← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 122

Sashe 23

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rufemin baki koh namaka abinda yafi na jiya d'an iska zauna anan, yana maganar yana nuna masa kasan tiles, kin zama lahab yayi sai da abbu yasa baki kafun ya zauna.

Kallon sa abbu yayi, yanzun lahab ka kyauta kenan kaje ka kama abokin ka kamasa duka kasan yaron laulayine dashi haka ake abota da dambe?

"Wallahi yaya shiya fara wai fa akan uncle ya bugesa shikenan yace wa yaya d'an iska shine na babbuge sa"

Kallon sa muxammil yayi nine dan iska kuma nabeel ne yace?

"Eh yaya"

Kamin daidai tashi ka tafi ka sanya uniform maza-maza 'yan uwan ka sun tafi makaranta.

Ai jin haka tuni inna ta soma bala'i don an gansu talakawa shine za'a cucesu a hanasu kuka, Allah ya isawa jikan ta, addayiya dai sai hakuri suke bata ita da Abbu amma muzammil kam mikewa ma yayi yabi lahab d'aki yana jiran sa ya gama shiryawa yakai sa makaranta.

*******************
Nnenna daren jiya koh lafiyayyen bacci bata samu ba wani irin tarine yake damun ta tanayi tana aman yawo mai yauki,haka ta tashi da safe da taren kamar zata mutu, koma bata fad'awa kowa ba, haka take ta fama da azaba.

Tana tashi da safe koh aikin sharan ta kasa don tana farawa da kura ya shigar mata hanci ji tayi kamar numfashin ta zai d'auke.

Hakan yasata kasa aikin gashi Dad bai kwana a gida ba sunje wani gari yad'a addinan su, gashi Abrahama bai isa ya shiga harkan ta mom nanan ba.

Yau peace doya ta soya musu da miya, har Nnenna ta iba mom ta kwace ta mayar kitchen tace tunda batayi aiki ba bazata bata abinci ba, Allah sarki rabon Nnenna da abinci tun daren shekaran jiya amma jiya cur abinci mai nama ake koh ta iba ba ita keci ba.

Ba yanda ta iyya haka ta sanya uniform nata ta d'au jakan ta datake jinsa yau ya mata mugun nauyi harda kule a ciki don har yanzun ba'asan tana zuwa makaranta da kule ba, fita tayi a gidan tana takawa da kafa ga kirjinta dake mata nauyi sosai ga tari ga nauyin jaka kallonta ma yau ya kara duhu duk da akwai glass a fuskar ta ga jiri dake dibarta, a haka take tafiya kad'an ta huta ta tafi kad'an ta huta.

********************
Lahab na sanya uniform abinci ma muzammil ya hanasa ci haka ya tura keyar sa har cikin mota suka wuce school.

Suna isa office suka fara nufa sosai ya kara jaddadawa disple kula da lahab, tare da karban number sa, har class ya raka Lahab kafun ya tafi, yana tafiya lahab dake zaune a bench sai malamin su dake koyar dasu, ga disple a tsaye a window, shammatar su lahab yayi ya hau window d'aya kusurwar ajin ya dirka.

Disple ma da gudu yabi ta cikin ajin ya hau window ya dirka yana bin lahab da gudu lahab na gudu, a haka suka soma zagaya makarantan sai da suka shigo tsakiyar makaranta disple ya fara cewa malamai a taro masa lahab, aiko take aka fara tare-tare sai lahab yazo saitin ka sai ya kauce yabi d'aya gefen, abinka da mayen ball, ana haka disple saura kad'an ya kama lahab kawai ya shammace sa ya kauce take disple ya fadi ji kake timmmm.

Me yara dake classes nasu zasuyi in ba dariya ba, da gudu lahab yayi cikin gonaki, daidai wani bishiyan gadina yahau har reshen sama ya zauna.

Disple na samu ya mike cikin burga ya bi bayan lahab cike da kunya, amma yayi iyya dubawan sa bai fahimce inda lahab ya nufa ba, dole tasa sa komawa cikin makaranta, amma yaki kiran muzammil kaman yarda sukayi duk abinda lahab yayi a kirasa a sanar dashi, gudun kar muzammil yaki kara masa kudi kamar yanda yace masa muddin ya saka lahab zaman class duk wata yana da 10k.

Lahab kam gyara zaman sa yayi akan bishiya ya zaro wayar sa yana dannawa duk da yana jin yunwa amma baici ta sauka yanzun ba don get na school in d'aya ne.

*************************
Nnenna ba ita ta isa school ba sai kusan 10 na safe, lokacin an fita break ma tana shigowa mai gadi ya hanata shiga duk yanda tayita masa magiya ki yayi karshe ma sai yaje ya kira principal, yana zuwa yace mata bafa zata shiga school in ba, haka tanaji tana gani aka hanata shiga.

Zama tayi a bakin get na school in sai tari take da amai, wanda yasa maigadin bude karamar kofa ya lekota tambayar ta yayi lafiya koh dai bata da lafiya ne?

Kuka ta sake tana had'asa da iyayen sa akan yabarta ta shiga ciki, amma yaki karshe dai daya tausaya mata yace zai barta amma karta shiga aji tunda dai principal ya hana bai kamata ya barta ba.

Gyada masa kai tayi ta sabe jakanta tashiga cikin makarantan direct hanyar da ta saba zama watoh gonar makaranta gunta nufa a hankali take tafiya tana dafe kirjinta harta iso gonar, nusawa tayi ciki sosai har gindin bishiya ta zauna tana haki.

