← Book details Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 122

Sashe 80

Alkawarin Masoya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tashin hankali Nnenna ta sabe wayarta da boron makarantan ta Koh riga Bata tsaya ta d'auka ba don tashin hankalin da take ciki bana Wasa bane, window dakin ta ta waje shita bude,tana bude glasses in ta hau ta dirko ta waje tana dudduba kiki don Bata gansa a dakin ba,take karnukan Suka hafto Jin motse da gudu tabar gidan Suna binta Wanda kukan karnukan shiya jawo hankalin su mom dake falon kasa Suna tsattsaye a kofar dakin Suna bugawa tare da kwalama Abraham Kira, Suka hankalta da kukan karnuka a waje.

da gudu Nnenna tabar layin karnukan basu bar binta ba har Saida ta Shari kwanar barin layin kafun suka koma baya Bata damu da dare bane gudu kawai take tana sa hannu tana Kare kirjinta don gudun da take kirjin zafi yake Mata,layin su Lahab ta Shiga duk da Bata San gidan su ba amma haka kawai jikinta ya Bata Nan ne layin nasu tunda yace mata unguwan su daya,amma Bata canki gida ba a kofar wani gida ta tsaya Inda babu wuta don sauran gidajen kofar gidan solar ne aka kafa haske Kamar Rana ita Kuma a yanda take Bata bukatar tsayuwa a haske Koh dankwali babu daga ita sai wandon bacci da yageggen vest,rasa Ina zata tayi babu Wanda ya Fado Mata a Rai sai Lahab.

So take ta kirasa amma Kuma inta kirasa tace Masa meye?a daren nan,wayarta ta d'auka ta danna Masa Kira Harya Fara ringing da Sauri Kuma ta kashe, mannuwa tayi da ginin tana tunanin in wani Abu ya samu Abraham Ina zata Shiga in Dad ya koreta daman ya Mata kashedi tun farko zuwan ta Amma bazata iyya zuba Ido ya keta Mata mutunci ba..

Lahab dake zaune akan sallaha idar da sallansa kenan don yau mummunan mafarki yayi shiya farkar dashi daga bacci,yayi Alwala yazo yayi sallah raka'a shida,Kamar ance ya d'aga kansa kawai yaga wayarsa dake gefen katifar sa tana wuta don wayar na silent ne, da mamaki ya mike toh wazai kirasa war haka agogon dakin ya haske karfe 2:20 ne na dare mikewa yayi ya dau wayar,ganin Nnenna ne yasa sa bin Kiran.

da Sauri ta dau wayar ganin kirann sa kafawa tayi a kunnen ta"Nnenna"ya Kira sunan ta fashewa tayi da kuka a hankali tace"na'am Lahab"meya faru Kika kirani yanzun lafiya Kam"shuru ta Masa tana nazarin ta fada Masa gaskiya ne Koh ah ah"Jin shuru batace kome ba yasa sa duba wayar ganin tana Kan layi ya sake tambayar ta"lafiya Nnenna"kasa basa amsa tayi saboda gaskiya yau taji tsoro fiye da lokacin da yan fashe Suka taresu yayin shigowar ta gombe,hankalin sa ya tashi wanda ya Sasa mikewa tsaye"lafiya Nnenna kina inane"a hankali tace Ina layinku.

Waro Ido yayi yace"layin mu fa kikace are u out of ur sense kinsan karfe nawa yanzun"?kikace kina layin mu?eh Ina Nan Lahab ka taimake Ni kaf duniya banda Wanda zai taimakamin sai Kai"?ai baisake cewa kome ba ya bude kofar su a hankali cikin tsanda ya fita a dakin tafiya yake a hankali a hankali,Harya iso kofar falon nasu budewa yayi ya fita da Sauri ya karaso bakin kofar gate nasu gate in a rufe yake kirim,hannu yasa yana kokarin bude sakatan gate in irin Mai karfin Nan ne in ka taba sakatansu zasu tona maka asiri.

