Sashe 48
Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ameen Adda tace ta Mike tabar dakin,ajiyar zuciya kawai Ruky ta sauke tare da kwanciya akan katifar ta.
Adda na fita daga dakin nasu wajen mama takoma Zama tayi tafara ma mama magana,uhmm mama kinsan Ruky da rashin hankali Wai harxata samu Mai sonta da aure ta tsaya tana yanga?
Mikewa zaune mama tayi d'aga kwance da take a taburma,kaji Yar banzan yarinya zata sake reshe ta Kama ganye watoh abinda ya faru tsakanin ta da Nasir baisa tayi hankali bako?
Kedai Bari mama Wai saurayin kawar Nan tata mubeena take Koh wa? tace batason Yaron shine fa shi Kuma yaga Rukayya Yana so Wai ta tsaya tana lagwa-lagwa Yar banza in tayi aure Ina zataga ita mubeenar bare ta tuna saurayinta ta aura?
Uhmmm lallai Rukayya bata gaji da zaman gida ba Aiko wallahi Koh bataso Ni Zan ma baban ku magana in yaron ya sake dawowa ace ya turo don ubanta a halin da muke cikin Nan Nan gaba ma kudin makarantan nata ba iya biya zamuyi ba sannan ta samu Mai son auren har zata tsaya wani kafli da badi mubeenar kanwar uwarta ne Koh na ubanta?
dariya ne ya kufcewa Adda Jin yanda mama ta zage sai masifa take harda cewa zata shiga dakin nasu ta samu Ruky taci Mata mutunci daker Adda ta samu ta sassauta masifar tare sayin Alwala ta wuce dakin ta bayan tama yaran Saida safe, daman baba ya shiga tuntuni,Adda ne ta Mike taje ta rufe kofar gida ta karkata kannen nata zuwa cikin dakin su kwalli d'aya da suke kwana dukansu su biyar a ciki, Nan ma ta mayar da yaranta biyu kenan gidan baban su shiyasa Suka samu saukin matsin da suke ciki na wajen kwana don daki biyu garesu daya na mama da baba daya nasu.
*******************
Mahaifiyata Kika Mara?kallon Anwar Mami tayi kafun tayi magana,eh na mareta Anwar na mare uwarka Koh zaka rama Mata ne nasan lalle kunsha a no-no?
Umaima data shigo durkusawa kawai tayi a wajen tana kuka Anwar har lokacin Yana Nan a tsaye yayin da Shareef ya sunkuyar da kansa a kasa uwa uwace duk da mamarsu ce bata da gaskiya amma yaji mugun haushin Mami na marar Masa uwa bare ma Mami da kadan ta girme Anwar don kwata kwata bata wuce shekaru 35 ba a duniya ba.
Mamu da tayi mutuwar tsaye hannunta dafe da kumatu tana bin yaran nata da kallo ganin gabaki dayan su babu Wanda ya yunkura zai rama Mata hawaye ne ya cika a idanunta lokacin da takai dubanta ga Abbu muzammil da Addayiya babu Wanda ya nuna Koh damuwa a fuskarsa,da gudu tayi kitchen ba'ajima ba sai gata ta fitoh da tabarya tayi Kan Mami, wallahi yau sai nayi ajalinki saikin gane baki da wayo harni Zaki mara,ta d'aga tabaryar da karfi zata bugawa Mami,gabaki d'aya Yan falon mikewa sukayi cikin bacin Rai Abbu ya daka Mata tsawa,wallahi halima in Kika buga Mata tabaryar Nan a bakin auren ki na gaji da halayen ki a gidan Nan, shekaru sunja amma ke banga hankalinki ya daidaita ba.
