← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 122

Sashe 35

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Eh gidan kune Amma nasan tabbas zaman ka a ciki bazai yuba ban hanaka zuwa ba Amma gaskiya Banda ikon ja da maganar da Hamma zaice Kuma nasan Koh yace ka zauna muzammil bazai amince ba don haka bazance kome ba.

Shuru Lahab yayi yana tunanin abinyi don shi harga Allah baison Zama a gidan yafison sai muzammil in sun koma kafun Shima ya koma,mikewa kawai yayi ya fita a dinning in,bangaren su Hashim ya wuce direct ya bude kofar dakin ya shiga zaune ya samu Majid a Kan kujera Yana waya ga dukkan alamu da mace yake wayar sai wani make murya yake kamar kwarto,kwanciya Lahab yayi akan gadon Yana wani irin jinsa incomplete Yama rasa tunanin me xaiyi na damuwar abokin sa Ade Koh na Nnenna dake son samun waje a zuciyar sa.

Ok baby Zan kiraki anjima ok Love you too,Majid yace Yana yanke wayar in kallon Lahab yayi,Kai mutumina kwana biyu baka lekomu ga Uncle ya samin Karan zuga shiyasa na daina zuwa gidan ku kwata kwata.

tsaki kawai Lahab yayi sai Kuma yace"mtwssss kaga aramin wayan Nan naka kabarni da abinda ya dameni"

Mika Masa wayar Majid yayi,a gaskiya Lahab kana ganin takura wannan uncle muzammil Nan anyi mugu wallahi shiyasa bana ma yarda na hadu dashi last dana hadu dashi ma a kofar school namu na gansa lokacin Muna level100 kaga an Jima Kuma ba zuwa gidan Nan nake ba.

"Taya zaizo Majid bayan basa shiri da nannen ka kasan shifa duk Wanda xai taka Masa birki akan hukunci toh fa sun Kulla tsama kenan"

gaskiya Kam don nanne ta dade da manta rikicin Nan Amma shi har gobe Yana Kan bakansa na gaba.

dariya kawai Lahab yayi Yana Kara wayar a kunnen sa bayan ya loda number Adewale a ciki, ringing uku yayi ba'a d'auka ba karshe ma rubuta Masa messagei yayi ya tura Masa.

*************
Adewale dake kwance abin duniya ya damesa ya rasa ma da wanne zaiji da masifar papa Koh da matsalan mubeena don shidai bai wani d'aga hankalin sa ba Akan Case in school Sam,yaji ringing in wayan sa Amma ya kasa tashi ya d'auka gani yake duk Mai kiransan Nan baida damuwa ne,Amma Jin shigowar sako yasa sa mikewa zaune a hankali tare da dafe Kan nasa Jin yanda yake azaban ciwo sosai hannu ya Mika ya kunna wutan dakin wayar nasa ya d'auka ganin an turo Masa sako da Sabon number,"Ade Lahab ne pls pick the call kaji"

tsaki kawai yaja don harga Allah haushin Lahab yakeji ganin harda Shima baiyi supporting na soyayyar sa ga mubeena ba.

Komawa yayi ya kashe wutan dakin ya kwanta tare da aje wayan a gefen sa wasu kiranne Suka ringa shigowar Yana basarwa gajiya yayi Kuma ya kasa hakuri sanin da yayi in dai har Lahab nama mutum nacin Kira haka toh da biyu me, daukar wayar yayi ya Kara a kunne,Hello..

Ta bangaren Lahab Kam sai Kira yake duk da Ade bai d'auka ba Amma haka bai hakura ba bai Kuma kula Majid dake masifa ba Wai dole ne sai babyn nasa tadau call in ya Kira so daya bai Isa ba.

Jin Adewale yayi picking Yana cewa hello"Ade fushi kake dani"?shine tambayar da Lahab ya Fara Masa.

Eh Lahab fushi nake dakai.

"Akan. Me toh"?

Au tambayana ma kake Lahab bakasan me kamin ba?

