali don zai iya rasa ransa gabaki d'aya haka zalika baza'a Kara basa abinci Mai Kara jini ba,farfadowar sa gabaki d'aya saiya chanja shi baya magana baya cewa kome ba uhmm ba uhm uhm sai dai kaga ya sunkuyar da Kai,toh baya Kara dagawa sai yaji Kiran sallah zai tashi yaje yayi Mami Kan intaga Lahab cikin irin wannan yanayi sai kaga ta fashe da kuka,ita a yanzun burinta Lahab nata nada ya dawo tafi kaunar ganin sa cikin walwala inyaso ana kawo Mata karansa tana Masa fada yafi Mata wannan shurun nasa so dubu duniya kenan waya taba tunanin wata Rana Lahab zai zama haka.

A cikin satutuka da Suka gabata kowa na dangin kokari yake yaga yasa Lahab farin ciki Amma Ina Lahab baisan anayi ba Adewale ma wuni yake tare dashi Yana Masa hirarraki amma Lahab Bai dagowa bare yasan anayi, sau uku Inna da mubeena suna zuwa dubasa,Allah sarki mubeena kallo daya zaka Mata ka gane ba karamin damuwa take ciki ba a rayuwar ta, watan su Lahab biyu a hospital aka sallame sa ya dawo gida, Adewale haka zaizo tun safe suna tare da Lahab Yana Masa hiraraki abubuwa, duk da Lahab baya ce Masa kalallahu sai dare yake tafiya abinci wannan Lahab sai anyi da gaske yakeci so daya a rana yawan tasa hoton su Wanda suka d'auka da Rahab yasa aka kwashe duk hotonan Rahab aka boye,sai Kuma ya koma tsayawa a gaban Miro tayita kallon fuskar sa Kamar tababbe.

Zaune yake a garden na gidan su, Ade na gefen sa sai kokari yake yaga Lahab yaci Koh wani Abune amma Lahab yaki,bude gate na gidan Mai gadi yayi sai ga mota baka kirim guda daya ta shigo gidan mutane uku ne suka fito a ciki Suka nufi cikin flat na gidan ba'a Jima ba saiga Addayiya dasu Abbu tare da mutanen sun nufo garden in,wani irin zaku tafi dashi meya muku gashi Yana under medical don haka koma menene bazaizo ba sai yaji sauki"am sorry sir Dole zamu tafi dashi munso tafiya dashi tun bayan mutuwar da akayi amma mukayi hakuri har yakai iyau"
Chapter 112 · 0% Book details