Mamu Kam kafewa tayi da tabarya a hannu har lokacin kunnenta baibar jiyo Mata da abinda Abbu yace Mata ba, a tsawon zaman su bai taba Mata wasan saki ba bare barazana sai yau,Wai Ina zata sa Mami ta daina kallonta ne? ga ummu itace kishiyarta amma batajin kishinta Kamar mami,Wai inkin buga Mata a bakin auren ki?ita Haleema Kuma a gaban yaranta.
gabaki d'aya jama'an falon sun girgiza da maganar Abbu sosai Wanda hakan yasa Addayiya kasa hakuri hartayi magana,Kai Umaru wannan wani irin rashin hankali ne mekake cewa haka so kake ka dasawa yaran ka wani tunanin daban a ransu ne Koh Yaya?kace zaka saki uwarsu akan uwar wasu,yau Haleema da Amina Suka Suma tsama ne da zaka Fadi haka kul bana son sake Jin magana irin wannan.
Jan numfashi Abbu yayi sannan a hankali ya koma Kan kujera ya zauna tare da dafe kansa shikaran kansa yasan hakan bai kyautu ba amma ya zaiyi ransa ne ya baci yasan halin Halima da rashin hakuri,ummu Kam Koh a jikinta yima tayi Kamar bata San meke faruwa ba sai daddan na wayanta take,Mami Kam juyawa tayi zata bar falon da Sauri Lahab ya kirata,Mami ayya jirani Ina zuwa minutes biyu tsayawa tayi shikuma da gudu ya mike yayi cikin falon su daki ya shiga a hargitse ya zaro akwatin kayansa ajewa yayi a kasa tare da bude wardrobe na kayansu jido kayayyakin sa yake Yana jugawa a akwatin Koh takan Nade baibi ba takalma duka ya zuzzuba har Saida akwatin ya cika yaja zip da sauri ya dau jakar makarantan sa ya goya tare dajan akwatinsa ya fita a dakin kofar falonsu ya bude ya fita.
duka Yan falon da Ido Suka bisa ganin sa. D'auke da Kaya Niki Niki ya nufi mami hannunta ya Kama Suka nufi kofar ba tare da yayi magana bama,Kai Rahab Ina zaka kayan Nan fa?Abbu yace Yana kallon sa a tsorace don harga Allah baison ganin fushin Rahab gara Masa na Lahab kunayin abu anjima ya watsar amma wannan shegen rikone dashi da d'acin Rai.
Juyowa Rahab yayi cikin girmamawa yace,kayi hakuri yaya ban taba sanin cewa zaman na da dan uwana shiga hakkin ku muke ba sai yau,ga gidan Nan mun bar Mata sai ta rayu daga ita sai yayan ta da wa'inda takeso ba shikenan ba?
Kai ba shikenan ba dan uwarka kana da gidan da yafi wannan ne Koh gidan da zaka yanzun na ubanka ne?Addayiya ce tayi maganar a zafafe Shima Rahab a zafafe ya Bata amsa,bana ubana bane amma Ina da tabbacin babu Wanda zai goranta mini daki a gidan Koh uwata Koda kuwa shekaru dubu zamuyi a cikin sa,mikewa muzammil yayi Jin bakar magana da Rahab kewa mahaifiyar sa,nufo Rahab yayi Kamar wani zaki Yana huci Shima Rahab bai Koh mutsa ba Yana tsaye domin a wannan lokaci ransa yayi kololon baci hannu muzammil in ya d'aga zai kwadawa Rahab a kumatun da Sauri Rahab ya riko hannun nasa jikinsa har rawa yake ya Soma ma muzammil magana cikin kaushin murya,ka tsaya iyya matsayinka na Yayana karka wuce iyyakarka wato na baiwa mahaifiyarka amsa kaji haushi?Ina ga Ni danayi hakuri da irin cin Kashi da kake Ma tawa mahaifiyar baka kallonta da daraja amma a hakan Muke kiranka da wa,don haka baka Isa nima yau kace zaka bugeni akan taka uwar ba,kaji na rantse maka d'aga yau bazan sake bari hannunka ya taba jikina da sunan duka ba in ko ka gwada hakan toh tabbas Zan rama nima karfin Nan babu wanda bai dashi don haka ya isheka haka ya isa bazan lamunta ba bazan lamunta ba kaji na rantse,Yana karasa maganar ya sake hannun muzammil yayi mutuwar tsaye agun Wai shi yau Rahab kecewa inya buga zai rama gara ma in Lahab ne ya fada Masa haka toh bazaiyi mamaki ba amma yau wannan ne ke fada Masa da kansa lallai abin nayi ne,Ni kake cewa zaka buga ai bazanga laifin kaba tunda uwarka bata nuna maka Ina da mutunci ba.
