Sashe 108
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Magana tayi girma a nageria Koh Ina ka leka zancen ake, ashe daman Lahab da yarinyar Nan Suna tare amma yayunsa sukayi tsayuwar daka da naira aka sakesa magana sosai tayita karade Koh Ina da Koh Ina,abinka da nageria babu Inda zaka zaga babu hoton Lahab da family sa,ga case in Nnenna ya Zama sabo, nageria ta Mika bukatar ta ga America na son kamo Lahab a dawo dashi amma Suka kasa samun daman hakan saboda matukar amfani da Lahab yake dashi agunsu haka zalika sukace au Basu da kundin laifinsa Koh daya haka Kuma su a wajen su haihuwa ba tare da aure ba ba abin tashin hankali bane,dole nageria ta hakura yau kwana uku da faduwar abin Lahab Kam ciwo yaki ci yaki cinyewa zazzabi yaki sauka da ciwon Kai ga nazeefa ma na fama da ciwon ciki amma Ita Nnenna ta kaita hospital Kuma jikin nata da sauki sosai.
daren yau Kamar bazai Kai safiya ba saboda yanda ciwon ya tasar Masa ga amai duka, hankalin ta ya tashi Kuma ta tsorata da ciwon nasa don duk yabi ya rame, tunda abin ya faru Koh abinci baya ci sai ruwa,kuka ta sanya Masa da asuba akan kin zuwa hospital da yayi gashi Yana tashi zaije yayi Alwala ya Fadi a toilet,gari na wayewa ta sanya Sabon kuka tare da Kiran Ade yazo tare da ita da Ade Suka basa Baki daker ya yarda Ade zai rakasa suje hospital in,Kaya ya sauka Suka tafi,lamarin kasar turawa su abinda ya faru bai wani Zama abin magana ba Koh labarin abin ba'a Yi,daga isan su Lahab aka kamasa a gado tare da daura Masa laidan ruwa da allurar bacci saboda tsawon kwanaki daya d'auka Bai rimtsa ba.
Sai yamma lis aka sallamo sa daga hospital in Suka nufo gida,tunda Suka tinkaro gidan nasu yakejin wani irin mummunan bugawar zuciya,kamar zatayi tsalle ta fito daga kirjinsa amma sai Kara maimaita kalmar innalilahi wa'inna'ilahu raji'un kawai yake Yana dafe da kirjin,a hankali ya malle marfin motar ya fito a sannu yake takawa Kamar zai Fadi da Sauri Ade yasa hannu ya bude Masa kofar falon yana binsa a baya da laidan magani,turuss yayi ya Lahab ya tsaya a tsakar falon tare da durkusawa daga tsayen da yake zuwa zaune,saboda mutanen da ya gani a falon"Mami ce da wata kawarta Mara mutunci,ga Nnenna zaune akasa Kamar wata marainiya ta wufi y'ay'an ta a gaba Kamar kace kit ta ruga da gudu"karaso bakin munafuki algungumi d'an iska"Mami tace tana mikewa tsaye cikin kakkauran murya tayi maganr babu Koh dogon sassauci a cikin furucinta.
Hawaye ne ya cika a kunyan idanunsa amma ya kasa daga kafarsa daga Inda yake"bazaka karaso bane Koh Sai Nina karaso"?mikewa yayi a hankali ya taho gareta dukawa yayi akan kneel nasa ya riko kafarta kana ya bude Baki da niyar baiwa mahaifiyar tasa hakuri ji kake kauuuukauuuukauuuuu Mami ta wankesa da wasu irin razanannun Maruka masu gusar da tunani take hancin Lahab ya fashe saiga jini Shaaa,Bai damu da jinin ba ya sake yunkurin Kama kafafunta kafar tasa ta hankad'asa gefe.
Sai da ya buge da center table,da gudu yaransa suka nufi uban nasu Suna kuka tun ihun farko da Mami ta daka Masa, Suka tsorata suka Soma kuka, Nnenna ma da gudu ta nufi mijin nata rigan nazeefa ta cire tana tare jinin dake biyo hancin sa,mikewa Mami tayi da Sauri ta Shiga kitchen saigata ta fito da wuka gadan-gadan tayi Kan Nnenna lura da hakan yasa Lahab zabuda da Sauri ya ture hannun Nnenna daga jikinsa ya turata gefe har Saida ta Fadi da ita da yaran akan rashin sani ta sauka a hannun nazeefi wani irin kukan azaba yaron ya sake Wanda Koh tantama babu kariya ya samu a hannu"nuna Nnenna Mami tayi da wukar tana zare Ido tace"wallahi summa tallahi Kika kuskura Kika Kara tinkarar yarona Koh inuwar sa saina daba Miki wukar nan Inga waye ubanki,Yar iska karuwar mayya kinzo kin likema yarona Yana mutuwa akanki harda haifan shegu toh wallahi badani ba kaf zuriyana dana ubansa babu shegu baza'a Fara akansa ba.
Lahab da hankalin sa ya tashi da Sauri ya nufi nazeefi don ganin meya faru dashi"wallahi tallahi Inka Kara taku daya a wajen saina tsine maka albarkan jikinka Lahab,karkaga kowa ya zuba maka Ido kafi karfin kowa toni uwarka Zan nuna ikona,tsayawa Lahab yayi Bai Kara Koh taku daya ba yanajin wani irin zafi a ransa Jin kalar kukan da dansa yake itama nazeefa tana tayasa Nnenna sai faman girgizashi take amma yaki shurun,shima Lahab baisan lokacin da kuka ya kubuce Masa ba, Adewale dake tsaye a tsakar falon har yanzun wani irin kukane ya tawo Masa da Sauri ya fita a falon ya wuce flat nasa dakin sa ya shiga ya kulle Yana sakin kukan tausayin yaran sai Kuma ya sake fitowa ya koma falon, karasowa yayi yasa hannu zai d'au nazeefi da niyar kaisa hospital yaji Mami tace"toh bakin munafuki d'an arna dakai da yar'uwar taka kunzo kun likewa d'ana, waya sani ma Koh kaika Mata cikin......haba Mami haba Mami wannann wani irin magana ne Taya zakina shegantamin yara tass tasss Mami ta sake wanke fuskar sa da Mari kana ta nuna Adewale"Kai aje yaron Nan"?