Maigadi dake bacci da Sauri ya zabura tare da lalubar toshinsa Mai hasken gaske ya fito a dakin nasa Yana cewa wayene daidai lokacin Lahab ya bude kofar ya fita Aiko da gudu Mai gadi ya biyosa a baya tsayawa Lahab yayi ya jirasa Harya karaso kusa dashi Yana tambayar sa Inda zashi"kaga rufe gate Nan Ina zuwa Zan dawo yanzun yanzun Kuma bance ka fadawa kowa ba kanajina Koh baba"amma in............baibari ya karasa maganar ba ya d'aga Masa hannu yace "don Allah kaje nace Koh"ba yanda maigadi ya iya haka ya koma cikin gidan ya rufe gate yayi zamansa bai koma bacci ba Yana tsammanin dawowar Lahab da Kuma Inda zashi.

Lahab na fita ya kunna wayarsa kiranta yayi tana Masa kwatance Harya karaso Inda take kallon ta yayi sau d'aya Bai Kara marmarin kallon taba sai korin shaid'an yake a zuciyarsa jallabiyar jikinsa ya zare ya Mika Mata,karba tayi ta saka,"meya fitar dake a daren nan Kuma a haka babu suturan kirki"?hawaye ta share ta sanar dashi duk abinda ya faru da mamaki yake tambayarta daman Abraham ba yayanta bane Dad ma ba babanta bane,gyada Masa Kai tayi,tunani ya shiga yasan Koh hauka yake bazai dau Nnenna yakai gidan su ba Kuma tace Masa daga Enugu tazo.

A wajen Suka nemi dutse suka zauna sai misalin karfe uku na asuba Lahab ya mike tare da cewa ta jirasa Yana zuwa,gida ya koma lokacin da ya shigo har lokacin idon Mai gadi biyu da Sauri ya shiga dakin nasu har lokacin Rahab na bacci wandon baccin jikinsa ya cire yasa wani wando da riga ATM card NASA ya d'auka,ya bar gidan shidai maigadi sai Ido babu halin tambaya gashi yace Masa Koh Abbu zai nemesa yace Masa ya fita sallan asuba da wuri,da kafa Lahab Suka ringa takawa da Nnenna har wani karamin hotel dake gaban unguwan su kad'an, kama musu Roomi and falo yayi na kwana daya lokacin da suka shiga dakin ce Mata yayi taje ta kwanta a bedroom tunda jiya Bata samu bacci ba shima kwanciya yayi a falo.

Kasa bacci Nnenna tayi har 8 na safe idanunta biyu,Lahab dake bacci Jin Karan knocking in door ya farkar dashi mikewa yayi ya Isa bakin kofan, room service ce ta kawo musu breakfast amsa kawai yayi ya maida kofar ya rufe har ya koma zai kwanta sai Kuma ya mike ya nufi bedroom in,da mamaki yake kallon ta ganin ta a zaune ta zuba tagumi kallo daya zaka Mata kasan tana cikin damuwa.

Xama yayi a kusa da Ida tare dasa hannu a hankali ya Kama nata yace"Labiba ki kwantar da hankalin ki kinji insha Allah Zaki koma gidan ku"?gyada Masa Kai tayi tace"daker ne wallahi mom ta barni na Kara xama tare dasu kaga yanda kansa ya fashe kuwa"?mikewa yayi tsaye yasa hannu ya mikar da ita bandaki ya shigar da ita ya ajeta a toilet sit ruwa ya Iba ya wanke fuskar ta sosai yajawo towel ya goge Mata tare da cewa"tunta bazakiyi bacci ba ai shikenan sai kizo kici karyawa ga yanda idanunki Suka kukkumbura fa"?

Banajin yunwa,da Sauri yace ai Baki isaba wallahi shige muje da karfin dole ya fito da ita falo har lokacin jallabiyar sane a jikinta abincin ya bude Mata shinkafane da doya,tura Mata yayi a gaba hannu tasa badon taso ba ta Soma Sakura tanaci shikam komawa yayi zai kwanta sai Kuma yaji wayansa na ringing daukar wayar yayi ya Kara a kunne amma baice kome ba sai Kuma yace"ah ah Ade ban hau online ba meya faru"?ok ok kawai yace ya katse wayar tare da mikewa yadau remote ya kunna TV.