Jin abinda muzammil yace yasa Mami harzuka,Kai muzammil karka kuskura karka soma wallahi in ba haka ba Zan rufe Ido inci ma mutunci kasan Ni nasanka wallahi Ni nafi karfin na nunawa yarana su Raina barema bare dan uwansu kaida yake dama mugun Hali gareka dole kana kallon kowa ma haka,nuna Rahab tayi Kai wuce muje ta bude kofar falon ta fita Rahab na binta a baya da kayansa,mamu Kam sosai taji dadi ganin fadan yabar kanta ya koma na muzammil da Mami gashi Rahab yabar gidan don ita a duniya babu abinda takijini Kamar ta bude Ido taga Mami a duniya da yayan ta Suna walwala Koh cigaban su bataso.
Kuka Addayiya ta sake kafun ta soma magana, yanzun umaru kana ji kana gani amanarka zai bar hannunka karfa ka manta kafun mahaifinku yabar duniya sai da ya baka wasiya Koh bayan ransa y'ay'an sa su zauna a hannunka shine yanzun zaka wani barshi yabi uwarsa yaje Yana agolanci a gidan uban wasu,sai Kuma ta Kuma sakin wani Sabon kukan.
Abbu Kam da kansa ke kasa ji yake Kamar Kan zai tsage ace Yana matsayin babba ga mahaifiyarsa duka zaune Suna fadace fadace a gabansa sannan ga damuwar rashin Inda karamin kaninsa ya shiga na tsawon kwana biyu ga kukan da yanzun Addayiya keyi,dan Allah Addayiya ki rufamin asiri kiyi shuru mubi kome a hankali.
Kin shuru Addayiya tayi muzammil Kam ji yake Kamar ya ketta wa kansa aShana Wai yau shine Rahab yama rashin mutunci gaskiya ne da hausawa sukace karka Kai Mai hakuri bango.
*****************
ai da Sauri Inna ta juya ta kamo kafadun mubeena da karfi ta girgiza cikin masifa tace,keee mubeena ashe baki da mutunci oh baki sonsa toh uban wa kike so nace uban wa kikeso? ki fadamin Mara hankali munafuka kawai Inna tace tana girgiza mubeena dake ta kuka durkusawa tayi a wajen tana wani irin kuka Mai cin Rai da tsoro.
Inna ma Zama tayi a wajen ta Kama Kai tana kuka tana magana,mubeena kin cuci kanki mubeena mekike nema a wajen namiji Wanda Ahmad bai dashi yaro Mai sonki Mai kaunar ki yamiki goma Sha,yanzun da abinda Zaki saka Masa kenan wai kice baki sonsa toh wallahi sai kin fadamin uban wa kike so din?
Shuru mubeena tayi bata yi magana ba haushi ne ya cika Inna Jin sai magana take Mata ita Kuma taki bata amsa,nace Miki wanene In kike so da har Zaki rabu da yaron kirki Mai kawo min goro duk juma'a Ina tambayarki kin min shuru,shuru mubeena bata bata amsa ba hannu Inna tasa ta wanke fuskar mubeena da Mari daidai lokacin Nabeel ya shigo gidan akan idanunsa Inna ta wanke Yar uwarsa da Mari cikin tsoro ya karaso Inda suke ganin su cikin wani irin yanayi na damuwa,Inna lafiya meya faru Aunty mubeena meke faruwa ne?
gabaki d'ayan su shuru sukayi babu Mai magana sai kuka da mubeena keyi Inna na tayata,wallahi ku fadamin meke faruwa Koh Kuma Bari naje na Kira bappa Ado yace Yana mikewa don harga Allah ya tsorata ya d'auka wani babban al'amari ne ya faru bai kawo Koh a ransa akan Ahmad bane.