Mami ciwo yaji fa a hannu"uwarka nace uwarka dan iska kawai sakeshi ya mutu ma Mana dan ubansa"keee ta nuna Nnenna mike maza ki tattara shegunki kubar ma d'ana gidan sa Koh a mafarki karki sake tunanin Zaki Kara rayuwa dashi shegiya mayya makashiya Ashe kina Nan kina like da dana ya makale Miki baya ji baya gani toh wallahi daga yau kome yazo karshe indai Nina tsunguna na haifi Lahab,mikewa Lahab yayi da gudu ya nufi Mami dukawa yayi ya Soma wani irin kuka Yana Bata hakuri akan dan Allah kada ta koreta dan Allah wallahi ya tuba yabi Allah bazai Kara rashin ji ba,tsawa Mami ta bugawa Nnenna tare da nuna Mata kofa"dan Allah mama kiyi hakuri Bari naje daki na dau kayana"Nnenna tace hawayen tausayin kanta dana yayanta harma da mijin nata Yana ratsata ga yayanta sai kuka suke.
Waye uwarki Allah ya tsareni da had'a zuriya da mayu,Kuma Uban me kika zo dashi gidan Nan bare har Zaki dau Abu?babu abinda Zaki d'auka karuwa kawai"rumtsa Ido Lahab yayi yanajin kansa na wani irin juyawa Jin sunan da mahaifiyar sa ta Kira matar sa dashi"ah haba hajiya Amina ki barta ta dau Koh suturun su ne,da Visa tunda Kinga tana tare da yara"kawar Mami da jikinta ya gama sanyi ta fada don harga Allah sun Bata tausayi.
Babu abinda zata d'auka taje ta mutu da yaran, Khadija bazaki fahimci yanda nakeji a Raina bane da ace wani nakine yayi abinda Lahab yayi da wallahi baza kice haka ba,tafiya Nnenna ta Fara a hankali zata fita a falon da Sauri Ade ya matso kusa da Mami ya Soma Bata hakuri akan ta bar Nnenna ta dau wasu abubuwan daker de aka samu Mami ta yarda zuwa lokacin har Nnenna ta fita a gidan da gudu Ade ya kirata ta dawo dakin ta shiga ta aje yaran akan gado sai kuka suke nazeefi har hannu ya kumbura yayi dam dashi jajazer kuka ta Soma a hankali ta jawo akwati ta bude, Madaran yaranta ta Soma sanyawa a ciki sai pampas nasu da kayan su dasu flask kayanta Koh kala daya Bata d'auka ba na yara take sawa, ta Shiga Neman visanta don ba ita ta aje ba Yana hannu Lahab.
Har lokacin gwuwowin sa na kasa hawaye baibar zuba ba mikewa yayi a hankali ya nufi dakin da Nnenna ta shiga Mami dake zaune sai huci take tsawa ta daka Masa tana tambayarsa Ina zaije namamajo duk ya Kare a gindin karuwa"dan dakatawa yayi sai Kuma yace dan Allah Mami kiyi hakuri na dauko Mata visan ta don Bata San Inda na aje ba"wani uwar harara ta watsa Masa,kawarta tace yaje,da Sauri ya shigo dakin daidai lokacin tana zuge zip na akwatin karasowa yayi bakin gadon da Sauri yasa hannu ya d'auki nazeefi tare da d'aga hannun aiko Nan yaro ya Kara karfin kukan har wani kwarewa yake gabaki d'aya sun cika dakin da kara,aje yaron yayi ya nufi Nnenna da tunda ya shigo dakin bata d'ago Ido ta kallesa ba rungumar ta yayi a hankali kana yace"dan Allah Nnenna kada ki tafi,sai Kuma ya mike da Sauri ya fita a dakin,sai Kuma ya dawo dauke da wani envelope ya shigo dakin Mika Mata yayi yace"gashi visan ki na ciki da ATM card nawa kidau yaron Nan kuje hospital a duba hannun sa,kome ya Kama kiyi kawai sannan dan Allah karkibar London ki zauna daidai kome ya daidaita ga wayarki zamuna communication"?
d'aga Ido tayi ta kallesa sosai jikinta yayi sanyi ya bata tausayi ita Karan kanta tasan Lahab na sonta so na gaskiya bana Wasa ba"Lahab kayi hakuri amma wannan karon ya Kamata nayi abinda ya dace"zaro Ido yayi yace"meya dacen kenan kike nufi"?dafa sa tayi a hankali Suka zauna a bakin gadon yasa hannu ya dau yaronsa Yana girgizawa"Lahab banason Inga an cigaba daga inda aka saya ya Kamata wannan Karo na yankewa kaina abinda ya dace Koh na zauna dakai toh bani da kima a idanun dangin ka kallon karuwar Nan har abada shi zasuna min,don haka Ni Zan tafi ban maka Alkawarin Zama a London ba amma na maka Alkawarin jiran ka har karshen rayuwa ta mundin tsawon Rai Zan jiraka wannan *ALKAWARIN MASOYA* ne.