"Indai maganar dazun ne kayi hakuri Amma gaskiya na fada maka"

Jin abinda Lahab yace yasa Ade uhmm kawai baiyi magana ba.

Shuru Lahab yayi Jin bai basa amsa ba a hankali yace"baka da lafiya ne friend"?

Babu abinda ya shafe ka da rashin lafiya ta Koh lafiya na yanzun dai ka Fadi abinda yasa ka kirani in Kuma baka da abin fada na kashe wayata?

rike Baki Lahab yayi cikin mamaki don shifa bai d'auka Ade zai dau maganar daya fada Masa da zafi ba,a ganinsa me amfanin zaman tare in baza'a fadawa juna gaskiya ba"shikenan Ade Allah ya baka hakuri Amma wallahi kaf duniya Mai sonka ne kadai zai fada maka gaskiya Amma tunda ka nuna baka so is ok,daman maganan da Zan fada ma shine daman zance maka akan Case na makaranta gobe Kar Wanda yaje.

Jin abinda Lahab yace yasa Ade kase wayar ya kashe gabaki d'aya ya wurgar Yana tsaki Yana cikin wannan matsalan da zullumin soyayya har Yana da bakin kawo Masa wani case na school in banza.

Bayan Lahab ya aje wayan kallon sa Majid yayi yace,toh Wai nikam Lahab me dan Arnen Nan yake bakane da har zaina ma wulakanci Ni wallahi na tsani yaron Allah.

Koh kala Lahab baice Masa ba sai kwanciyar sa da yayi,mikewa Majid yayi ya dawo gefen Lahab,yau akwai birthday party na wani friend nawa yau da da dare Koh zakazo muje?

Kallon uku sauran kwata Lahab ya masa cikin masifa yace"a daren nan kake maganar muje fati ka gannin nan Ina dawowa sallan Isha bacci Zan kwanta nayi banson damuwa"

Kutt sai kace mace Kai dai wallahi anyi matsoraci menene a ciki don munje partin dare?

Mikewa kawai Lahab yayi ya wuce toilet yayi Alwala tare da kallon Majid,toh nidai babu Inda zani kaida kaga zaka iyya sai kaje,Yana karasa maganar ya wuce masjid.

Bayan sun dawo kwanciya Lahab yayi Amma Ina ya kasa bacci gabaki d'aya ma ya rasa meke Masa dadi ya rasa nutsuwarsa kwata kwata so yake yajisa cikin kwanciyan hankali Amma Ina ya kasa sosai,Yana kwance likimo yayi a blanket Yana kallon Majid ya wuce bandakin xaiyi wanka ganin 9 na dare yayi.

Lahab dai na kwance har ya fito wanka yazo Yana shiryawa Harya Gama zai fita sai Kuma Lahab ya mike"dan jirani Majid mu fita wallahi na gaji da kwanciyar Nan nama kasa baccin kwata kwata"

Kadaiji dashi lokacin dana ce kazo mu tafi aiki kayi sai yanzun dana shirya zaka wani ce in jiraka toh bazan jira ba,don zaka sani late a banza.

Da Sauri Lahab ya mike"kama Isa party makaranta ne Koh ma'aikata da zakace kayi lattin"Yana karasa maganar ya shiga toilet Zama yayi Yana jiran Lahab.

Shafshaf ya fitoh ya bude wardrobe in Majid ya zaro kayan Majid in wando da riga Mai azabebben kyau wando baki sai riga fari da takalmi Baki yayi kyau sosai Suka fita tare Amma abinda ya bawa Lahab dariya da mamaki Ashe Wai Bata gate zasu fita ba"Wai Majid ya Naga haka baga kofar falo ba Naga Kuma kana bin wannan corridor in Ina zamu"

Mtwss rabu dani pls Lahab yanzun nufin ka ta kofa zamu fita toh Bari kaji Daddy yace Kar security su Kara barina na fita sai da izinin sa.

"Toh yanzun ta Ina zamu fita in ba ta kofa ba"?