Lahab dake saman bishiyar jin motse yasa sa kara labewa da kyau gudun kar a gane akwai mutum akai.

Tari Nnenna ta fara da karfi tana amai ga kuka data fashe dashi na wahala, jin kukan mace da tari yasa lahab leko kansa ta gindin bishiyar, ga mamakin sa mace ya gani zaune ga dukkan alamu Christian ne kanta a duke tana amai.

D'aga kafad'a yayi irin ba ruwan san nan yaci gaba da abunda yake, amma dai ya kasa samun nutsuwa jin yanda take tarin tana kiran jesus.

Daga kan bishiyar yaji karan bugun bell da sauri ya duba agogon hannun sa 10:30 watoh sai lokacin aka koma break kenan, amma har lokacin Nnenna tari take tana haki kasa hakura yayi ya kama reshen ya dirko daga saman itacen.

Nnenna dake duke koh d'ago kanta batayi ba saboda hakin da takeyi, binta da ido kawai lahab keyi zuciyar sa na wani irin wawan bugu, tsungu nawa yayi a gabanta,"ke baiwar Allah lafiya"?

Koh D'agowa batayi ta kallesa ba, duk da taji mutum a kusa da ita harma magana yake cikin hausa don ita bajima take ba, amma halin da take ciki bazai bari ma ta saurare waye bane.

"Ke ba magana nake miki bane kin mini banza sai kije shan ki mutu tunda baki san hanyar clinic b......bai karasa ba ya dakata saboda d'ago ido datayi ta kallesa, gaban sane ya fadi cikin tsananin tarin mamaki da Al'ajabi wannan kuma yaushe ta shigo school nasu ga kyaun ta har yanason yafi karfinta.

Da sauri ya mike zai bar wajen, cikin gegeta Nnenna da numfashin ta ya soma d'aukewa ta kamo hannunsa, magana take son masa amma tari yaki barinta sai sarke ta yake, kara matsowa kusa da ita yayi shima yayi linkdown kamar yanda tayi, yana rike kafad'ar ta ganin jikinta sai bari yake,"wai lafiya baiwar Allah ba baki da lafiya bane? kije clinic mana"

Baya baya tayi luuuu zata fadi, da sauri yasa hannu ya tarota ta fado a kirjinsa, bugawa kirjin nasa yayi da karfi fiye da da, wannan abune daya zo masa a bazata koh yace sabo a rayuwar sa, tunda ya girma yayi wayo koh wasa da mata bayayi bare ma har su taba masa jiki, inka cire muharraman sa, sai yau ga yar inyamurai dumu-dumu a kirjinsa.

Hankalin sa a tashe ya soma girgizata jin gabaki d'aya ta sake numfashin ta baya fita, "nashiga uku kar yar mutane ta musu a hannuna" yana maganar yana mikewa tsaye ciccibar ta yayi da dukkan karfin sa ya wanshakalar da boronta da wayan sa ya goyata a bayan sa da gudu ya nufi school Area da ita.

School clinic ya nufa da ita Allah ya sosa ma an koma break babu dalibai a waje, kuma hankalin su bai kawo kansa ba, da gudu ya shiga cikin clinic sai kwalawa Dr kira yake su karan kansu Dr da nurse hankalin su ya tashi ganin Nnenna koh motse babu.

Kwantar da ita akayi a gado bayan karban ta da akayi a bayan lahab, a take likita ya rufu a kanta, pharmacy aka je aka karbo ruwa dasu Allurai shap-shap aka d'aura mata ruwa nurse tazo ta d'auki jinin ta zuwa lab.

Lahab dai na zaune a Kan kujera a bakin d'akin ya zabga tagumin tausayin baiwar Allah nan kome ke damunta sai Allah, yana nan zaune sai ga principal ya shigo da sauri yana tambayar wace yarinya ce aka kawo, anan lahab ke sanar dashi shima bai santa ba.

D'akin da take kwance ya shiga ganin Nnenna ne yasa sa fita da sauri yad'au waya ya kira mom, amma kusan 2 hour's babu wanda yazo daga gidan su Nnenna, karshe dai dole tasa principal d'auko wani Dr daga babban asibiti sukayi su biyu ana ta kokar tawa sai kusan 1 na rana Nnenna ta gane hankalin ta.

Likitan ne ya fitoh a d'akin kallon lahab yayi dake zaune a kujera ya buga tagumi, kai ne ka kawo ta?

"Yes sir nene ya jikin nata"?

Da sauki iyayen ta sun zo ne?

"ah ah sir principal yace ya kira mom nata amma har yanzun shuru ba wanda yazo shiysa ma na zauna nake jiran su zo kar na tafi a nemi wani abu bamai sayowa"

Karka damu duk abinda za'a mata daman d'awainiyan makaranta ne, don daman a cikin school fees naku akwai kudin jinya, sannan ka sameni a office zamuyi magana.

"Ok Lahan yace ya mikewa yabi bayan Dr.

Suna zuwa office likitan ya masa nuna da kujera ya zauna, ba musu lahab ya zauna yana kallon likitan jin tambayar da ya jefo masa wai yasan Nnenna?

"Gaskiya Dr ban santa ba"

Ok koh ka san gidan su koh wani nata?

"Gaskiya Dr ni ban taba kallon ta bama sai yau wani abun ne ya faru"?

Gaskiya kam ga dukkan alamu yarinyar nan bata tare da iyayen ta.

"amma likita meyasa kace haka"?
Chapter 23 · 0% Book details