Kara Nnenna dake zaune ta sake da karfi tana ihu jikinta na rawa shi Karan kanshi Lahab yasha jinin jikinsa bana Wasa ba gawan Abraham ne kwance cikin jini kansa a faffashe ga shatin wuka da aka daba Masa a ciki,tare da Karin bayani akan an kashe matashi Mai Suna Abraham Godwin a cikin gidan su sai Kuma aka nuna mom tana kuka tana cewa Nnenna ta kashe Mata d'a sannan ta gudu a cikin daren ba'a San Inda take ba sai Kuma aka Nuno hoton Nnenna boro boro a screen in TV, innalilahi wa'inna'ilahu raji'un shine abinda ya Fara fita a bakin Lahab ya mike tsaye tare da nuna Nnenna da yatsa Yana cewa"keee Daman kisan Kai kikayi kikeson ki sani a matsala"wani irin kuka tafashi dashi tana kafa gwuwowinta a kasa tana cewa"bani na kasheshi ba Ni ban kashe Shiba buga Masa lamp nayi aka Amma wallahi ban soka Masa wuka ba,tana kukan jikinta na rawa tana cewa"shikenan nikam rayuwata ta lalace,gwara ma kawai na mutu na huta da ganin wannan bakin cikin.

tana karasa maganar ta Mike da gudu ta zaro wukar dake Kan center table akan plate na fruit da aka had'a musu dashi zata cakawa kanta da mugun gudu Lahab yayi kanta hannun yasa ya Kwabe wukar da karfin gaske ya murza hannun nata tare da had'ata da bango ya bita ya danne da jikinsa har Suna Jin numfashinal juna da Sauri Sauri kuka Nnenna ta Soma tanayi tana ihu akan ya Barta ta kashe kanta shi Kuma Lahab tashin hankalin sa d'aya shine Halin da ta fada ga Kuma kuka da take Masa gudun kada wasu suji a shigo dakin,wani ihu ta sake tana cewa ya saketa saita kashe kanta turasa tayi yayi baya Kamar xai Fadi da gudu ta nufi wajen wukar dake kasa tana dukawa ta dau wukan.

ta baya ya rungumeta da karfi jikinsa na rawa yasa hannu zai fizge wukar suka Soma kokowa sosai suke ta dambe a kasa cikin tashin hankali ya fizgota ya maka a bango daga zaune da suke,tana bude Baki ya danna lips NASA acikin nata,take jijiyoyin jikinsa Suka mimmmike Naman jikin na wani irin rawa,a zabure ya damke lips nata na kasa ya Soma tsotso da zafi zafi Yana maida numfashin dake kokarin barin jikinsa gabaki d'aya.

Hannunta dake damke da wukar batasan ya akai ta sake wukan da kanta ba hankali tashe ta Soma sauke kanta kasa har lokacin bakinsa na cikin nata Yana aikin tsotsar tausashen lips nata dukar da kanta take a hankali shi Kuma Yana Kara tallafo Kan sama da hannun sa,a hankali ya zame bakin sa daga Kan lips nata a hankali Yana tsude damshin yawonsa dake manne a lips Natan,a sanyaye ya zamo Kansa daidai kirjinta ya kwantar tare da Kai hannunsa ta bayanta ya mannata sosai a jikinsa Yana Jin yanda kirjinta ke mugun bugawa ya Soma magana cikin mutuwar jiki"Labiba duk abinda ya samu vawa jarabawace daga ubangiji meyasa bazakiyi hakuri da jarabawar ki ba,nasan ke ba musulma bace Amma babu addinin duniya daya hallata kisan Kai don an Shiga kuncin rayuwa na yarda dake na amince bazaki iya kashe kowa ba,Koda duk duniya zasu gujeki Ni Zan kasance a gefenki na Baki kariya.
Chapter 80 · 0% Book details