Kazo Mana zaka gani Suka Isa bakin wani kofa key guda uku a hade ya zaro a Aljuhun sa yasa wa kofar ya bude tare da kamawa ya wangale kofar.

Fita yayi Lahab ma ya fita kafun ya maida kofar ya rufe Lahab Kam bin wajen yayi da kallo bayan flat nasu ne Wanda ba kowa zai d'auka akwai kofa a wajen ba kasancewar garden ya kewaye wajen Harya boye kofar,gaba Majid ya Kara Lahab na. Binsa a baya har Suka iso wani kofar gate Wanda ake Kira da back door na gidan Nan ma key Majid yasa ya bude kofar Suka fita kafun ya maida kofar ya rufe harda Murda key.

Bayan layin su Majid Suka bullah Wanda nisan sama daga babban gate na gidan zuwa Inda Suka bullah tafiya ne Mai tsawo sosai.

Waya Majid ya d'auka yayi Kira ya kafa a kunne,yes na fitoh ka karaso muna kusa da wajen suya,Yana aje wayan ya kalli Lahab dake ta kallon sa don shi wallahi sosai yake mamakin abin ashe duk rashin jinsa Majid ya damasa ya shanye tunda shi baitaba ya fita gida a boye ba cikin dare,muje Koh Lahab wajen Mai suyan Nan mujirasa a wajen.

takawa sukayi sukayi danyi tafiya kafun Suka iso wajen wani Mai nama Zama sukayi a gefen sa Suna jira Kamar yanda Majid yace.

Ba'a Jima sosai ba sai ga wata azabebben mota tayi packing a gaban Mai nawan kadan mikewa Majid yayi ya kalli Lahab,muje.

Mikewa Lahab yayi yabi bayan sa,bude gaban motar majid yayi ya shiga Lahab ma baya ya shiga yaron dake tuka motar bazai wuce 21 ba zasuyi tsara da Majid ma Yana tukin Suna shekiyanci da Majid d'aga ganin sama dan gata ne sosai Kuma dan manya,Dan juyawa yayi ya kalli Lahab,sannu Lahab Koh? ai Majid na bani labarin ka sosai Amma bamu taba haduwa ba sai yau.

"Ayya,kaiwai Lahab yace Yana bin titi da kallo ta glass in motan don shi yanzun ba surutu bane a gaban sa,kyelesa kawai faruk Abu ke damunsa shiyasa ka gansa sai wani basarwa yake,Majid yace don yaji kunyan abinda Lahab yayi Masa yanda yake bawa faruk labarin sa ba haka ya gansa ba.

toh Allah ya gyara Mana shine abinda faruk yace sukaci gaba da hiran Yan Mata sunata surutun su Amma Lahab baice kome ba Yana daijin sune kawai.

20 minutes ya kaisu wani kayatancen hotel Mai shegen kyau tun d'aga gate zaka gane lallai ana party Kuma na manyan yara yaran ma matasa shiga gate in sukayi faruk yayi packing a packing space dake hotel in duk Suka bude kofofin Suka fitoh,bin wajen kawai Lahab yayi da kallo tunda suke shida su Ade basu taba zuwa waje irin wannan ba ga yan Mata Kota Ina ga matasa Nan birjib wasu na shiga Hall wasu na fita wasu na Hira a waje.

Zuwan su Lahab shiya d'auki hankalin matasan dake wajen a take Suka Soma ihu suna sowa,gaaa MJ ga MJ da fazey.

Wani doro majid yayi Yana wani dan iskan tafiya irin na Yan iskan Nan shida faruk har Suka Shiga cikin hall in tsabar fasa Kai sun ma manta da Lahab,shikam ganin wasu kujerun plastic dake kusa da flowers da aka kayata hotel in dashi yasa sa matsawa ya zauna akan kujerar Yana bin Koh Ina na haraban hotel in da kallo har idanun sa Suka fada kanta tana tsaye sanyi da wani Y'an iskan wando da riga sun matukar matseta sai gashin attach dake zube a gadon bayan ta fuskar Nan Tasha make-up sosai.
Chapter 35 · 0% Book details